NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Kuri tayima hajiya da ido kafin ta muskuta tace”Shikenan yaya zan duba komai zai wuce”Jin haka yasa hajiya washe baki tace”Yauwa diyar albarka kokefa,maza tashi kije tundazu yakura keta tambayanki” da mamaki tace”Kina nufin da yakura aka zo”Hajiya tace’Eh ita da matar baban yarinyar”jin haka yasa Ummi mikewa tana fadin’bari na leka “Har ta wuce ta dawo tana fadin”af nace su mu”azzam basu dawo bane banji duriyansu ba.

  Hajiya tace”Inafa tare suka iso,suna ciki kila suna watsatsake gajiya ne kinfa san maiduguri ba kusa ba”batayi mgana kawai takada kai tawuce kowani taku intayi kamar ta kurma ihu takeji yau matar shettima da diyan Fadi sune zaune cikin gidan danta kai shettima yagama cutarta ta ko’ina.

.

    Da sallama tashiga falon,mahgana ne zaune afalon,tana ganin Ummi ta shigo ta mike da sauri kallonta kawai tayi ta fahimci itace suhaimar data dade tana jin lbrinta daga bakuna da dama,kwarjininta yasa mahgana saurin sadda kai tana fadin”Sa..nn..u ha..Ji.Ya”Cikin rawan murya Ummi tajuyo ta kalleta akaikace tana wani kyabe baki ko tankata batayi ba, tafara taku zuwa cikin bedroom din bayan ta sakarmata dogon tsaki,bayanta mahgana tabi da kallo aranta tana fadin'”Baki ba mara da kunya ba,bala”i yanzu ina zahirah zata iya da wannan jaraban”Tafada aranta tana kuma kama baki kamar tana jinta.

     Knooking tayi akofar bedroom din yakura dake ciki tana lallashin zahirah taci abinci tace”Waye shigomana,mahgana”Bata taba zaton Suhaima bace,da siririyar sallama ta shigo dakin lokaci daya suka hada ido da Yakura,da sauri yakura ta mike tana fadin”wai suhaima nake gani haka kodai idona gezo yakeman”Mirmishin kasaita Ummi tayi kafin ta tako cikin isa da takama tana fadin”Nice dai Suhaimar dakika sani yakura ba gizo idonki,
ke miki ba, kina gidan dana Mu”azzam ne”Tafada cikin izza lokaci daya tana sauke idonta kan zahirah wacce ke zaune kan gado ta cire lifayan daga ita sai doguwar rigar shaddan dake jikinta yarintarta tafito fili kirjin nan ma yanzu yafara tasawa kura mata ido Ummi tayi lokaci daya tagano kamarta da uwarta kamar an tsaga kara ankarya Tuni fuskar Ummi ya chanza tahade rai sosai tana binta da wani kallon na zaki ci ubanki ne.

  Zahirah kuwa da sauri ta sunkuyar dakai jikinta yahau rawa tuni idanunta suka ciko da kwallan tun sanda Ummi ta shigo kallon farko zahirah ta mata gabanta yafadi balle dataga yadda take kallonta Allah sarki tuni tafara hawaye da hannu tasaka tana sharewa jikinta kuwa bai bar rawa ba.

  Yakura dake tsaye tana kallon Abunda ke faruwa itama cike da tsausayi take kallon zahirah kan takoma ta kalli Ummi tayi karfin hali cewa”ai nasan muna gidan danki mu”azzam ne kawai mamakin ganinki nake shekaru fa dayawa”Tafada itama bakinta yafara rawa Ummi tayi mirmishin dayafi kama dana takaichi kan tace”eh hakane kam yakura ya kwana dubu kuma”Tafada ammh still idonta na kan zahiirah.

.Yakura tace”Sai alheri shikenan kin guji maiduguri ko’Tafada da sigar zolaya,hoho ai nan da nan Ran Ummi ya baci takankance ido tace”Yakura kika ce me? na guji maiduguri “Tafada bayan ta sakarmata idanunta wa”inda suka fara chanza launi Yakura ta kalleta sai yanzu ta tuna tayi fa baram barama, Kafin tayi mgana Ummi ta kariso kusa da ita tana fadin”Ai maiduguri itace garin da duk aduniya in aka ambaceta nakejin kaina cikin bakinciki wani lokacin ma har na koka,garin da tunda nasaka kafata cikinsa ban kara farinciki ba sai da na barsa,garin da aciki aka kasheman mijina wanda naso rayuwa dashi koda bamai yawa bane.! garin da nashiga kunci da takura da halin kakaniyan rayuwa duk acikinsa,kin manta yakura kece kike tallafamin da abunda zanci aboye dani da dana,? kin manta? nace kin manta ne? tafada tana zare mata ido kuma cikin tsawa.

