NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAAW
16/11/2021, 23:23 – ????????????: ASSALAMU ALAIKUM WARAHA MATULLAH YAN UWA MUSULMAI, , , , , ,

Idan nace Allah ya isa in kin karata baki biya ace akan novel ina jan Allah ya isa to yar uwa dake da kika fitar mun da novel da ke da kika karanta baki biya alkalin mu Allah na barki gare shi yar uwa.
Kuna raina kalman hada mutun da Allah alhali kun san Allah zai iya yafe maka laifin dake tsakanin ka dashi amma ba zaii yafe na tsakaninka da wani bawan sa ba mai hankali da imani kadai zaigane inda maganata yadosa nagode .
Koda na sauko karfe sha daya saura ba rana don haka banyi tsamanin yana gidan ba a lokacin tunda yarshi da matar suna asibiti nasan hankalin shi yana gurin su a nawa tunane ya tafi tunda safe baya gidan.
Kallon yadda gidan ya danyi mun kura na kwana biyu da bai samu gyara ba don tun kan in kwanta ciwon marin dana sha wanda yai min rabon da na tsaya na gyara gidan.
Na sauko ina bin gidan da kallo aikin gyaran gida na fara saida naga komai yayi yadda nake so na feshe ko ina da kamshi.
Sai na koma kitchen nan ma gyara na fara kafin in dora girki sai da na kusa gamawa naji kamshin turaren shi ya daki hancina hakan ya sanar da zuciyana yana gidan.
Don in tabbatar da zargina a kanshi na dan juya da zuman lekawa koshi din ne ya fito sai mukai arba dashi tsaye kofan kitchen din.
Ina kwana nace mai daga inda nake tsaye lafiya yace ya karaso cikin kitchen din zuwa wurin fridge ya dauki goran ruwa ya fita.
Sai a lokacin na dan sake zuciyana can naji shi yana bugun kofa da kankara ya taushe shi ta baya.
Ya samu kofan ya bude ya fita lokacin na fito kitchen da abinci na aje a saman dining naga ya kara shigowa bai ko kalli inda nake ba ya dauki wani abu naga ya fita.
Ashe kankarane ya rufe motar daga dare zuwa wanan lokaci shine ya dauki abin kawar da kankara da ake fesawa ya fita ya fesawa motar.
Zuwa lokacin na fahinci kamar fushi yake dani don haka nima na fita batun shi dama ba shiga nake ba sai idan ya sakani ciki.
Ya dan dade a wajen har na karya na koma dakina bai shigo ba naso inga ko harda abinci yake fushin da ban san dalilin shi ba tun barowa gidan Yusuf yola da mukayi.
Ko daya shigo ban falon hakan ya bashi daman zama yaci abincin daya gani aje saman dining din sai da yaji ya koshi.
Ranan dai motar da bai shiga ba ke nan sai jirgi yabi zuwa wurin queen ya dubata bai shiga wurin merry ba.
Ya fito ne a daidai lokacin da wasu kawayen merry suka shigo don duba jikin yarinyar dakuma yi mata addu,a.
Yafito ya barsu a dakin a zaton su gurin merry ya nufa saida suka gama da da yarinyar suka nufo dakin da merry take .
Bayan sun gama abinda sukeyi ne suke tambayan ina mijin ta tace baishigo ba yau itama shi take jira don likita yana son ya sallamay ta yace sai sunga mijin ta.
Da mamaki suke kallon juna su kafin guda yayi karfin halin fadin yanzu yabar dakin da Faith take kwance mun dauka yana nan ne gurin ki muyi maku addua a tare.
Fuska ta bata don bataji dadin jin hakan ba daga gare su don suna cikin masu adawan auren ta dashi don dai church din su dayane an kuma taso tare yasa bata rabu dasu ba suma dai black American ne a can aka haifesu sai dai su suna ban addinin su sosai irin sisters din nan ne su.
Ya tafi gurin likitane ina gani ta basu amsa da hakan don kawai kada su zargi komai a zuciyar su.
Fitan su ta mike zaune don dama taji sauki sallama kawai take jira don sai ya saka hannu za a yarda a sallamay ta saboda case din su har yanzu ba akare ba.
