NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

    Zuciyar mu”azzam tayi wani dam..”!Wato Ummi ta amince ne don babu yarda zatayi ammh abun na zuciyarta rausayar dakai yayi kafin yace”Hajiyarmu Ummi tana so na kamu da ciwon zuciya ne”? yafada cikin rashin hayyaci,Girgiza kai tayi kafin tace’Suhaima duk duniya bata da wani sanyin idaniyanta irin Ka,duk abunda kaga tayi tanayi don Sun bata mata,eh dole zataji ba dadi don hakika shettima da Fadi sun zalunceta ammh kuma rayuwa babu yafiya kofa Allah muna masa laifi ya yafemana ballantana mu mutane”

  ajiyar zuciya mu’azzam ya sauke kan yace’aie shikenan Hajiya Randa Ummi tawayi gari na fadi na mutu sai ta duka tadauka”Yafada kamar zaiyi kuka bai bata zarafin mgana ba yace”Ashirya abinci da dakunan saukan baki gobe jirgin karfe tara, zamu biyo”Daga haka ko mgana hajiya batayi ba, ya yanke wayar ransa na masa kuna,Ranar wlh barcinsa ragaggene sallah ya kwana yi da rokon Allah ya saussauta zuciyar Ummin akan,,wannan Auren Tunda bakin alkalami ya rigaya daya Bushe.

Washegari

   Tun wajen Bakwai suka gama Shirye shiryensu suka Nufo gidan Baffa saboda kada su rasa flight,Koda sukaje angama shirya amarya zahirah wacce tunda daren jiya Shettima ya zaunar da ita yayi mata nasiha mai kashe jiki kan ya gangaro kan cewa zata bi mijinta zuwa inda yake aiki,ai ada auren bai dameta ba ammh jin zata bar bahna dinta,da yakura da baffa,harda mahgana da kannenta sai fashe da kuka Baffan yayi ta bata baki,ai data koma daki kwanciya tayi tacigaba da kukan,yakura bata da karfin bata hakuri saboda tsausayin zahirah ne ke cinta itama kukan take aboye.

      Yau din ma cikin liyafayan aka nannadeta kamshi kawai ketashi tare da ita,Zahirah taci kuka idanunta har sun kumbura saboda kuka,damuwarta daya gunwa za”a akaita gashi kuma bata son kowa ba ,duk da Baffa yace gun goggon ta zata zauna da matar Kawuntane da yarasu kuma danshi ne ya aura mata.

   Lokacin da suka iso Baffa ya bukaci ganawa da dan nasa na sirri cikin wani daki suka shiga,bayan sun zauna baffa ya riko hannun mu”azzam yana cewa”dana nagode maka bisa yimin biyayyah dakayi,nakuma ji dadi matuka,ammh don Allah ina neman alfarmar “Yafada yana kallonsa.

Mu”azzam yace”Wata irin alfarma ne baffa fadeta indai batafi karfina ba zan maka ita,”Yafada kansa tsaye. gyada kai,baffa yayi kan yace”Alfarmar don Allah kada kabari laifina da ni da Fadi ya shafi rayuwar marainiyar Allah zahirah,wlh yarinyace karama tana da karancin hankali uwa uba gata yarinyace mara son tashin hankali,don Allah kamin alqawarin yimata katanga ga Fushin da zai sauka akanta na mahaifiyarka( ji baffa da karfin hali..Wannan ai shine ga bugu ga tsinke jaka)

kuri Mu”azzam yayi ma baffa yana jin kansa na masa Nauyi aransa yana fadin”Baffa da Ummi so suke su kasheshi lokacinsa baiyi ba”Damke hannu baffa yayi kafin yace”Naji baffa zanyi iya bakin kokarina duk da kasan sai ahankali kawai albarkanku da addu”anku muke bukata”Jin haka yasa baffa Rumgumosa yana godiya da saka albarka harda hawayen farinnciki,mikewa yayi ya fita da kanshi yaje har daki inda zahirah take ita da bukar da Mahgana,wacce ke kuka ta rike mahaifinta gam hannu baffa yasa yariko zahirah batare da yayi ma kowa mgana ba ya nufi dakin da mu”azzam yake.

