NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Karime tayi murna harda dan gutun hawayenta,tayi kuma alqawarin kula da zahirah da abunda ke cikinta da dukkan karfinta,yafadamata adinga bata abinci akan lokaci kuma ta dinga samun hutu sosai sai magungunanta daya nuna mata yadda zata dinga bata,jinjinakai tayi alamar duk ta gane,godiya shima ya mata kafin ya fice zai koma office ne yanzu ma haka excuse ya dauka.

haryazo yatafi Ummi bata da lbri kusan fa Hajiya suhaima daman yar mulki ne,ranar da abun suka motsa ko kafarta ba”a gani a kasa tana samanta ko abinci in bata ga dama sai dare zata ci ita haka take,wani lokacin tana da iko da takama bakowanni lokaci ake gane yanayinta ba,to yau din haka ta kasance shiyasa har mu”azzam yazo ya tafi bata da lbri.

Kwanan Zahirah uku bata leka ko kofar dakinta ba komai take bukata karime na mata shi sukansu su uwani suna iya bakin kokarinsu akanta,don Uwani ke zuwa kullum da safe ta gyara mata dakinta ciki da bai,ta wanke mata tiolet harda kayan sawanta in mai wanki bai zo ya tarrara ba,itako lami itace hidima kan abincita komai take sha”awar ci da hanzari zataje ta sarrafamatashi,ita kuwa karime itace ke kula da ita bata magunguna da bata shawarwari saboda kusan manya sunsan Abunda yadace da masu ciki,shiko uban gayyah shike mata wanka da safe kafin yatafi ya shiryata tana fitar kamshi,ta ko”ina zahirah tana ganin gata wanda yakara sa hankalinta ya kwanta duk da bai kwanta duka ba,Har waya ya siyamata kirar Cmon 11 yabata ta rike ahannunta saboda ko wata mtsala ta taso yanzu hankalinsa ya kwanta tunda ko yaje office yana jinta ta waya so damuwartasa kadan ne.

game da Ummi kuwa duk shige da ficen dasu karime keyi bangaren zahirah bata taba lura ba,saboda komai suma da taku sukeyi,kafin ma ta sauko daga sama sun gama mata komai,lokacin kuma da zata koma sama,sai su kara shiga,,kuma Allah bai taba nuna mata daya daga cikinsu ba shiko mu”azzam Zahirah tayi tayi ya fito yafadama Ummi gaskiya saboda gujema faruwan wani mummunar abu a gaba,ammh yaki yace tabari zai fadamata ba ammh ba yanzu ba,sai lokaci yayi.

Ba haka zahirah taso ba,taso ya sanarmata da bakinshi kila abun zaizo da sauki akan tagani da idonta tunda ciki fa dan duma ne,duk boyonsu dole watarana ya bayyana hartagani don dai ma cikin yabi jikinta ne ammh inda zata tsaya ta mata kallon kwarai tsab yadda Ummi take da Saurin gane abu sai ta ganosu to inda Allah ya tarfama garinsu Nono Ummi bata ko Kaunar ganin Fuskar Zahirah saboda yadda ta tsani Uwarta Fadi,kuma ita zahirah tana kama da uwarta shiyasa ummi koda wasa batama ko kaunar kallon Fuskarta.

Ranar data kwana biyar a gida Aranar Sai ga Asma”u da yammah ita da maminta direba ya kawosu lokacin da suka shigo falon Ummi suka tarar ta amshesu hannu bibbiyu domin bata sansu ba sai da suka gama gaisawa kana Asma”u ke tambayan zahirah,awani shekeke Ummi ke kallonsu ita da mami araine dai bazata taba rainasu ba domin da ganinsu Naira tuni ta zauna afatarsu da jikinsu cikin dakewa Ummi tace”Ke wacece ko kuma nace ku suwaye kuma daga ina kuke..?'”Mami ta kalli Asma”u wacce idanun Ummi suka bata tsaro ammh ta dake tace”Sunana Asma”u ni class mate din Zahirah ce wannan kuma mahaifiyayace munzo dubata ne,tun ranar da ta bar school batada lafiya bata dawo ba..”Tafada itama cikin confident.

