NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Mirmishi Ummi tayi kafin tace”Alhamdulillahi..Yanzu burina ya cika na tabbata in kika koma ma shettima da wannan sakon kadai ya isheshi yaji abunda suka saka naji alokacin..”tafada tana saka hannu ta fizge Zahirah tana fadin”Sakeshi tunda batare kukazo Duniya ba,yanzu sai abi wani sarkin ko,nidai na yarda kwallon mangwaro na huta da guda..”

hannunsu na sarke da juna suna kallon juna suna kuka,Ummi ta ja hannun ta raba tana fadin”Munga laila da majnun saketa don ubanka..”tafada cikin dakamai,tsawa,sakinta yayi yana dafe kansa kuka yake kamar karamin yaro,zahirah da cikinta yake hautsinawa kamar zai fito duniiya alokacin daya ta yi karfin Halin mikewa Ummi ta izata tana fadin”Toh sai ki ficemin daga gida wlh ko daki bazaki koma ba, mayyah Tafi kije ki fadama Shettima komai banison kirage komai so nake zuciyarsa ta buga kema nayi takaichin mutuwar uwarki don nasan da tana raye kilama zuciyarta ta buga ta mutu,..”tafada tana ingiza keyar Zahirah zuwa waje ko tsausayi bashi aranta.

Zahirah dataji wani karfi yazo mata ta daddake ta ture ummi,wacce sai tayi taga taga zata fadi dakyar ta iya tsayawa kan kafafunta,Kallonta zahirah takeyi cikin tsana da Bacin rai kafin tace da karfi…” Kinji kunya wlh Tir da ke,mekikayi kenan,kinyi abun burgewa don kin saka danki yayi saki uku alokaci daya,sakin da Allah da kansa ya hana,wanda ko daya akayi sai al”arshin Allah ya girgiza,ammh ke uku kikasa akayiman aka sakeni da tsohon cikin jokinki ajikina,To kije duk Abunda kikayi Allah nagani,kuma da izinin lahi hakkin na, dana ya mu”azzam sai ya kamaki,sai ya kamaki barganin kina mtsayin ,mahaifiyarsa aike ba Allahnsa bane…“Tafada cikin tsawa idanunta sun Firfito Da hanzari Ummi taja baya tana rike baki domin yarinyar tabata tsoro kan tasamu zarafin mgana zahirah ta cigaba da cewa”Ko baki ce natafi ba zama ne yakare acikin gidan,nan,kuma sakon dakikace na kaima baffa zan kaimai,ammh kisani Sakon zaije garesa,ammh kisani ki kara sani zai Tafi ammh kema zai dawo gareki zai dawo gareki ki rubutu ki ijiye sai kinfini kuka da shiga kunci..”Tana gama fadar haka ta fice tana jan jikinta cikin tsananin bakinciki da halin ciwo.

Ummi datayi mutuwar tsaye ta rakata da fadin”Oho dai nidai,gidane dai dole mutum ya barsa tunda ba da kudin mai dattin hula aka gina ba..”tafada tana tafa hannu..

mu”azzam dake kife dakai ya dago da Sauri yana kokarin mikewa Ummi ta dakamai tsawa da cewa”Kana motsawa wlh zan debama albarka maras mutumci kawai…”Tafada cikin tsananin Fusata,kallonta yayi idanunsa sunja launi wani kallo na Anya kekika haifeni ma,Ummi kuwa taji kallon ajikinta shiyasa tace’Kai don ubanka wani irin kallo kakeman,ni ne dai Suhaima,kuma nice nan Uwarka nina haifeka,in ma kana tamtama ne kadaina..”tafada tana zama kan kujera ta harde,maida kansa yayi ya cusa cikin gwiwa yana jin kansa na barazanar fashewa ga kirjinsa dake ruwan lugude yanaji kamar wani abu kamar dutse aka dora masa awajen.

Zahirah na fitowa kofar falon taci karo dasu karine durkushe suna kuka,alaman sunajin duk abunda ya faru,kallonsu zahirah tayi hawaye suna zubomata ta sanya hannu ta share tana fadin”Sai wata rananku,har abada bazan manta da alherinku gareni ba nagode muku sosai..”Tafada kuka nacin karfinta tajuya da Sauri tafara tafiya karime ta mike ta kwalamata kira.”Diyata..”Tafada tana mai zubar kwallah.

Cak ta tsaya hartazo kusa da ita dankwalin kanta ta ciro ta yafamata kafin ta hau kunce haban zaninta ta warwaro kudi masu yawa yan dubu dubu ta mika ma zahirah tana fadin”Karbi wannan diyata kije dashi kiyi kudin mota nasan baki dashi..kije Allah ya saka miki ..”Tafada tana juyawa da gudu,da kallon zahirah tabita,tanajin kwallah na taruwan mata,sharewa tayi tana kara damke kudin dake hannunta Allah sarki mama,dazu da safe yallabai ya biyasu kudin Albashinsu shine ta bata,Allahu ya sakama wannan matar ta fada aranta kafin tagyara dankwalin dake kanta kafarta ko takalmi babu tajuya tafara tafiya gayadda cikinta ke murdawa ammh hakanan ta daure.

