NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Su karime sukansu suna tsausayama zahirah yadda ta dawo saboda ciki,gabadaya halitarta ta chanza ko”ina na jikinta ya kumbura ko tashi bata iya yi ita kadai sai an Taimaka mata saboda yadda cikin yayi kasa ya sakarmata Nauyi..Wani lokacin sai dai tayi ta kuka ita kadai don gani take shikenan tata ta kare ne,Asma”u ma tana yawan zuwa dubata tare da kwantar mata hankali natadaina saka ma kanta damuwa insha Allahu komai zaizo da sauki,Allah yasa kawai Zahirah ke cewa ammh ita kam tagama sanyi da al”amarin Ummi.


Ranar Friday da yammah Misalin karfe shidda na yammah zahirah na cikin dakinta zaune afalo sungama waya da mu”azzam kenan,kishi ya kamata gashi babu kowa akusa dakyar ta rarrafa ta isa ga fridge din ta bude don tadauki ruwa,sai dai kash babu ruwa ko daya sai dai lemuka gashi kishi ya isheta bazata iya jiran wani ya shigo ba

Dakyar da kama kujera ta mike tana tafiya dakyar ta manta sam da daukan hijabi saboda yadda makogaronta ya bushe,tana Tafiyanta dakyar ta fito falo babu kowa da dan Saurinta ta karisa dan karamin fridge din dake falon ta bude ta dauki ruwan Swan na gora ta bude takafa kai tana sha,sai da ta shanye fin rabi kafin ta ijiye tana maida Numfashi tuni dan jikinta yafara motsi yana wuntsilawa,binsa dake da kallon cikin doguwar rigarta kafin ta sanya hannu ta dafe gun tanajin kaunarsa na ratsata ta ko”ina.

Ummi dake saukowa,daga sama kunnenta makale da waya suna magna da wata hajiya Saratu ne,mai saida lesuka,kaya Ummi zata siya shine takirata suke mgana kuma dayake dama tasaba siyayyah agunta,kamar amafarki haka take hango wata mata atsaye afalon hannunta dafe kan wani tulelen ciki abun yabata mamaki,bakuwa kuma sukayi,kafeta tayi da ido,itako zahirah batasan wainar da”ake toyawa ba hankalinta na kan cikinta.

Ummi ta cigaba sa saukowa tana kara kallon zahirah da farko bata ganeta ba,saboda yadda ciki duk ya chanzata,ammh lokacin data karisa saukowa,kawai fuskar yarinyar ta hau mata gizo,lokaci daya zuciyarta ta buga ammh sai ta karyata idonta,murza idonta ta kara yi still dai zahirah na nan tsaye,hajiya saratu na mgana batama jin metake cewa ta shiga rudani Saurin yanke wayar tayi tana karisawa kusa da zahirah tana karemata kallo daga sama har kasa,so take ta gane cewa da gaske yarinyar ne kokuwa dai mai kama da ita ne.

Kamar tsayuwar mutum zahirah taji abayanta,shiyasata dagowa taga kowanene,karaf idanunta suka hadu dana Ummi,saboda razana bata san sadda tayi baya ba, zata fadi sai da ta rike gefen kujera,lokaci daya taji cikinta yawani murda maranta ta daure,jikinta babu inda baya rawa saboda tsoro da firgitan yadda Ummi ta kafeta da ido,da Sauri tajuya tafara tafiya tana cije baki,so take tayi Saurin shigewa daki takira mu”azzam.

Ummi data sandare a tsaye jinta da ganinta suka dauke na dan wani lokaci dakyar tayi karfin halin cewa”Ke..Meye nake gani ajikinki..”?Tafada cikin karyewan murya cak zahirah ta tsaya jikinta yahau rawa tama kasa waigowa Shan gabanta Ummi tayi kafin ta cakumo wuyanta tana fadin”Don Ubanki cikin shege kikaje kikayo ko dama sai da na fadama son ,ya sakeki ki koma garinku,domin nasan karshenta ki kwasomana abun kunya tunda agida an gada..” dora hannu Ummi tayi aka tashiga kwarara ihu su karime dake madafa suka fito hankalinsu tashe,su Sani maigadi da Falalu suka shigo Asittin suka fado falon suna tambayan lafiya.

Ummi da hannunta ke bisa kai ta shiga nuna zahirah tana fadin”Kun ganta daga taimakonta taje ta kwasomana cikin shege, agida”Atare su karime suka rafka salati suna kallon yadda zahirah ke kuka,kuka mai cin rai,Ummi kuwa inda take shiga banan take fita ba Sani maigadi kuwa fadi yake”munbani hajiya ciki acikin gidan kuma..”Yafada yana kallon zahirah donshima koma ganeta baiyi ba.

