NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

   Mahgana dake gefe tace'”Ja ma kuwa wlh”Tafada cikin damuwa zahirah data daskare zaune tanajin wani lbri mai kama da mafarki takalli Yakura hawaye sun wanke mata fuska tace”Laifiin Umma ne dana Baffa ya shafe ni ko”Tafada cikin sagewa kafin tagyada kai tace”Insha Allahu zanyi,kuma zan iya,zan zauna kodan cikama baffan burinsa inafatan koda zan dawo sai in Ummi ta gafarta musu abunda suka mata”Tafada cikin karfin gwiwa ammh hawaye sun kasa tsaya mata.Mamaki yakamasu ganin yau zahirah tayi mgana har ta wuce kalma goma lalle abun babbane,kara mata nasiha sukayita da shawarwarin domin gobe tunsafe suke son komawa zahirah dai kuka kawai take ammh kuma tana nuna karfin hali,akasan ranta kuwa data tuna kallon da Ummi ke jifanta dashi sai Taji cikinta ya murda.


   Ummi kuwa tana shiga daki tafada bisa gado tana kuka kamar wata karamar yarinya babu abunda take tunawa sai yadda suka zo Nigeria kamar haka tare da moodu da Khamis tana mararin rayuwa mai inganci,rayuwa da masoyinta na har abada,sai gashi fadi da shettima suka suka taru suka ruguza mata dukkan Farincikinta tunda kafarta taka gidan nan,bata taba farinciki ba kona minti daya ba,shikanshi moodun bai samu daman sakewa da ita ba,har yabar duniya,ko cikin mu”azzam rabo ne kawai daga Allah,ammh da haka zai bar duniya ko kwansa bai ijeba.

   Tadade tana kuka kan ta share hawayenta Tiolet ta fada ta dauro alwala,kafin tazo tadata sallahr la’ssar domim ta gabato ammh idanun nan nata sun kumbura sunyi luhu luhu alamar tasha kuka,.

   Har dare babu wanda yaji duriyan Ummi hajiya ne da zulaika keta hidima dasu Yakura ko mu”azzam tunda ya shiga daki zazzabi ya rufesa Shureim ne ya dubasa yamasa allura dayake suna da first Aid box agidan,ko sallolinsa  cikin dakin yayi su gabadaya jikinsa baimai dadi abinci ma sai da hajiya ta matsa kana yaci,sai yamzu yakara tabbatarwa wlh Ummi ce mahadin rayuwarsa Fushinta kadai dafi ne agaresa.

  Haka dukkan zuciyoyi suka kwana babu dadi,Ummi ta kwana kuka da nadamar ma amincewa da auren datayi ma gabadaya,shiko mu’azzam ya kwana cikin zullumi da damuwa da Halin da Ummi ke ciki,shibama ta amarya yake ba,don Tunda suka zo Ko dakin bai leka ba, ba,Itako abarayin baiwar Allah Zahirah har su yakura sukayi barci idanunta biyu,maganganun Ummi kadai kemata yawo bisa kwanya wanda ko muryanta ta tunano sai tsikar jikinta ya tashi,saboda tsabar yadda ta tsorata da ita,tanaji ajikinta karshen tane yazo domin yadda taga idanun Ummi kwata kwata babu Rahama balle ragowa.

•°•°••°

      Garinn Allah na waye da wuri su karime suka kammallah breakfast hajiya ta umarcesu da sudiba sukai barayin zahira amarya,wacce suma suka tashi da wuri suka gyara kansu bayan sun gyara zahirah wacce tunda tatashi ta dasa kuka,lura datayi su yakura fa, yau nan zasu barta tareda Ummi ai sai Allah.

  Itama hajiyan suna gama karyawa suka fito domin Shureim nason zuwa aiki aranar shiyasa,lokacin da suka fito zasu tafi ne hajiya tashiga har dakin Ummi ta mata sallama tareda Nasiha na nunamata kawai tayi taji,ammh kasan ranta ko sauraran hajiya batayi,har haraban gidan Ummi ta rakosu bayan hajiya ta shiga gun su yakura ta musu sallama,suma suka ce yanzu zasu tafi,mu’azzam din suke jira,hajiya tama zahirah nasiha sosai kafin tafito cike da tsausayinta aranta tana fadin”Wayyo Sun sa yar yarinnya cikin mtsala.”