Ga iyayyenta basu zo ba don yau sun makara saboda matsalan snow da aka tashi dashi sosai a kasan mutame basu faye wani zirga zirga ba.
Amma wa yan nan yan tsaurin addinin haka suke bi cikin wanan yanayin suna wa mutane addua don kada a sake hanya abi wani addini na daban.
Karshe dai dole saida merry ta jira zuwan iyayyenta don su sukai komai har saka hannu akan zata kai kanta police station.
Sai dai ita Faith har lokacin ba,a bata sallama ba don yarinyar tafi jin rauni a jikin ta saboda koda abin ya faru tana gaban mota ita da uwar a lokacin.
Matsala shine don suna a cikin maye sukai tukin ganganci wanda hakan doka ne na kasan London din.
Sai dai duk abinda ake ita merry hankalinta yana ga mijin ta da bata san dalilin rashin zuwan ta ba sai dai ko maynene yana da nasaba da dan matsalan da suka samu ranan a asibiti dashi harda iyayyen ta da suka so saka baki a cikin case din lokacin.
Wanan abin yayi matukar bata mamaki da haushin yadda ya share su din saidai abin mamakin dataji gun yarsu shine kullun uban na zuwa ya duba yarshi asibiti haduwa ne kawai basuyi dashi.
Gashi tayi neman layin shi har ta gaji ance baya shiga duk lokacin da ta kira layin nasa din.
Haka yasa ta kulle shi a rai sosai tasan duk zai gama fushin ne ya dawo ya nemay ta ko ya samy ta a can garin da take aikin ta din.
A nawa bangaren kuwa zaman doya da manja muke a gidan daga gaisu sai kuma gobe in mun gaisa din sai dai bai fasa cin abincin da nake sakawa dashi ba ko yaushe .
Watara sai dare yake fita ban sanin dawowan shi watarana kuma tun safe idan ya fita sai yamma yake dawowa gida.
Gashi zaman shi a nan ya bala,in takurawa rayuta sosai don banda halin leka ko waje kamar yadda nayi mai alkawarin yi din kafin in dawo gidan.
Har Allah ya nuna mun koma makaranta muna cikin wanan halin dashi hakan ba karamin dadi yai min ba don ina haduwa da abokai a can ina dan rage miyau na.
Ranan na dawo na samu takarda saman dining ya aje min cewa zaiyi tafiya sai ya dawo bai fada min inda zai tafi ba nima kuma ban damu da in sani ba.
Zaune yake a cikin jirgin da zai kaisu kasan Malaysia a hankali ya runtse idanuwan shi ba abinda ke yawan fado mai a rai sai irin karfin halin wanan yarinyar da yakewa daukan yar kankanuwar yarinyar amma sai wayau da hali irin na manyan mata a tare da ita.
Zarah ya furta a hankali shi kadai yake magana kamar zarare ya dan sake murmushi a fili tare da mayar da kanshi saman kujera ya lumshe idanun shi.
Taso yin kamanni da uwarta maimuna sai dai ta dara uwar da abubuwa da dama yanzu ko ta halaiyan su yasha bamban.
Yasan zarah yarinya ce mai hazaka da kokari don yawan bibiyan karatun na da yakeyi ba tare dana sani ba.
Ga komai tanayin shi a bisa gaskiya da koyi da addini da abinda iyayye suka koyar da ita a gida.
Ya kula yarinyar batada kyashi ko hassada a rayuwan ta don da watace da yanzu ya fara gani ko ji akan irin zaman da sukeyi zata iya samun shi makale da merry a jikin shi amma bata taba nuna bacin ranta ba.
Yasan da ace merry ce da wani fitina ya afku yanzu don da kowa ya gama jinsu ko.
Zarah tana da kunya da kamun kai don bai taba ganin wani shiga a wurinta na asha ba tun zuwan su nan ko a gida ya kulatafi saura kula da kama jiki a gidan su.
Ya kula yarinyar bata da yawan magana amma akwai bakar magana da manyan magana a bakin ta batare da kiyas tawa ba.
Ya lumshe ido tare da fadin yarinya karama da halin manya nisan tunane da sanin ya kamata ga babba saboda irin biyayyan dokan daya sa kuma tabi.
Ya kara mayar da kai yana fadi a ranshi yarinyar tana da saukin kai da saurin shiga mutane ko shine yasa take saurin samun sabbin abokai a nan wanda ya hana mata hakan.
