NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

KANO 

A hankali Aliyu ke jan motar kamar bai son tukin yayin da dan uwan ke zaune gefen su ya dafe goshin shi da hannun shi daya hankalin shi na akan wayan shi.
Niko bros zanso muyi magana idan kana da lokacina yanzu Aliyu ya fada tare dan kallon yayan nasa.
Ina jin ka yace ba tare daya dago kanshi yana kallon shi ba a lokacin jin hakan dan uwan shi ya girgiza kai yana fadin.
Gaskiya bros kan wayan danaji kanayi shekaran jiyane sai naga kamar har yanzu zaman ku bai saitu ba yadda iyayyen mu suke zaton hakan .
A ganina hakan ba girmaka bane ba kuma mutuncin ka bane bros don ranan da iyayen mu zasu fahinci hakan gaskiya girman ka zai fa, , ,
Dakata Aliyu ya isheka hakan ni zaka kalla ka fada min wanan maganan don raini ko may ?
Kayi hakkuri idan ranka ya bacine bros gani nayi duk duniya babu mai fada maka gaskiya kan hakan kamar mu.
Kaga ko Habbib daya fi kowa a cikin mu danyen kai ranan danaje gidan su Abuja sai da nasha mamaki .
Akwai cutarwa sosai da danne hakki a cikin zaman ku da yarinyar nan ba zanso wani daga cikin family din mu ya fahinci hakan ba bros.
Naji kana fadin wai mai ta fadawa mama twices data kirata idan ma bata fada mata komai a yanzu ba na gaba zata fahinci hakan daga hiran su.
Sake juyowa yayi ya kalli dan uwan nasa rai bace yace ke nan kai zaka koya min abinda zanyi da iyalina ko ?
Dan murmushi Aliyu yayi ya girgiza kanshi tare da fadin ko daya bros gaskiyane ko daddy yayi ba daidai ba za,a fada mai gaskiya balle mu yayan daya haifa.
Well zaka iya fadin komai don ba laifin ka bane yace yana kawar da kanshi daga cikin motar yana kallon titin da suke tafiyan.
Kaini gida yace kai tsaye ba tare daya kalle shi ba Aliyun yace gidan daddy zamu yace a hasale gidana nace ka kaini malam ban son yawan maganan nan don Allah.
Mun fasa zuwa gidan gonan ke nan bai iya bashi amsa ba don ya gaji da surutun shi a lokacin.
Kwana ya karya ya dauki hanyar gidan shi dashi ba tare daya kara cewa da dan uwan nasa komai ba suna shiga get din gidan yace tsayanan in sauka.
Baibi ta nasaba saida ya kaishi gab da kofan shiga cikin gidan ya tsaya yana cewa in dawo anjima mu tafine ya bude motan ba tare daya kula shiba ya fice motan.
Kai Aliyu ya girgiza yace a fili ka yi kuskure bros ba aiwa mace hakan da kake nufin yi nan gaba zamu sha kallon idan muna raye.
Shiko sarkin tsabtan yana shiga gida dakin shi ya nufa kai tsaye ya fara cire kayan jikin shi ya fada wanka duk da zai fita yai wankan.
Saida ya saka kaya ya fito falon kujera ya hau ya kwanta ya rintse idanuwan shi a zuciyar shi yake tunanen shi yaya zaiyi da matsalan yarinyar nan a rayuwan shi.
Ko Amma duk yaje gurin ta da sunan gaisheta sai ta bulomai da maganan wata a ruwa can kafin ya tashi gurin.
Shi ke nan shi baida wani damuwa ko matsala a yanzu sai na mace macen kuma karamar yarinyar da bata gama mai.
Ga kuma hjy su data matsa mai lamba kan yarinyar lalai sai ya saketa ko su samu matsala dashi.
Ga marry da yanzu ta sauya sosai da halayanta ga zamantakewan su ta dauko sabon akida ta dora a rayuwan ta.
Shi da wani zaiji cikin wanan shifa idan ba dole ba gaba dayan su sai ya sahile masu da wanan auren.
Don hakane ma yake rage yawan shiga gidan nasu ko wurin daddy da yanzu yana gane kowa yana magana kada watarana ya tambaye shi wanan yarinyar wani amsa zai ba daddy din .
Ga Aliyu kuma yaji wayan shi da yarinyar nan har ya fahinci halin da suke zama kadafa yaje gurin surutu ya fadawa wani wanan maganan ko da kuwa matar shice.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:19 – ????????????: ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH, , , , ,