Su uche da sani maigadi da falau suna gefe suma sunyi zugum tazo ta wuce ta isa get din kenan sani ya rugo ya budemata yana kallonta kada kai tayi tafice kafin ta waigo tana kallonsu suna share kwallah,mirmishin yake ta musu tana daga musu hannu take fadin”Sai watarananku…”Cikin siririyar murya kafin tajuya tafara tafiya cikin sauri duk da ciwon dake cinta gashi dare yayi don lokacin har anyi mangariba babu kowa atitin kowa ya shige gidanshi.

Sai da tayi dan gaba kadan kana ta waiga tayima gidan Kallon karshe don bata fatan ta sake dawowa cikinsa tayi tafiya mai nisa don harta fita daga anguwan kafin tasamu mai,Keken napep,da da farko da ta tsaidashi kin tsayawa yayi don shi azatonshima mahaukaciya sai da yadan lura dakyau,kafin ya dawo baya,rikonsa tahauyi kan ya taimakamata yakaita tasha inda zata hau motan maiduguri,kallonta yayi ada baiyi niyyar taimakonta ba,ammh ganin halin data ke ciiki ne yasa yace ta shiga suje,da hanzari ko tafada tana danne maranta cikin fitan hayyaci take kiran Sunan Allah.

Gabadaya Tunaninta ya chuse tanajin wani yanayi atare da ita,yanzu maiduguri ta nufa awannan daren,kodai taje gidansu Asma”u ne? to in tama je,gun wa zata,ta daura ma Asma”u Nauyi,to ita bama zata iya gane gidan ba,kai ko ma zan gane gwara na koma mahaifata domin Sune kadai gatana ayanzu,tana wannan Tunanin suka shigo tashan,ganin halin datake ciki ne,mai napep din da kansa ya fita ya sama mata mota inda Allah ya taimaketa mutum biyu suka rage Sharon din ta cika,zuwa yayi yace ta fito ga mota jikinta na rawa ta fito ta warwaro dubu daya akudin ta bashi,cikin tsausayinta ya girgixa kai yana bin tulelen cikinta da kallo yace”a”a ki barshi ni don Allah na taimaka miki..”yana fadin haka yayi gaba yana fadin ta biyoshi,cikin sagewar gwiwa tabishi tana daga kafa dakyar har motan ya kaita dakyar ta iya shiga saboda yadda ko”ina na jikinta ya saki,kallonsa tayi bakinta duk ya bushe tace”Nagode..”gyadama ta kai yayi yana fadin”Allah ya rabaku lafiya yakuma tsare hanya…'”Yafada yana wucewa.

Hawayenta ta share da haban dankwalinta,Mutum daya aka kara kafin Sutashi,sai da aka hada kudaden mota kana Direba ya shiga suka dau hanya..Suna tashi matar dake kusa da ita ta duba agogon wayarta 9:00pm na dare.

Runtse ido tayi tana kara takure jikinta ga maranta yadda yake kartamata cikin gwiwanta ta saka kanta tana ZUBAR KWALLAH,lokaci daya tana addu”a Aranta Allah yasa tana da rabon ganawa da iyayaanta,dakuma fatan ta rabu da cikin jikinta lafiya….

Comment,share and vote

Intelligent writer”s

Janafi

Uwar mijina..!# 

UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

Hakika jiya naga Tarin masoya wanda ni MAMI JANAF Bantaba tsammanin haka UWAR MIJINA YA SAMU KARBUWA BA..bansan dawani kalma zanyi Amfani da ita ba wajen godiyata ga Allah(SWA) ba Ammh duk da haka ina mika godiyata garesa taredaku gabadaya, Allah ya saka da alkhairi yabar kuma so da kauna na har abada

Attention:zan danyi tsokacine, gameda masu cewa wai sakin da mu”azzam yayi ma Zahirah wai bata saku ba,who told u ehe?to malamanmu sun fadama mana ko acikin maye ,mutum ya saki matarsa ta saku,balle wanda yayi cikin hankalinsa,mahaukaci ne kadai akace inda ya saki matarsa to bata saku ba,kuma masu cewa saki ukun dayayi mata amtsayin guda daya ne? waya fada muku,malamai sunce indai akayi saki uku lokaci daya to abarshi a Saki daya ne,ammh duk sakin da”akayishi A rarrabe ma”ana mutum yace ya saki matarsa saki daya,na sakeki saki biyu,na sakeki saki uku,to Aurensu ya haramta har sai in Wani ya doramata idda,to da hakan nakeso na fadamuku Auren Hirah Da mu”azzam ya haramta harsai wani ya doramata idda,Allah shiyafi kowa sanin Daidai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button