NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Mu”azzam kuwa aiki ne ya rikesa a office sai pass9 yadawo gidan a matukar gajiye yana shigowa falon yafada kan kujera bayan ya ijiye suit dinsa gefe lumshe ido yayi yana fadi cikin wata irin murya” My Hirah where are u? yafada kamar mai neman agaji Ummi data tsaye kansa tayi masa zuru da ido tana mamakin me kuma yafaru da tilon danta yakoma yana sambatu,tun tsayuwar motarsa ta sauko falo agabanta ya shigo ya zube bisa kujera.

Jin shuru ba alaman kowa afalon ne yasaka shi mikewa dagowan dazaiyi, karaf suka hada ido da Ummi,wani razana dayayi sai da yakoma ya zauna yana kallonta cikin Fitan hayyaci Ummi dake tsaye sai tasha jinin jikinta daure fuska tayi tana fadin”Dawo cikin hayyacinka Nidin dai nice baka so dawowata ba ko?,saboda wani bazan dalili naka wanda bansan dashi ba,kuma nakeson ji yanzu din nan”Tafada cikin kakkausan murya.

Ajiyar Zuciya Mu”azzam ya Sauke yana kokawa da Nunfashinsa kan ya mike ya isa ga Ummi ya rumgumota yana fadin”Nayi kewarki Ummi na…”wani sanyi taji aranta Fushinta yadan sauka,sai tasaka hannu tadan buga bayansa tana fadin”Nima haka my son..Ammh meyahana ka turawa,adauko ni?,ashe yanzu akwai aikin dazai fini muhimmanci agunka?”Tafada tana dagosa daga Jikinta.

Riko hannunta yayi yana fadin”haba Ummi bazaci haka daga gareki ba,kowani yafada miki ni ibrahim zan fifita wani abu sama dake ai kya karyatashi,Kwata kwata,cikin satin nan bamu samu zama,ba shekaranjiya na dawo daga kogi kan case din nan,naso nadan samu lokaci nazo mudawo tare ammh bansamu ba,dama hop dina gobe ne ko weeked naje muzo tare ammh wlh tallahi Ummi kinji Rantsuwa daya kenan,ban da wani buri na duniyar nan banda na faranta miki ranki,ammh tunda ranki ya baci,kiyi hakuri ki gafartamin kada Allah yayi Fushi dani..”yafada yana kokarin dukamata.

Dagosa tayi tana tana kallonsa bayan maganganunsa duk yagama kashemata jiki,tasani mu”azzam na mata biyayyah wlh ta tabbata ko Wuta tace ya fada da gudu zai fada duk don kar ya musa mata,shafa fuskarsa takeyi tana fadin’Bakayi laifi ba my son,koma kayi nariga ya dana yafemaka,kawai kasan halin dan adam ne,nima ka yafemin kaji..”Tafada idonta yana kawo kwallah Saurin Rumgumeta yayi yana sakin ajiyar zuciya,ammh rabin hankakinsa na ga rabin ransa zahirah ya suka karke da Ummi.

Tare sukayi dinner duk don ya wanke mata rai,kuma ya saki jiki sukayita shan hira,yana bata lbrin case din dake hannunsa,sun dade suna hira har kusan 11 kafin Ummi tafara hamma tace yaje yakwanta barci takeji sai kuma gobe,ransa yayi masa dadi dama gabadaya rabin hankalinsa naga shashen zahirah ko motsinta baiji ba hankalinsa yaki kwanciya sai da ya raka Ummi har cikin bedroom dinta takwanta shi ya rufamata blanket ya tofamata addu”an barci ya fice itakuma tana sakamai albarka.

Yana fita direct dakin zahirah ya nufa bata afalo,cikin bedroom din ya shiga ya isketa kwance kan sallaya tayi barci harda abayan data gama sallah,tsausayinta ya kamashi ya isa gareta ya ciccibota ya maidata bisa gado ya kuma zare mata hijabin jikinta,sai asanan ya lura yadda lebenta ya kumbura daga sama da hannu yasa yana shafa gun,ko kaffara bazai yi ba aikin Ummi ne,lokaci na farko dayaji tsanar wani shashe na halin Ummi haurowa gadon yayi yakara ciccibota ya azata bisa jikinsa bakinsa ya sanya bisa leben nata yana zagayo harshensa akai yana mata wasa dashi,cikin barcinta taji kamshin Turarensa,tana bude ido taci karo da Fuskarsa dab datata,yana xagaye harshensa wajen daya dan kumbura,karaf suka hada ido,cikin fitan hayyaci tayo rimi ta afkamishi tana sakin marayan kuka,rikota yayi yana kara kamkameta lokaci daya yana shafa bayanta alamar lallashi.

