UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL
UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF
Tafada direct tana kallon Mu”azzam wanda yayi kamar baijitaba,kuma da ganya ta fada,domin tarigaya data gama sanin she fall in luv kuma baba kowa bane sai na mu”azzam don kullum da tunaninsa take kwana tana tashi,ga tsananin tsausayinsa datakeji,inbata ganshi bata sukuni ko asibiti taje tana Sauri ta dawo ko dawowa tayi bata ganshi a falo ba zata bishi har dakin mooh tana gaisheshi Yana amsamata cikin sakin Fuska ammh daganan zai bata fuska tagama felekenta ta kara gaba.
Abbie kuwa,yanata shirin zuwa Nagaria ne,sai da ya kammalla duka shirinsa kana yake shaidama mu”azzam kan yabasa Full address na gidansu achan Abuja Nageria,kuma yace yazamansa anan ko yaje bazai gayama Ummi yagansa ba sai inda yaje yadawo sai su koma tare,mu”azzam yaji dadin haka,kuma yayi na”am nan da nan ya rubutama Abbie full address din a takarda yabashi,Dama bayason komawa gida ayanzu saboda bayaso yakoma yaga hiransa tayi aure zuciyarsa bazata iya dauka ba sam.
Kwana biyun da yin haka Su mu”azzam suka raka Abbieb khamis filin jirgi yadaga zuwa nageria Mu”azzam jiyake kamar yace zai bishi,saboda yadda yayi kewan Ummi da Shureim harda hajajju,ammh kuma kalubalen dake tattare da komawansa ne ke kashe mai karfin Gwiwa,ammh koma mene zai cigaba da fadama Allah komai yazo da sauki.
Tare da lubna suka je,haka tun suna mota ta dinga nacinsa da kallo,tun yana basarawa harya Fusata yahade musu rai ita da mooh wanda keta mgana yana amsama sa a gajarce,ganin haka sai ya kyalesa yana tunanin kila baya son mgana ne a dat time din.
Suna komawa gida ya wuf ya shige daki,domin yau babu shakka,an tonomai abubuwa daya game da rayuwarsa na baya kwanciya yayi Ruf da cikin yana Tunano rayuwarsa da zahirah ta baya,kowani dakika yana jin daci aransa,wani waje yayi dariya wani Wajen in ya tuna ya sharbe hawaye,haka ya wuni yana kwance ko mooh daya nemi su fita,kiyawa yayi yace yaje kawai yau bayason Fita.
Comment dinku yafara yin low yanzu,wlh i hv a lot to do nake rage lokaci ina baku update kullum ammh yanzu kun rage sharhi kamar da,..Ina so nayi na kammallah ne kafin muyi resume skul,kuma ga tafiya agabana da zanyi,kuma da zarar na tafi bazan dinga samu time nayi muku typing ba gaskiya,so in kuna son update gobe kip ur commenting Janaf fans,in kuma kun rike kayanku,nima sai na rike update dina.,na hutama kwana biyu????
Janaftyjami
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)
Mallakar:JANAF
Wattpad:Janafnancy12
Dedicated to my blood Sisters JANAF
GIFT TO:Hussain80k
Intelligent writer’s Asso✏
NOT EDITED????
NO 34
“””Washegari nayi su Ummi suka koma bayan tarin abun arzikin dasuka bawa su yakura kafin su tafi,haka suka tafi anatama juna godiya mai yawa saka albarka kuwa kamar baffa zaima Shureim kuka,yana yi yana rokon Allah ya bayyana mu”azzam duk inda yake,yakuma karkato da hankalinsa gida.,haka suka mika hanya ransu duk ba dadi,ko bakomai rayuwar ta shettima akwai ban tsausayi aciki,ga talauci ga ciwo ga rashin haihuwa suka shikadai lalle yaga jarabta haka hajiya ke fada sanda suke hanyar komawa Abuja.
Koda suka koma hajiya taso bin Shureim Sukoma zaria ammh Ummi tayi narai narai da Fuska zatayi kuka,dole hajiya ta dakata da binsa sai zuwa wani zuwan,domin Ummi hada kayanta itama tayi tace kafarta kafar Hajiya,gidane Su karime su cigaba da zama,daman zaman tadakeyi don mu”azzam ne,kuma yau bashi to bataga amfaninta ba,indai hajiya zata koma zaria to sai da sutafi tare bazata zauna kadaici ya kasheta ba,domin ita yanzu wani kawan duniya da kyale kyalenta Duk yafitan mata aka,ganin haka yasa hajiyar zama domin tace bashi kyautuwa abar gida babu kowa sai yan”aiki koda an yarda dasu hakan kuskure ne,kuma ko yau mu”azzam ya dawo ta tabbata bazai ji dadin hakan ba.
