NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

  Baffa na hawaye yake fadin”Wlh bakimana komai ba Suhaima,dukkanmu masu laifine,Allah ya yafemana gabadayanmu,yarabamu da aikin danasani..’Yafada cikin Farinciki gabadaya dakin suka amsa da Amin,kafin kuma ashiga gaisawa,lokacin kuma ushe ya shigo da kayan abinci godiya sosai yakura da baffa ke jeramai shureim da addu”an Allah yakara budi.

   Baffa ya kalli Shureim yace”Shikenan kuma babu lbrin mu”azzam haryanzu ko”Baffa yafada cikin jimami,shureim yasaki ajiyar zuciya,kafin yace”wlh baffa bawani lbrin duk inda nake tunanin samun dan”uwa,wlh babu shi babu lbrinsa,sai dai mucigaba da addu”an duk inda yake Allah ya karkato da hankalinsa gida”Dukkansu suka amsa da Amin Ummi ko dukar dakai tayi tana share kwallar idonta,Hajiya da yagana suka kalleta cike da tsausayawa domin itace abun Tsausayi ayanzu.

  Sai gashi nan suka zauna anata maida zence ana jajantama juna,baffa ma dake kwance,bakinsa ya bude sai hira suke da Ummi,suna tuna da,suna takaichin,abunda suka aikata abaya suna fadin dama basuyi haka ba,to daman irin wannan Ranar ake gudu wato Ranar nadama,sallar kawai yatadasu,sukayi suka dawo su xauna Yakura ta dafamusu shinkafa da miya suka zauna sunaci,ana hira cikin farinciki da Annushuwa koba komai Ummi tasamu natsuwar zuciya saboda ta sauke wani nauyi daya tsayamata arai shekara da shakaru akirjinta dayaki wucemata sai yau,data roki gafaran Shettima takeji kamar an Saukemata wani Nauyi.

   La”asar nayi,Suka shirya dukkansu zuwa gidan Bukar,wanda yakura take shaida musu yau ne,ranar da Zahirah zata tare adakin mijinta,Ummi dataji mganar kamar saukan aradu,taji wani yamm,ajikinta ita tarigasu yin gaba saboda kukan daya tasomata,Shureim  kadai aka bari gun Baffa don yace bazai iya zuwa ba,Yaga zahirah za”a kaita gidan wani,koba komai yana taya dan”uwansa kishin zahirah,harga Allah yaji ba dadi,duk dai ko batayi auren ba,yasani ta haramta ga mu”azzam.

    Lokacin da suka isa gidan nasu zahirah ya kachame da yan”uwa da abokam arzuka anata hidima cikin daki kuwa Ashe ne ta takarkare tana ma Zahirah kwalliya tanayi tana masifa tana cewa”ke wai wata irin amaryace babu gyara,ballatanama kwalliya,haka zakijema mijin Fuska kozai kozai,dake, to in zaki mike ki mike wannan karan gidan KISHIYA zaki ba gidan UWAR MIJI BA…”

Tafada tana kokarin sakamata eye shadow runtse ido zahirah tayi Ashe tayi Saurin cewa”Wlh kika kuskura kika zubomin da hawayen banzan nan naki,alqur”an zan ci ubanki adakin nan,bar ganin kina da danyen jego..”tafada tana dugurinta akai,saurin shanye hawayenta tayi saboda tasan halin inna Ashe tsab zata aikata.

  Kamar amafarki takeji muryan wata kamar na Ummi Suna mgana da mutane Afalo,Saurin kwace kanta tayi daga hannu  Ashe ta fice da Sauri ta bar Ashe da masifan cewa”Ke kinyi haukane wai…?take fada,bayan ma tuni zahirah ta fice,wacce ke sanye da wani ubansu Swice less blue yana da ratsin milk colour ajiki,kayan sun amsheta matuka sun mata das dayake ruwan zafin ya amsheta matuka tayi kyau da ita.

  Tana fitowa falo abunda tagani yasata ta daskarewa a tsaye jikinta lokaci daya taji hawaye sun cikomata ido,UMMI ce durkushe gaban,bahna dinta tana,kuka mai cinrai fitowarta yasa falon yayi tsint kallon yadawo gunta,yan”uwan mahaifinta ne,sai hajiyar Shureim,da kuma yakura sai Ummi dake durkushe tana gunjin kuka,Jin shurun yayi yawa ne yasa Ummi kallon barayin da Zahirah take,Nan suka hada ido hudu ana juna,cikin wani yanayi zahirah tahau ja baya idanunta na zubar kwallah,lokaci daya jikinta na rawa juyawa tayi zata koma daki bayan ta saka hannu ta toshe bakinta da kukan dayakeson kubcemata.

