NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Rabuwar Hajiya baraka Da Suhaima Rabuwace ta kuka ta sabo..Wanda suka shude shekaru tare..Ammh yau zasu Rasu..Sunaji suna gani Dr Shuraim yawuce Da mahaiyarsa zuwa Zaria yayimda Mu”azzam suka lula Abuja..Wanda acham ne suka fara gina Sabuwar Rayuwa mai cike da jin dadi,Dr Shuraim yayi Aure da matarsa Zulaika…Ayayinda Hajiya baraka girma yafara kamata tana fama da ciwon kafa ne..Wanda danta ke tsaye kanta da kudinsa da lafiyansa.

  Mu”azzam ya zubema Ummi yan aiki acikin gida Tundaga farfajiya har cikin gida ga tsalatsalan motoci ya zubemata da direba..Ga masu girki da masu gyara mata dakuna..Kai komai najin Dadin Rayuwa mu”azzam ya mallakamata shi..Baya da buri Sai nata komai ya Samu UMMI NA komai ita domin itace ginshikinshi domin bada din Tsayuwarta kanshi dayanzu wuya ta kashesa..Mu”azzam aboye yake aikama Baffansa Shettima sako in kuma yasamu lokaci yana zuwa gunsu da Abun arziki..Cikin shekaru biyu Brr mu”azzam yayi dukiya mai tarin yawa domin bayan aikinsu Shida Shuraim suna da hannun Jari akasashen waje inda suke gudanar da Kasuwancinsu cikin Turawa.

  Ummi tasamu jindadin Rayuwa Da kwanciyar hankali ammh daidai Rana daya bata manta da Abunda Su Shettima suka mata ba..Lokaci bayan lokaci in ta tuna to Ranar wuni zatayi kuka ko dan lelen nata bai isa ya rarrasheta..Tabawa Mu”azzam lbrim Abokin Mahaifinsa khamis wanda yayi mata alqawarin bincikarsa akasar Sudan din..Ummi duk Sanda taji son ganin HajIya baraka direba kawai zata ma mgana ta shirya yakaita sai yamma su kamo hanya..Suhaima Tadauki hajiya Baraka mtsayin yayartace itace kadai zata iya fadamata taji ammh bayan nan babu wanda ya isa..

  Zuwan Da Mu”azzam yayi Maiduguri ne Baffa Shettima ya tareshi da wata mgana wacce ta girgizasa ainun takusa sawa Numfashinsa daukwa..Na yabashi ZANNIRAH DIYAR FADI YAZO YA AURA wanda babu yarda ya iya Baffa mtsayin Ubansa yake gani inhar ubansa in yanada Rai zai basa Umarni yabi haka Baffa Shettima zai bashi yabi..Babu yarda ya iya illah godiya da nuna biyayya wanda ya sanyayama Shettima Rai harda zubda kwallah..zullumin da Mu”azzam yadawo dashi kenan yana hanya yasamu kiran Ummi wanda daman bai shaida mata zuwanshi maiduguri ba,sakamakon bata tashi ba,Sanda yafice daga gidan bayan yasamu kiran Baffan na gaggawa…

Lokaci daya Shettima yasaki ajiyar zuciya Bayan yadawo daga dogon Tunanin daya dauka Tunanin Abunda yashude achan baya..hawaye suna Shatata bisa idanunsa..gaban babban Rigansa yajike sharkaf da hawaye harda majina lokaci daya, yasaka hannun rigarsa yana sharewa yake Fadi afili..” NASANI ADA NA TAFKA KUSKURE AMMH YANZU INA NEMAN HAYAN GYARAWA..NABIYE SHARRIN ZUCIYA DANA MACE TAKAINI TA BARO,AMMH YANZU DA IZININ LAHI ZAN KULLA WANNA AURE FATA YAZOMO HAYAR WARWARAN KOMAI..YA ALLAH KAGA NIYYATA KADAFAMIN yakarshe fada yana fashewa da kuka yakura dake labe agefe itama kukan take lokaci daya tana jin Tsausayin zaniirah domin ta tabbarta bazata taba jin Dadin zama Da Suhaima Saboda yadda ta rike Abun Aranta..

Tabdijam akwai badakala..Tayaya Ummi zata amshin wannan zencen..Shin yaya Rayuwar marainiyar Allah ZANIIRAH zata kasance..Duk kubiyo ni cikin Salona na UWAR MIJINA…UWAR MIJINA…Salon na daban ne kada ku manta Janaf dinku ce..????

COMMENT, SHARE AND VOTE

#Intelligent writer’s#
#Uwar mijina..!#
#Janafi#
INTELLIGENT WRITERS ASSO????