Tana da saurin shiga zuciya duk wanda ya ganta don ladabin ta ga gaisuwa dole jama,a su so zarah don ita din kyakyawace mai kyawon hali.
Ido a lumshe yace zarah kedin kyakyawace kina da duk wani abinda da namiji yake bukata gun mace musanman wanan idanun irin na uwarki har sunfi na uwarki dara dara ga yawan lumshesun da takeyi musanman idan tana cikin hushi hakan yana kara burgeshi da shiga ranshi.
Kai ya girgiza yace ke komai kin iya karamar alhaki dake zarah tafiya kamar wace take tsoron kasa a cikin natsuwa komai sauri take takon ta.
Raban da bata da lafiya yaga gashin kanta ya dauka kari tayi amma daya fahinci nata ne saida yaji tsoron yawan gashin kan nata saidai baya samun gyara yadda ya dace shiyasa
Wanan kuma yasan laifin shine da bsya bata kulawan daya dace ta samu daga guri shi.
Astangafurullah ya furta da sauri tare da fadin Umar may kakeyi hakan wani nauyi ka daukanwa kanka haka ?
Ka kawo yar mutane nan bisa amana ka watsarda ita tana rayuwa a cikin kunci da kadai duk ta dalilin shi.
Saboda tsoron ya lalatawa yarinyar mutane rayuwa ya keyin hakan don kawai shida ita su kaucewa furcin mahaifiyar shi ya dannewa yarinyar mutane hakkin ta haka.
Gaskiyan Aliyu dayace dashi ranan da mahaifin su ya fahinci hakan da wani ido zai kalli mahaifin nasu dashi.
Zaiji kunya matuka yasani don ko Amma fushi sosai zatayi dashi yan gidan su dama wasu mutanen zasu dauka tsoron matar shi merry ne a zuciyar shi.
Wani irin daci da bacin rai ya ziyarci zuciyar shi lokaci guda bai sake bude idanun shi ba sai lokacin da yaji mai sanarwan jirgin na fadin sun iso kasar malasia jirgi zai sauka kowa ya shirya.
Washe gari ya kama weekend ban fita ko ina ba sai zagewa sosai danayi na gyara gida na tsabba na wanke kayana da duk wani abindake bukatan wanki a gidan.
Har dakin yaya ban barshi hakana ba dukda fushin da yakeyi dani kafi ya tafi tafiyan dayayi.
Na gama nayi wanka na dawo falo dauke da littafin kawa,idina ina karantawa.
Bell din gidan yayi kara ina mamaki waye zaizo min da wanan ranan anty farida ne da dukkan yan gidan su akofan da murna na tare su ina fadin kushigo babana sannun ku da zuwa.
Tace yau dai gaki ga baban naki kullun sai damun yakeyi yaushe zaki zo ko a kaishi gidan wanan anty da takece min babanta.
Babana yau gaka a gidan yarka da fatan a nan zaku kai dare a gidan nan anty farida tace muna nan hardare tare dake.
Littafin dana aje zainab ta dauka tana kallo kagin tace anty wanan kur,anine haka ?
Dan murmushi na sake a fuskana nace wanan litafin idan baki sanshi ba zainab addinin mutum ragage ne malamai sukace.
Fuska ta bata tare da fadin yanzu anty ana nufin ko wani musulmi sai ya iya wanan littafin yake musulmi ?
Na girgiza mata kai nace ita musulunci addine mai sauki da saukin fahinta zainab kinga wanan ya kumshi babin sallah da ka,idojin wanka da saura su ana son ko wani musulmi yasan wasu abubuwa daga cikin shi ma,anan wanan littafin ke nan.
Tace yauwa anty sai kuma ta kalli anty farida tace barshi kawai anty.
Anty farida tace kiyi tambayan ki kawai idan kina dashi tace a dan marairaice dama tambaya nake son yi akan wankan tsarki.
Kaina girgiza kafin ince kai haba zainab aiba akunya ga addini kowa dan koyo ne ki saki ranki kiyi tambayan da kike so.
Ni anty idan zaki mun duka aizanso wallahi nace to shike nan da farko dai ai kin san wanka ya kasu akan abubuwa uku ne malaimai sukace zuwa hudu.
