NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

BAYAN SATI DAYA.. 

   “”Tabbas Asatin dayan da mu”azzam yayi adakin Lubna zata dora tarihi akan haka,Domin koda bai bude baki yace Lubna i Love u ba,Tasani cewa ta samu mtsayi mai girma azuciyar mu”azzam daidai gwargwado yana bata kulawa sai dai Abunda ya gaza,hakuri kan da kauda kai Dole tayi domin Soyayyar zahirah azuciyar mu”azzam bazata taba boyuwa ba,koya boyeta bayyana take,ita din wata abace,na in bata babu rayuwa mai dadi,kuma uwa uba zahirah bata yadda ta biyemai inyana wasu abubuwan Domin koba komai bazata So akuntatama lubna ba,harga Allah yarinyar bata da laifi tana mata biyayyah daidai gwargwado,bazata so ta watsama Ummi akasa a ido ba Shiyasa take kokarin Nisanta kanta da mu”azzam alokacin dayake tare da lubna,saboda tasan Halinshi baya iya boye soyayyarta agaban kowaye kuwa.

Yau din daya dawo dakinta ita kanta tasan tayi kewar mijinta don Tunda suka Shige ciki basu Fito ba,sai Washegari bayan Rana ta dago,Babu wanda yadamu da rashin Fitowarsu yarane Suna wajen Lubna dayake ma basu da rigimar shan Nono,data fito ta basu suka sha,suka koshi zasu koma wasansu sai kuma dare,Dole washegari Mu”azzam ya tarrara Ya koma bakin aikinsa domin Hutun yayi yawa,kada kuma ashiga hakkin jama”a

  Zamane mai Tsafta da Fahimtar juna ke gudana acikin gidan,Domin kowacce ta rike matsayinta Zahirah ta rike girmanta,kuma batayi amfani da soyayyar da mu”azzam ke mata ba,don ta batama Lubna ba,ko daya Ita kokari take Ta daidaita kanta da ita,ita kuma Lubna tana ganin girman Zahirah kodon saboda yadda take kokarin kyautatamata,da yadda take kaucema wani Abun agaban idonta Duk don kar ranta ya baci,Ta yarda ta amince bazata taba kamo zahirah azuciyar mu”azzam ba,sai dai Tayi hakuri da yadda kaddara tazo mata,ko ayanzu kasuwa Tatashi dan Koli yaci riba,tunda yanzu har mu”azzam na iya kallonta yamata mgana cikin Tsausayawa,kuma ranar girkinta yahada Shimfida da ita,duk wani Lokacin sai Ta nema da kanta,domin yakan basar ne,in Ranar ita kedashi,dayake mai Son dan Tsuntsu shike binsa da jifa,dat why bata Fushi komai yayi mata take kokarin dannewa Tundama itace akasansa.

Ummi kuwa bata yarda ko Afuska ta nuna bambamci Tsakanin zahirah da Lubna Tace duka ya”yantane so babu bambamci kowa natane,duk Wanda yayi ba daidai ba zata kirashi ta watsawatsarmasa,Shiyasa sukejin dadin zama da Ummi babu nuna bambamci balle Wani kyara,Shikanshi mu”azzam ya samu kwanciyar Hankali har yar kiba ya fara kamar bashi ba,tuni ya maida hankalinsa kan aikinsa,bayan ya karbi Takardun lubna yabawa Dr.Abduljabar yace ya samamata gurbi anan Asibitin dayake aiki da Taimakon Zahirah don ada Da Ummi ta Tunasar dashi maganar Aikin na lubna Kin amicewa yayi da Ummi ta nemi jin dalili sai yace Saboda Hirah bazata ji dadi ba,shi bayason Abunda zai batamata Rai,jin haka sai ta kyalesa,sai kawai takira Zahirah tana fadamata ,takuma Umarceta datayima mu”azzam din mgana don Allah yabar Lubna tayi aikinta Tunda aikinta na Taimakon al”ummah ne,Aiko illai Datayimai mganan cemata yayi ita bata aiki so Itama yace bazata yi ba,zahirah tace”Sam wanann ba Adalci bane,ni banyi karatu mai Zurfi fa,Tayaya zan Samu aiki,ita kuma tayi harta kai matakin zama Likita don me bazaka barta Tayi aikin ba,alhalin da aikin ta ta bari ta biyo ka nan,gaskiya in kayi haka kazama mara adalci..”yadda Zahirah ta Fututtukene harda kwallah yasashi barin Lubna tayi aiki Wanda ko Sati ba”ayi ba Dr.Abduljabar ya saman mata aiki a bangaren data karanta dayake tanada good Result dayake kuma daman Nageria tana da karancinsu irinsu Tuni suka dauketa,Murna wajen Lubna ba”a mgana Tuni tafara zuwa aikinta cikin Farinciki da Annushuwa,don bata taba saka ran zata koma ma aikinta ba,ammh sai da tasha dokoki akan kada ta kuskura saboda tana aiki tana kama Kudi ta gorantama zahirah,duk randa yaji wlh ita da aiki har abada..,To inama zata Fara Tunda Ta Lura zahirah kamar wata Ruhi ne ga mu”azzam din.

