NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAN IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:42 – ????????????: RABBANA ATINA FIDDINIYE HASSANATAN WA FIL A FIRANTAN HASSANATAN WA, KIN,NA AZZABAN NAR

Wani kallo take mai ba don taso ba ta kyale shi don ya fito mata a namijin sak ranan babu hanyar ko daman da zata fada mai wani magana kuma akan wanda ya fada mata don duk abinda ya fada tasan gaskiya ne.
Lalai tana da rauni a zamantakewan su to amma ai duk da yan aiki keyi komai kamar yadda yace bata gaza wurin basu umurnin komai ba.
Ganin bai kulata ba sai harkan gaban shi yakeyi ya barta zaune a dakin kamar ba mutum wurin yasa ta tashi fu fu fu ta fice zuciyar ta cike da bacin ran shi.
Tana gani bai mata adalcin ba akan komai kokarin yake ya fifita wasu yanzu a kanta abinda ko ba zata taba bari ya yuyu ba ke nan a gidan.
A hanyar ta na fita ne suka hade da hjy maryam zata shigo ko kallon arziki bata samu ba a wurin ta, ta wuce ta fuuuu ta dan kalleta tare da sauke murmushin keta a gefen fuskanta.
Da sallama ta shigo dakin ya dago ya bita da kallo ranshi a bace har lokacin ta dan dade a tsaye bai dago kai ya kalle ta ba sai da tayi gyaran murya ya juyo a fusace yana fadin.
Kin zo hada wani sheri ne a nan kuma ke may yasa baki barin halin ki na sarika noke ne a gidan nan nasha sanin kina wanan halin ina zuba maki ido ko zaki canza sai dai abin naki ya fara kureni a yanzu.
A marairaice tace may kuma nayi kake fada min haka Alh da shigowana ban san matsalan ku da matar ka ba zaka aza min laifi irin haka na zargi ?
Ba zargin ki nakeyi ba don Jummai ta fada min kece kika kai mata tsegumin yarinyar nan Fatima yar wirin maimuna.
Wiki wiki tayi da ido tana dukar da kai kasa tana cewa ni bada wani manufa na fada mata ba don dai naga yarinyar ta girma ne shine nake magana amma in hakan ya bata ma rai kayi hakkuri.
Yace wanan abin ya isheni kun dauki tsana kun sakawa yar mutane may ye laifin maimunaa wurin ku har make ita jummai din wa ta bari a cikin ku tunda tun akan auro kine bamu da kwanciyar hankali da ita a gidan nan.
Abinda baku sani ba shine hadin kan ku yanzu na dauko hanyar gyaran shi tunda ba na Allah da Annabi bane sai kuje can ku hade kan ku ni kuma zan hade maimuna din mu gani.
Yarinya kuma tazo ke nan da zama a gidan nan babu idan zata sai ku dafata kuci idan kuna iyawa ku zauna lafiya
Yana fadin haka ya juya yana kokarin saka babban rigarsa nan ya barta ya fita batunta tana tsaye kanta a sunkuye ta kasa koda furta wani abin kuma balle ko ta motsa don bata taba tunanen mijin nasu yasan sari ka noken da takeyi tsakanin shi da matar shi ba uwargidan su.
Sai gashi yau daga sama yana fada mata halayen ta a natse gashi ta kasa fadin abinda ya kawo ta dakin don nauyi da kunyar abinda ya gama fada mata.
Yana gamawa zai fita ya kara fadin ku baku ko tunanen kaddara da mutuwa ya kawo maimu da yar ta cikin mu yanzu kun manta kaddara tana iya fadawa a kan kowanen ku don Allah babu inda baya ikon shi a duk lokacin da yaso.
Wani irin yanayin nadama yazowa hjy maryam sai dai kafin tayi magana ya gwauta ta yai ficewan shi daga dakin ya barta tsaye tana sauke ajiyan zuciya.

Ina zaune a falo babu kowa sai tv dake ta faman aiki shi kadai  babu abinda nake sai faman tunanen makoma a gidan Alh sani da akace zama a yanzu ya dawo nan din din din.

Hjy maimuna ta fito daga daki ta tsurawa diyar nata ido na wani lokaci haka yasa ta fahinci yarinyar tayi nisa a tunane wanda tasan ba na komai bane sai na kakarta.
Ke sayadi shiru sai data fada sau biyu firgigit Fatima ta dawo cikin hankalin ta tare da dago kai tana kallon mahaifiyar nata sai kuma tayi kasa da kan ta don kawar da idonuwan ta da suka tara hawaye a lokacin.
Take tausayi da soyayya yar ya tarsu a zuciyan ta wuri ta samu gefen yar nata takai zaune sai data sauke ajiyan zuciya kafin tace.