  Yakura tayi kasake kawai tana binta da kallo Ummi ta damke hannu yakura tana fadin”Shine kuma kike tambayana na gujeku alhalin kuka fara gujeman,ku,kuka fara kyamatata,saboda mene, ni bazan nisanta kaina daku ba,kuma na nisan ta duk wani ahalina,daga rabarku ba”Tafada tana sakin hannunta lokaci daya tana sakin ajiyar zuciya kafin tajuya tana kallon zahirah wacce ta rabe jikin gado tana kuka tace.

    YAKURA KINYI KUSKUREN BARIN SHETTIMA YA YA AURAMA MU’AZZAM DIYAR FADI,HAR ABADA ZAN CIGABA DA KALLONTA AMATSAYIN MUGUWAR UWARTACE, WACCE BABU IMAMI KO KADAN ARANTA,KUMA WLH TALLAHI SAI TA DANDANI KUDANTA FIYE DA WANDA UWARTA TA DANDANAMIN DAT IZ MY PROMISE

  Tagama fadar haka tajuya afusace lokaci daya idonta na fitar da kwallan bakinciki da takaichi,yakura dake tsaye itama hawayen takeyi tace’ * SUHAIMA* da karfi wanda har mahgana dake tsaye falo sai da taji cak Ummi ta tsaya yakura tatako zuwa gabanta tace”Kiyi wa girman Allah suhaima kiyiwa rayuwar marainiyar Allah duba,kada ki hukunta ta kan laifin da bata araye sanda uwarta ta aikata shi,kiyi afuwa gareta don Allah,wlh da ina da yarda zanyi danayi na hana wannan auren ammh banda yarda zanyi,illa in baki hakuri don Allah suhaima kada ki cutar da Zahirah don girman mahaliccinmu “Yakura tafada lokaci daya tana fashewa da kuka itama suhaimar cikin kukan ta waigo tana fadin”Wlh bazan iya ba yakura,da zan iya da tuni na yafe musu,ammh indai Fuskar mai kama da Fadi zata zauna dani to har abada abun zai dunga dawomin duk sanda na ganta,kiyi hakuri”.

  Tana gama fadin haka tafice tana kuka,haka ta wuce mahgana dake falo wanda jikinta yagama yin sanyi domin ta dan jiyo wasu maganganun sama sama,hajiya dake falo ita da mu’azzam da Shureim wanda suka dawo daga taka ma abokin aikin Dr.Shureim ya wuce cikinn Abuja zashi wani guri daga chan zai wuce gida,suka ga Ummi tafito daga dakin zahirah tana kuka mai cin rai ta haye sama da sauri ta shige daki ta bamko kofa.

  Muazzam yayi sauri zai bi bayanta yana Fadin”Ummi..”Hajiya tace”Dawo mu”azzam kai kasani yanzu suhaima baza ta taba sauraranka ba’Tafada itama jikinta yayi sanyi,cikin sanyi da kasala Mu”azzam ya juyo yana fadin”Hajiya zuciyata tafara Rauni da Da abunda ke damun Ummi,bazan juri ganin kukanta koda yaushe akaina ba,zan sauwakema yarinyar nan,kawai in zasu wuce su wuce da ita kawai”yafada cikin son nuna gaskiyansa.

  Hajiya ta kada kai tace”Kul kada ma kasoma hakuri dai zakuyi daga kai har ita din,domin abun bazaiyi,sauki ba yanzu,sai dai ahankali kawai”Tafada cikin sanyi itama Shureim dake gefe,yayi ajiyar zuciya yana fadin”Kai ni wlh lamarin nan har ciwon kai yake sani wlh”Mu’azzam yakallesa kawai yakada kai yabi hanyan shashensa ransa na masa kuna.

   Achan bangaren su yakura kuwa Ummi na ficewa mahgana tarumtuma cikin dakin tana fadin”yakura mun shiga uku wlh ganinta ma yafi lbrinta”Tafada cikin mamaki,yakura kuwa dakyar ta iya daga kafa ta karisa ga zahirah wacce ke rakube tana zubar kwallah ta rumgumota tana Fadin”yata sai dai kiyi hakuri,domin kin shigo wata rayuwa wanda babu mai fiddaki,Shawarata gareki shine sai kin zama mai hakuri da kauda kai,biyayyah da taka tsantsan,Kibita sau da kafa don UWAR MIJINKI CE kuma bakomai itadin goggon kice”Tafada tana sharemata hawaye.

  Zahirah tadago kanta tana kallon Yakura cikin sarkakiyan murya tace”Me..Me..Yafaru..Ne,naji tana ambatom mama na ne,metayi mata? tafada cikin Hawaye kallonta Yakura tayi wata zuciyata tace”Ki sanar da ita komai domin yanzu ne ya chanchanta ta sani'” gyara zama yakura tayi tafara bawa Zahirah lbrin duk abunda yafaru daga farko har karshe ta kareshe da cewa” Dole ki koyi hakuri da kawaichi,yahna akwai aiki agabanki”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button