NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Sunyi sa, a sun sami tsohon a gida bayan karfe biyar da suka koma gidan akai masu sallama dashi jin sune yace su shigo falon shi da yake zaune.
Ya tare su da fadin ko dai kunyi batan hanya ne don naji kuna garin nan tun kan ayi sallah sai yau kuka tuna da dan tsoho.
A cikin jin kunyar abinda tsohon ya fadi suka karasa shigowa suna neman wuri a nan take ya umurci wani jikanshi da ya shiga ya kawo masu abin motsa baki a cikin gida.
Bayan sun gaisa ne yake tambayan su bayan rabo suka dai dan taba hira sai dai basuci komai daga abinda aka kawo masu din ba.
Can Umar yace cikin girmamawa malam wurin ka muka zo neman taimakon ka don Allah ka shiga cikin wanan maganan don kai kadai ne yanzu muke ganin zaka iya shawo muna kan mahaifin daga fushin da yake yi dani .
Subbahanallahi may ya faru yake fushi dakai kuma daga dawowan ka kasan nan shi ba abin alfahari bane ganin haka.
Bakuji irin dadin da naji ba lokacin da kuka shigo falon nan yanzu kun zamay muna abin alfahari a cikin zuria .
Aliyu yace haka ne malam sai dai yayan mu yayi kuskuren yin aure a can ba tare da sanin iyayyen mu ba shine tashin hankalin dake tsakanin su da Abban mu yanzu.
Nan dai Aliyu din ya kora ma tsohon duk bayanin komai da yadda maganan ta fara har fushin da mahaifan su keyi dashi umar din.
Subbahanallahi tsohon yace yana girgiza kai tare da fadin innalillahi yaya hakan ya faru kaiko abokina da ilimin ka da tarbiyan ka zaka aikata muna hakan.
A sanyaye Umar yace kaddarace malam kasan mutum duka bai wuce kaddaran shi a rayuwan shi.
Malam Nuhu ya jinjina ganshi kafin ya fara karanto masu ayan Allah yana fassara masu ayoyin alkur,ani mai girma wanda yake magana akan hakkin iyayye da sharian aure.
Bayan ya gama masu bayani yaga yadda jikin su yayi laushi sai ya fara nuna ma Umar kuskuren shi na rashin daukan iyayye da muhinmanci dayayi .
Yace yanzu barin ji inda mahaifin naku yake sai dai ita Amamatan wani mataki ta dauka akan wanan magana sai umar yace .
Itama dai ta dauki zafi da farko amma yanzu naga ta sauko sosai ba kamar farko ba kawu ya dauki wayan suka gaisa yake tambayan shi yana ina ne ?
Yace yana kasuwa yanzu zai koma gida yamma tayi yace a dawo lafiya yace dasu barin shiga ciki in fito mu tafi gidan naku ayishi ya kare can.
Sun yi daidai da kawu ya dawo daga kasuwa ya shiga part din mahaifiyar shi suna gaisawa da ita sai ya tura a kira hjy jummai ta samay su a part din Amma don da ita za ai maganan
Suna zaune sai ganin su sukayi sun shigo gaba dayan su har da kanin mahaifin su kawu din malam nuhu.
A cikin girmamawa Amma na fadin ina kafito da wayan nan gardawan a bayan ka yace to gasu nan dai waya sani ko satoni sukayi.
Aka sa dariya banda su a falon su umar suka zube suna gaida mahaufin nasu yayi kamar bai jisu ba.
Ganin haka malam Nuhu yace bakaji yaran na gaida kai bane Sani ashe abinda naji gaskiyane ba karya ba.
Amma kina cikin gidan nan kika bari abubuwa suna gudana haka aure ne dai yaron na ya rigada ya aikata son ranshi sai ayi hakkuri.
Na fada masa ya aikata babban kuskure to amma abin lura a nan shifa yaron nan dan Adam ne shima kuma kowan ku nan yasan dan adam ajizine bai wuce yin kuskure a rayuwa.
Sai lonacin kawu yai magana yace baba indai maganan yaron nan ne na sallama da zancen shi a raina.
