NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

   Ajiyar zuciya Mu”azzam ya sauke kafin ya damke hannu Ummi yafara mgana da cewa”Armm Ummi bawai ina kyamatar Lubna bane,ko na tsaneta ne ta bane,kawai ni bantabajin sonta bane,infact ma zuciyata ayanzu bata da Sha”awar sake bawa wata gurbi Ummi ,zahirah tacike ko”ina ta mamaye i don”t know How to do,..”Yafada kamar zai yi kwallah.

   Rumgumesa tayi tana fadin”Shiii…Is ok Son Ko baka bata waje azuciyartaka ba,just ka kula da ita domin ko ba komai kanwarka ce,kuma Abbanka khamis bazai ji dadi ba in kayi mata rikon sakaiyar kashi ba..”

  Ajiyar zuciya yayi ta saukewa yana kokawa da Numfashinsa kafin yace”Shikenan Ummi na,bazan iya tsallake Umarninki ba,Allah ya shigemana gaba..”Da Amin Ummi ta amsa tana sanyamai albarka kafin ta mike tana fadin”Yanzu zata dawo nan dakin da kwana,ko kawai ta shiga dakin zahirah ne”da Sauri mu”azzam yadago yana fadin”No Ummi karta shiga Zahirah fa zata dawo muhallinta very Soon,kuma in tazo taga wata acikin ranta bazai yi dadi ba zataga kamar na manta da ita ne,Tazo nan din kawai Tunda ta nace..’Yafada yana kauda kai ransa na kuna Tuni Fuskarsa ta sauya.

  Yar dariya Ummi tayi tana fadin”Oh ni Suhaima,sha kuruminka ko ni bazan bari tashiga dakin zahira ba,dakinta na nan sai tadawo kuma insha Allahu ciki zata gina wata sabuwar rayuwa akaro na biyu..”Tafada tana ficewa,da kallo Mu”azzam yabita kafin yaji komai ya ficemai aka,tattara komai yayi ya maida a muhallinsa,Toilet ya fada Afili yana fadin”Tazo gani gata,dama tashafama kantaa lafiya,domin ni Tunda na rasa zahirah nadaina jin kaina amtsayin Namiji..”????????

Ummi na fitowa falo tacema lubna taje ta kwaso kayanta ta maida Dakin mu”azzam da mamaki take kallon Ummi,gyadamata kai Ummi tayi tana fadin”eh kikoma dakin mijinki,Ki yi hakuri Lubna ki taimakeni ki kara hakuri da duk abunda zaki Fuskanta wajen Son,watarana sai lbri kinji..”Hawaye suka kwaranyoma Lubna tasaka hannu ta share tana gyadama Ummi kai,rikota Ummi tayi ta mike tana fadin”To share hawayenki maza ki haura ki kwaso komai naki ki koma chan..”Da hanzari Lubna ta haura sama,ta dauko akwatin kayanta tazo ta wuce Ummi tana fadin”Ummi sai da safe..”Allah tashemua lafiya diyata..”Ummi tafada tana binta da kallo.

Koda tashigo falon wayam tagani ba kowa sai ta karisa bedroom din tayi Nooking shuru babu motsin kowa bude kofar tayi ta shiga tana sallama,bin bedroom din tayi da kallo babu kowa cikin lokaci takarema dakin kallo komai tsaf kamar dakin mace,bata gama tunani ba taji bude kofar tiolet Mu”azzam ne ya fito jikinsa sanye da rigar wanka,kansa kuma karamin Tawel ne,yana goge kansa,dashi kallo daya yayima Lubna ya dauke kai ya isa gaban mirrior yana bude lotion din dayake shafawa yafara kokarin shafawa.

Cikin wani yanayi Lubna ke binsa da kallo,ganinsa da rigar wanka,Surarsa duk ta bayyana awaje ga kirjinsa gargasa tayi kwance luf taji ruwa,kuresa da ido tayi,shiko ko ajikinsa yana gama shafa mai yayi Cimbing din kansa,ya isa ga makeken wardrope din dake dakin ya bude ya ciro Kayan barcinsa riga da wando,pjs,ya shige Tiolet ya sa ya fito daya Fito ne yaga still tana tsaye da akwati ahannunta Tsaki yaja yana fadin”Ke in bazaki shigo bane ki koma don zan kwanta ne..”

