NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Yinin ranan ya kasa bude wayogin shi tun lokaci da salma ta kirashi tana fada mai halin da mahaifiyar su take ciki yace bai gari ya kashe wayoyin nasa.
Can ya mike ya fito ya nufi mota ba inda zai tafi haka yasa ya nufi beach don ya sha iska a can tafiya yake a bakin beach din hannayen shi duka biyu a cikin aljihun wandan shi sai dan kafan wandon daya tankwashe su kada ruwa ya bata mai.
Kusan awa daya ya dauka a haka bai kaiga samo ma kanshi mafita ba a lokacin can yaja ya tsaya a guri daya yana fadin.
Imposible imposible yana girgiza kanshi a hankali, nan ya fara tunane baiga dalilin hana shi abinda ranshi ke so a yanzu ba saboda wani akida can da bai sabawa addinin shi ba.
Shidai yasan ba zai iya auren wata yar hausawa ba yanzu a yadda yake ganin su lulube ko yaushe a cikin hijjab gani abin rufe fuska da suke wani amfani dashi suna rufe fuska wanda bai san dalili su na yin hakan ba ?
Kai ya girgiza daya tuna harda wanan yar ficiciyar yar maimunan wai rufe fuska take wa mutane ko may take boyo oho ?
Sai kuma yaja guntun tsuki lokacin daya tuna yadda na fito babu wanan abin rufe fuskan gaba daya sun yi mamakin ganin irin surar da Allah yai min.
Ko shi yasa Alh ke ji dani a cikin yayan gidan kamar yadda mama ke yawan korafin yana mun tsuki ya kara ja yana fadin how comes maimuna ta samu ya haka kamar halfcase wai ?
Ita kanta maimuna inya tuna lokacin data tashi ai haka take da zuben kyau how he wish shima yasamu yara kyawawa haka a rayuwan shi kamar yadda diyan maimuna suke biyo ta da kyawo.
Maimuna maimuna ya furta maimuna you deceved all this care wurin Alh don ya tuna suna secondary maimu din tana da hali mai kyau wanda tun a lokacin maza ke rushing a kanta.
Mama why baki hakkuri don yarinyar nan tafiku da komai da maza ke so a wurin mace don idan ba don wanan alakan auren ta da mahaufin shi ba daya sa yanzu bai sakar mata fuska da can mutumiyar shi ce sosai a baya don kusan tashin su daya tare sukai karatu.
Idon shi ya dan kara runtsewa iskan teku na bugun shi tare da guguwan ruwan dake fesowa har inda yake yana saukar mai da wani yanayi mai dadi dake kwantar mai da hankali.
Zubur ya budo idanuwan shi tunawa da mahaifiyar su na iya shiga wani hali akan maganan da bata san mafarin shi ba.
Tafiya ya dan fara yi a cikin sauri ya nufi inda ya aje motar shi a can nesa da bakin ruwan ya shiga.
Hotel din daya sauka ya nufa ya Sarafa yana sanar mai ya karkare proces din da suke zai tafi kano a lokacin yayi dai dai jirgin marance na shirin tashi a lokacin.
A kano yayi sallah isha,i bai shiga gidan su ba sai da ya dan samu abinda ya cima cikin shi don rabon shi da wani abu ya shiga cikin shi tun safe da ya dan sha ruwan coffee.
Sai dai yayi rashin sa,a don abinda yake gudu ne ya faru dashi a gidan yana shiga suka hade da mahaifin shi da ya fito part din Amma.
Kamar yadda suka saba gaida shi haka ya duka yana gaida mahaifin nashi da sukai haduwan bazata dashi dai dai sabanin yadda suka saba gaisuwa a da can da babu matsala suka hade din nan zai tsaya su dan taba hira kamar wasu abokai.
Sai dai wanan karon yana gaida mahaifin nasa a cikjn tafiya ya karba mai kamar bai san inda ya fito ba a lokacin ya barshi a gurin tsugune yana mashi kallon mamaki.