Cikin zafin nama Ummi takaimata duka gefen cikin nata wanda sai da Zahirah ta duke tana rike da cikin aiko Ummi ta shiga dukanta tana fadin”Allah ya waddan ki tsinanniyar yarinya,mara mutumci ashe abunda kikeyi kenan,yau dinnan zaki koma inda kika fito da wannan shegen cikin jikin naki..”dukanta take tana hambarin cikin itako zahirah na kwance ta kasa kwatan kanta banda kuka ba abunda takeyi.

Karime ce taga zalunci yayi yawa tajuya da gudu ta fice tana kuka,zahirah kuwa jin yadda Ummi ke shegentata da abunda ke cikinta yasa wani karfi yazo mata,ta ture Ummi dake kanta cikin kuka ta rarrafa gefe tana kallonta lokaci daya idanunta suka janza launi,ga cikinta dayake harbawa ga maranta daya tamke tace cikin tswa”Karki kara shegantamin ciki Ummi,cikina dan Sunna ne wanda shedu suka taru suka daura..”Tafada muryanta ya kekashe.

Ummi tayi mutuwar tsaye kafin tace”Dan Sunnah…”bakinta na rawa zahirah tace”Kwarai cikin jikina cikin jikokinki ne wanda danki mu”azzam ya samar dasu yazama dole ki sani domin lokacin hakan yayi saboda haka,kada kikara kiran cikina da shege ‘””.

Yadda zuciyar Ummi tayi lugude haka na mu”azzam yayi daidai lokacin daya sawo kansa falon,Tundazu suke bakin get suna hon shuru babu megadi babu dalilinsa,ganin haka yasashi Fitowa ya kwankwasa get din karime ce tazo ta bude mai tana kuka yana tambayanta lafiya tana nunamai cikin gida tana fadin”Hajiya zata kasheta…”

Yanajin haka gabansa ya amsa cikin azama ya wuce wani zufa na ketomai ya sawo kanshi falon ne Yaji furucin zahirah wanda sai da jakar hannunsa tafadi yana fadin ya salam,shikenan kuma babu sauran boye boye.

Ummi ta saka hannu ta dafe saitin zuciyarta idanunta sunyi jawur take kallon zahirah tana maimata kalamanta cikin kwakwalwarta kafin tace tana nuna kanta”Ni..Mu”azzam din yayi miki ciki…”tafada cikin rashin hayyaci gyadamata kai zahirah tayi tana fadin”kwarai ma kuwa da gaske gashi nan abayanki ki juya ki tamabayeshi…”Tafada cikin karfin hali.

Kamar wata doluwa haka Ummi ta juyo ga mu”azzam tana fadin”Karyata ta son,karya ne ko? kacemin karya neeee…”Tafada cikin wani yanayi da sagewar Tunani.

Runtse ido yayi yana jin wani kuna ransa,matsowa tayi kusa dashi ta riko hannuwansa tana fadin cikin kuka”kacemin karya ne son ko zuciyata zata dawo daidai,i know my son bazai taba cin amanata ba,ka karyatata son ka karyatata,kace bahaka bane…”Kallonta yayi kafin yakoma ya kalli zahirah wacce ke cije lebe saboda yadda maranta ke karta

Riko hannun Ummi yayi yana fadin”cool down Ummi,ki saurare ni kiji mana…”Fizge hannunta tayi tana ja da baya take fadin”kenan da gaske ne? tunda kakasa karya tawa, kenan da gaske ne Abunda tafada ko”?Tafada kamar zata fita daga hayyacinta Runtse ido mu”azzam yayi kafin ya durkusa bisa gwiwowinsa yana fadin” EH UMMI NA,DA GASKENE CIKIN JIKIN ZAHIRAH NAWA NE..NAWANE NINA DIGASHI…. ” yafada cikin dakewa lokaci daya yana sadda kai saboda yadda Ummi take kallonsa tana wani mirmishi tace”Fine and good Ibrahim kafada da baknka kai kayi ma diyar Fadi ciki ko? yayi kyau Ni suhaima ni zaka ci amana ko..”Tafada tana ja Da,baya kafin tayi wani yunkuri jiri ya debeta ta fadi jikake Timmmmmm….”

Babu yawa,kuyi manage plz

Intelligent writer”s

Janaf

Uwar miji

UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

   *Mallakar:JANAF*
   *Wattpad:Janafnancy*

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

Kowani marubuci indai ya dora Alkalaminsa kan Takardarsa,ko Wayarsa,ko tap dinsa da niyyar Rubuta wani abu to yana da babban dalilinsa bawai iya yasaku nishadi bane A”a don ya baku wani darasin dazaku fadaku akai ne,walau darasin mai fitane daga farkon farawa,wallau kuma sai kun himmatu wajen hakurin karatu kafin kuci ribar abin….Da wannan dan bayanin nawa nake kira ga yan TEAM HIRAH DA MU”AZZAM,dasu dauki kaddara Abunda Allah ya rigaya ya rubutu babu mahalukin daya isa ya chanzasa,wannan itace KADDARARSU…Assalamu Alaikum Janafi????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button