NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

  Sani maigadi dake zaune shida Falalu suna hira sukaji buga get,kallon juna sukayi domin abun ya zaman musu sabo,su hon suka sani ba buga kofa,da hanzari sani ya mike ya isa ga get din yana fadin”waye..?

  Abbie ya gyara tsayuwa yace”Nine..”kai ne wa..? sani ya tambaya,mirmishi Abbie yayi kafin yace”bude ka gani mana..”jim sani yayi kafin Falalu yayimai,inkiya daya budemana su gani,budewa yayi kadan yana leke,nan yaga Abbie tsaye yana kallonsa,sama da kasa ya kallesa kafin ya kalli Fuskarsa,cikar kamala dana zati tare da kwarjini  su suka kashema sani jiki,cikin dakewa yace”mallam waka ke nema”?

    Abbie yace”Suhaima nake nema Ummin mu”azzam..’Kura masa ido sani yayi kan yace”toh toh..ammh gaskiya sai dai kajira a fado mata” dan mirmishi Abbie yayi kafin yace”aright…”har sani ya rufe get din ya juya sai yakara dawowa yana fadin”Am yi hakuri wa za”a ce mata ne..? Abbie yace”Kace mata khamis ne daga Sudan..”

  juyawa yayi ya nufi cikin gida,sallama ya doka afalon hajiya ta amsa tana tambayan waye? shigowa sani yayi ya zube akasa yana gaida hajiya da Ummi wacce ke zaune gefe tana binsa da kallo,hajiya ce tace”ah Sani ya”akayi ne..?

Sani yace,”lafiya lau hajiya,Hajiya Ummi ce tayi bako awaje..”Tare Hajiya da Ummi suka kalleshi hajiya tace”bako kuma? daga ina? tafada tana kallon Ummi wacce tayi kasake tanajinsu,don haryanzu bata fiye mgana bane sosai,duk da ansamu cigaba ba laifi.

  Sani yace”Toh Nidai yace min Khamis daga..”yafada yana daga kai alamar tunani,tunda ya ambaci khamis tayi tsam da ranta tana kallonsa sai chan yace”yauwa hajiya daga Sudan yace” Da dawani Sauri Ummi ta mike harta neman Faduwa take fadin”Daga Sudan kace? tafada tana zaro ido

  Kai yagyadamata kafin yace”eh haka yace hajiya..”ai kafin kace mene Ummi tafice da gudunta hajiya da Sani maigadi suka bita da kallon mamaki,jin kasar da,aka kira yasa hajiya mikewa tana bin bayan Ummi da Sauri,shiko sani da aka barshi zaune ya rike baki yana mamakin to mekuma ke Shirin Faruwa.

  Da gudu Ummi ta nufe get tana kiciniyar budewa ammh ta kasa,falalu ne ya karisa yana fadin”lafiya kuwa hajiya? dagowa tayi tana kallonsa kan tace cikin tsawa”Budemin get dallah mallam..”jikinsa na rawa ya karisa yana budemata domin tukafin tafiyar mu”azzam rabon dayaji muryan ummi cikin Fada haka,yana budemata Ummi ta fice da Sauri sai ko taci karo Abbie khamis tsaye yana kallonta nunasa Ummi ta hau yi da hannu bakinta na rawa lokaci daya hawaye yana wankemata fuska.

    “Kha..Mis…”Tafada jikinta na rawa duk da girma da kuma shekaru sun lullube,khamis ammh bazai taba bacemata ba,balle ma hutu da jin dadi baisa yawani chanza ba,sai dai shekaru da sukaja,shima cikin taruwar hawaye yake kallonta sama da kasa ganin yadda Suhaimar ta rame kamar ba ita ba,ko abaya ba haka take ba lalle rayuwa ta matukar juyama Suhaima baya
  
Shima cikin mamaki ya kirata”Suhaima.? yafada yana kallonta kawai sai ummi ta duke ta fashe da kuka tana fadin”ka makara khamis kazo lokacin da Amininka ka,kasa tadade da shafe idanunsa,Da’nsa kuma da muka haifa nayi sanadiyar barinsa kasar nan gabadaya ya tafi bamu san inda yake ba,yanzu nikadai ce nake rayuwa ina girban Abunda na shuka” tafada cikin mtsanancin kuka daidai lokacin da hajiya ta fito tana fadin”suhaima shi wannan din waye?  tafada tana kallon Abbie khamis dayake tsaye yana jin Ummi da Sauraranta

  Cikin kuka Ummi tace”Abokin moodu ne,yaya tare na fara ganinsu ranar da nafara dora ido akan moodu gidanmu na chan sudan” da kallo hajiya ta bishi ta fadin”Allahu akbar kabiran yanzu kake tafe..”dan mirmishi ya saki yana fadin”eh hajiya..”yafada lokacin da wata siririyar kwallar ta zubomai ta gefen dan Siririn glass din dake idonsa.

