NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Lubna ce tazo giftawa ta emergency sai taci karo da Ummi da Karime ciikin mamaki ta karisa tana fadin”Ummi me kukazo yi asibiti kuma.?.”ganinta yasa Ummi mikewa cikin wani yanayi tace”Wlh Kuwa kedai bari zahirah ce,tunda kika fita kika barta bata da lafiya zazzabi mai zafi,to adai Sume muka kawota nan,banzo da wayata bane shiyasa ban kira ki ba..”Zaro ido Lubna tayi kan ta dafe kirji tace”na shiga Uku Antyn tawa ce kuka kawo asume..”Tafada cikin Firgici kafin ta juya Cikin azama zata nufi Emergency Sai dai kafin tayi wani taku itama jiri ya kwasheta koda su Ummi suka lura kan Su karisa gareta ta zube kasa kamar bata Numfashi,hannu Ummi ta dora akai tana kwalama Dictors kira,cikin azama akazo da gadon daukan marasa lafiya wasu Nurse su uku suka cicccibi Lubna suka shiga da ita inda zahirah take da hanzari,dabas Ummi takoma ta zauna tana fadin”hasbunalli Wani”imal wakil..”Take nanatawa tana dafe kai,Dr,Abduljabar na ciki aka shigo da Lubna itama Cikin mamaki yake kallonta kafin yace”wht wrong wit her,ba yanzu sukayi aiki tare da Dr,Farha ba..”Sadda kai Nurses din sukayi kan suce”We don”t know Sir,tana tafiyane ta fadi..”kallonta yayi yana dafe kai,gadon dake kallon na zahirah yace su daurata itama jininta yace su diba kafin ya cigaba da kokarin nemo Numfashinta yanayi yana kallon zahirah wacce yayima Allurar barci yana fatan Abunda yake zargi game da matan na Brr,ya tabbata.

Yasamu nasaran Daidatan Numfashinta,tunda daman ba nisa yayi ba jiri ne ya dibeta ta fadi da kuma Firgici,Yayi mata alluran barci ammh yadda jininta keda karfi ne,yas bata samu barci ba,da kanta tatashi bayan yabata ,yar kwalbar nan yace tayo Fitsari aciki,koda tayi ta fito ta kawomai amsa kawai yayi ya fice daga dakin,Lubna gefen gadon Zahirah ta karisa bayan taja wata farar kujera ta zauna ta riko hannuna tana kallon yadda Ruwan Drip din da”aka samata yake Diga ahannunta ahankali,Sai ta maida kanta kan yadda take sauke Nunfashi awahale saboda Tsausayi kamar tayi kwallah,duk sai tajima ta samu karfin jikinta,koda Dr ya aiko wasu Nurse tazo ta sakamata drip ki tayi tace ita taji sauki dole ya kyaleta,cikin lokaci kadan Sakamakon ya fito Mirmishi dauke bisa fuskar Dr,Abduljabar ya kariso wajen Ummi dauke da sakamakon ganinsa yasa Ummi mikewa cikin Damuwa tana fadin”Dr ya jikinsu..”Dan murmusawa yayi kafin ya mikamata fararan Takardun yana fadin”Jikinsu da sauki Ummi,ciwon Surakan naki duka na karuwa ne,Domin Zahirah na dauke da cikin na tsawon wata uku da kwanaki Ita kuma lubna wata biyu da kwana shida..”Dafe kirji Ummi tayi kafin tace”Kabari don Allah,yanzu dukkansu ciki garesu..”dariya yayi kafin yace”Kwarai gama Shaidan a hannunki Ummi..”da baya Ummi takoma tayi dabas kan kujera tana fadin”Alhamdulillahi ,Allah nagode maka ya Allah..”Take fada tana hawayen Farinciki karime na tayata,kadai kai kawai Dr,Yayi ya wuce zuwa office dinsa,yana Shiga ya dauko wayansa Yafara laluban Brr,mu”azzam harta karishi Ringing dinta bai dauka sai ya kyalesa,fita yayi daga office yakoma Dakin dayasa aka kai zahirah Tunda Lubna taki hawa gado tace ta warke,yakara dubata yakuma ragemata gudun zuban Ruwan,haryanzu dai tana barci bata tashi ba, koda yaje ya iske Ummi ciki Ta rumgume Lubna tana ta sakamata albarka tana share hawaye,da Farko Lubna bata fahimci mai Ummi kema Kuka ba,sai da ta bata sakamakon Ta duba tagani,sai kunya ya kamata ta sunne kai tana mirmishi lalle rabo ya Wuce wasa,yanzu ita keda cikin Mu”azzam lalle Allah ne kadai ke tsara Abu sanda yaso kuma ya faru asanda ya yaso a boye ta dinga fitar da kwallar Farinciki koda mu”azzam bai sota ba,ya mallakamata Abu mai daraja arayuwarta ma”ana ya digamata kwan Haihuwa ko ahaka ta godema Allah.