Kiyi hakkuri sayadi ki dauka wanan wani abu ne kaddarare ya hau kan mu dani dake duka nasan akwai zafi a yanzu raba ki da kakar ki danayi a lokacin da kuke bukatan junan ku.
Amma ba yadda zanyi ne yin hakan ya zama dole a gare ni don samun ci gaban ku baki daya nan gaba .
Munyi maki alkawarin duk hutu idan kina son zuwa wurin ta za a kaiki ko ita tazo nan tunda naji Alh na maganan taimaka muna ma ta hanyar dauko zuwa asibiti nan.
Kin san kuma don ke ce zaiyi hakan daba haka ba sai dai a barta can ta halaka kina ji kina gani tunda babu abinda zakiyi.
Tun zaman ta data fara magana sai yanzu naji sanyi ya ratsa min zuciyata jin za a dauko min manjo kusa dani da gaskiya.
Tace amma fa hakan bai faruwa har sai kin sake ranki a gudan nan ya gani haka zai sa yaji karfin dauko manjo din kusa dake.
A hankali nasa hannu na share hawayen da ya bata min fuska da farko na sauke ajiyan zuciya tare da dago kaina na kalle ta a karo na farko data zauna a gurin .
Tace kwarai amma fa sai kin daina wanan tunanen yaga kina walwala a cikin mu kin sake jiki da kowa a gida nan kin rugumi yan kannen ki kin saka su a jikin ki.
Kin mayar da hankali a wurin karatun ki na boko dana mahamdiya hakan zai sa ya ji dadin tallafa muna amma idan kina cikin wanan halin karshen shi ma yace a mayar dake can din kin ga ke nan ke kika cuci kakan ki mai neman taimako a yanzu da kanki.
Da sauri na kara kallon ta tace eh ke kika cuce ta mana tunda kin ki ki kwantar da hankalin ki mukai ga manufan na son ya taimaka maku tunda ba halin in fito baro baro ince ga yadda nake son aiwa mahaifiyar tsohon mijina daya mutu.
Da kyat na bude bakina da yai min nauyi nace mamu na daina insha Allah zanyi kamar yadda kika ce inyi insha Allahu.
Tace da kin kyautawa kanki tana mikewa take fadin hakan daga haka ta fice a dakin ta barni ci gaba nayi da tunane can dai na dan gano abinda take kokarin fahintar dani din da sauri na mike na tsiri gyaran falon dole har zuwa dakunan kwanan mu duk dako a gyare suke a lokacin.
Ta dan dauki lokaci sai gata ta shigo tsayawa tayi tana bin falon da kallon aikin danayi har zuwa bedroom din ta sai dai bata tarar dani a falon ba lokacin na shiga wanka.
Na fito daidai lokacin ta leko dakin nawa tana fadin yanzu Alh ya bugo min wai gobe za a kaiki makaranta ai maki inter view.
Sai dai ina ganin kamar makaranta daya zaku dinga zuwa da sauran yaran gidan nan don haka nake son ki koyi kawar da ido a kansu domin su din ma kamar sunfi iyayyen su kishi dani a gidan nan.
A Cikin rashin kuzari na amsa mata da to kawai babu abinda zancen bayan wanan amsan don yanzu ba zance ga diyan gidan ba tunda ban san ko dayan su ba har lokacin.
Takai kofa ta juyo tana fadin kina iya yin sallah yanzu don azahar ya yi nake gani idan kin idar sai kije gun Gwago tana tambayan ki wai kwana biyu baki shiga ba gurin ta ba.
Duk a sanyaye nake jarbawa do har lokacin ban gama walwalewa daga damuwn da nake ciki ba.
Ban gama shiryawa da wuri ba don haka na bata lokaci zuwa sashe Amma din har lojacin da kanne na suka dawo gida daga school.
Wanka nayi masu ba tare da umurtan mamu ba don gani dama na kawai cikin kokarin ganin na sake kamar yadda mamu ta bukaci inyi.
Sai dana shiryasu muka zauna cin abinci wanda na gani ga fuskan mamu hakan yai mata dadi ba kadan ba saidai bata fito fili ta fada min hakan ba.
Mun samu amma zaune da yan matan mama hadiye da suka dawo makaranta basu ko cire uniform din jikin su ba suna zaune dashi muka shigo part din da sallaman mu.
Amma tace wa nike gani nan kamar yar bauchi wai nikan aruwa uwarki rowan ki takewa mutane ne a gidan nan.
Ace muna gida daya tun shekaran jiya rabon da in saki a idona ko da yake takawo min uzurin baki da lafiya ne.
A raina nace Allah sarki uwa ke nan ta boye halin da nake ciki ashe bata fada masu gaskiyan abinda nake mata a part din ba don in na shige ban fitowa ina ciki zaune ko kwance ga matsin da nakewa yaranta koda yaushe.