Yaje yayi duk abinda yaga dama a duniya tunda har yake ganin shi ya isa mu bamu isa dashi ba sai dai ya sani duniya ta isa da kowa.
Malam Nuhu yayi murmshi gami da gyara zaman shi yace a daiyi hakkuri tunda ya gane kuskuren shi yanzu.
Ubangijin daya hallice mu ma muna masa laifi idan mun rokeshi ya yafe muna don kai zakace ka yafe shi ma, ana yaje yabi duniya ko ?
Kawu Yace baba haka naga ya zabawa ranshi kamar umar yace ni zai tozarta a garin nan a idon jamma,a.
Aure ne fa sani ba wani aikin shedan ya aikata ba a can sai dai matsalan yarinyar a hallul kitabice ita ko shine zafin ku dashi.
Amma duk da haka idan kukai duba da ubangiji bai hana hakan ba sai a sasauto mashi hakana amma kai ka hau mahaifiyar shi ta hau har ke Amamatan kin hau dashi da sauran iyayyen su.
Yaya kuke ganin karshe zaiyi ai sai ya koma can wurin matar tashi da yan uwanta su karbe shi tunda dama haka suke so.
Nan dai tsohon yaci gaba da lurar dasu duka bangaren biyu kuskuren su ya kare da yiwa iyayyen nasu nasihan suyi hakkri an san ya tabaka kuskure sosai.
Bai kyauta ba inda ya tare su yin magana ya umurci umar da ya kara neman yafiyan iyayyen shi .
Idanu shi suna zubar da hawaye ya mike zuwa wurin ko wanen su yana neman yafiyan su.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:55 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR, RAHHAMANIN RAHIM, , , , ,

Haka ranan suka kwana rayukan su babu dadi a cikin sa tun dai na uban aikin umar wanda shine ya dauko maganan.
Washe gari haka suka daka sakko zuwa gidan tsoho inda a nan ma suka samu yayi sammako zuwa daurin aure garin zaria.
Haka suka dawo da haushi a zukatan su na rashin samun tsohon a gidan rayukan su har lokacin babu dadi a cikin ta gashi suma hjy jummai duk ta hade dasu tana fushi.
A guje na fito daga part din Amma inda muka gama gardaman littafi da Aisha ta biyo ni aguje ina dariyan kwace littafin a hannun ta.
Ban san da mutane ba tafe mukaci wani uban karo dana gaban sai da ya dan tangaleni danayi baya zan fadi ga zafin da naji kamar zan kare.
Wani tsawa Habbib dake bayan shi ya buga min don shi ko isar shi kallo ban yi ba yana kamani banje kasa ba ya jaye daga gurin.
Cikin wani irin tsawa habbib din ya ke fadin ke wace irin makaciya ce a daidai lokacin da hannun shi ya sauka a fuskana.
Yaci gaba da fadin ke makauniyace baki ganin mutane a tafe ne da zaki fito haka kamar gidan ub, , , , ,
Kai kai kai haba habbib why da zaka mare ta haka da safen nan kan dan wanan abin haba hakan bai dace ba kana saurin dukan kannen ka mata.
Aisha da ta sandare wuri daya don jin zafin marin kamar itace aka mara ta juya da sauri ciki tana fadawa Amma sai ga Amma a fusace ta fito a daidai lokacin da yayan nasa ke masa fada.
Kai mara mutunci mai wanan yar marainiyar Allah tai maka ka mare ta haka da safen nan don radgin imani da tausayi ?
A hasalen ta juya gurina tana fadin mai kikai masa ya mare ki haka A ruwa cikin rawan murya da idanuwa da suka kawo hawaye nace ban san suna tafe ba na bangaji wanan yayan nasu shine ya mare ni.
Amma habibu ka cika mara imani da tausayi wai ma kai ta bangaza ko shiyan kane nan in sani tana tambayan shi cikin tsatsare shi da idanuwa irin na tsofin da ransu ya gama baci sosai.
