NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

    Suna komawa mu”azzam yabada kudi aka siyoma yakura atamfofi da lesuka da da dogayan Riguna,aka bata aka dinkamata,da sabon hijabai,da takalma masu kyau,kaya kamar zasu bude shago,tare da Ummi suke zaune adaki daya saboda Ummi ta bukaci kodon ta dinga daukema Yakura kewa da kadaici,to babu laifi dukkansu suna iya bakin kokarinsu tunda yanzu tafara sakewa dasu.

Cikinsu su zahirah yanata girma,mu”azzam bai gaza da kulawan dayake basu ba,sai ma Abunda yakaru,yanzu haka na zahirah yana wata na shidda ayayinda na Lubna ke wata na biyar,dukkansu cikin nasu ya fito yayi kato mussaman ma Lubna don zahirah dama bata da girman ciki,mganar shirye shirye biki kawai sukeyi tunda anan gidan za”ayi sha”anin Sai angama biki ango da amarya dasu Abbie su koma sudan tare ko kayan aure mu”azzam yahadama Mooh din ,Odar sukayi daga Dubai akwatuna 22 duka shake da kaya,zahirah Abun ya hademata gata barayin ango gata babban kawar amarya,tuni Asma”u tabaro sokoto gabadaya,saboda dama aji daya take batayi nisa ba,yanzu an bari ne sai takoma chan Sudan din mijinta ya neman mata wata ya sata,takowani bangare Shirye shirye ke gudana babu kama hannu yaro,abunga da masu dashi komai cikin kwanciyar hankali ake gudanarwa.

Mom biki yarage saura sati biyu tazo ita da kannenta guda biyu su mooh da Abbie sai satin gaba,taji matukar dadi lokacin data kayan alherin da mu”azzam yayi mooh tayi godiya sosai,nan take su little suna maiduguri,duka gidan sun sha kewarsu saboda sabo mussaman ma Mu”azzam da lubna sunfi jin jiki saboda yaran sunfi shakuwa dasu fiye da uwarsu,to ammh kowa yaji sai yace ai babu damuwa gasunan da ciki haihuwa yanzu sukasa kafa,tunda dukkansu yarane dagashi har matansa Sai dai fatan Allah ya saukesu lafiya.

Comment
Share
Vote

   Janafty

UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

NOT EDITED????

        NO 49

    “Sati daya ya rage bikin,mooh da Abbie suka diro Nageria tare da babban Aminin mooh Mutallif,Hakika Abbie yaji dadin Alherin Mu”azzam nan yayi ta sakamai albarka,sai zuwansu ya samu yima yakura gaisuwa sun dade tare yana ta bata baki tare da nasihohi,masu ratsa jiki kan tayi hakuri tadaina ma baffa kuka domin yanzu addu”anta kadai yake bukata.

Washegari suka kai kayan gidansu Asma”u dama Abunda yahanasu kaiwa saboda ana jiran zuwa Abbie ne,lalle sunga inda ake arziki gidan masu dashi,nan akayi musu sha tara na arziki Ummi da mami dama ansan junan nan aka hadu ana ta barkwaci babu nuna bambamci,zahirah ko da lubna na tare da amarya don dasu akazo kawo kayan,sunci sunsha da kayan lashe lashe,nama ko,nako wani dabba akwai shi sai wanda kazaba,Abinci kuwa Sai wanda kaga damar ci,gasunan kamar a Hotel sai wanda ranka yayimaka zaka diba,basu bar gidan ba sai yammah harda Tukwaicin dubu dari biyu daga Uban amarya,Ada sunki karbane minister da kanshi yakira waya aka hadasa da Ummi yace dole su amsa,domin ko nawa yabasu bai gama biyansu alherin da sukamai ba,shida zasu auranmai diya,ai babu babban alheri irin aga naka kuma ayaba ace ana so har aso hada zuru”a daga nan fa Ummi tayi ta godiya kafin suyi sallama,Kayan ci dasha kuwa sai da aka sa masu aiki suka zuba musu a booth suka taho dashi suna bada lbrin Dimbin kirkin mami da manister,lalle Mooh yayi dacen mata matukar tayi gadon hankali da kirkin iyayanta.