Ranan monday karfe bakwai na safe kamar yadda na saba fita daga gidan na isa bakin titi don tare taxi din da zai saukeni school.
Jikina saye da dogon riga da coat doguwa har gwiwa sai half sunna hijjab din daya rufe min wuyana da saman kai banda tafin hannuna da fuskana baka iya ganin komai a jikina lokacin.
Wanan shigar yana daukan hankalin mutane da dama don shedace mai nuna ni din musulmace a duk inda aka ganni.
Wanan shigar kusan ko yaushe hakan nake yin shi idan zan fita don london kasa ce mai bawa kowa daman yin akidar shi dayazo dashi kasan.
Idan ka ganni kasan ina da dan damuwa a tare dani ranan don ban irin dan walwalan da nake a cikin kawaye idan mun hadu.
Gurina samu inda babu kowa na zauna ni kadai tare da harde hannayena saman kirjina na kurawa guri daya idanu.
Har aka zauna kusa dani sai lokacin nayi ajiyan zuciya tare da juyowa inga ko waye ya zauna kusa dani lokacin.
The guy na gani yana min dan murmushin shi mai tsada duk da akwai dan tazara tsakanin mu hakan bai hanani kara matsawa ba kadan daga inda nake ?
Yace yan mata waya bata maki rai hakan ya hanaki walwala yau don da ganin ki ba sai an tambaya ba kina cikin damuwa hakan.
Dan murmushi na sauke a fuskana nace as you say amma ni banda wani damuwa a tare dani sam na fada ina kokarin mikewa tsaye.
Yace no kada kice zaki gudu don ni zarah ki zauna ki huta abinki saidai ban son ganin ki a cikin wanan yanayin haka ko mijin ki ne yayi maki ba daidai ba tunda kince kina da aure.
Wanda ni har yanzu na kasa gaskanta hakan a raina don ban taba ganin alaman hakan ba tare dake.
Da mamaki na dago kai ina kallon shi tare da fadin wani alama ke ga masu aure din da ake gane su.
Saida ya mike tsaye yake fadin well tare da dan kakabe wandon shi kamar wanda ya kwashi dadti a jikin shi yace .
A bangaren ki irin kamun kan masu aure nake gani a gare ki sai dai ba lalai ne in gaskanta hakan gare ki ba gaskiya.
Har yau ban ga mijin naki ba kodai bai damu dake bane zarah ya fada yana kallon fuskana kamar may son gano gaskiya a cikin idona.
Nace idan baka sanshi ba aishiya sanka don ko wanan tsayin da mukayi yana da labarin komai yanzu.
Ido ya zaro waje da dan mamakin maganata yace kice dai yana da security a boye ke nan saidai ba abin mamaki bane maganar ki don mazan kasan mu masu kudi basu kyale mata kyawawa irin ki dama, har mu matasa mu samu.
Mikewa nayi gaba daya nace sai an jima ba zan iya sauraren nan zancen ba nidai na fada ma wallahi da aurena a kaina tuntuni na barshi a gurin yana bina da kallon mamaki.
Ya sauke ajiyan zuciya tare da shafo kanshi kafin ya girgiza kai tare da kada hannun shi koma waye mijina har in ina dashi zai gano shi indai dan Nigeria ne.
Na dawo kamar kullun ina shiga wayata na ruri kira da kyat na zaro shi cikin jakkata ina duba mai kiran nawa mamu na gani .
Kin dauka nayi saidaya katse na kirata tare da fadin mamuna nayi missing din ku ina Fauziya dasu yan biyu ya jikin kawuna ?
Ya fara fita kasuwa da sauran gurare mamu na jera mata tambaya a jere tace wani zan fara amsa maki a ciki dan dariya nayi nace na kawuna mamu.
Tace kawun ki yana jin ki yanzun haka gashima yana dan murmushin jin muryan ki ai.
Dan ihu nayi nace Allah nagodema dakaba kawuna lafiya Allah yakara bashi lafiya da sauran mudulmai baki daya naji yace Amin yar kawu.
A cikin ladabi na fara gaidashi tare da jera mai sannu yanayin yadda yake magana yasa na gane har lokacin yana jin jikin sa wai a hakan sauki ke nan suke fada yaji.
Kawune ya dan katse shirun da tambaya yar kawu Allah yasa inga diyan ku a duniya kafin in tafi shiru nayi na kasa amsa mashi saida yace hello kina jina Fatima ?
Ina jin mamu tana fadin kaima kasan ba zata amsa ma wanan addu,an ba ai ta karbi waya tare da fadin bana gida ina nan gurin kawun ki dana ba su fauziya kun gaisa don suna damuna da zancen ki ko yaushe.
Tundai da sukaga mijin ki yazo ba dake ba kuma suka shiga tambayan ki yaushe zaki zo ko a kaisu gurin ki.
Mamu ya umar bai fada min zaizo ba dana bayar da sako a kawo masu kuma sai ya kirani yana fadin wai may na fada maki ?
Wayan ta danyi kara alaman katsewa na dago na kalli wayan ina mamakin jin ya katse dukda nasan akwai chages mai yawa amma kudina bai isa karewa ba a lokacin.
Nayi neman layin kuma baya shiga ko kadan don haka najefar da wayan gefena tare da kaiwa kwance saman kujera ina lumshe idanuna.
Sai dana dauki lokaci a hakan kafin cikina ya fara kukan neman abinci na tuna banci wani abin kirki ba ranan bayan ruwan tea dana sha kawai.
Daga idonayi na kalli agogo karfe takwas na dare saura lokacin don haka na mike ba shiga kitchen don samawa kaina abinda zanci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button