NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ENGLAND

A hankali na bude udanuwana na sauke akan yaya dake tsaye kaina ya kura min ido cikin wani yanayi na tausaya min.
Dan murmushin karfin hali na sake mai ina kokarin yunkurawa da sauri ya kai zaune gefen gadon da nake kwance yana bi sannu baki da lafiya zahra.
Banda lafiya yaya na fada cikin murya na marasa lafiya kai ya gyada min alaman eh ya kai hannun shi a hankali saman ciki yana nuna min sai lokacin na tuna da cikin jikina.
Aiki akai maki aka cire maki babeis jiya sai yau kika farfado da kyau yaya abin cikin nawa yana da raine na tambaye shi ?
Suna raye ya bani amsa har lokacin ban fahinci may yake nufi ba da zancen shi sai na mayar da idanuwana na lumshe a hankali.
Hannuna ya rike yana dan matsawa a hankali zuciyar shi cike da kunci a lokacin shi kadai yasan irin yanayin da yake ji a lokacin.
Likitace ta shigo tare da wasu nurse a bayan ta shigowan shi yasa ya daga daga yadda yake zaune tare dani.
Dubani tayi tare da yan tambayoyi tana rubutu kafin tace dani in mike zaune zan iya ko da sauri yaya yaso magana ta tare shi da hannu.
Da taimakon nurse din na samu na daga, daga kwace har lokacin jikin nawa akwai dan tsami kadan tace in sauka daga sama gadon na sauka a hankali.
Tare da dan umurtana in taka da tsoro na fara dan takawa sai najini wasai dani ba yadda nake tsanmani ba.
Shi kanshi yaya yayi mamakin hakan wanda hakan yasa shi dan murmusawa yayi yana mai jin dadu har cikin ranshi.
Likitan tace zasu sallame ni zuwa safe idan sunga yadda jikin nawa ya kara sauki suka fita bayan ta umarceni da in zauna kada in kwanta kuma.
Daga inda nake zaune ya koma bakin gadon ya zauna ya tsura min ido a hankali ya kira sunana bayan ya sauke wani nauyayyen ajiyan zuciya yace Zahra.
Na dago kai a hankali na kalle shi cikin yanayin ciwo da nauyin jiki yace kin san may kika haifa min ?
Kaina girgiza mai a hankali alaman a,a yace cikin daga yan yatsun hannu shi biyu yara biyu maza kika haifa Zahra.
A zatona wasa yake min sai na dan murmusa kawai shigowan su Ramla da mijin ta yasa muka katse maganan mu.
Da murnan su na gani zaune suka shigo suna muna ba,a yanzu kan hankalin shi zai kwanta tunda yaga na farfado ban mutu ba.
Sai dan murmushi yake sakewa kawai a fuskan shi sun dade wurina kafin su fita tare dashi zuwa ganin babeis din.
Washe gari aka sallamay ni daga asibitin kamar yadda likitan ta fada a zatona gidan su Ramla zamu nufa sai naga an dauki hanyar wata unguwana daban wanda ke unguwar sarauniyar kasan england.
Daga gidajen zaka iya hango gine ginen masarautan daga can nesa kadan gidane wanda ya amsa sunan gida ko a can maigirma gidan yakai abin kallo.
An ma gidan kwaliya irin na al,adan turawa da furanni masu launi kalan fari da pink gwanin ban sha,awa.
A hankali nake takawa bayan na fito daga cikin motan ina karewa gidan kallo da mamakin nan kuma inane aka kawoni kuma ?.
Daidai shiga gidan an yi rubutu da flowers wellcome to new world dan dagowa nayi na kalli yaya dake rike da hannuna zuwa cikin gidan.
Mamaki bai gama kasheni ba saida naga photo na dashi sai na yan yaran kamar ayi magana mu fito fili.
Wani dadine ya kamani har kasan zuciyana wanda ba zan iya musultashi ba a lokacin da taimakon anty Ramla ne ta kaini har dakin da yake mallakina bin dakin nayi da kallo ina mamaki wanda har ban iya boyewa a lokacin.
Rayuwa ke nan Ramla tace min idan baka mutu ba ba,a gama hallitan ka ba mijin ki ba karamin so yake maki ba Zahra.
Yanzune lokacin da zaki kara zage damtse ki kara kama mijin ki a hannun ki.