Na farko shine wankan shiga musulunci sai na biyu wankan janaba saina haila dana Nifasi sai cikon na biyar shine idan Allah ya karbi ran bawan shi shima akwai wanka na barin duniya da ake masa.
Farilan wanka kuwa sune yin niya yayin farawa da gagautawa da cudanyawa da gama jiki ko ina da ruwa.
Sunnonin wanka kuwa sune wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu kamar yadda kikasan kina yin alwala nakai mata har karshen shi.
Sai kuma mustahaban wanka sune shine farawa da wanke najasa ma,ana wanke gaba inda a nanne zakiyi niyar wankan abinda zakiyi wankan kanshi nan ma nayi mata bayanin komai yadda zata gane.
Don nasan tunda tayi tambayan nan tana da bukatan bayani a natsene.
Har anty farida ido ta zuba min sai danace zainab da fatan kin fahinci abubuwan dana fada maki yanzu.
Anty farida tace ai ba zainab harni kin tuna min wasu abubuwa a nan a gida fa na karanta wanan har karshe amma saboda rshin bita a nan kinga na manta wasu abubuwa daga ciki.
Nace anty karatu baison ka manta dashi sai shima ya manta da kai komai ilimin ka kuwa don kinga ni ban yarda na aje karatuna addini ba tunda nazo.
Mun kai wani lokaci dasu a gidan munsha hira ranan sosai kafin su tafi mijin ta ya zu da dare ya dauke su ina jin kamar kada mu rabu da juna dan dan zaman a tare ya tuna min da abubuwa da dama gamay da gida Nigeria.
Bayan tafiyan su gidan ya koma min ni kadai kamar bashi bane yake da hayaniya dazun dan lumshe idona nayi daga inda nake zaune saman kujera ina tunane sai ga hawaye yana zubowa a idona.
A daidai lokacin da ya umar yake can kasan malaysia yana gudanar da aikin daya kai shi can na gyaran matatan su na kasan.
Sai safe ya farka ya dan fito haraban masaukin su ya tsaya yana kallon yadda suke zirga zirgan su duk da ya sha yawo kasashen duniya sai dai hakan bai hanashi mamaki mutanen kasa ba.
Yana ganin yanayin su da wahalan su kamar yan tashi kasan Nigeria sai dai nan din ya dara Nigeria sosai da abubuwan zamani naci gaba amma akwai tallakawa masu tarin yawa a kasan.
Yayi mamaki ikon Allah yadda ubangiji ya tsagosu a wanan nahiyar kuma suna musulmai don kusan fiye da rabin kasan duk musulmai ne.
Mata suna saye da siket da rigar wani nau,in yadi irin nasu da dan hijabi iya wuyan su yayin da mazan yawancin su suke daure da zani da hula irin ns kasan su.
Ya gama kallo da shan iska ya koma ciki don ya shirya don yau da yamma yake son komawa kasan London din daya baro.
Sai ya samu kanshi da sha,awan son yayi tsaraba ga iyalin shi akaro na farko a rayuwan shi don shigan matan mudulman kasan ya burge shi sosai.
Kasuwan su ya shiga ya dan zaga ya zabi masu tsada harda hijjaban su dan ya kula da irin hijjab din da nake amfani dashi ne gurin fita iya kafada.
Da iri kudin su na kasan daya canza zuwa ringgit da suke amfani dashi ya biya su ya dawo masaukin shi ya shirya bai tsaya wani abuba motar da zata kaishi airport tazo ta dauke shi tare da checks din magudan kudin daya samo a kasan.
A wanan daren da nake zaune ina kewan gidane ya iso har ya bude gidan ya shigo ban ji shigowan shi ba saidai gani mutum nayi a gaba ya tsaya yana kallona da mamaki karara a fuskan shi.
Ganin gani zaune ina tunane sai hawaye ke zubo min a idanuna yanayin fuskan shi ya dan sauya.
Ya tako har inda nake zaune sai lokacin na dago kai na dan fitgita da ganin shi yace zauna abinki kin tsorata da ganina ko ?
Ban zauna din ba don sai na daburce na mike tsaye ina masa sannu da zuwa tunda ko banza ai ya sallamayni a takarda.
May ya samayki kike kuka haka zarah ke kadai a gida yana tambayana cikin kura min idanuwan shi akaina.