Faruq ka kyaleshi har ya sauko sai ku fuskaci juna dashi da yardan Allah komai zai zo da sauki kasan yanzu yana cikin fushin abin ne da kai.
Muryan mamu ne da tafito sashen Amma gaida ita, shine ta biyo bayan mijin nasu don bashi abin shan sa da maganin shi don baida lafiya duk wanan lokacin.
Sannu a hankali ya mike yana fuskantar inda muryan nata ke fitowa daga bayan shi duk da a yanzu ba wani mu,amula a tsakanin su tunda ya dawo kasan ya samay ta a matsayin matar mahaifin su.
Saidai yaji dadin nuna kulawata a lokacin gare shi don ko ba komai ta fada mai gaskiya haka yasa ya kakaro murmushin dole a fuskan shi.
Yana fadin ba komai na gode ya yaran karo farko ke nan wani maganan arziki ya shiga tsakanin su tun bayan dawowan nasa tace suna lafiya.
Kadawo ke nan ashe, ya hanya yanzu nake ji a gurin gwago wai kayi tafiyane ashe ?
Yace eh na tafi dan wani aikine a lagosa tun shekaran jiya ina can na gods daga haka bai kara furta komai ba ya wuce kai tsaye wurin Amma.
A kofa ya tsaya yana sallama kamar kulun idan zai shiga sashen don yasan ba ita kadai bace a part din don haka yake tsayawa daga kofa yayi sallama.
Yana saye cikin wani yadi mai laushi fari na maza mara nauyi zaka iya hango farin singlet dake cikin jikin shi gashin kanshi ya kwanta a kanshi sai sheki yake kamar ya shafa mai, maia cikin muryan shi dake ruda matan dake binshi yayi sallaman.
Yayi sa, a daga ita sai mama hadiya da suka gama hira da mamu ta fita ta barsu zaune da Amma suna hiran raman da Alh sani yayi a cikin kwana biyun da zancen nan ya bullo.
Mama hadiye ce tace a a mutan legas an dawo ke nan a ranshi yace ikon Allah ba halin mutum ya motsa sai kowa yaji halin da yake ciki sabanin can da ko daga wurin aiki tafiya ya kamashi zai iya tafiyan shi babu wanda ya sani .
Amma sai gashi nan duk da bai fadi zaiyi tafiyan ba dan fadawa salma dayayi yana lagos duk ya karade kunnuwan mutanen gidan ko.
A, a ashe ya sallamai kine da kike taron shi yayi dan murmushi yana gaida mama hadiye dake kokarin mikewa a wurin da take zaune.
Yana dan shafan keyan shi yace Amma ba a fa shiga tsakanin da da mahaifi ke gaki kina kokarin hadani da gwagona fada yanzu.
Fada kan ai ba,a farashi gare ka don kowa a jirace yake dakai a gidan nan wallahi yanzu dai na gane sadauki baka da kirki sam ?
Tafiya irin wanan har ikko ka kasa fadawa kowa dan rashin daukan mutane da muhinmanci da bakayi ko may ?
Ya dan kara sake murmushi yana zama yace tunda kin gama hadin fada ai zakice haka amma tafiya kuma ayi hakkuri daurowa yayi hakan nima bada niyar tafiya na fita ba a raina aikine ya taso min can na gagawa.
Sai Amma tayi wani hade rai tana fadin ku dai san abinda kukeyi yaran nan ku dinga daukan iyayye da muhinmanci a rayuwa .
Amma ban dauki wanan a laifi ba amma za a gyara da yardan Allah shike nan ko ya fadi yana kallon Amma din sai mama hadiye data kai kofa tace shike nan matar na tuba bata laifi tunda yace ayk hakkuri fada ya kare hajiya.
Ya saki ajiyan zuciya bayan mama hadiye ta shiga yace Amma ya bayan rabo kuma ?
Tace har lokacin cikin rashin walwala sai alheri sai dai mahaifan ka dake cikin tashin hankalin sakon daka bani in basu har yanzu.
