NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

   Suna ta hayaniya da ihun murna sakinsu yayi yana musu alama da suyi shuru yana kallon Abbie yace”Abbie kufara shiga,ni sai shigo daga baya”haka ko akayi su Ushe suka kwashi kayansu sukayi cikin gida suna murna su Abbie suka rufamusu baya,shiko mu”azzam tafiya yafarayi ahankali yana bin ko”ina da kallo yadda fulawoyi suka bushe wasu ma sun mutu,komai na gidan ya chanzamai,gabadaya gidan ya yi kura,motocin hawansa kuwa duk sunyi kura alamun ba”a hawansu kenan,kwallah ta ziraromai yayi Saurin Sharewa.

   Da murna Su Ushe suka shiga falon,hajiya ce kadai ke zaune tana kallon Tashar Arewa24 anayin Shirin nan na akushi da rufi,suka shigo da mamaki take kallonsu kan tace”kai daga ina? wayan nan kayan fa.?.”Sani yace”Hajiya bakin Sudan ne,kuma da..”Falalu ya bige masa hannu yana fadin”ba”ance ayi shuru ba tukunnah…”Kallonsu hajiya tayi kafin tayi mirmishi zatayi mgana kenan Abbie yayi sallama ya shigo falon bayan sai mooh kafin mom da lubna subiyo bayansa dauke da sallama abakinsu.

  Da hanzari hajiya ta mike tana fadin”La ba shakka kuwa,sannnunku da zuwa marabanku da bakin lrabawa”take fada tana washe baki cikin murna da farinciki kafin tahau kwalama Ummi kira tana fadin”Suhaima,maza ki fito ga khamis yazo shida iyalansa gabadaya..”

Ummi dake sama,taji mganar hajiya daga sama,ahanzarce ta sauko bakinta yaki rufuwa tana fadin”a”a maraba maraba masha Allah,..”Take fadi tana saukowa daga saman Stairs cikin Farinciki wanda rabon datayi tun kafin tafiyar mu”azzam.

  Tana Saukowa ta isa ga mom ta rumgumeta tana fadin”,Lale marhababika yar”uwata..”Rumgumeta mom tayi tana amsamata cikin harshen labarci,kafin ta saketa ta isa ga lubna tana fadin”Ko ban tambaya ba,wannan diyata ce ko”kai tadagamata tana mirmishi kwallah ya cikamata ido Rumgumeta Ummi tayi tana yafito Mooh da hannu tana fadin”Kaima son taho nan na ji duminka,Allah sarki inama dan”uwanku na nan Da naga tsantsan Farincikin dazai shiga na ganinku..”

Tafada kwallah na ziraromata,karisowa mooh yayi ta hadasu ta rumgume tana kwallah,kafin akoma afara gaisawa cikin Farinciki,Ummi da kanta ta shiga kichen ita dasu lami suka hau jido ma su Abbie kayan motsa baki,dana tande tande kafin adora musu girki,Yau din Ummi tana cikin Farinciki sosai wanda har yakasa boyuwa bisa fuskarta.

  Mu”azzam dake bakin kofar falon yakasa hakuri,bai san sadda ya fada falon ba,da Sallamansa cikim muryansa mai cike da zati Ummi dake duke tana zubama su Lubna lemo ta dago da Sauri domin ko amafarki taji muryan Mu”azzam zata shaidata,gabanta ne yayi mummunar faduwa lokacin da idanunta sukayi arba da mu”azzam tsaye kikam yana kallonta yana hawaye,sanye yake cikin american Suit dark blue and white,Fuskarsa tayi fayau yakara fari kuma ya rame sosai kamar ba shi ba,mirmishi yake yimata hawaye suna gudu bisa kuncinsa.

  Kofin glass din dake hannun,Ummi ya subuce ya fadi,tana hawaye take fadin’,”Nasan gizo kakemin son..,kamar yadda kasabamin,’Take fada tana kuka tana ja da baya,inda take nunawa suka bi da kallo da hanzari hajiya ta mike tana fadi da karfi..”wanake gani kamar mu”azzam..”? Hajiya ta fada tana dafe kirji.

Abbie khamis yace”Ba kama bane hajiya shine..”yafada yanamata mirmishi ai da wani gudu hajiya ta karisa kusa dashi tana fadin”Ibrahim mu”azzamu…”Tafada hawaye suna zubomata,Mu”azzam dake tsaye baisan sanda ya fada jikin hajiya yana fadin”Na”am hajiyarmu nayi kewarki..”yake fada cikin kuka,Rumgumesa hajiya tayi kafin ta waigo tana fadin”Wlh Suhaima mu”azzam ne,shine ..”Take fada tana dariya lokaci daya da hawaye

  Ummi data daskare atsaye tana bin mu”azzam da kallo ta nuna sa tana fadin”Mu”…az…zammmm…..”Tafada cikin kyarman baki,da gudu ya saki hajiya ya isa gareta da wani irin Rumguma ya fada mata yana fadin”Ummi nah..”Yake fada yana kamkameta kawai sai ji yayi Ummi ta sulale daga jikinsa tasume,cikin tashin hankali yake jijjigata yana fadin”wayyo Ummi na,ki tashi gani na dawo bazan karayn nisa dake ba..’yake fada yana girgizata.