Ban iya bashi amsa ba don tsareni da idanuwan shi dayayi a lokacin madu firgitani da tsoro shi wani lokacin.
Ganin ba zan bashi amsa ba naga ya juya ya fita daga gidan bai jima ba naga yana shigowa da manyar jakkuna a hannun shi ina tsaye na jingina jikina da kujera.
Saida ya gama shigo da komai gidan ya tsaya yin waya daki na shige abina na barshi gurin ban fito ba sai safe na samu yaci abincin dana tuka na semo da mukaci da su anty farida wanda na raga zanci da dare na kasa ci.
Gyaran gurin na shiga yi har zuwa gidan na hada muna abin karyawa don satin ukun da yayi baya kasan naji dadi kasancewa ni kadai sosai.
Bayan na gama na shiga nayi wanka ina zauna na saka kaya ina dan kara gyara fuskana duk da ba wani yin kwaliya na damu dashi ba dama.
Ya shigo dakin ya samay ni ina rufe powder dana shafa a fuskana kallo daya zakai mai ka gane dan fadawan dayayi wanan lokaci.
Ga ba walwala a fuskanshi ko kadan tun shigowan shi na kula da hakan gare shi.
Ganin shi nayi saurin tashi tsaye ya nuna min indana tashi yana fadin komaki zauna magana nazo muyi dake ai.
Ban iya boye mamakina ba nakai zaune sai naga yakai zaune bakin gadona tare da hade hannayen ya tokare haban shi dashi yace.
Zarah may ye damuwan ki danazo na samu kina kuka ya tambayeni cikin kara tsureni da idanuwan shi.
Ban iya bashi amsa ba kaina kuma yana kasa na kasa dagowa in kalleshi ganin ba zan amsa shi ba ya sake fadin tambayan ki nake zarah ?
Na dago kai ina kallon shi nace ba komai yaya idona suna tara hawaye ko ina tauye maki hakkin kine zarah ki fada min ?
Jin hakan dayace yasa na dago idanu nadan kallo shi sai na kara dukar da kaina kasa.
Gani nayi yanauin fuskan shi ya sauya min sosai da alama yana son jin abindake damuna din lokacin.
Kiyi hakkuru zarah nasan ina danne maki hakkin ki nima hakan ba da son raina bane hakan ke faruwa a kanmu.
Wani mamakin ne ya kamani a karo nabiyu na sake dago kai ina kallon shi .
Hawaye suka soma zubo min naji yana fadin na tambaye ki maynene matalan ki zaki fara min kuka.
Jikin shi ya danyi sanyi ya dago a hankali ya mike tsaye tare da takowa zuwa inda nake naga ya miko hannayen shi yana kokarin mikar dani tsaye daga zaunen da nake.
Bayan ya mikar dani ya dago fuskana yana son mu fuskanci juna dashi da sauri nace yaya ni banda matsalan komai in ma ina dashi ai kasani.
Murmushi naji yayi ya dan rungumoni zuwa jikin shi kokarin kwace kaina nayi ina fadin amma kasan hakan bai dace ba a tsakani mu yaya.
Yace cikin mamaki kina a matsayin matata kike furta hakan gareni zarah ido na dago ina kallon shi jikina na rawa nace.
Na rokeka yaya ka barni inyi rayuwata a yadda nake kai mana adalci dani dakai tunda kasan a matsayin da auren mu yake .
Yace ban san komai ba ga auren mu sai kin fada min yanzu zan sani yana kallona cikin son jin bayani a bakina.
Amma kasan hjyn ku abinda ta furta akan mu ko ka manta ne yanzu ya girgiza kai ya sake ni tare da juya bayan shi yace.
Wanan kuma abinda ya shafeni ne nida zuciyata ba wani ba don nike auren ki ba hajiyata ba.
Amma ai tana iko a kanka ko don uwa ba wasa bace ya juyo ya fuskance ni yana fadin idan muna magana kada ki kara jefo zancen iyayyen mu ciki don ina so mutum mai daraja iyayye.
Naka ka sani don banga kana daraja nawa uwar ba don tsaban darajan da bata dashi a gare ku kowan ku kaf yan dakin ku maimuna kuke kiranta dashi babu darajawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button