Sallama Shureim yamusu ya tafi bayan ya biya ma”aikatan hakkinsu na wata,dama shike biya tunda mu”azzam din ya tafi,kuma ya tabbatar da ya cika musu store da kayan abun bukata,Shima bai wani jin dadin zaman chan,ga kewan hajiya gana dan”uwa,aiki ne kadai yake taresa ammh da badon haka ba,shima tattarowa zaiyi ya dawo nan shida zulaika da yara,don mganar gaskiya he fell alone achan.
MAID
Yau zahirah take da kwana uku cif agidan mijinta wanda zuwa wannan lokaci sau daya takara saka Alhaji kabiru a idonta tun bayan zuwan da yagana tayi ta tarashi suka fita bata kara ganinshi ba sai da aka kwana aka wuni da daddare ya shigo dakinta, shima asace yanayi yana waigo su little Ummi ya dauka yana musu wasa koda ta gaisheshi kasa kasa ya amsa yana binta da kallon sha”awa wanda dama tana, sanye da wani riga da sikat na shadda kayan Sun amsheta ganin kallon dayake mata yasa ta dauko mayafinta dake kan gadon ta yafa,dariya kawai yayi yana fadi afili..”To amarsu miye na rufewa,karfa ki manta komai wayan amarya sai ansha manta..”
Sunkuyar dakai tayi tana wasa da adon mayafinta,bata ko dago ba,tambayanta yake ko suna bukatar wani abu ta girgizamai kai,jin kamar motsin tahowa ne,ya shi saurin mikamata Moodu dake hannunsa,ya Fice jikinsa narawa,da mamaki Zahirah ta bisa da kallo kan ta tabe bakinta ko ajikinta ya cigaba da zama a inda yake wlh dayafi mata.
Tun ranar kuma bata kara ganinsa ba,Saudayama tataba fitowa falo washegarin ranar da”aka kawota data fito raka yan garinsu zasu koma kano,kuma iyakarta cikin falon daganan tayi komawarta ciki,akwai mai aiki zulai itake kula da komai agidan hatta bangaren girki,abinci har daki ake kawomata,gyaran dakin nata ma ita ta hana mai aikin yi ammh da farko har ciki ta shigo zata gyaramata ta hutar da ita,in tatashi da safe,daga wanka tayima yaranta babu abunda takeyi sai danne danne waya tana game kowani abu,yagana kuwa bata kara ganinta ba ko alama,itama bata nemeta don tama manta tana rayuwa agidan,itadai babban burinta Mijinta Ibrahim mu”azzam ya dawo gida sukoma ma Aurensu yanzu shine agabanta.
Ranar da Zahirah tacika kwana ukun takira kawarta Asma”u awaya tana fadamata tayi aure,kin yarda Asma”u tayi sai da ta rantse mata,Asma”u har kwallah tayi na tsausayin mu”azzam bayan zahirah ta fadamata lbrin barinsa gida,Nan Asma”un take fadamata suna WAEC ne yanzu,sai da zahirah taji tahowar kwallah a idonta sai ta share bata nunama Asma’un komai ba sai ma addu’an Fatan alheri dataita mata.,Sallama sukayi kowanne zuciyarsa babu dadi,shuru zahirah tayi tana jin daci aranta,yanzu adan shekarunta tayi aure biyu?ga mtsalolin rayuwa sunki karewa,ga yadda taci burin karatu arayuwarta ammh komai ya ruguje,share hawayen tayi tana fadi cikin ranta”bakomai haka Allah yaso in inada rabon karatun agaba zanyi..”tafada cikin dakewa lokaci daya tana sakin mirmishi ita kadai.
Dauko su little Ummi tayi ta goya moodu abayanta da zani,itakuma little Ummi tana rike da ita tana dan zagaya dakin alamar lallashi domin ta fahimci yau din sunajin rigima.
Tashar Tasin dayayi Tundaga Airport ita ta saukeshi akofar gidan na mu”azzam mai Taxxin yana fadin”Ga gidan nan yallabai..”yafada yana kallon inda aka makala lambar gidan 16maitama Distrit.,Saukowa Abbie yayi da yar jakarsa ta matafiya kafin ya ciro wallet dinsa ya zaro 5k ya mikama mai taxxin yana mai godiya,ganin kudin daya bashi ne yasa ya dingamai godiya hannu kawai ya dagamai kafin ya karisa bakin get din lokaci daya yana karema anguwar kallo yana jinjina kai,domin haduwar ta wuce wasa,maida kallonsa yayi ga katon gidan da akace mallakin Mu”azzam ne,kafin Ya karisa bakin get din ya saka hannu yana kwankwasawa.