  Yana zaune mu”azzam na zaune ya zaunar da zahirah kusa dashi yana fadin”Dago fuskarki yata kiga Mijinki kuma aljannarki ina miki fatan zama dashi har karshen rayuwarki”Jin haka yasa mu”azzam yadago kai dai dai lokacin da zahirah ta bude lifyafan data rufemata fuska fes suka kalli juna lokaci daya gabansu ya amsa atare Dam”

   zahirah tayi ka sake tana kallon mu”azzam kallo na rashin hayyaci tana mamaki wannan dan gayun shine mijinta,shiko mamakin tsantsan kankanta da yarintarta yake gani,to shi wannan ai reno aka basa yarinya yar ficila haka,tsaki yaja ransa yana mamakin Baffa daya mtsa sai yahada auren nan yo shi ko giyan wake yasha ai baya haikema Wannan ba sai ta mutu

  Kauda kai yayi yana daure Fuska,Ganin haka yasa ta dukar dakai tana kukan zucci,nan baffa yashiga yimusu nasiha haka bukarma yazo yayi nashi kafin sufara haramar wucewa Airport don lokaci ya kusa,Wa inda zasu bi zahirah Yakura ce sai Mahgana wato matar mahaifinta saura ance duk suyi hakuri daga baya saje.

  Yan kayayyakinta kadai aka daukanmata akwati daya sai Abubuwan da ba”a rasa ba,Da zahirah taga dangi kowa rumgumeta yake yana kuka ai itama sai ta burkice ta kamkame babanta tana kukan bazata ba shi yadauketa cak yakaita mota yana hawaye yace”yahna..Kibar kuka kiyi hakuri da rayuwa saboda ke macece watarana ma uwa zaki zama,ina miki fatan sassautan al”amura gareki yata,”Daga haka yajuya yana kuka,mota biyu sukayi zuwa filin jirgin wanda mu”azzam ya matsu su tafi don hankalinsa na gun Ummi.

    Anfara kiran sunansu bayan angama tantancesu A first class suka zauna Zahiirah tana makale jikin yakura mahgana na gefe chan gefe kuma su mu”azzam ne suma wanda suke gulman amaryan mu”azzam din suna fadin”wannam ai kwailace yanajunsu banza yayi musu yafara karanta jarida duk da bakomai yake fahimta ba.

   SAFE LANDED..Azzamhirah

Comment
Share
Vote

#intelligent writer’s#
#uwar mijina#
#JANAFI#
????UWAR MIJINA..!????
   (Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)

          Alkalamin:JANAF
          wattpad:Janafnancy

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

NOT EDITED

Attention:Ina wacce takeson fatarta ta murje yayi taushi da kuma fresh?ina wacce takeson idan an ganta sai an wanke hannu kan atab’ata don tsabar murjewa?maza garzayo ki sameni zan miki recommending cream bana bleaching illa zai gyara miki kalarki ne,sannan kuma muda maganin toilet infection kowani iri ne wanda mike kira da martabar mata,yasin idan baki dashi an barki agidan baya,kuma muna da man dandruff da kuma man gyara suma,if interested pls do chat me up @ 07065481260…thank u all as u patronize!!

           NO 11

     “””Har suka iso Abuja Airport, Zahirah na makale jikin yakura tana kuka itako,kamar ranta zai fita,tun yakura na lallashinta har takoma ta kyaleta domin bazata hanata takoka ba,kodon dacin dake ranta yafita.

     Jirgin na saukesu Mu”azzam yayi ma Ushe waya kan yazo yadaukesu,Bayan kuma yakira hajiya yafadamata isowarsu,Dr Abduljabar da shima yayi ma direban sa waya kan yazo ya daukesa,cikin lokaci kadan suka kariso,motar mu”azzam ita Aka saka zahirah da yan”uwanta sukuma suka shiga ta Dr.Abduljabar.

        Lokacin da Ushe ya dannah hon abakin wani babban get mai kyau da tsari baki da hanci su yakura suka saki suna kallon tsaruwa kai tun ma da suka doso anguwan,suka saki baki suna bin ko”ina da kallo lalle Duk wanda baizo Abuja ba yabar kallo,haka yakura da mahgana keta fada aransu.

      Sani maigadi jikinsa na rawa ya wangale get motocin guda biyu masu kyau suka sulala cikin gidan,motocin na tsaya a parking space sai ga Su zulaika dasu karime sun fito suna rangwada guda suna ma amarya lale da zuwa hajiya baraka ce agaba taci adonta cikin wani dakakken leshi,mai kyau da tsari,Ita da kanta ta bude ma Su Zahirah mota tana fadin”Brka da zuwa Amarya ta ango”Tafada farinciki ya nuna har bisa Fuskanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button