Ana Saura kwana uku biki Tuni gida ya cika da yan”uwa da abokan arzuka Abun mamaki sai ga hajara matar Alhaji kabir tare dasu little Ummi da moodu wanda suka kara wayau sunyi kiba gwanin ban sha”awa alaman suna samun jin dadi sosai,tare da mahgana suka taho,da Ashe,su Ummi sunyi murna kwarai da gaske,nan da nan suka shiga cikin mutane anata shagalin biki,Ana gobe biki amarya tayi kamunta,wanda zahirah lubna da Zulaika matar Shureim wanda sukazo ana gobe daurin Auren,Kamun yayi kyau domin iya haduwa ya hadu sai wanda yagani,Anan zahirah tahadu da yan ajinsu wanda Tafara Nurul bayyah dasu nan fa suka yamaimayeta cikin mamaki ana gaisuwan Yaushe rabo da juna,sai dare suka dawo gida da kayan kamu niki niki,Su little Ummi ko sun iya kiran Mama da baba,da gwarancin mganarsu harda Ummi sunyi iya fadi,Dasukaga mu”azzam da gudu suka nufesa suna fadin”baba,baba..”yakamasu ya rumgume yana dariya tare da kewansu,ammah fa sun shaku da hajara don duk inda take suna manne da ita,hidima ko Alhaji komai ya samu sune,ko gajiya bayayi,Yan”uwansa sunso zuwa har Abuja yima mu”azzam godiya Shiyahana awaya sukayi mgana harda inna tayi tamai godiya yana amsamata da babu komai,wlh matarnan harda hawayenta tana sakamai albarka tana rokon yadda yasaka kabiru farinciki Shima Allah ya sakashi.

Washegari Ranar Daurin Aure karfe 11:30am na safe aka daura auren Amasallacin dake cikin villa,Daurin Auren daya samu hallatan manyan mutane yan”siyasa ministoci,da gwanonin Arewanmu kaf,ba wanda baizo ba harda lauyan lauyoyi,da lauyoyin kansu,da yan kasuwa,harda maigirma Shugaban kasansmu na yanzu dashi aka Daura Aure wanda sune ma agaba,gaba wajen bada Aure tareda gwanoninmu na arewa,babu ruwana bazan kama suna ba azo har zaria ayi ram dani takan Rubuta Uwar mijina????????????

  Bayan Daura Aure akayi walima ta maza anan cikin villan kafin kowa ya watse yakama gabansa,tawagar ango kuma suka koma gida inda Sha”ani yake,babu wani bata lokaci da la”asar aka dauko amarya daga gidansu zuwa gidan mu”azzam nam zata zauna kafin Su wuce,da daddare akayi wata lafiyayyiyar Dinner mai rai da lafiya,zahirah itace amatsayin babban kawa,ga cikinta Ga less din data saka dinkin doguwar riga duk inda tabi sai binta ake da kallo,kishi yakama mu”azzam dole yasa aka soke wata babban kawa yakama matansa suka kebe waje daya suna zaune,shida Shureim wai su adole manya sun girma????an ci,ansha kuma anyi rawa tare da barin dukiya kafin 12 na dare nayi aka tashi kowa yakama gabansa,washegari Ummi ta shirya walima akayi wa”azi tare dayima amarya nasiha,da kuma tsoratarwa akan zaman aure da hakkin miji kan matarsa da shi kanshi hakkin matan kan mijinta,nan ma anci ansha kafin atashi daga walimar,washegari kuma minister yaba sanarwan jirgin yawo guda daya wanda duk mai bukata yazo atafi sudan dashi,nan fa yan”uwa aka shirya domin wannan karan zuwan na mussaman ne,Acikin masu raka amarya Asma”u bayan yan”uwanta guda hudu,dangin babanta biyu na Ummanta biyu,sai tawagar mu”azzam duka iyalansa da Ummi,sai yakura da Hajiya da Shureim Shima da iyalansa sai mom da Mooh dashi kanshi mu”azzam din harda mahgana da bukar da hajara da su little Ummi,da Alhaji kabirun shi kanshi da Dr,Abduljabar da abokin mooh Mutallaf,sai Abbie Jirgi dai guda kuma duk da gudummuwan minister ne,Da daddare suka tashi aka bar gida daga Ushe sai Falalu dasu karime dake cikin gida.

  Hakika Ummi ta tsinci kanta cikin Farinciki lokacin da hancinta ya shako mata iskan kasar na Sudan,rabonta da kasar tunda tataka ta bi moodu,Sai yau Allah yayi dawowarta shekara Talatin da biyar da wani abu,ko”ina na kasar ya chanzamata,Gidan amarya aka Wuce direct Wani makeken gidane sama da kasa,wanda ma”aikatansu mooh ta bashi,gidan yaji komai na alatu rayuwar Duniya in kashiga gidan kamar kana Aljannahr Duniya,babu wanda ya kwana gidan Amare duk gidan Abbie aka dumguma akaje aka baje zama,akaci abinci kowa ya shiga daki ya kwanta yana warware gajiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button