NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

  Tafada cikin wani yanayi,gyadamata kai zahirah tayi tana mata mirmishi tace”macen takwaranki ce ummi,namijin kuma sunan Abba,ya mu”azzam yace asamai..”Tafada bayan hawaye ya zubomata,Cikin kukan Fitan hayyacin Ummi ta rumgume jikokinta tanajin wani irin kaunarsu na ratsata,matuka cikin kuka take fadin”Ni wata irin azzaluman uwace,ni wata irin Uwar miji ce,mara rabo aduniya,nayi sanadiyar raba,uba da ya”yansa,bayan burin kowani uba yaga kwansa aduniya kaichona ni Suhaima Kaic…..”Zahirah ce ta saka hannu ta rufema ummi baki tana fadin”a”a Ummi kibar fadin hakan,komai kika ga yafaru daga indallahine,ba laifinki bane Ummi dama chan rubuttacene daga rabbil izzati.

  Juyowa kawai Ummi tayi tahadata da ya”yan ta rumgumeta tana kuka take fadin”nagode zahirah..Nagode nayi takaichin raba Son da nagartacciyan mata kamarki,nayi takaichi har in na tuna kamar na kashe kaina nakeji..”Tafada cikin kuka itakanta zahirah kukan take,ganin kukan nasu yafara yawa ne,harsu little Ummi sun fara nasu kananun kuka,bukar yace don Allah subar kuka komai ya wuce,daki zahirah takoma chan ta basu little Ummi mama,tanayi tana kuka tana fadin”ya mu”azzzam kana ina? yau ga ranar daka ke mafarkin zuwanta,yau ga ranar da Ummi tayarda tayi nadaman Abunda ta aikata..”taketa fada tana kuka.

  Karfe shidda daidai aka Fito da zahirah bayan tasha tarin nasihohi,gun iyayyanta,itako Ummi hawayenta yaki tsaiduwa,tun lokacin da Ashe ta karbu su little ummi dayake suna hannun Ummi ta kwakwumesu tana kallonsu tana kuka,tunda aka Fito da zahirah Ummi tayi Wuf tafada tiolet tana gunjin kuka,kaichonta Yanzu ita da kanta ta jagoranci wani yaketa gonar danta,wayyo ta cucu kanta,tana ji tana gani aka saka zahirah awata bakar benza wacce mijinta ya aiko aka dauketa aciki,bayan Sauran motocin gudu uku,Su yakura ne kan gaba,Hajiyar shureim kuma taso ta doje Bukar yaroketa kan taraka zahirah to babu yarda zatayi,Ummi kuma an nemeta ba”a ganta ba,kowa yasan boyewa tayi,to ai babu dadi ne sai hakuri tunda aikin gama ya rigaya daya gama,zahirah tayi kuka kamar ranta zaifita har saida muryanta ya fara dishewa,bama zata iya fadan irin Tashin hankalin datake ciki bane,ammh lokacin data yada kanta bisa kafadan yakura tana kuka acikin mota babu wanda take tunawa sai mu”azzam ajirgi sanda take rumgume jikin Yakura tana kuka za”a kaita gidan mu”azzam ammh sai gashi Tarihi ya maimata kansa,ammh kash yau gidan wanin mu”azzam za’a kaita tafiyan tasha bambam da wanda sukayi na farko,Su little Ummi ko na hannun hajiya Suma sunsha kwalliyansu shar,suma zasu gidan sabon papane dole su chakare????


  SUDAN

  Tayi parking din motarta cikin haraban asibitin ta fito tana takunta d’ai d’ai,cikin shigar pakistan Riga da wando sai wani siririn gyale data saka bisa kanta,takalmin kafanta mai dudu ne sosai,tana gabda shiga mainpalour din asibitin sukaci karo da juna,da kallo tabisa yana dagowa suka hada ido,Daure Fuska yayi ya ratsa ta gefenta ya wuce yafara tafiya cikin takunsa na sanyi.

  Cikin mamaki take binsa da kallo kan ta bisa tana fadin”Hy where are u giong…? tafada tana shan gabansa,zuramata ido yayi kafin yakara yunkurun binta gefenta ya wuce taki basa dama,marairaicewa tayi tana fadin”plz mr man,am Srry da yadda na dinga takurama rayuwarka,don Allah kazo mu koma ciki i promise u kana kara samun sauki i will let u go but not now..”Tafada tana hada hannuwanta alamar roko.

