NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

  Lubna kuwa itama ya”yanta biyar bayan su momi,tayi Shureim da Hannatu,sai na karshensu Mai sunan baffa sheettima suna kiransa da Baffa,ayamzu haka gidan na CHAIRMAN OF BAR ASSOCIATION OF NIGERIA(wato Shugaban lauyoyi na kasa baki daya) MU”AZZAM MUHAMMED MOODU cike yake da ya”ya Alhamdulillah koda Ummi tsufa yakamata da manyanta bata daina godema Allah ba,domin koda ta haifi mu”azzam Shikadai yau gashi sanadinshi ya tarata mata zuru”a masu yawa,bayan tsawon wannan Shekarun anyi rashe rashe,Yakura da hajiya baraka  Allah yayi musu rasuwa shekara shida da suka wuce,wanda rashinsu wani Abune dabai zai taba goguwa azukatansu ba,domin sunyi Rashi babban musssam Ummi wacce tazama ita kadai ta rage acikinsu.

Ayanzu haka basu a gidansu na maitama Abuja,suna garin lagos cikin wani dankareren gida mallakin mu”azzam din mai hawa biyu ne,gidan indan ka shiga tamkar kana Aljannar duniyace saboda tsaruwa da kyau da tsari basu dawo da kowacce yar aiki ba,duka mu”azzam ya sallamesu da kudi mai yawa duk sun koma garinsu cikin ya”yansu ,Ushe kuwa tuni ya musulunta shima Mu”azzam yayimai aure ya siyan mai gida yabashi jari shima yakoma garinsu haka sani maigadi da falalu suma haka yayi musu aure ya siya musu gida yabasu jari kowanne yakoma garinsu ammh haryanzu da mu”azzam dake wannan mtsayin bata chanza zani ba,yana nemansu in zai musu wani alheri.

  Dr,Shureim yazama babban Consultan a Babban asibitin ABU dake Shika,bayan Rasuwan hajiya yasamu cigaba sosai afanin rayuwa,yananann zaria sai dai cigaba da chanjin muhalli daya samu,yanzu haka ya”yansa biyar don shi haihuwan nasa ya tsarasu ne,Sai Dr,Abduljabar shiko Tuni yana kasar India tunda wani asibiti ta gayyaceshi aiki na shekara biyu bai dawo ba,chan yayi zamanshi yacigaba da aiki dasu,yayi aurensa da wata ba indiya, ba musulma bace,ya musuluntar da ita ya aureta,ammh har yanzu basu daina zumunci da juna ba,Mutanen sudan kuwa,Tuni Asma”u itama tazama kargen ya”ya,domin haihuwanta Hudu itama tayi duka mata Suna zuwa Nigeria domin sun maidata kamar gida wajansu,saboda tsufan dayakama Abbie sai mu”azzam yahanaa zuwa su suke zuwa duk lokacin da yuyuwar haka yataso.

Alhaji kabiru kuwa haryau Allah bai bashi haihuwa ba,ammh kyautar da mu”azzam yayimai ya mantar dashi bai haihuba,duk da Su little din sunsan cewa bashi ne mahaifinsu ba,ga asalin iyayansu chan,basu taba chanzamai,sun daukeshi amtsayin mahaifi na hakiki Shida hajara wacce suke cema mamanmu,sai Alhaji Babanmu,duk gatan duniya babu wanda basu dashi sai dai su bawa wani,yanzu haka suna da shekara goma sha hudu aduniya ne,dukkansu sun kammallah Secondry sch dinsu moodu mktantar Sojojin kasa yagama wato Command seconry sch Kaduna,sai Little data kammallah Nigerian Turkish acadmy dake nan cikin garin Abuja yanzu haka suna lagos ne sunzo hutun karshen shekara wajen iyayan nasu,tunda iyanzune,zasu iya samun duka iyayan nasu agida,saboda sai karshen shekara suke samun hutun wato Annual leave kenan.

Wannan kenan.
   


  Zahirah ta shiga kwalama moodu kira tana fadin”Ina kake,Fitowa zakayi kuzo ku koma gidanku wlh mun  gaji da hutu,ina dalili daga zuwanka sai faman zaluntarmana ya”ya kakeyi bazai sabu ba,kuzo ku hada kayanku koma gidanku..”

Wanda Aka kira da moodu ya fito daga cikin wani bedroom yana tura baki,wani dogon yaro na gani Fari ne tas kallo daya zakamai ka gano babu inda yabar mu”azzam akammanin hatta yanayin tafiyarsu dayane sanye yake da riga da wando na kamfanin armani Ya dago daradaran idonsa yana zabgama baffa dake jikin zahirah yaLafe harara kan yace”Momi baki ga barnar dayayimin ba,system din ya buga akasa ba,shine bazan dakeshi ba,wlh momy yaran nan yafi kowa kinji agidan nan..”yafada kamar zai yi kuka,dakuwa tayimai tana fadin”kaga nakanan,kai bakayi Rashin jin bane,kuma in kanason kayanka meya hanaka ka adana Abunka,kaima da gangan kayi kasan in suka gani basu bari ba ko,? to Allah karka kara dakanmin yaro,in ba haka ba na ramamai kaji na fadamaka..’