Yace a a ke ta bangaza ita bata ganine da zata fito a guje ko tsaban rashin kunya da samun wuri ne haka ?
A gidan ka ta samu wuri mara ta ido nace ko nan din gidan ka ne yau zaka san ka mare ta a gidan nan kuwa yace oho ko zaki rama mata ne don dama ance kece ke daure mata gindi tanawa mutane iskancin dataga dama a gida.
Umar da ya gaji da zancen su yace haba ya isa haka Amma ke kuma ki kula idan kina tafiya da yanzu kin fadi kinji ciwo fa ?
Amma na fadin a a haa wanda dai ya isa dakai zan sa ya rama mata tunda kai kana ganin kafi karfin mu sai jin muryan Alh mukayi yana fadin hajiya lafiya kike fada haka da safen nan ?
Gaba daya suka juya wurin da sukaji muryan suna zubewa don gaishe shi Amma na fadin wallahi wanan mai zubin arna ne ya wanke yarinyar nan da mari tunda safen nan.
Subbahanallahi mari kuma yana yi yana kallona da mamaki karara a fuskan shi ya sake mai mai ta mari akan wani dalili ka mari yar mutane haka ?
Ga shafin hannun ka nan radau a fuskan ta har lokacin hawaye yana zubo min a fuskana iskancin naku da kuka koyo har yakai ku dakan min diya a gidana ?
Fada mashi dai don ni ya tsaya yana min iya shegen daya koya a can don shi bai ganin kowa da ta ido a gidan nan sai daukan kan tsiya da girman kai karshe dai nasan wata yarniyar kai ma zaka kwaso dan wanan halin naka sai su.
Haba Amma kin cika mutane da rigima don Allah baki jin daddy yana masa magana ne wai Aliyu yace haka a hasale ta mika mai dakuwa da yatsun hannun ta tana fadin kaci gidan ku a zulunci yarinya ka hana ayi magana.
Don Allah daddy ayi hakkuri nayi masa fada ai, , , , hannu ya daga wa umar din kafin ya fara fadin nayi nadaman tura ku waje karatu a rayuwata don baku koyo alheri ba can.
Na dan gega kawu dake tsaye zan wuce na kalli umar ina fadin ya umar kayi hakkuri don Allah ban san kuna tafe ba ba da gagan na buge ka ba .
Na wuce naji Amma tana fadin kaji ba nace ko kaji yar arziki ka doketa ta baku hakkuri yanzu bakaji kunyar kanka ba don Allah.
Kamar ka ka mari wanan yarinyar aiko baka san inda ta fito ba taci ragowan matsayin ta na ya mace a gurin ka da badon naji dan uwanka na ma fada ba da sai na rama ma wanan yarinyar marin ta wurun nan.
Ya dago jajjayen idon shi yana kallon ta yace ki rama mana udan kin isa ganin daddy ya kallo shi yasa yayi saurin sauke kanshi da sauri Alh yace ina yanzu idan kuna da hankali kun banbance tarbiyan kasan nan da wanda kuka koyo a can to ba agida za ai wanan shashancin ba.
Uwar yarinyar nan bata kasa daku har yau akan zancen wanan babu irin magiyar da batayi min in yi hakkuri ina facale ta gefe.
Amma ku idon ku ya rufe wurin bakin kishi da uwar ku ta cusa maku a zukatan ku kuna maza nasan idan nayi kukan safe akan ku itako na marance zatayi don Allah ba azzalumin kowa bane.
Amma da taga fadan yai yawa yana so wuce wuri tace ya isa haka ai ya koyi darasi ita ya zalinta amma ta basu hakkuri ko wanan ya ishe su nadama .
Banga abinda yar nan ta tsare maku a gidan nan ba ko bamu san A ruwa ba yau ai mu masu taimakawa rayuwan tane ko tunda tana bukatan taimako.
Hajiya bance wani ya taimaka min cikin rikon yar nan ba tsakani da Allah na dauko ta hannun iyayyen ta don in tallafawa rayuwan ta don haka ba zan lamunci wani iya shege a gidana ba akan kowa.