  Kama Ummi hajiya tayi tana fadin”bar kukanan Suhaima mu shiga daga ciki,bawan Allah shigo daga ciki maraba da zuwa..”hannunta ta rike suka koma cikin gida Abbie khamis na binsu abaya har zuwa baban falon gidan hajiya da kanta ta shiga kichen ta umarci su karime da su kawoma bako Abunsha da abun tabawa,kafin takoma falo su shiga gaisawa da Abbie khamis,Ummi kuwa na gefe tana ta rafzan kukan kamar ranta zai fita.

  Hajiya tace”Tun lokacin da katafi baka sake waiwayo ba,abubuwa dadama sunfaru ciki harda rasuwar amininka,da kuma barin danku gida”jinjina kai Abbie yayi kafin ya zare glasa din dake idanunsa yace”Inada lbrin rasuwar Abokina,haihuwar dansa da kuma bacewarsa ne bani da lbri..”nan ya shiga basu lbrin zuwansa da irin wulakancin dasu Shettima da fadi sukayi mishi ya kareshe da cewa”tundaga lokacin bankara farinciki ba Suhaima,sai da na samu lbrinki ta hanyar wani abokin karatunmu wanda muka hadu dashi afilin jirgi sanda zan rakoku Nigeria har muka gaisa dashi,shi yabani tabbanci Abuja kike zaune cikin wannan anguwan”yafada yana share kwallah.

Tuni kukan Ummi ya tsananta sulalewa kawai tayi akasa tana fadin”Wlh Amanace tacini khamis,amanar da moodu yabaka to wlh dansane ya maye gurbinta,tunda Mu”azzam yafara mallakan hankalin kansa baitaba sabamin da gangan ba,karfinsa,lafiyansa dukiyansa da komai nasa akaina yake karewa,ammh ni zama wata uwa mara tsausayi farinciki ko sau daya bantaba basa,ba sai ma nayi sanadiyar durkushewar rayuwarsa tunda gashi ya barni ya bar aikinsa da duk abunda ya mallaka,kaicho ni kaicho ni Suhaima…”take fada tana buga kanta akujera.

  Tsausayinta yakama Khamis yaji kamar yafadamata mu”azzam na tare sai dai kuma baizai iya ba,tunda ga yadda suka rabu da shi,gyada kai yayi yana fadin”to wai duk meyafaru kuman bayani yadda zangane”ummi ta gagara mgana sai kuka,hajiya ce ta bashi lbri kaf,kamar yadda mu”azzam ya bashi takara da cewa”tunda nake ganin soyayyar uwa da d’a bantaba ganin soyyayar da d’a yakema uwarsa ba kamar yadda mu”azzam kema suhaima,ya yarda ya bata komai ciki harda ransa matukar zatayi Farinciki zai iya mallaka mata,yaron nan gabadaya rayuwarsa akanta yake karewa,saboda biyayyah sujjada ne kadai baya mata,ammh yau duk waya gari ya,waya,yau ina fadi,ta mutu ta bar duniya da abunda ke cikinta,yau ina shi sheetima da abunda yake takama? babu shi,ba yan’uwansa duka Allah ya karbi abinsa ga shi Allah bai basa haihuwa ba ga ciwo ya kwanatar dashi duk dalilin tafiyar Danki,yayi nadama tuni,da ace suhaima kinajin mganata da duk haka bata faru ba..”

  gyara zama Abbie yayi yana fadin”tabbas hakane,duk abunda kaga mutum yayi to yajira sakamakonsa wajen Allah,yanzu shettima duk abunsa yana kwance babu lafiya to wace dubara za”a ma Allah, kai abu baiyi dadi ba sam,suhaima ai ba”a rama cuta da cuta,da alheri ake ramawa daga karshe sai ka ga kaine da riba,ammh babu komai anytin will be alright zan nemo mu”azzam duk inda ya shiga afadin duniyarnan,koda kuwa duk abunda na mallaka zai karene nayi miki alqawari suhaima,so kibar kuka,duk abunda yabaru mukaddari ne daga Allah,kuma jarabtane daga indallahi..”haka yayi tama Ummi nasiha kana tahakura tayi shuru,shashen mu”aazzam aka sauke Abbie ya shiga yayi wanka ya sauya kaya kafin akawomai abinci yaci,ya kwanta ya huta.

Tun aranar hajiya takira shureim tana Shuraim tafadamai zuwan Abbie khamis yayi murna sosai,kuma yace insha Allahu yana nan tafe cikin satin dazai kama zai taho,hakika zuwan Abbie ya ragema ummi damuwarta haka zasu zauna suyita hira yana bata lbrin cigaban da aka,samu achan sudan din,yafadamata rasuwar iyayansa,har sai da Ummi tayi kwallah tana tuna hallacinsu gareta,nan yake fadamata yayi aure ya’yansa biyu lubna da muhammed takwaran moodu,kuma yayi mata alqawarin yana komawa zai dawo tare dasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button