Cikin zakuwa yace tashin hankali kuma Amma may nayi aure ne fa nayi ba wani alfasha na aikata ba ?
Kan Amma ya daure da maganan shi tace ban fahinci ba fadin ba wani laifi kayi mai tsauri ba don kayi aure ?
Auren da kake tunkaho kayi a cikin tsarin addinin mu kayi shi ko yaya kai yanzu ka kwatanta a kanka idan diyan cika sukai maka haka zakaji dadi a rayuwan ka ?
Ya saki wani wawan ajiyan zuciya a lalace yace may ye a ciki idan yaro yace ga abinda yake so yi amma sai in mashi fatan alheri final.
Galala Amma ta tsaya tana kallon shi don ta fahinci idan ba sunyi da gaske ba ga yaran sun fara nisa ga barin al,adan su na gargajiya.
Allah ya kyauta ta furta tare da fadin kaga ka samu iyayyen ka ku sulhunta a tsakanin ku yanzun mahaufin ka yabar nan .
Na rasa gane ma jikin shi tun ranan da ya samu wanan labarin ga ba zaman lafiya tsakanin shi da mahaifiyar ka tun faruwan maganan.
Ya gyara zama yana fadin yaya zan tun kari Daddy da wanan zancen a yanzu Amma yanzun nan ma din ai mun hadu ina gaida shi bai karba min ba.
Nasan yana cikin fushi da nine har yanzu ina son in bashi lokaci har ya sauko mu fuskaci juna dashi sannan ni banga abinda zai sa Daddy yaga laifin mama a cikin wanan zancen ba.
Don itama bata da labarin komai so a daina zargin ta a cikin wana magana don Allah Amma .
Kai sadauki in fada maka gaskiya kayi kokarin gyarawa da iyayyen ka don suna cikin fushi da kai sosai ko ni nan don nakai zuciyana nesa ne nasan baka shaku da kowa a gidan nan ba sama dani yasa nake dan sasauta maka.
Ya lumshe ido yana nazarin zancen tsohuwar kafin ya budd idanuwan nasa yace Amma ban taba zaton wanan abin zai kai haka ba wallahi.
Domin irin macen da nake sha,awan samu ne na aure kuma ni zan zauna da abata ba wani ba kuma muna zamun lafiya da ita yarinyar.
Kai rufa min baki mara hankali kai auren fari har kasan abinda ya dace da kaine in ba zamani ba daya kawo mu irin haka.
Ya dan yi dariya cikin dauriya yace Amma ke nan kin san shekara nawa nake nema a yanzu ki duba inda yar maimuna takai fa ga girma da ace nima macd ce da yanzu kin san na haifi sa,anta ko ?
Kai rufa min baki don Allah shekarun ka na banza da bai amfana maka da komai ba sai shiriri ta ina kai ina kwaso muna kafira cikin zuri,ata ?
Haka dai shigowan nasa ya kasance tsakanin shi da Amma don ya fuskaci har tsohuwar take kufule dashi a lokacin duk kan dalilin auren nasa dai.
Mikewa yayi yana shirin fita sai ta kalle shi tace zaka fita bakaci komai a cikin ka ba ba yanzu ka dawo daga tafiya ba ?
Sai da ya mike da kyau yana gyara rigar sa data danyi sequzin yace bana jin yunwa zan fita akwai inda zanje idan na fito wurin mama don ban shiga mun gaisa ba ko dasu.
Allah ya tsare tace a daidai lokacin da ya fara tafiya do barin part din yana jin cikin ranshi babu dadi a lokacin.
Ta rakashi da kallon tausayi don tasan duk abinda yakeyi a cikin dauriya yake yin shi a daidai lokacin hjy maryam ta sawo kai zuwa part din Amma din .
Nan suka hade hanya da shi sama sama suka gaisa da ita ba tare da ta furta mai komai ba ya wuce abin shi.