???? UWAR MIJINAH..!????
        (Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)

       ALKALAMIN:JANAF????
        WATTPAD:JANAFNANCY

DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF

   
Assalamu Alaikum janaf fans,ya kuke, hop kuna cikin koshin lafiya,kamar yadda nake..Afuwan plz game da yadda na dinga comfused dinku,Akan Sunan ZAHIIRA..Wani Wajen sai na dinga saka ZANIIRA,Afuwan don Allah, wlh dauka nake sunan duk dayane????, but by Now zamu cigaba da amfani da ZAHIIRA..Tanque so much masoyana, da gyaran ku gareni,hakan ya nunamin kuna biye dani..One luv????

   NO.6

    “””Kamar amafarki yake jiyo kiran sallah a masallacin dake kusa dasu, cikin mutuwar jiki,da gajiya ya farka,mika yafarayi kan ya sauke kafafunsa akasa wa”inda sukayi masa Nauyi sakamakon kwana atakure,Baiyi mamakin ganinsa kwance kan kujeran falon ba ma”ana anan yakwana bargon Ummi ne dake gefensa ne yabashi mamaki,gefe daya kuma sai ya murmusa daya tuna tabbas Ummi ce ta sauko tazo tayafamai,dan cije lips dinshi yayi kafin ya mike,ya tattara wayoyinsa ya wuce zuwa shashensa wanda ke kasab daNa Ummi domin dauro alwala.

  Agurguje yayi alwala yafice zuwa massallaci domin har an tada sallar..Bayan an sallame sallan saboda barcin dake cin idonsa ko Wa”azin da”ake bai tsaya Sauraraba,Wanda baya wucesa dawowa yayi gida, ya shige dakinsa mai kama da aljannah Duniya babu tarkace adakin daga wardrope dinsa,wanda takusa cinye rabin dakin sai madubi da gado sai kafet…gabadaya dakin blue ne komai da komai,komai dai cikin Tsari.

  Cikin mutuwar jiki yafada gadon dayaji lafiyayyan zanin gado ya baje,ya cigaba da barcinsa wanda ya daukesa mai Nauyi kuwa.

   Ummi kuwa tana Shiga daki kan gado tafada tacigaba da kukanta kamar karamar yarinya,tanaji komai har sanda mu”azzam,Ya shigo yazo yana mata magiya..Sai datagama mai isanta kana ta shiga bayi ta wanke fuskarta tayi alwala tazo tayi shafa”i da wuturi kana ta sauko tana zuwa taci karo Da mu”azzam kwance barcin gajiya ya kwashesa tadade tsaye tana kallon fuskar tilon dan nata,ganin tayi ya takure gu daya alamar Sanyi yakeji sai ta kashemai Ac din kafin takoma bedroom tadauko mai blanket tazo ta rufamai bayan ta shafa mai addu”a tasani saboda ita yazonan ya kwanta shafa kanshi tayi kafin tabashi Sumba,komawa sama tayi Ranta namata kuna na yarda tayi sake Shettima na neman Rabata da tilon danta.

***  ****  *****

   Cikin barci yaji sautin kiran wayansa cike Da haushi mu”azzam ya lalubo wayar akasan filon dayake kwance kasheta yake da niyar yi ammh sunan daya gani ne yasakashi Saurin picking” DAN UWA ya furta cikin muryan barci Daga chan bangaren Dr Shureim yace”How far Dan”uwa”Cikin kasala Mu”azzam yace”Am not Fine wlh”Yafada cikin damuwa.

Saurin Ture Zulaika Shureim yayi wacce ke kokarin dauramai Nektie yana Fadin”Wht wrong dan”uwa..? yafada cikin tashin hankali “Tsaki mu”azzam yaja mtseewww…”Kafin ya mirgina bisa gadon yana fadin”bana Fadamaka zani maid jiya ba”,Shureim ya amsa da “yes.Wht hppend” mu”azzam yace” wlh baffa ya ballomin ruwa dan”uwa..Wai Diyar inna Fadi data mutu ta bari yabani na Aura'”

   “Kutumar ubanchan..”Shureim yace lokaci daya da dafe baki wanda sai Da Zulaika wacce ke kokarin gogemai takalmin dazai sa ta waigo cikin mamaki don bata saba jin irin wannan ashar din daga bakin mijin nata ba,cikin Rawan baki shureim yace'”Ka amsa Mu”azzam..?”Yafada cikin rawan murya.

  Ajiyar zuciya Mu”azzam ya saki kan yace”I hv no option dan”uwa..”Yafada cikin muryan karaya,jinjina kai Shureim yayi kan yace”Ummi fa..”Shuru mu”azzam yayi kan yace”Ummi batasan ma da zence ba, kawai na tafiyata maid ne daban gayamata ba,tahau koke koke, to inaga taji babban Abun..Kila tsinemin zatayi wlh”Yafada kamar zaiyi kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button