Yana fadin haka ya kai kasa daga inda yake yana fadin hajiya mun tashi lafiya duk sai sukaji wani iri matsayin mahaifi su da shekarun shi bai hana shi neman albarka a wurin mahaifiyar shi da Allah ya bar masa raye ba.
Duk sai sukaji sun muzanta a gabab mahaifin nasu duk da dai suna iya kokari su wurin ganin sun kwatata abinda suke gani ga iyayyen nasu wurin girmamawa.
Hakan bai isa shesu mamaki sai jin yadda uwar kewa danta fatan alheri da gamawa da duniya lafiya sabanun nasu uwar da suna gaishe ta tana masu zancen su bata wani abin.
Nan mahaifin su ya juya ya wuce bai kara bi ta kan su ba bayan sun gama gaisawa da mahaifiyar shi din ta juya wurin su tana fadin kun gani.
Har yanzu mahaifin ku fushi yake da dan uwan ku kai kuma kazo ka kara dada wani zancen dukan yarinya a kai.
Aliyu yace a dai ba daddy hakkuri Amma don in kiyi mai magana zai ji amma wanan fushin da sukeyi da bros yayi yawa wallahi.
Kai rufe min baki mara kunya da zai aikata hakan ya manta yana da magabata a gida ko may ko shi yanzu da ya mari yar mutane wani ya turo shi ya duke ta haka.
Ko yaushe kuna kokarin tozarta yar mutane don kawai Allah yayi zaman ta a gidan ku komay idan wani na waje yai mata haka ashe dadi zakaji.
Kuyi hakkuri Amma don Allah umar yace ni kaina banji dadin marin da yaiwa yarinyar ba ai kinji ina masa fadan.
A a aini ya wuce a wurina sai dai ku kula don ku maza ne ba a san diya maza da shiga kishin mata ba balle ku da ilimin ku da shekarun mai zaisa ku kama amfani da abinda baku gani ba da idanun ku.
Idan ma an fada maku wani hali nata na daban ne ai sai ku natsu ku kwantar da hankalin ku ku karanci halin ta ko ?
Yanzu kuko wanan abin da tayi maku ai ya isheku nadama kai ka mare ta ita kuma ta baku hakkuri da hawayen ta.
Duk shiru sukayi suna sauraren zancen da Amma ke kora masu din wanda duk gaskiyane zalla a cikin sa ta fada don dai ba zasuce ga rashin kunyar da yarinyar tayiwa dayan su ba.
Daga umar har habbib ido suka kurawa Amma dake magana sai dai a ransu tunane sukeyi basu taba ganin an saka su gaba irin wanan lokacin ba a rayuwan su.
Don Amma bata da zafi iri hakasin san ran tsohuwar a bace yake dasu sosai sai suks kalman da zasu bata hakkuri dashi.
Wayan shi dake cikin aljihun sa ya dauki ruri a lokaci daya haka yasa hannu yana lalaban wayan don ganin
kiran nasa.
My wife ganin haka yasa ya juya da sauri dan nesa da wurin da suke yana daukan wayan tare da fadin.
Hy merry how are you dear ?
Omar ka tafi ka barmu baka kulamu all this days why Omar ta karasa cikin muryan kuka tana fadin dama abinda nake gudu ke nan gashi tun yanzu alama ya nuna ka daina son mu.
Cikin karfin hali ya hade wani miyau mai daci daya taru a bakin shi yace .
Why zan daina son ku merry ba wai na daina son ku bane kwana biyun nan muna case da parents dina ne akan matsalan mu.
Kema kin san kina makale a zuciyata ko wani lokaci lokacin zama ne ban samu ga aiyukan da nake a nan yanzu aikin yake tafiya da na shigo kasan.
Merry ta saki ajiyan zuciya tace na dauka ko iyayyen ka sunyi nasaran raba tsakanin mu ne ai yace saboda may zasuyi muna haka ai suna da understand sosai.
Ya kawar da maganan don baison dongon zance saboda yanayin da yake ciki na bacin rai yace ya baby mu ?