  Tura baki moodu yayi kafin yace”Naji momy..”yafada yana karisawa kusa da wata yar budurwa doguwa farace itama bata da kiba siririyace sosai,tana zaune kan kujera tana latsa waya tana sanye da riga da wando na kanti kanta babu dankwali sai gashinta mai dauke da kitson kalaba yazo tagaba da bayanta,wayar ya fizge yana fadin”lil sis Say some thing wlh am tired da zaman gidan nan ,Abbah yayi yara da yawa wlh..”yafada yana bata rai,sai yanzu ta dago kai wazan gani da badon Fuskar yarinta ba,sai nace Ummi ne,saboda babu abunda yarabasu da kammani,yamutsa fuska tayi kan tace”Wlh me too bruh,juz call babanmu kafadamai wlh mungaji da gidanan,yaran nan sun damemu da hayaniya gasu yan gata iyayansu basu son laifinsu,mamanmu tazo tatafi damu ko mubi Flight din maid gobe mu koma ko ya kace..”gyada kai yayi yana fadin”Haka za”ayi zan kirasa yafada yana mikamata wayarta ta amsa tacigaba da Abunda takeyi daga ganinta bata da son hayaniya rike baki zahirah tayi domin tanajin Abunda suke cewa,..Kallonta moodu yayi kafin ya dauke yana daure fuska,kada ma momy tace wani abu suma sun gaji da gidan,gidansu zasu koma inda daga su sai babansu da mamansu babu mai takura musu.

  Lubna ce ta fito daga daki,tana sanye da wata shadda doguwa dark blue medicated glass a idonta tana fadin”Anty wai yau lafiyan,Daddy kuwa,bai fa tashi ba tun bayan dawowarsa daga sallar asuba..”Hannu Zahirah ta yarfa tana fadin”bari kedai yanzu nashiga na taya Amina hada breakfast din,na fito da niyyar zuwa tasosa,Sai baffa ya fito da kuka babbam kwabo yaci zalinsa..”Dariya lubna tayi tana kallon moodu da little da suka wani hade rai suna mgana kasa kasa,karisawa tayi tana fadin”wlh gwanda ya dinga dukansu yara saboda rashin jin kamar masu amfani da inji..”Tafada tana zama kusa da moodu ta rumgomosa tana fadin”Srry momy ce ko? ku kyaleta kunji..”Dora kansa yayi kan kafadanta kafin yace”Dat my mami..l love u buh mu gobe zamu koma gida mungaji..”yafada yana kallon Little gyadai tayi kafin tataso itama ta zauna kusa da lubna sun sata atsakiya kowanne yadora kansa bisa kafadanta,fuskarsu take shafawa tana fadin”ku kyaleta zamu kai karanta wajen Daddy in ya fito zai hukuntata..”Tura baki little tayi tana fadin”Umh mami tab,ai gwanda kifadama namecy na,Daddy dabayaso  laifin momy ko kadan..”dariya Lubna tayi tana kara rumgumesu tana fadin”Nikuma banison laifin ku ya”yana so ku kwantar da hankalinku babu mai kara mtsama muku acikin gidanan..

tsaki zahirah Taja kan tace”Mtseeww..,Kike biye musu Allah raka taki gona in banda fin karfin in akataba zaluntar dan gida kuna baki,wlh mun gaji kuzo ku koma gidanku ya”yana suma su samu sakewa..”Waye ake kora haka..? Sukaji anfada daga bayansu dukkansu suka waiwaya jin muryan Daddynsu Koda na waiga mu”azzam nagani yazama Dattijo dan kimanim shekara hamsin da Duriya Abun mamaki kansa haryafara Farin gashi,yana sanye da bakar jallabiya da wani Siririn Farin glssa,wanda yakarama Fuskarsa kyau,yakara fari da manyanta,ammh fa kwarjin nan nashi na nan da cikar zatinsa.

  Da hanzari baffa ya karisa yana fadin”Daddy…”Shabesa mu”azzam yayi yana fadin”Na’am Baffa na,how far..’Kwabe fuska yayi kan yace”yaya ya dukeni..”yafada yana nuna moodu wanda ke zabgamai harara,Kallonsa Mu”azzam yayi kafin yace”ok dakai Mommynku ke fada ko,meyasa kacika saurin hannu ne,Abbana..? Lubna tace”Laifinsa zaka gani,bazaka tambayi meyayi mai ba..”Harara ya sakarmata kan yace”Bazan tambaya ba,uwar son kai bakison laifin yaran nan, sam mamin yara,komiye yayimai Aishi babbane sai ya kyaleshi yaci girma ko..”Little ce ta mike tana fadiin”Wlh Daddy akomai sai ka nuna sonkai kan duk Abunda momy tace akai,kusha kuruminku goben nan zamu barmuku gidanku ko bruh..”gyada kai yayi alamar hakane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button