Har kasa nakai ina gaida ita yayin da yan matan biyu dake zaune ban ko ishesu kallo ba a gurin tana min ba,a tace ke ni kawar ki ce ki daina tsugunna min.
Ga kujera can ki zauna yarinyar albarka kin samu tarbiya irin wanda ya dace diya mace tayi ba irin wa yan nan marasa hankalin yaran gidan nan ba tana magana tana nuna jikokin nata dake zaune.
Sai kuma ta sake juyawa wurin su tana fadin ga yar uwarku nan nasan baku santa ba diyar maimuna nane tadawo nan gurin mu da zama ke nan ita ma.
Kara sako min idanuwa sukayi suna kallona dayan tace a nan gidan itama zata zauna ke nan ?
Amma tace gashiko kin ji na fada maku dama ai itama yar gidan nan ce ba bare ba a binda yayiku shiyayi ta itama don haka ina son a zauna lafiya a tsakanin ku.
Suna wani ya mutsan baki tare da fadin mu may ye namu a ciki sai dai idan wa yancan dake kurin gidan su ne kullun.
Amma tace rabani da zancen su daku dai nan nake magana idan kanku yana hade wane su su kawo maku wanan iskancin.
Dayan ta koma ta kwanta ba tare da ta furta komai ba sai mu ke fira da Amman jefi jefi wanda ba wani hira bace ita dai ce mai tambayana labarin kakata ina dan bara amsa daya dace.
Mun dan dauki lokaci a gurin ta na kado kan yaran muka dawo part din mamu inda muka samay ta tana girki.
Ban zauna ba na nufi kitchen din gurin ta tare da tambayanta abinda zan kama mata dan murmushi tayi tare da fadin.
Koma ki zauna na kusa kammala ba abinda zaki iya min yanzu kan nace nafa iya girki don nike girka muna abinci a dakin mu kuma manjo na cewa yayi dadi.
Tace eh lalai manjo kan tace yayi dadi tunda girkin mu ba iri daya bane ki bari sai nan gaba kyayi ai ban dai fita ba na kama dauraye kayan da nagani tayi aiki dasu kafin in fito kitchen din.
Ban yi wani hiran dare ba tunda ban saba kai wani lokaci a falke ba da anyi magariba nake shigewa barci don hakane muna gama cin abinci nayi masu sai da safe.
Washe gari tunda na tashi ban kwanta ba a zatona tare da yaran zamu fita amma sai naga har sun fice batace min komai ba.
Haka yasa na kara shigewa na kwanta ban sani ba ashe barci ta dauke ni a can cikin barci na nake jin ana tasheni a hankali na bude idona mamu tana tsaye a kaina tace ki tashi ki shirya ga mai kaiki school nan zuwa .
Tana fadin haka ta fita ta barni a dakin na shirya wani dogon rigar na saka na tamfa sai hijjab dina dana dauko.
Na dawo falo na zauna ita kadaice duk yaran sun wuce makaranta a lokacin don haka dags ni sai ita a lokacin muryanta na tsinkayo tana fadin.
Don Allah ki natsu idan kunje don a san ajin da zasu ajeki a nan din don karatun na yasha bamban dana can sosai nna gyada mata kai kawai bata kai ga ci gaba da maganan ta ba mukaji sallama daga kofan part din ta.
Ta amsa tare da fadin Ahmed shigo mana ka tsaya kuma can ya shigo yana dan gyara natsuwan shi a natse suna gaisa wa ta kalloni tana fadin ga yayan ku na nan nace ina kwana ya amsa a dan sake da lafiya.
Anzo lafiya ko yaya mutanen gida ?
Nace suna lafiya ba tare da ya karasa shigowa ba yace idan kin shirya sai ki fito mu tafi don Alh najirana zamu fita dashi.
Hjy tace a shirya take zuwan ka take jira kawai a dauki hijjab dina dake gefe ina kokatin sakawa a jikina tace ubangiji Allah ya bada sa,a na amsa da amin tare da fadin sai mun dawo.
Ta kara fadi Allah ya tsare ya bada sa, a muka fice mun fito daga part din tane naga hjy Jummai a karon farko tun shigowa na gidan mace ce kamar basamudiya ga tsawo ga kiba sai dai bakace sosai amma tana da dan kyau fuska gaskiya.
Kallo daya tai muna ta kawar da kanta gare mu daga itama fita zatayi a lokacin don makulin motar da take kadawa a hannun ta ya nuna alama.
Kamar yadda naji ya gaida ita nima haka na gaishe ta sai dai banji alaman ta amsa mako dayan mu ba.
Muka fice itama ta fito a daidai lokacin ta shiga nata motan tare da wata mata daga cikin motar mu ina kallonta sun zuba muna ido musanman mani din suna magana.