  Dr.Abduljabar nakomawa Office kiran Brr,na zuwa ya dauka yana Fadin”Shugaban lauyoyin duniya gabadaya..”yar dariya mu”azzam yayi kafin yace”Haba waneni..Bari don Allah da min makamin da bankai chan ba..”Dr,yace”injiwa ai ka kai,har ma kawuce,kai dai kawai kajira lokaci muna fatan hakan..”Tabe baki mu”azzam kan yace”To Shikenan,yane naga kiranka lokacin muna gaban justise ya”akayi ne,domin kai dama baka kiran banza..”dariyan shakiyanci Dr,ya saki kan yace”gaskiyarki bana kira sai da dalili yanzu din ma wani good news nakeso nabaka buh duk Abunda kakeyi yanzu ka ijiye kazo office dina ka sameni Koda ka sume ne,sai na dubaka..”Tsaki mu”azzam yaja”Mtsewww..,kaifa wani zubin na dawane wlh,komiye gayamin ta waya plz”Dr yace”Ina baka kana Roko so nike kaji kuma kagani wlh am Serious am waiting For u”yafada lokaci daya yana datse kiran.

  Ba”a dau tsawon wani lokaci ba sai Mu”azzam Ushe ya kawosa Asibitin Tun aparking space yaga Abun mamaki Domin motarsa Corollahx yagani ya kalli ushe,shima ya kallesa kan yace”oga na dis ur car..? Kurama motar ido yayi kafin yace”ya is my,buh wayakawota nan..? yafada da Sigan Tambayan Alhalin babu mai bashi amsa,ganin haka yasa ya fito daga motan Cikin azama ya dumfari cikin Asibitin,Dr,Abduljabar yana Shirin Fitowa daga office sai ga Mu”azzam ya Shigo ajiyar zuciya ya saki kan yace”Ka kusa ka makara..”

  Gyara tsayuwa mu”azzam yayi kan yace”Wani yazo nan daga gida ne..? meka gani.? Dr,ya tambaya Shafa kansa yayi kan yace”Motata na gani a haraban Asibiti..”yar dariya Dr yayi kan yace”See dis guy da wanne matarka ke zuwa aiki..”dafe kai mu”azzam yayi kan yace”ohh am very Srry wlh na manta,Na zata da 4matic din take zuwa banzata tana hawantaba,yanzu meyasa kakirani Aiki nake dashi a office wlh.”Hannunsa kawai Dr ya riko keee,suka Fice daga office din,sai dakin da zahirah take ciki ya tura suka shiga,daskarewa mu”azzam yayi ganin da Lubna da karime zazzaune acikin dakin bai gama mamaki ba ya hango zahirah kwance ana karamata ruwa,ammh lokacin ta farka Lubna ma ta taimakamata tatashi zaune.

  Da hanzari ya isa gareta yana riko hannunta yace”Subhannallah,Hirah what wrong With u? bada safe muka Rabu lafiyanki kalau ba,Ummi meya sameta.?’kafin Ummi tayi mgana Dr.Abduljabar ya rigata da cewa”ba wani ciwo bane Na damuwa,ciwon nata na karuwa ne,inamai Farincikin shaidamaka matarka zahirah na dauke da cikinka har na tsawon wata uku da kwanaki,Lubna too ma,tana dauke dashi na Wata biyu da kwana shidda,so congratulatin  brr,kai mai sa”a ne..”yafada yana mikamai hannu,zaro ido mu”azzam yana kallon zahirah wacce itama sai yanzu taji batun,maida kallonsa yayi kan Lubna sai yaga ta sadda kai tana mirmishi Ummi yakalla sai ga tana dariya ta gyadamai kai,ai ban sadda ya damke hannun da Dr,da karfi ba yana fadin”Are u Serious Dr..? gyadamai kai yayi kafin yace”ya,very sure ga Resuilt nan hannu Ummi in baka yarda ba..”

  Mu”azzam kasa kawai ya sulale yayi Sujjuda ga Allah(SWA) daya bashi rai da lafiyan da zai ga wannan kyautan addu”an kawai yake kwararowa tare yabo da kirari ga Allah mai kowa mai komai,yana dagowa ya rumgume Dr yana fadin”thanks Dr for d good news Lalle ka chancahanta Kyautarta shine dis year insha Allahu zaka Saudiya ka sauke farali..”Dariya Dr yayi yana fadin”Kai masha Allahu..”yake fada yana kara rike mu”azzam,dukkansu dariya suke harda Ummi,mu”azzam wajen Ummi ya nufa ya duka yadafa kafanta yana fadin”Ummi kinga Kyautar Ubangiji ko”? gyada kai Ummi tayi kan tasa hannu tana shafa kanshi tace”nagani Son,Mun godema Allah da dukkan ni”imarsa sai Fatan Allah ya saukesu lafiya..”Ya amsa da Amin kafin ya tashi ahankali ya nufi gadon Zahirah kusa da ita yazauna lokaci daya ya riko hannunta,kallonta yake idanunsa sun ciko da kwallah,ganin haka yasa ta sakarmai mirmishi kafin tace”angon karni karni..”tafada ahankali Dan marinta yayi afuska kafin yace”mai jajage..”yafada yana dalle mata baki,kuka tasa na shagwaba tana kallon Ummi tace”Ummi kingansa yana Cin zalina ko? Ummi tace”Barimana Mu”azzam baka ga halun datake ciki bane”bata Fuska yayi yana kallonta itako tanamai dariya,kallonsa ya maida kan Lubna wacce ke gefe kanta aduke,Hannu yasa ya yafito da kafin ya kirata”Lubna..”Ahankali ta dago tana kallonsa,Kai yagyada mata alamar tazo,mikewa tayi ta isa garesa,Ummi na ganin haka suka fice waje ita da karime,Dr,dama tuni yayi waje.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button