A falon hjy jummai ya samay su zaune da yan uwanshi dake cin abinci suna ganin shi suka tare shi da murnan ganin ya dawo lafiya.
Hjy jummai dai tana zaune kamad bata ganshi ba ya shigo su salma dake dakin su sukaji muryan shi sai gasu sun fito da murna suna taron shi.
Wani tsawa ta bugawa yaran a take suka sha jinin jikin su a aurin da suke bata bari sin karasa surin shi ba.
A hankali ya daga yana kallon mahaifiyar tasu dmamaki don sanin halinta dayayi akansu sai yau yaga sabanin hakan gare shi.
Haka yasan ba karamin kuskure ya tafka a rayuwan shi ba na rashin sanar masu da zancen tun farkon faruwan almarin ya kamata ace ko bai fadawa kowa ba ya sanar da mahaifiyar tashi gaskiyar alamarin.
Habbin ne ya aje spoom din hannun shi a hankali yana fadin why mama zaki hanasu zuwa gare shi ?
Idan kin mashi haka da wani zai ji da fushin ko dana daddy da Amma ko da namu da kike kokarin hana mu zuwa gare shi ?
Habbib ni kake son yiwa nasiha akan wanda ya maidani ba kowa ba a wurin shi har sanadiyar laifin shi yana barazana da aure na da yafi shekara nawa da kulluwa da Alh hakan bai taba faruwa a tsakanin ba sai akan wanan maganan.
Kasa ci gaba tayi da maganan da takeyi saboda kukan dayazo mata a lokacin yaci karfin zuciyar ta.
Bata taba tunanen irin ranan nan agaresu ba dukkan su gani haka a sanyaye ya mike yana fadin mamakiyi hakkuri idan wanan abin ya bata maki rai don Allah ?
Habbib ne ya mike yana magana a cikin harshen turanci yake fadin bros mu tafi har ta huce don wanan hawayen indan tana ganin ka bai daina fita yanzu.
Bai ki ta kanin nasa ba suka fice daga falon sun danyi magana da habbib din ya fita daga gidan sai ga habbib din ya dawo shi kadai yana fadin Aliyu ya taso su fita.
Ba bata lokaci ya biyo yayan nasa don shima a rude yake ganin mahaifiyar su tana kuka akan dan uwan nasu.
Sun samay shi har ya tayar da mota zai fita suka dakatar dashi komai na rayuwa yayi masa kunci a lokacin.
Hakan da suka samay shi ya sun kara tausayawa dan uwan nasu motar suka bude suka shiga suma sai habbib ya kira sunan yayan nasu bros.
Umar ya dago kai yana kallon su yace ina ganin wanan case din ya kamata mu hada da baba Nuhu muje muyi masa bayanin komai yadda zai iya fahintar mu.
Don yanzu baba Nuhu shi kadai ya ragewa su daddy a matsayin uba da suke jin nauyin shi a garin nan shi kadai zai iya kawo karshen fushin nan da sukeyi haka dakai.
Aliyu yace kwarai hakan yayi daidai don tsohon nan kadai zai iya saukar da Daddy a garin nan kaf don suna jin maganan shi sosai.
Don ko su baba Bala suna hake dakai da wanan maganan don jiya na samay su da hjy maryam suna magana tana kara zugashi.
Suna gani na ita ta bat zancen shiko baba bala yana fada yana fafin su zaka mayar kananan mutane a garin nan ka kwaso masu wata arniya a cikin zuria su ba zasu yarda da wanan shashancin ba.
Habbib yace kai ina tsoron wanan matar wallahi a cikin matan daddy kaf don munafukace ta karshe baka lura da irin munafunci da take kawowa mama na maimuna .
Sai dai sunyi rashin sa, a koda suka isa gidan kofan gidan a kargamay yake a lokacin har tsohon ya rufe gidan shi ya shige ko.
Haka yasa suka juya zuwa gida sai dai umar yana sauke su ya juya don baijin zai iya kwana a gidan mahaifan shi suna cikin fushi dashi haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button