Comment,Share and Vote..

  JANAF
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

I Dedicated dis chappy to u my Everlasting Friend????,my Swt Qawa,????my Swhrt ????my Bby dol.????..,d Person Of HAFSAT ALMUSTAPHA MUHAMMED..,knows as HAFSAT HAFNAN,u ar so amarzing dear,A relli Appreciate ur Luv,d way u Support me,d way u care for me,Tanque Sahiba,Tanque For been their For me,Allah ya barni dake har A aljannah FIRDAUSI..,Sahibarki Jamelajanafty na matukar kaunarki har cikin Rainta,SON KAUNA WANDA BAYA YANKEWA✌????????????

NOT EDITED????

        NO 47

    “”Baza”a taba Cewa azaman zahirah da Lubna babu sabawa ba,domin ko Harshe da hakori akan saba balle Mutum da mutum,to hakan ta kasance Wani Lokacin Lubna bata iya jurewa Wani Abun in mu”azzam yayi sai kiga Ta nuna afuska koda bata Furta ba,Itako Zahirah duk yadda takai ga Kawaici wani Lokacin kishi kan Turniketa harta dan chanzama Lubnar Fuska ammh na dan Lokaci ne zasu dawo daidai,Ummi na Lura da komai dayake bakowani harkansu take Shiga ba,sakamakon ita babbace kada tazama Uwar mijin baya wacce ke saka ido kan ya”yan Cikinta,kyalesu take Domin tasan zaman Tare ne dama dole ne watarana Asabama juna.


Abbie yazo Nageria mganar Auren Mooh wanda Mu”azzam da Shureim da Abbie sukayi ma gidan minister tsinke,Babu shakka minister yaji dadi sosai kuma nan take yabama mooh Auren Asma”u ammh yace sai ya fadama yan”uwansa yadda suka yake kan mganar Auren babu mtsala shi nashi mai Sauki ne,to Abbie bai koma ba sai da dangin mahaifin Asma”u suka tada dan mutum har Sudan akayo musu binciken Mooh da alahalinsa,kuma Alhamdulillah Lbri ne mai dadi ya iskosu,nan da nan Suka kira su Abbie koda sukazo nan fa suka gudanar da kayan nagani inaso da sadaki aka sanya musu rana wata uku..,Wayyo murna zahirah da lubna sunshata kamar su zuba ruwa akasa su sha kar uban gayyah yaji lbri mooh Amarya Asma”u ko na mkranta sai dai taji lbri kwatsam ta bakin Zahirah,koda takira mami nan Takara tabbatarmata,To kunsan amaran zamani itama ranta fess,sai ma kiran angon nata datayi tana mai shagwabar meyasa bai fadamata ba nan ya rantsemata da cewa,wlh Shima baida masaniyar komai banda zuwan Abbie,To haka dai ta yarda suka cigaba da tsara yadda rayuwar Aurensu zai gudana.

Abbie bai koma ba,sai dayaje maiduguri ya duba Baffa kana yakoma Sudan cikin jin dadi domin yaga yarsa hankalinta kwance,ga aikinta tanayi da lbrin dayakomama mom kenan Domin yaga tadamu da jin yaya rayuwar Lubna yake gudana agidan mu”azzam duk da suna waya,buh nasan koda wani Abu na faruwa Lubnar bazata fadamata ba,hankalinta ya kwanta dajin lbrin da Abbie yakaimata nan da na Ta saki jikinta taci gaba da Shirin bikin dan Fari wato mooh.

Kwantashi babu wuya Awajen Allah gashi Zahirah nada wata hudu da tarewa gidan mu”azzam akuma yau din Tatashi da wani mugun zazzabi wanda har saida yasata ta suma,mu”azzam bayanan yana office Ummi ce kadai agidan sai su Little dasu karime,Hankali Tashe tayima karime mgana tazo takama mata zahirah suka kaita mota Ushe bayanan Tunda ya fita da mu”azzam zuwa office bai dawo ba,may be yana chan Tare dashi,su lami tabar Su little Ummi Tunda Lubna batanan Tana wajen aiki,Ummi da kanta ta tukasu zuwa Special Hop,Karime na baya tare da Zahirah,suna zuwa babu bata lokaci aka Shiga da ita emargency saboda rudewa ko waya Ummi bata Fito dashi ba,Ana shiga da ita Dr.Abduljabar na ganinta ya ganeta zahiran Barrister ce,Umarni yabada adibi jininta aje dashi lab,saboda akwai Abunda yake zargi,Bata jima ba ta farfado sakamakon zafin zazzabin shi ya sata suma Tana farfadowa ya Umarci Nurse datakaita Tiolet tayi Fitsari acikin wata yar kwalba babu nusu takamata takaita bayan Ta taimakamata tayi,Suna fitowa takara kwantar da ita,itakuma ya Umarceta dataje dashi lab,yanzu akawonai Sakamako da girmamawa ta amsa kafin tafice daga office din zuwa lap din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button