Tunda muka fara tafiya ya kunna kira,a a motan na shek Abdullahi Abba zaria a hankali nima nake dan kama inda na iya a cikin karatun.
Mun danyi nisa da tafiya naji yace fatima kike ko na amsa a sanyaye da eh amma wasu suna kirana da sayadi wasu kuma suce min A ruwa, sai dai kakanina kawai ke kirana da a ruwan nan.
Yace Fatiman dai yafi dashi zamuyi maki amfani a school din ke nan na gyada mai kai yakara cewa, kina zuwa islamiya a can nace eh sai dai ba ko yaushe ba don ni ban iya karya ba.
Subbahanallahi naji yace har sai dana firgita ina kallon titi ko wani abu ya gani ya firgita shi ashe wai magana tace yake wa tasbihi.
Don may baki zuwa kullun yace baki san shine zai cece kiba gobe kiyama wanan ai yafi na bokon da kikaga an mayar da hankali gare shi ma,ana sosai.
Ko baki san da haka ba ya kara tambayana yana mai juya tare da dan kallo na nace naji ana fadin hakan .
Sai naga ta dan saki murmushi kadan tare da fadin ji ma kikayi baki tabbatar ba nace hakana ne gaskiya yace to kin gane ina son kiyi min alkawari daya don Allah daga nan idan mun fito zan biya islamiya dake kusa da layin ku in maki register a nan.
Don Allah ki mayar da hankali sosai ga karatun duka biyu wataran zasu amfane ki sosai jin nayi shiru yace kinji ?
Nace eh cikin gyada mashi kai kawai yace alkawari fa kika dauka zakiyi tsakani da Allah kada in kai ki kwana biyu kuma kice kin daina.
Nace a sanyaye zanyi don ko mamu naji tana maganan islamiya din gare ni yace dakyau shiyasa nake kara son halin hjy maimuna wallahi akwai sanin Allah ga al,amarinta .
To yanzu kin gani tunda itama tana so kinga hakan zai mata dadi ni kuma nayi maku alkawarin zuwa in kaiku kullun kuma in dauko ku kin yarda da hakan ?
Nace na yarda, banji kince in sha Allahu ba yace cikin dan kallo na nace insha Allahu din.
Dan dariya yayi mai sauti yace bari mu gama da nan din sai mu wuce can ganin yana shiga wani gida mai kyau yasa na mayar da hankalina ina tunanen ina zai kaini kuma ?
Sai da muka shiga naga ashe babban makaranta ne haddade mai kyau ga yan makaranta nan birjit dasu maza da matan su kowa harkan gaban shi yakeyi a gurin.
Wani wuri muka tsaya da motar yace bissimilah muje na fito bayan ya bude min motar don ban iya budewa ba.
Office din shugaban makarantar muka nufa namiji mutumin sai dai ba wani mai shekaru ba sosai muna zuwa suka gaisa da alama sun san juna sosai dashi don sai da suka dan taba hiran yaushe rabo dashi kafin su dawo zance na.
Niko ina zaune sai raraba idanuwa nake a office din sai can naji yace wanan ne yarinyar yace eh itace kanwar tawa.
Ya juyo gareni yana fadin maye sunan ki nayi saurin Fatima Abubakar Azare kallon Ahmed din yayi yana fadin na dauka ai yar garin ku ce ?
Yace a, a diyar Alh nane a azare ake tayar da ita yace masha Allah fatima wani aji kike a can nace to a can ina jss 3 muyi exam din zuwa ss1 ne .
Yace kai ya akayi karama dake karatun ki yai sauri haka amma ba matsala bari mu gwada ki mu gani.
Waya ya daga ya kira wani layi ba a dade ba sai ga wata malama ta shigo suka gaisa ya nuno mata ni yace ina son ki gwada min wanan yarinyar ko zata iya wucewa ss.
Tace yes sir tashi muje ko ta fada tana kallona na mike na bita ashe da ace ina zuwa makaranta dani gifted ce har ga Allah don Allah ya taimaka na amsa duka tambayan da tai min sai wurin lissafine na fadi daya.
Muka dawo fuskanta dauke da murmushi har suna hada baki wurin tambayan ta to yaya tayi making ?
Tace ba matsalan komai wallahi nan gaba ma zamuyi alfahari da samun ta a school din nan in Allah ya yarda.
Ahmed yaji dadi tare da washe baki mutumin yace ta biyo ka ke nan wurin kokari unlike sauran yaran da ka kawo muna gaskiya sai a hankali lamarin su.
Bamu fito ba sai da yabiya kudin komai da aka bukata har uniform sai da aka bani kafin mu bar wurin zuwa islamiyan nan ma sai da akai min gwaji akasan ajin da za a ajeni suma har uniform suka bani kafin mu dawo gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button