UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL
UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF
Shiko Shettima Koda yakura tace haka yajitace ne kawai ammh bawai don ya yarda ba,domin yafi kowa sanin wacece Suhaima shiyasa kai tsaye yace”Lamarin zai daidaita ammh ba yanzu ba yakura kamar yadda kika fada ba:”jin yace haka sai ta kallesa tace”Ah to ashe kanama son komai shine kake tambayana ai bai kamata kanemi karin bayani ba,Cutane dai kam acucu yahna sai dai Fatan Allah yabata ikon cin jarabawa,tana gama fadar haka ta shige daki tana kuka,shiko Shettima tasbihi yake tayi cikin Ransa yana jin a jikinsa komai zai daidaita lokaci kawai yake jira.
Hakama Washegari Tunsafe Zahirah tatashi bata koma ba,dama Tunda tazo gidan bata taba barcin Safe ba,Tunkan Hajiya ta sauko Karime ta tatayata suka gyara falon Tas,karime tayi mopping dinshi ta kunna Turaren Wuta,dakin Hajiya ne sai ta sauko daman dokarta kenan ba”a Tashinta in tana barci.
Kichen suka koma suna aikinsu suna hiransu yau dai ta dake,tare sukayi wanke wanke ita da lami,kuma ita ta goge kichen din duk tanayi kamar bata da jini ajiki ammh haka take kokarin yin komai cikin hanzari,cikin lokaci suka kammallah breakfast din suka jera koma bisa Table suka koma daki,yau din cikinsu ta karya domin hakan ya fimata dadi,don yana sawa ta Tuna da gida kuma hakan yana sakata cikin nishadi.
Suna jin Sanda Hajiya ta sauko Ta nufi dakin dan lelenta,suka Fito tare takaishi Dinning Suka karya har Fitansu ma sunaji sanda ta rakashi,aransu suna mamakin wannan karfin hali mace da mijinta ammh ki maidata boyu boyu ackin gida,wlh basu zata Ummi da wannan Mugun halin ba.
Ganin Ummi ta dade da Saukowa yasa Karime tace Zahirah tatashi suje su gyaramata dakin nata,suna ko Fitowa sukaci karo da ita Falo,bisa daya daga kujerun Falon anci ado,kafa daya kan daya,akwai jikin Zahirah na rawa ta durkushe tana gaisheta ko amsawa batayi ba illa dagama hannu datayi tana fadin”bani bukatar gausuwarki malama,karime haura da ita,ki nunamata yadda kikeyi,don bani son akin amaja”Tafada tana wani yamutsa Fuska da Toh karime ta bita suka haura sama tare.
Karime ta gwada mata komai,ita ta gyara bedroom din,itakuma ta shiga Tiolet ta wanke wanda sai da karimen tazo ta amsa don harta gama gyaran nan ammh ita zahirah ko Rabin wanke bayin batayi ba,Karime ko tsausayinta ke kamata domin Tasan tabbas zasu samu mtsala da hajiya,don Tatsani mutum mara karkashi gashi ko ita ko Zahirah haka Allah yayi ta,komai cikin hanzari take yinsa ammh kuma sai ta dau lokaci tanayi bata gama ba.
After one week
Zuwa wannan lokacin duk wani ukuba da wahalan Rayuwa zahirah ta gansa muraranta domin Gyaran dakin Ummi kullum sai ta mareta sabida yadda take bata lokaci bata gama ba,tunda kuma ta fahimci in sunje da karime na kamamata ne,yasa tace karimen ta daina zuwa,kullum haka zata gyara falon ta kuma yi mopping dinshi kafin taje dakin Ummi kan kace me tayi baki ta lalace duk ta bushe dama ba auki ba,duk da wai basu fara bata girki ba sai abunda ba’a rasa ba aboye don Ummi bata sani ba,Zahirah yanzu tama daina kuka domin ta gane a wahala zata dauwana har ta mutu,don akwai Ranar data wankema,Ummi Bayi ta manta batayi ma Ummi mopping din kasan bayin ba,ta zo shiga tsantsin Ruwa ya dibeta ta kusa fadi,wlh Ranar sai ta gunmaci mutuwarta don Ummi a fusace ta fito falo takwala mata kira tana zuwa,bata yi wata wata ba ta saka hannu ta wanketa da kyawawan maruka har guda biyu bayan ta saka kafa ta kwasheta ta fadi warwars bisa kafet,Wanda sai da bayanta ya amsa da kafanta wanda sai da tayi targade,Ummi tayi ta bala”i wai da gangan Tayi saboda tana son kasheta,haka ta tasata gaba sai da taje takara wanke mata bayin ta goge,Koda ta koma daki taci kuka kamar ranta zai Fita kafin dare Kafa ta kumbura tayi Sumtum koda su karime suka gani,sukaje suka Fadama Ummi cewa tayi”Ba kumbura ba tama Rube ita ina ruwanta,jin haka yasa Uwani duba kafar nan tagano Targade ne,ai ko Zahirah taji kuka lami da karime suka riketa taja mata,dayake ta iya babanta yakoyamata tun a kauye,Su kansu sun tsausayamata matuka man zafi suka Shafemata kafan dashi kafin sumata sallama su fice.