   Su karime dasu lami harda su arakiyan, Shisshiga mota sukayi Ummi da mu’azzam suna zuba musu godiya ita da surikarta Zulaika,suna tsaye suka zuba hon sani maigadi ya wangale musu get suka fice sukuma suna daga musu hannu,Ummi dake tsaye tajuya zuwa cikin gida,mu”azzam dake bayanta sanye da bakar jallabiya yayi saurin binta ya cinmata yana fadin”Ummi na barka da safiya”

  Shekeke ta kallesa kan tace”Yauwa..”Agajarce kamar bataso takuma yi saurin yin gaba ta barshi cike da takaichi yabita da kallo kafin kawai ya kada kai zuwa ciki,dakinsa ya wuce direct yaje yayi wanka ya shirya cikin ,wani yadi fari mai tsantsi wanda hatta farar singlete dinsa ana gani,bai saka hula ba yafito zuwa falon,kai tsaye dakin da”aka ijiye zahirah ya tura tare da sallama.

    Dukkansu suna falo zahirah na zaune akasa sanye da farin hijabi babba ta rufe jikinta kuka take ta shirba yakura da mahgana suna tsaye da alamun Nasiha suke mata,amsa sallamar sukayi suna gaisheshi da kwana cikin girmamawa ya gaishesu yana fada musu cewa basu,ganshi jiya ba, wlh suna karisowa zazzabi ya rufesa sai yanzu yaji dama dama.
 

  Fatan samun lafiya suka mai kan yakallesu yace”Badai kuma kun shirya ba”Yafada yana kallon akwatunsu dake gefe,yakura tace”Insha Allahu kuwa mu”azzam mai zamu jira tunda komai ya kare sai fatan zaman lafiya” Jin haka yasa ya jinjina kai yana fadin”To hakane ku fito kuyi sallama da Ummi yanzu direba zai zo yakai ku tasha yasaka ku a mota”jin haka yasa yakura cewa”Yauwa dama kuwa yanzu nake shirin maka mgana zamu kai Zahirah gunta bisa al’ada” Mu”azzam najin haka ok kawai yace ya fice wanda tunda ya shigo kallo daya yama zahiran ya kauda kai aransa yana mamakin kamar mai ciwon kuka duk sanda zai ganta tana cikin kuka,ganin ba damuwarsa bane yasa ya kauda kansa yana wani basarwa.

   Yana fitowan Falo yaci karo da Ummi zaune kan daya daga cikin kujerun falon ta dora kafa daya kan daya tana,girgizawa fuskarnan tata babu Annuri ko kadan,kallo daya,mu”azzam yayi mata ya dauke kai saboda yadda gabansa yafadi yana fatan kada Ummi ta gwada hali gabansu Yakura.

   Suko suna fitowa yakura rumgume da zahirah,ganin Ummi zaune yasa tace”ah kina ma nan ashe”Tafada suna karisawa akasa suka zaunar da zahirah kusa da kafar Ummi wacce ta zabura ta janye kafarta tana fadin”ah karki tabani..”Tafada lokaci daya tana matsawa mu”azzam dake tsaye yakalli Ummi ya lamgwabar dakai tako banka masa harara wanda dole yakama hanyar ficewa yana kokarin kiran Ushe da wayar dake hannunsa.

  Mirmishin yake yakura tayi kafin tace”Toh Suhaima mu zamuyi harama don kinsan garinmu da nisa,ga amanar zahirah nan,kin dai san ko bata auri danki ba,yatake agurinki ko,?to mudai mun damka miki ita kowani riko kikayi mata wannan ya rage naki ke kuma zahirah kiyi mata biyayyah kinji..Uwatake agunki,ko badon kina auren danta ba,Allah yabaku zaman lafiya”

  Inkunce tak Ummi ta tanka sai ma kara volume din Telebijin,datayi tanayi tana kada kafa,mahgana da yakura suka kalli juna kafin su mike jikinsu asanyaye,yakura tace”To suhaima Allah sa mugana don Allah akara hakuri zahirah dai yarinyace” Tafada cikin karaya jin sun mike yasa itama zahirah mikewa tana kuka ta malkalkalesu tana fadin”zan biku,kada ku barni anan BAN SABA BA…!”

     mu’azzam dake tsaye bakin kofar falon tundazu yaji kawai lokaci,daya tsausayin yarinyar ya tsirgamai, barinnma yadda take ta kuka tana karsu barta anan,Ummi dake zaune ta kwalama karime kira,da hanzari karime ta fito tana fadin”Gani hajiya” cemata tayi taje cikin dakinta kan side drower zata ga kudi da wata leda ta daukomata,da hanzari karima tatafi ba jimawa sai gata da rafar kudi yan dubu dubu har guda biyu,da leda cike da kaya, duka tahada ta mikama yakura tana fadin”mungode sosai,da cika alqawari,ga wannan babu yawa,kiyi amfani dashi” yakura tace”Suhaima kuma harda,wani dawainiya”mirmishi Ummi tayi kan tace”a”a ba dawainiyyah bane,kinsan alheri danko ne baya faduwa kasa banza alherinki gareni har yau nakasa mantawa dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button