Yafada yana hawa gado lokaci daya yana jan blanket,cikin sanyin jiki ta kariso dakin kafin ta jinginar da akwatin gefen madubin dake dakin,ranta namata Suya,ji yadda miji ke wukalantaka wai kuma kana mtsayin amarya,bude akwatin tayi ta dauko rigar barcinta ta shiga tiolet itama tayi wanka ta saka doguwar pink din rigar barcinta,Daga tiolet din tasaka abunta ta fito ta goga humrarta,kafin tamaida akwatin ta rufe gabadaya,tsaye tayi tana tunanin ina zata kwanta domin taga mai gado ya mamaye gadon yama juyamata baya,cikin sanyi jiki ta isa ga kujera kwara daya jal dake bedroom din ta kwanta ta takure jikinta waje daya mu”azzam dake kallonta tsam ya mike ya isa ga wardrope ya bude ya ciro wani blanket sabo ya mikamata hannunta na rawa ta karba tana fadin”thanks..”

Bai kalleta ba ya wuce ya haye gadon bayan yayi offlight da wutar dakin kafin ya kunna musu Dumlight addu”a ya shiga karantawa kafin taji yayi dif alamar barci ya kwashesa na gajiya itako takasa barci kwata kwata Tunaninta ya tafi ga yadda rayuwa zata kasancemata haka,tayarda ta amince matukar tana son mu”azzam yadawo daidai har ya kulata to tabbas sai Zahirah da ya”yansa Sun dawo garesa,,ita ta yarda ta amince ita din baiwar mu”azzam ce,duk abunda zai shashi Farinciiki tana kokarin taga tamallakamai Shi koda cewa ita din zata Cutu ne,to ammh taya ya?alhalin cewa Zahirah na gidan mijinta kuma shima Soyayyah yasa ya aureta..,Da wannan Tunanin Lubna barci barawo ya kwasheta bata samu mafita ba.

   Koda Asuba ma sallar kawai yatada ita,yawuce masallaci,yana dawowa yayi wanka yayi Shirin fita office,breakfasat ma agurguje yayi Shima don Ummi ta matsane,Shiysa,haka dai Suka cigaba da kwana daki daya ammh ko mgana bata hadasu dashi,wani lokacin ma da gangan tana mgana zai mata banza,banda gaisuwarta baya amsata,Bata damu ba kuma bata cire rai ba,tana kokarin kyaukyautamai AmtsayinShi na mijinta kuma wanda takeso..

Sai dai Acikin Satin datayi tare dashi ta fahimci ciwonsa ya dawo saboda tanaganinsa kullum da hoton zahirah bisa kirjinsa yake iya kwana,wani lokacin sai gabda da Asuba yake iya samun barci ba,bata dauka bayan kwana da hoton akwai wata mtsala ba,sai ranar bayan yatafi office tazo zata gyara gadon taga yadda gefen side drower tacika da Tissue duk an share jini dashi,kuma bedsheet din ma duk jini ya diga ido ta zaro cikin rudewa in bata manta conditin din likitoci ba sunce yana kokarin shiga stage din karshe na ciwonsa,wanda za”a iya rasashi lokaci daya.

  Bata tsaya wani Tunani ba ta rumtuma falo tana kwalama Ummi kira,Ummi dake zaune tana kallo ta mike tana tambayan lubnan Lafiya hannunta kawai Lubnar taja keee..Sai bedroom din mu”azzam takaita har gaban gadon tana nunamata dafe kirjin Ummi tayi tana fadn”Na shiga uku ni Suhaima,wannan jinin na waye..”

  Rausayar dakai lubna tayi kan tace”Na ya Mu”azzam ne Ummi,wlh ciwon sane ya tashi,ammh yaki nuna kowa hakan don kar ace za”a kaishi asibiti ko ki tisalstamai ya tsaya na dubasa”Dafe kai Ummi tayi tana salati kafin ta fashe da kuka tana fadin”Wayyo ni kaina,yanzu mu”azzam kashemin kansa yakeso yayi,”Tafada tana sharbe hawaye

  kafadunta Lubna ta dafa kafin tace”Eh tabbas za”a iya rasasa,akowani lokaci Ummi,domin yakai stage din karshe ne..”Hawaye suka tsinkema Ummi tace”To yanzu mecece mafita..?”

  Lubna tace”Akwai mafita Ummi..”

Ummi ta kalleta kafin tace”Menene mafitar Lubna ki fadamin bani son in rasa dana..”Tafada tana zubar kwallah

Hannunta Lubna ta riko tana fadin” ZAHIRAH ITACE MAFITA UMMI,ITAKADAICE MAGANIN LALURAR YA MU”AZZAM WANDA DATA DAWO GARESA ZAI WARKE TAMKAR BAITABA WANNAN CIWON BA..”Tafada tana kallon idanuwan Ummi.

Ummi tayima Lubna zuru kafin ta furta.”How Lubna,nasani Zahirah itace matsalan Son ayanzu but,tayaya zamu dawomai da farincikinsa alhalin zahirah na gidan aurenta..”Tafada cikin karaya,juya baya lubna tayi tana fadin”,Bansani ba Ummi,wlh Nima bansani ba..”Take fada tana share kwallah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button