NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

  Lumshe ido yayi kafin ya dagamata kai,Wayarta dake kan Side drower ta mika hannu ta jawo tana fadin”Bazan bari saboda son ganin zahirah ka mutu ba Son,insha Allahu Zahirah takace let me Talk to yakura..”Tafada tana kara wayan akunne gyara zaman kansa yayi bisa cinyarta bayan ya kamkame hannunta yana sakin mirmishi,Da sallama yakura tadaga kiran Suna gaisawa,Ummi tace”Amrm yakura nace ba”yakura ta gyara zama tana fadn”Inajinki Suhaima..’Ummi tace,,”kan mganar Zahirah ce,ya ake ciki ne,ga mu”azzam ne wlh ya damu wai Shi sai yazo ya ganta..”yakura tace”Tama kwana gidan Sauki Suhaima yataho kawai,Tunda ma Bukar yaje ya daukota ya maidota gida Tun ranar,Ni banje ba,mahgana ce takirani tana fadamin wai Zahirah tace bata komawa mu”azzam,zama zatayi ta rike ya”yanta,Shikuma bukar yace duk yadda ta zaba,bazai Takura mata ba..”Cikin mamaki Ummi tace”Ita Zahirah tace bazata koma gidan Son ba..”Tafada Tana mamaki.

  Dariya yakura tayi kafin tace”Eh wai tace yayi Aure ya manta da ita,kishin danki ne,ke damunta da da zarar yaje Shikenan”Tafada cikin zolaya yar dariya Ummi tayi tana fadin”Umhmm yaran zamani,to Shikenan yataho din babu mtsala”yakura tace”Eh yataho babu mtsala..”da haka sukayi sallama da Ummi daidai lokacin da Mu”azzam ya tashi daga kan ciyar Ummi yana kallonta.

  Ijiye wayar tayi,ta zuramai ido kafin tace”Is ok,ka shirya sai Ushe yakai ka chan maidugurin Tunda ka matsa,zaka kwana ne,ko yau zaka dawo..”? Saukowa yayi daga kan gadon yana fadin”Wai Ummi ita zahirah ce,tace bazata koma wuri na ba ko?yafada yana nuna kanshi.

  Yar dariya Ummi tayi kafin tace”Eh Tace Tunda kayi Aure,ita bazata dawo ba..”bai kara cewa komai ba,ya juya ya fara tafiya yana fadin”Lalle Zahirah ta raina ni I will deal Wit her..”yafada cikin dakewa,Da kallo Ummi tabishi hannunta bisa habanta tana fadin”kwaji dashi dai,katafi kuje chan ku karata”Tafada taba komawa ta kwanta lokaci daya tana jan blanket.

    Da Sassarfa ya sauko daga Saman ya nufi dakinsa yana Shiga Ya iske lubna,kwance bisa gado,gabadaya jikinta na cikin blanket,kanta ne kadai awaje,bai wani tsaya ba ya fada,Tiolet yayo wanka sanda ya fito sanye da rigan wanka kansa karamin Towel yana tsane ruwan kansa dashi,lubna ta bude ido tana kallonsa baibi ta kanta ba,ya isa ga dressing mirrior,ya shafa lotion kafin yayi Cumbing din kansa,Ga wardrope dinsa ya isa ya bude,ya ciro wata Shadda Wagambari, Navy blue,tana yarari tana maiko da kallonta zaka san tabama Dubbai baya,hula ya dauko zannah bukar ya saka bayan ya hau Feshe jikinsa da Turarensa na MAN,Takalminsa yadauko Sau ciki ya sanya yana dagowa suka hada 4eyes da Lubna wacce ke kwance tana kallonsa da duk Abunda yakeyi.

Kuramai ido tayi kafin tadan muskuta tace”yaya,ina zaka da safe haka kaketa Shiri ahanzarce..? yana gyara zaman Hulansa kansa yace”Maiduguri…”zaro ido tayi kafin tace”Wajen wa..? wani banzan kallo ya watsamata kafin yace”wajen wa kike tambayana,? ban tsammaci wannan Tambayan Daga gareki ba,domin kinfi kowa sanin muhimmanci garin awajena..”yafada cikin bacin rai.

  Mirmishin dayafi kuka ciwo tayi kafin ta yaye bargon ta sauko tana fadin”Am Srry yaya,wlh bansan sadda tambayan Ta fito min bane,kayi hakuri baran kara ba”Better….”ya fada yana juyamata baya,Bayansa tabi da kallo,kafin ta gyada kai ta share kwallar data zubomata ta dago kenan Suka hada ido da mu”azzam yana kallonta,Saurin Wucewa tayi Tana fadin”Allah kiyaye hanya,ka gaida Antyna da yarana..”tafada cikin sanyin murya”da kallo ya bita lokaci daya yaji Tsausayinta ya tsirgamai Baki ya sa yakirata”Lubna…”yafada yana takowa gabanta.