  Lubna ne,ta isa ga fridge ta bude ta dauko Ruwa mai sanyi tamika ma mu”azzam ya shekama Ummi yana shafa Fuskarta yana hawaye ajiyar zuciya Ummi ta sauke kanta ta bude ido tana bin mu”azzam da kallo hawaye na kwaranyomata,yasaka hannu ya sharemata yana fadin”Stop craying Ummina,bazan sake tafiya in barki ba..,”Yafada yana riko hannunta.

Damke hannunsa,tayi Tana fadin..”Son,why..? take fada tana kwaranyan hawaye Rumgumeta Mu”azzam yayi yana fadin”Ki yafemin Ummina,na tuba bazan kara ba”Rumgumesa Ummi tayi tana kukan tana fadin”Ka yafemin Son,namaka laifi na muzgunama rayuwarka daga karshe nayi sanadiyar rabaka da matarka uwar ya”yanka,wlh sai bayan tafiyarka nasan kaine rayuwata,bazan taba jin dadi rayuwa ba,in baka,ka yafemin don Allah..”Take fada tana kuka.

  Dago Fuskarta yana sharemata hawaye yana fadin”bantaba rikeki koda da rana daya ba Ummina,wlh Allah dayane banji ko digon bacin rai ba,game da hukunciki gareni,kawai wani abu ne da zuciyata ta kasa dauka,Ummi zahirah tana da wani gurbi azuciyata wanda rashinta agareni tamkar rasa wannan gurbin ne,ki yafemin tafiya danayi na barki Kinji Ummina,na dawo bazan kara barinki ba”kamkame juna sukayi Ummi na fadin”Bakamin laifi ba Son,nice nan nabatamaka,kuma nayi nadama na gyara kuskurena bazan kara ba,Allah yamaka albarka Ibrahim yajikan mahaifinka”Take fada tana kuka,shikuma yana sharemata kwallah yana fadin”,Amin Amin Ummina.”

  Duk wanda ke falon sai da ya zubar da kwallar tsausayi,lubna takura musu ido tana kallon tsabar kauna da shakuwa ta uwa da da,wanda ko afinafinai batataba gani ba,lalle bakaramin shakuwace atsakaninsu ba hayaniyarsu ce ta fito dasu karime daga kichen ganin yallabai yasa suma suka rude da kukan Farinciki karime na sharbe kwallah tana fadin”Yallabai ina katafi kabarmu,gida yayi kewaarka,kabar hajiya cikin tashin hankali da damuwa,wlh yallabai mu kanmu muna rayuwa ne,ammh zuciyoyinmu babu dadi saboda rashinka,”yana mirmishi ya riko hanunta yana fadin'”Insha Allahu bazan sake tafiya ba,nima ina chan ne,ammh ruhina da zuciyata yana tare daku..”
   

  Gabadaya ma”aikatan suka taru afalon suna nuna jin dadinsu na dawowar yallabai,wanda hakan shi ya tabbarma Da Abbie cewa mu”azzam yana da kirki kuma adalin megidane ga wadanda ke karshinsa,sallamansu Ummi tayi kafin tabada umarnin Su karime su gudnaar da launinka Abinci kala biyar saboda baki,jikinsu na rawa suka wuce suna mai bayyana murnansu matuka na dawowar yallabai gida.

  Nan take Abbie bai boyema Ummi komai ba yafadamata tun zuwan mu”azzam garin da halin dayake ciki da taimakon da Lubna tayimai da kawosa gidansa,har zuwa abunda yafaru da aurensa da lubna duk ya fadamata ya karishe da cewa”Abunda yasa zuwan danayi ban fadamiki ba,saboda alqawari na daukan ma mu”azzam banzan fada miki yana wajena,ba ammh harga Allah danazo na ga halin da Suhaima ke ciki sai naji kamar na fadamata gaskiya,girman alqawarin danayi masa ne,yasani kin fada,ammh na kuduri niyar ina komawa gida zan mtsamai yataho mudawo tare dashi.

Kowa afalon Shuru yayi hajiya ta gyara zama tana fadin”lalle kowani bawa danashi kaddaran,wato dai kaddaran haduwa dakai ne,ya fitar dashi daga gida,tare da kaddaransa na Aure lubna,in mukayi duba da duk abubuwan dasu faru,lalle Allah shine masanin komai ba,Allah ya bada zaman lafiya,kai kuma kayi hakuri in kuna da rabon sake zama da juna da zahirah wlh zaku dawoma Juna,Hakuri zakayi ka cire komai aranka haka Allah ya so..”Ummi dake gefe tana nanike da mu”azzam da kallesa tana fadin”kayafemin Son,duk nice silan komai,Da…”Shii…”Yasaka hannu bisa bakinta yana fadin”Bake bace Ummina,Komai dayafaru daga Allah ne..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button