Da gari ko ya waye karime tace zata amshi Zahirah da gyaran dakunan Ummi tace”Basu isa ba sai ta yi shi,hakanan, tana dingishi da komai,ga bayanta daya kage ta fito,tanayi kuwa tana kuka babu mai lallashinta kuma aboye don ko da wasa tabari Ummi taji ko tagani sai ta gane kuranta,kuma duk tsawon kwanakin nan bata kara saka Mu”azzam a idonta ba Tun Rannar dasu yakura suka tafi,tun da Ummi ta mata kashedin nan bata taba bari sun hadu ba kotana dakin su karime ne dataji da bude get zata taso takoma dakinta takulle,domin ta san tsab Ummi zata aikta yankantan datace ,don Ta lura wlh Ummi bata da imani ko kadan Aranta.
Shima anashi barayin bai kara sakata a ido ba,shifa yama manta da ita sam,saboda a kwanakin yana ta wasu shari”u masu zafi baima da lokacin kansa in yafita tun safe sai dare yake dawowa yana dawowa abinci kawai yake ci ya shige sashensa yana aiki bisa system dinsa yana gamawa sai barci gari na wayewa watarana ko karyawa bayayi yake ficewa shiyasa hankalinsa bai kawo ya Tuna da wata halitarta Zahirah ba.
“yau din Har fita office sai yayi mantuwa wani fayel dole yasa Ushe ya dawo dashi,ya shigo falon a gaggauce ya shige barayinsa ya dauki fayel din ya fito kenan ita kuma ta Fito daga barayinsu Karime zata shiga dakinta kawai taji ta bangaji hannu Mutum Har abunda ke hannun nasa ya watse akasa,cikin Rawan jiki ta duka tana tattara fayel din, hannunta na rawa,sai da tagama hadowa duka kana tadago tamikamai tana fadi cikin Sanyin Muryanta”Kayi Hakuriā¦”Tafada lokacin data dago kanta tana kallonsa Fes ko suka hada Four eye wanda lokaci daya gabansu ya amsa..Dam..Dam..Dam..
Tana ganin shi Jikinta yafara rawa ta tuna da kashedin Ummi kawai sai ta juya ta kalli sama,suka ka ko hada ido Hudu da Ummi wacce ke tsaye hannuta daya sakale da matattakalan bene daya kuma ta rike kugunta dashi,ai da azama Zahirah ta wurgar da fayel din,
datake mikama Mu’azzam wanda yayi suman tsaye ta rumtuma daki da guda harda saka makulli.
Mu’azzam dake tsaye ya bita da kallo lokaci daya kwakwalwarsa ke haskomaasa fa wannan itace fa matarsa da “aka dauro masa Daga maiduguri gabansa ne yafadi lokaci daya daya tuna bai taba tambayan lafiyanta ba ballatana ma ya dubata ko sau daya,yaga ya take rayuwa acikin gida,kansa ya dafe yana fatan kada Allah ya kamasa da laifin da ba laifinsa bane,ganin yadda ta rumtuma da gudu ne ya bashi mamaki ko shi take tsoro..Tunanin hakane ya sakashi sakin wani siririn mirmishi wanda baisan dalili ba.
Ummi dake tsaye tayi Suman tsaye shiyasa tafara saukowa tana fadi cikin dakakkiyan murya” Mu”azzam mai yadawo dakai,bayan kafita zuwa office? tafada tana sakarmai idanunta,jin muryanta asama ya saka ya kalli inda yaji mganarta haka kawai yaji gabansa ya amsa,don Ummi ta mishi irin wannan kiran to wlh bana alheri bane.
Comment
Share
Vote
JANAFI
[18/08, 14:18] 80k: ????UWAR MIJINA..!????
(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)
Alkalamin:JANAF
Wattpad:Janafnancy