  Cak ta tsaya bayan Ta waigo Shikuma daidai lokacin ya kariso idanunta yakeso ya kallah ammh taki bashi dama,saboda kada kwallar datake tarawa su zubomata,bata son ya Fahimci ta fara gazawa,Hannunta ya Riko duka biyu yana Matsawa kara kiran Sunanta yayi da cewa”Lubna,dago ki kalleni..”ya fada yana kallonta,Dagowa tayi ahankali tana kallonsa,Kuri yayi mata,itako jikinta ne yafara rawa lokaci daya tana jin kamar ta fashe da kuka,hawayen datake boyewane Suka zubo basu Shiryaba,Runtse ido tayi hawayen suka zubo sharr,hannu mu”azzam ya sanya yana sharemata lokaci daya yake fadin”Am Srry..I know wht i did,is hurt u..Banda zabi ne,Kiyi hakuri don Allah..”yafada jikinsa nayin Sanyi,Kara volume din kukanta tayi,Saboda tsausayinta baisan sadda ya jawota jikinsa ba ya rumgumeta,jinta akirjinsa yasata kara lafewa,hannu yasa yaana Shafa bayanta har zuwa kanta yana fadin”Srry kinji bazan kara ba,wlh ba da gangan nake miiki wani abun ba,Zahirah ta riga ta mamaye ko”ina a zuciyata,in har bata dawo rayuwata ba,Rayuwa ta bazata daidai ta ba.”ya fada yana shafa kanta.

  Dagowa tayi tana kallonsa Lumshe ido yayi kafin ya bude baya taja tana fadin”i know,ammh Don Allah kadaina kokarin Batama zuciyar datake Tsananin Sonka da girmamaka,na yarda ka cigaba da Son zahirah har karshen Rayuwarka,nikuma na cigaba da Sonka har karshen nawa rayuwa,haka kaddarata take..”Tafada hawaye na ziraromata.
     

   Tsam yayi yana kallonta kafin yamika mata hannu takama ,matso da ita yayi yana kallon kwayan idonta yace,”Plz kibar kuka,insha Allahu da zarar Zahirah ta dawo zanyi kokarin kamanta adalci atskaninku,sai dai Abunda na gaza don Allah kiyafemin kada Allah yakamani da laifin take miki hakki..”Sadda kai tayi kasa kafin tadago ta sanya hannu ta share kwallah tace”babu komai Yaya,Ni bazaka taba laifi awajena ba,Ai nina na shiga rayuwarku So,karka damu ina bayanka Allah yasa Antyna ta dawo..”tafada tana sakin mirmishi.

  Mirmishi shima yayi yana bata kiss akumatu yana fadin”Tanque my lil Sis u ar d Best,sai na dawo kinji,kuma bani son kukan nan,plz ki bari kada Ummi ta zargi ko nayi miki Wani abu ne..”Sandarewa tayi Tun sanda yabata Sumba abaki,saboda yadda taji abun abazata,bai jira cewarta ba ko Fahimtar halin data Ciki ba,ya fice daga bedroom din Cikin Takun isa,bayansa ta raka da kallo,kafin ta sanya hannu ta shafo inda yayi mata kiss takai bakinta tana shinshinawa kafin Ta rumgume hannu tana fadin”yes zan iya,nasamu cigaba,tunda har zai batamin yakuma bani hakuri,zan cigaba da hakuri nasan watarana nike da riba”Tana gama fadin haka tafada Tiolet ta wanke Fuskarta da hanzari Ta fito da bedroom din tayi falo,nan ta tarar da Mu”azzam afalo Ummi ta rakosa,tare suka rakasa har wajen mota,Ummi na jaddadamai cewa in Sunyi dare su tsaya su kwana,Amsamata yayi da toh,Ushe yaja suka fice daga gidan Suna dagamai hannu,kafin sukoma cikin gida.


  
MAID

   
     Zaune take afalo Tana kallon tashar Arewa,Ana Shirin Akushi da Rufi,Little da moodu suna ta zagayen Falon da kafarsu bayan su saka hannayensu sun dafa kujera,batabi da kansu ba hankalinta naga kallo,domin gidan babu kowa mahgana batanan Tatafi anguwa ita dasu Alee Bukar kuma bayanan Ya fita wajen aiki,ita kadai aka bari agidan,sanye ta da riga da zani na wani golden less,Rigar Fitted ce ta kamata,Sosai tayi Daurin maryam babangida,gashinta ya fito ta kasa cikin Band dinta.

     Bataji Sallamarsa ba sai dai kamshin Turaransa daya cika falo,ko mutuwa tayi ta dawo bazata kasa tantance kamshin yaya mu”azzam ba,Cikin wani yanayi Ta dago kanta karaf ko idanunta sukayi kyakyawn gani Mu”azzam tagani Tsaye a tsakiyar Falon Yana kallonta bayan ya saka duka hannunuwansa cikin aljihun wandonsa ya zubamata duka idanunsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button