  Kauda kai yayi yayimata banza harma ta fidda rai zaiyi mata mgana sai chan taji yace”masauki na zan koma,plz leave me alone nagode da taimakoki,ni nasamu lafiya kibarni natafi am begging u..”yafada shima cikin wani yanayi,tsuramai ido tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya tace”Naji zan barka katafi but sai kamin alqawari yarda nakaika wajen Abbie na nadade inabashi lbrinka,bayan nan in zaka tafi to,sai ka tafi babu damuwa.”Tafada cikin wani yanayi.

  Kallonta yayi kamar zai ce, a’a sai kuma yaga rashin dacewarka haka kai tsaye yace”agree but in one condition..”yafada kai tsaye gyadamai kai tayi tana kallonsa cigaba da cewa yayi”bayan kin kaini wajen Abbanki,zaki barni na tafi bazaki kara,bibiyar rayuwata ba,indai kinyi alqawari ,nikuma zan biki mutafi wajen Abbie ki dakikace zamu..”

Shuru tayi tana kallonsa ganin yadda tayi shuru yasashi saurun ratsawa zai wuce da Sauri tace”yes Acceppted…”tafada cikin comfident,cak ya tsaya bayan ya dago yana kallonta baizata zata yarda ba, shiyasa yahadamata wannan mganar,gun motarta ta nufa shikuma ya biyota aransa yana fadin it over aie,data kaini zan kama gabana i think ma yazama dole na chanza country don kada mayyar yarinyarnan tasake binshi.

  Sun fara tafiya yamata mgana kan subiya hotel din daya sauka,babu gardama suka fara zuwa chan,da shikadai yaso ya shiga ammh lubna taki yarda,dole suka shiga tare,shiko kallonta kawai yake,tana tunanin zai gudu ne,jakar briefcase dinsa dake da muhimmam Abubuwansa kawai ya dauko daman,ai iyakar kayansa kenan,fitowa yayi bayan ya samu ma”aikatan ya mikasu mukullin dakin da tiket dinsu kafin yayi Signing na barin wajen duk da yana da Sauran kudi,don baisan ma dakin adadin kwana nawa yakama ba.

  Suna isowa gidan ta buga hon maigadi yazo ya budemusu yana musu marhaba da harshen larabci,lubna ce kadai ta amsa,ammh banda mu”aazzam wanda yawani hade rai kamar wanda aka aikomai da sakon mutuwa.

  Tana gama parking din motar a parking space ta fito tazagaya ta budema Mu”azzam ya fito yana bin gidan da kallo,Gaba tashiga yana binta abaya har zuwa babban kofar da zata sadaka da falon gida hannu ta sa ta tura kifar gillas din dake wajen bayan ta kwarara sallama cikin zazzakan muryanta,tana shigowa tabawa mu”azzam hanya tanafadin”bismillah..”

  Abbie da mom harma da mooh dasuke falon,suna hira suka dago suna amsa sallamanta,jin tace bismillah ne suka kurama kofa ido suna so suga to yau kuma wa lubna sarkin Taimako ta jajibo.

  Shiko cikin wani irin taku ya shigo falon da sallama shima,ammh cikin muryansa mai cike da sanyi da gardi da Ake kira husky voice kafin ya bayyana afalon galala sukayi suna kallonsa lubna na gefe tana mirmishi tace”Abbie yau dai ga bawan Allah danake baka lbri yau na kawomaka shi har gida..”tafada tana nuna mu”azzam wanda ke tsaye kikam yana bin Su Abbie da kallo.

  Abbie daya daskare azaune ya mike jikinsa na rawa ya Nufi mu”azzam bayan ya zare siririn gilashin dake idonsa,ya isa garesa yana shafa fuskarsa yake fadi cikin rawan murya’Fus..Kar..wa na..Ke..ga..ni..Ka..marta Aminina MUHAMMED MOODU ” Abbie yafada muryansa na rawa lokaci daya ya kuma sha fuskar mu”azzam din kamar wanda akacemai zai bace.

Gabadaya suka shiga rudu,mom ta kalli mooh shima ya kalleta,lubna takalli Abbie tana zare ido,shiko mu”azzam tuni kwakwalwarsa ta hasasomai wani abu cikin wata murya yace”Ba shakka sunan daka kira sunan mahaifina ne,ni dansa ne daya rasu ya bari wata hudu acikin mahafiyata”mu”azzam yafada yana kallon Abbie.

Jikin Abbie na rawa ya riko hannunsa yana fadin”ya sunan mahaifiyarka..?”Suhaima..”mu”azzam yabashi amsa,ai dawani sauri Abbie ya rumgumesa yana fadin ” Shine,wlh Shine da”n Moodu ne da Suhaima wlh Shine ” Abbie ke fada yana kuka lokaci daya yana kamkame mu”azzam din tamkar wani zai kwacemasa shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button