Ta dan shafa ciki tana fadin yana lafiya dear yaushene zaka dawo gare mu muna cikin kewan ka daga ni har baby din mu.
Yace very soon zatayi magana ya katse ta yana fadin dama ina son in kiraki don jin inda maganan mu ya kwana dake ?
Tace maganar may ke nan fa dear ta tambaya da son ji maganar don ta manta da zancen wani magana da sukayi dashi.
Yace ya mukayi dake akan karban musuluncin ki don baby mu ya taso a cikin addini daya da iyayyen shi kada mu raba mai hankali.
Tace Oh i remember wanan zancen bata waya bace kabari zan shigo Nageria nima sai muyi maganan a tsanake.
Yace cikin murmushin kasaita merry you think iam jork wanan karon da gaskiya nake zance tace ai kasan ina son ka zan iya yin komai saboda kai.
Mu dai ka kula muna da kanka don kasan kaine rayuwar mu ba zan iya rayuwa idan babu kai a tare dani ba.
Wanan karon murmushin ya kara sakewa a tausashe yana fadin kada ki damu kin san ai you are The best baki da damuwa da Omar dinki.
Wani irin son shi taji ya kara tsaya mata a zuciya tana lumshe tare da tunanen ita kan tayi sa, an miji shiyasa take kokarin jaye shi daga yan uwan shi baki daya su zauna su ka dai sai yayan su idan sun tara nan gaba.
Idan da son samu a kokarinta na juyeshi ya koma akidar ta yana nan mata daram a cikin zuciyan ta ita da iyayyen ta suka san shirin da suke yi akanshi.
A bangaren Umar kuma ya gane manufanta sarai na son dauke mai hankali ga komai suna gama wayan ya kagu dama ta katse layin.
Bai koma wurin da yan uwanshi suke ba ya nufi hanyar part din mahaifiyar su kai tsaye suna ganin haka suka mara mai baya dama sun gaji da badakalar da sukeyi da tsohuwar a nan.
Kusan a tare suka shiga falon hjy jummai tana zaune tayi tagumi da hannu daya tana tunane suka shigo.
Gaba dayan su suka tsurawa mahaifiyar tasu ido do basu saba ganin ta a cikin wanan yanayi ba a baya tana da kokarin jajircewa abu idan yazo mata.
A cikin kwantar da murya Umar ya fara mata magana yace mama ki kwantar da hankalin ki kada wanan abin ya tayar maki da hankali haka don Allah.
Mama nine fa kin sanni kin san halina akan abinda zai iya da wanda ba zan iya ba fushin ki gare ni wani komawa baya ne a gurina yanzu.
Kanta ta daga sama sai ga hawaye na zuba daga fuskanta tana kallon sama kamar wace ke tunane.
A hankali ya bar gurin da yake ya tako zuwa gare ta ya zauna daf da kafanta yana fadin na tuba mamaki yafe min don Allah .
Mama idan kinyi fushi dani haka ina zan saka kaina ga daddy shima ya dauki zafi dani na rasa abinda ke mun dadi a garin nan.
Sai lokacin hjy jummai taja wani irin ajiyan zuciya tace fushi babawo dole muyi dakai yanzu ina kake son nakai wanan abin kunyan da komawa bayan daka ja min a garin nan ?
Idan maganan nan ta fashe da wani ido zan kalli mutane dashi a matsayina na mahaifiyar ka ke nsn bamu baka ingantattacen tarbiyan daya dace da kaiba ke nan.
Mama nagane kuskure na yanzu don Allah kuyi hakkuri da abinda ya faru tace hakkurina daya ne babawo.
Gara tun wuri kayi hakkuri da wanan yarniyar ka cire ta a ranka kafitar da zancen kun taba zama a zuciyar ka.
Ya dago kai a raunane yana kallon ta tare da fadin mama idan nayiwa merry haka ban kyauta mata ba tana fa dauke da cikina yanzu haka.
Babawo idan kana son kanka da lafiya karabu da ita tun kan Alh ya yanke hukucin mai tsauri a kan mu baki daya don babban aiki ka daukowa kan ka nan gaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button