Ajiyar zuciya tafara saukewa kafin yadagota yana kallon kwayar idonta yace”Am srry kinji…Allah ya baki ikom cinye wannan jarabawan my hirah..”Yafada yana share mata hawaye,dan murmusawa tayi kafin tace”Amin tare dani kai ya mu”azzam domin duk abunda ya sameni ya sameka ne..'”Kara rikota yayi yana fadin”Sosaima my Hirah duka hakurin namu ne wlh,tunda Ummi dolenmu ce dukkanmu..”Yafada yana zarcewa wata tashar,tuni ta sakarmai jiki suka fara ya mutsa juna,cikin lokaci kadan suka fita hayyacinsu ganin Mu”azzam na kokarim cire mata zanin dake jikinta ne yasa tayi saurin dakatar dashi tana fadin”Ya mu”azzam…U..Ummi.Fa na nan”Tafada cikin sarkewan Numfashi,kara rikota yayi kafin yace cikin sarkewan Numfashi..”Um..mi..Ta riga data kw..anta..”yafada bayan ya zare mata zanin lokaci daya ya mirginata tadawo kasansa,kafin cikin hanzari ya fara raba kansa da kayan jikinsa,fadi yake”Tallabeni Hirata wlh ina cike da Bukatar ki..”Jin haka yasa ta rikesa gam ta hau bashi hadin kai kafin kace me, komai yacigaba d Kamkama cikin Farinciki da Annushuwa,ita kuma Ummi tana chan tana barci harda minshari.

..Washegari daya dawo sallar asuba dakinsa yakoma don ya kimtsa saboda baya son ma Ummi tafara fahimtar wani abu,Ummi kuwa dama da wuri ta tashi bakwai nayi ta isa ga shashen Mu”azzam wanda yayi daidai da shiga zahirah dakin nasa kenan,zata wuce mkranta shine wai bazata iya wucewa ba sai ta gansa,ta shiga kenan yana tsaye yana kokarin daura tie dinsa,da hanzari ta ijiye School bag dinta ta isa garesa ta amsa tana fadin”Gud mrning..”mrning how are u? yafada yana kallonta mirmishi tayi kafin ta rausayar dakai tace”am Fine ZUMANA..”Kur yayi mata da ido lokacin datake dage tana kokarin daura masa tie din yace cikin kasala”mekikace hirah,plz sake fada naji..”Sunne kanta zatayi yayi saurin taranta da cewa”No plz kisake fada indai kina son farin cikina..”ganin yadda ya marairaice,yasa tasake maimata masa ahankali ,rumgumeta yayi yana fadin”Da gaske ni zumanki ne,da gaske ina baki zuma?yafada yana kokarin su hada ido taki yarda suna cikin wannan yanayin ne,sukaji sallaman Ummi daga falo cikin Rudewa zahirah ta kwace kanta tana fadin”Ummi..”Tafada tana zaro ido.

Shima cikin rudewan yake shiyasa yakasa mata mgana jin takowar Ummi zuwa bedroom din ne,yasa yayi saurin Fizgan hannu Zahirah ya turata tiolet ya rufe kenan Ummi na shigowa ganin yadda yake zufa alamar ba gaskiya yasa tayi tsam da rai tana binsa da kallo,kakaro murmishi yayi yana bin kansa da kallo yana so ya mazaye saboda sanin halin Ummi na gani har hanji,yace”Gud mrning Ummu Ibrahim..”Yafada cikin son nuna bakomai.

Takowa Ummo tayi zuwa gabanshi tana kallonsa kan tace”Lafiyanka kalau kuwa..”? tafada idonta akanshi,mirmishi yayi mata yana fadin”Lafiya mekika gani hala Ummi? yafada kanshi tsaye shima yana kallonta kur tamai da ido kafin tafara bin ko”ina na bedroom din da kallo,shima ganin haka yasa yabi iinda takebi da kallo,karaf idanunsa suka sauka kan jakan mkrantan Zahirah gabansa ya buga dam..Yafadi yasan in Ummi taga wannan jakar wlh yau sai yagayama aya zaginta..Saurin shan gaban Ummi yayi tare da riko hannunta yana fadin”Oya Ummi muje muyi taking breakfast zan,mkra”Yafada lokaci daya yana jan hannunta,bata da yadda zatayi illa bin bayansa ammh zuciyarta bata bata ba.

Ko a Dinning din ma tana lura dashi duk hankalinsa ba”a kwance yake ba,ta tambayeshi yace babu komai,dole ta sakamai ido,sama,sama yakarya yayi mata sallama ya fice,agaban idonta suka fice daga gidan shida ushe,shiyasa takoma cikin falon saboda rashin yardan da batayi ba yasa takara komawa dakin Mu”azzam din,takara duddubawa bata ga komai zuciyarta dai duk da haka bai bata ba,harda su bude buden wardrope tayi ammh bata ga komai ba dole ta fice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button