Kada ki bari haihuwa ya rageki da komai ga mijin ki son shi dana yaran ki zaki auna ki kara akan komai a rayuwan ki.
Tsabta ya ganki yanzu zarah idan da kinayi yanzu ki kara ninkin baninki samada wanda kike dashi a baya.
Mun kai wani lokaci tana ban shawara kafin mijin ta yace tafito su wuce zuwa gida nan suka tafi suka barmu daga mu sai mu yaran a gefena na juya na kalle su ina mamakin wai a cikin cikina suka fito dukkan su.
Shine ya shigo dakin bayan ya dawo daga masu rakiya daga kofa ya tsaya yana kare muna kallo.
Dago kai nayi na dan kalleshi daga inda nake kishingide ya tako zuwa bakin gadon ya zauna a hankali tare da riko hannayena yace zahra may zance dake ne wai.
Sai ya dan rugumoni zuwa jikin shi yana fadin kin gama min komai a rayuwana ko haka kika barni da yaran nan biyu na godewa Allah a rayuwana.
Zai kara magana nayi saurin rufe mashi baki da hannuna ina fadin please yaya don Allah ka bar wanan zancen don Allah.
Ajiyan zuciya ya sauke mun dauki lokaci a hakan kafin dayan yaron ya motsa yayi saurin sake ni ya juya gare shi da sauri yana fadin ko nono yake so ne Zahra.
Yana kallona yake magana dan langabe kai nayi nace mai yaya yaya zanyi yanzu ?
Kokari bude gaban rigana ya shiga yi ya fitar da nono ya juya ya dauko yaron da kanshi ya kama yaron saida yasha nonon ina runtse idanuwa yaron yana ja.
Kulawa sosai dagani har yaran muke samu daga gare shi bai bari in yi komai har yaran shike masu komai da kanshi.
Jina shiru an koma school Anty farida ta shiga neman layin wayana tazo gidana yafi a kirga karshe wasu turawa ta samu a ciki suke fada mata munbar gidan.
Luckly ta kira layina ya shiga ina zaune ya tasani a gaba ina cin abinci saiga kira ya shigo min na dauka tace Fatima ina kika shige haka tsawon wanan lokaci haka ?
Naje gidan ki ban samayki ba sai wasu na samu a gidan sukace basu san ki ba.
Nace cikin cool voice anty na mun canza gidane kuma na haihu tace kin haihu ban sani ba fatima yaushe kika haihu nace two weeks ago.
Amma baki da kirki fatima ina garin nan baki sanar dani kin haihu ba yanzu kuna inane gani nan zuwa.
Kallon yaya nayi yana jin duk abinda muke fada sunan unguwan da kwatancen gidan yai mata bayan ya karbi wayan a hannu na.
Zuwanta yai min dadi sosai don itace ta samo min wata bakar fata mace saidai yar ghanace da zata dan zauna tare dani.
Hakan ba karamin dadi yai muna ba taban kulawa sosai tankar yar uwatace ta jini da ita da Ramla banda abinda zance dasu.
Don sun min karamci sosai a rayuwana wanda bazan iya godiyan baki a garesu ba saidai addu, a.
Ban san da zancen zuwan wani daga kwatsam naga Addah na sun shigo gidan tare dashi saida naji wani iri a rayuwana.
Don kamar a mafalki naga Addah tana shigowa maimakon inyi murnan ganin ta sai kawai na fashe da kuka yana tsaye yana kallon mu.
Tausayi na bashi don yasan kukan da nakeyi bana komai bane saina farin ciki ganin na gids yau a idona.
Sosai naji dadin zuwan Addah na don dagani har shi mun kara samun hutu sosai da zuwan ta ga maria mai kula da wasu abubuwa a gidan ga Addah.
Haka ya bashi daman fara fita wurin aiki nima hakana na fara zuwa makaranta daukan darasi anyi bukin suna irin namu na nan hausa.
Inda duk gaiyan na Ramla ne da Anty Farida mundai dan cika gidan inda yaran sukaci sunaye Abdulrahaman da Abdulsalam.
Zabin sunayen da mahaifinsu yai masu ke nan kuma dashi sukazo duk sunan da yaro yaci dashi yazo duniya.
Ina jin dadin zama sosai da Addah wace take yar uwa a gurin mahaifina ba karamin karama min dangina naga yayi ba ga hakan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:31 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHAHIM MALIK YUMMUDEEN, , , , ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button