  Da Hanzarin Ummi ta mike daga durkushen datayi tana fadin”ina zaki zahirah,kema gujemin zakiyi kamar yadda mu’azzam ya gujemin ya tafi ya barni..”Tafada muryanta ta sarke hawayenta na zuba ta cigaba da cewa”Don Allah don Annabi,kiyi hakuri zahirah,kimin aikin gafara karki gujemim ke kadaice nakeda da ita yanzu wacce zata san dafin dayake damuna azuciyata”Tafada tana durkusa bayan tahada hannuwanta tana kuka take fadin’Naji na yarda ni Suhaima na zama azzaluman Uwa ga mu”azzam,nakuma zama muguwa,mara imani gareki zahirah,kada kiyi duba da mugayen hallayanta,ki juyo ki kalleni kiyiman aikin gafara,wlh natuba nayi Nadama duka abubuwan dana aikata miki,Kiyi yafemi..Ki..Ya..fe..min..”Tafada tana kuka mai tsuma duk mai Sauraro kafin tari,ya sarketa ta duka tana rike kanta.

  Zahirah data ke tsaye hawaye sungama wankemata fuska,tawani juyo da wani irin gudu ta isa ga Ummi ta dagota tana fadin”Na yafemiki Ummi,wlh bantaba rike ki araina  daidai rana dayaba,duk abunda kikayimin bana ganin laifinki,kema batamiki akayi,Kullum burina kidawo ki yafemana mahaifiyata abunda ta aikata gareki,gashi yau burina dani da ya mu”azzam yacika,ammh kuma yau ta kasance babu shi,balle yaga wannan rana mai dimbin tarihi.”Tafada tana kuka da Sauri Ummi ta Rumgumeta tana fadin”Babu Son Zahirah,son ya tafi ya barmu Alhalin ya manta cewa bazamu iya rayuwa babu shi ba, ammh komai yafaru ni najama kaina,Allah ne yake hukuntani da laifin dana aikata..,Allah na tuba ka yafemin..”tafada kuka na kecemata,kamkame juna sukayi suna kuka mai cinrai.

  Gabadaya jikin mutanen dake falon sai da yayi sanyi,yakura da hajiya kuwa kwallah suke sharewa,Shikanshi bahna juyawa yayi yana share kwallah,ita kanta Maghana kwallar take sharewa,Gyarab murya bukar yayi yana fadin”kubar kukan hakanan kada wani mtsalan ta sameku,ku zo muzauna duka a taru ayafema juna,an zama daya,abunda Allah kuma ya kaddara babu mahalukin daya isa ya hana”yafada cikin sanyin jik,hajiya ce ta isa ga Ummi ta kamo hannunta tana fadin”Muje ki zauna suhaima kinsan baki da cikkakiyar lafiya,ki rage wannan kukan don Allah..”Tafada tana riko hannunta,kam kuwa ummi ta riko hannu zahirah suka karisa cikin Falon suka zazzauna,umarni bukar yabama kowa akan azauna.

  gyara zama bukar yayi yana fadin”Alhamdulillah Allah shine abun godiya,dama abunda ake nema mutum yaringa yi kenan,yayi nadama Tunda Wuri tunkafin lokaci ya kuremasa,Babu komai hajiya Allah ya yafemana gabadaya..”yafada cikin kulawa.

  Muskatawa Ummi tayi hannunta na rike dana zahirah tace”Nagode sosai Allah ya kara girma..”Tafada bayan ta waiga bayanta itama mahgana tana rokonta gafara,nan tace ta yafemata nan Ummi tabi kowa afalon yan”uwan bukar tana cewa su yafemata,nan duka aka ayafi juna cikin mutumci da karamci,zahirah ta mike Ummi ta kalleta tace”Ina zaki Dota..”

      Zahirah ta kalleta kan tace”Ina zuwa ummi,yanzu zan dawo..”Sakin hannunta ummi tayi tana binta da kallon Tsausayi,ita bama kanta take tsausayama ba tafi tsausayama Zahirah don ita akafi cuta itace yarinya,daki zahirah takoma ta dauko yaran duka biyu ta rumgumesu ta nufo falon dasu,Ummi na ganin Fitowarta ta nufeta tana amsan littale Ummi take fadin”kai,kika iya daukansu lokaci daya,baki tsorom su kubce miki..”tafada tana kurama little Ummi dake hannunta ido.

  Mirmishi zahirah tayi tana fadin”Ai na saba ummi,banajin komai..”tafada bayan ta ijiyemata moodu gefen cinyarta inda ta dora Little ummi,Kura musu ido Ummi tayi cikin wani yanayi na fita hayyaci hawaye nabin idonta ta dago tana kallon zahirah kafin ta maida kanta gun hajiya,gyadamata kai hajiya tayi tana mirmishi,maida kallonta tayi kan zahirah kan tace”yanzu wadannan yaran ne,acikin ki sanda na koreki..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button