Tsaki Ummi taja kan tace”mtseww..Kuma tacr muku nan ne gidansu..”Asma”u ta gyada kai tana fadin”Kwarai harma mun taba zuwa da ita..’kallonsu Ummi tayi kan tace”To ni bansan wata mai irin sunan da kika ambata ba,nan gidan dagani sai dana,sai ma”aikatana,kila kunyi batan hayan ne”tana gama fadar haka takoma ta zauna kafa daya kan daya tana musu sakaran kallo.

mami jikinta yayi sanyi aranta tana fadin”wannan mata akwai jaraba..”Asma”u ko mamaki ne ya cikata domin in bata manta ba dama zahirah tafadamata hannun goggonta take,kenan wannan ne goggon nata, mara mutumci ce ashe lalle zahirah na hakuri,suna kokarin tashi ne sai ga Karime ta fito ganin Asma”u yasa ta ganeta ta washe mata baki tana fadin”a'”a maraban ku da zuwa,muje ai zahirah tana ciki…’mikewa sukayi kamar akan kaya suke ammh sai da Asma”u tajuya tama Ummi wani kallo na cikin ido ko tsoro babu aranta,wanda abun mamaki har suka shige dakin zahirah Ummi takasa tashi balle tayi mgana kallon da yarinyar tayi mata ne yabata mamaki,tunda take ba wanda yataba mata wani banzan kallo irin na yarinyar ta kyale sai yau,kamar wacce tama asiri sai da suka wuce ta rakasu da tsaki tana wani gyara zama,niko nace aikin banxa.

Sai dai Zahirah taga Asma”u da Mami kwatsam wanda saboda murna sai da ta tashi ta rumgumeta kan ta duka tana gaida mami amsa mata tayi tana dagota tana tambayanta jikinta amsa mata tayi da jiki yayi sauki,zama sukayi suna gaisawa da Asma”u wanda keta kallonta yadda tacika gawani fari datayi fatarta tayi fresh da ita,ga Boobs dinta sunciko kamar zasu fasa riga,Mami ma kallonta take zuciyarta na saka mata wani abu ammh tayi saurin kauda tunanin hakan aranta,ganin Zahirah ai budurwace sai ta danganta hakan da ciwo da zaman Wuri daya.

Asma”u ko sai data ta bugama Zahirah zencen Ummi da cewa”Ke besty wai waccan matar da muka gani afalo itace goggon taki..”Gyada mata kai zahirah tayi gabanta na faduwa kada suce Ummi ta musu wulakanci tabe baki Asma”u tayi tana fadin”Tab ammh matar nan bata da mutumci kiinsan metacemana nida mami..”zaro ido zahirah tayi kan ta girgiza kai Asma”u ta cigaba da cewa”Cewa fa tayi wai munyi batan kai ne,bata ma san wata mai irin sunanki ba,kiji fa..”dan yake zahirah tayi kan tace”Uhm Ai Ummi haka take nima hakuri nake da ita…”Daga haka ta tsuke bakinta,lura da hakan da Asma”u tayi sai ta kyaleta,basu wani jima ba suka mata sallama bayan Asma”u tabata school bag dinta mami kuma tabata Leda cike da kayan Fruit harda kudi 5k amsa tayi tana musu godiya har bakin shashen ta ta rakosu kafin takoma abunta don mu”azzam ya gargadeta karta sake fita,ko fitan yakamata to ta sanya dogon Hijabinta,Su Asma”u na fitowa sukaga Ummi ko kallonta Asma”u batayi ba saboda matar sam bata kwanta mata ba,tacika wulakanci mami ce ma tace mata sai anjuma,in kun taka ku da kuke karatu ta tanka haka suka fice mami na mamakin wasu matan wa”inda suka dauiki duniya da zafi haka.

Aiko zuwansu Asma”u ranar mu”azzam yaga tashin hankali don Ummi tayi tsiya kamar ta ari baki,kan wlh kada wata tsagerar yarinya ta dawo mata gida itabatason rashin kunya hakuri shidai yayi ta bata dakyar ta hakura,achan daki kuwa da mu”azzam ya tsare zahirah da ya akayi Asma’u kawarta tazo tayima Ummi rashin kunya alhalin tafi kowa sanin halin Ummi,abunda Asma”un ta fadamata shi ta fadamai takara da cewa”kuma nasan harga Allah bazata ma ummi rashin kunya ba..””Tafada kamar zatayi kuka,rumgumeta yayi kawai yanajin takaicin halin Ummi na yarda take kokarin tona abunda suke kokarin Rufewa.


Sati biyu cur Zahirah ta kwashe agida kafin takoma mkranta sai da ta warke sumul sai abunda ba”a rasa ba,yanzu ko agida duk inda zata da katon hijabi take yawo acikin gida dokar mu”azzam kenan saboda kaunda idon Ummu,duk da bawani fitowa take ba,ammh duk sanda hakan takama,sai tasanya hijabi ta rufe Jikinta,saboda cikin nata yafara turowa ta cikin rigarta abun masha Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button