NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ankaisu fa kukace hjy rabi tace wallahi anty yanzu yaya yazo yana fada muna wai harsu asma,u sunje taron amare kawu ya turasu suka tafi.
Ni Alh zaiwa haka ni ni jummai zai tozar, , , sai ta kasa karasawa ta fashe da wani irin kuka lokaci guda.
Abinda bata taba tunane ba a rayuwan ta shine ya faru da ita ayau suma sin tsorace da ganin tana kuka don ba abu kadan ne zai girgiza ta ba a rayuwan ta har ta sake hawayen idon ta ya sauko kasa.
Da kyat suka shawo kanta tayi shiru duk shawaran da sukeyi tana jin su ta kasa furta ko a alokacin.
Sai mikewa tayi tana fadi ku tashi mu tafi .
Ina zamu tafi anty ?
Hjy rabi ta tambayeta cikin son jin inda zasu tafi din don kallon bata cikin hayacinta suke mata.
Wani tsawa ta daga masu tana fadin idan ba zaku tafi ba ku ban makulin motata in tafi ni kadai idan baku zuwa dole suka mike suna mara mata baya.
Sai dai suna zuwa wurin motar ta kawo masu cikas taki tashi kuma lafiya lau aka aje motan don cikinta suka zo gidan.
Wanan ya kawo masu cikas aka tsaya duba masu motar tana ji kamar tabi motar haya ta tafi inda tayi niya din.

Kawu sai hankalin shi bai kwanta yayi sa,a umar yazo gidan ya samu basanan zaifita sai gasu suka jera a tare zuwa falon shi .

Ya zauna shima ya samu wuri ya zauna tare da kura mai ido na san lokaci kafin yace Umar faruq dama ina son ganin ka a yau din nan.
Ga Amana yata nan na baka koda bana raye ban yarda kaci amanan yarinyar nan ba ban yafe wani kalman saki ya shiga tsakani ku ba ko wani mugun hali amana na danka maka kamar nima yadda aka ban amanan ta naga ya dace in ba wani ahalina wanan amanan .
Alhamdullahi kai ka zaba nayi farin cikin wanan zaben naka fiye dana kowa a cikin ku don dama kaine hope dina kanta.
Nasan zaka rike mun ita amana kamar yadda nake rikonta a nan zaka tayani cike mata gurbin da girma bai bari in cika mata shi a yanzu.
Umae faruq kai namiji ne nasan zaka kai hankali a inda na nufa a yanzu don nasan kasan girman amana sosai a wurin ka.
Sabanin yadda iyayyen ku mata suke hangen abin da wani manufa a zuciyar su sai suka fassara abinda kishi a nasu manufan .
Idan ka lura yar nan marainiyace a ckin mu dole mu riketa kamar yadda Annabin rahama yace mu kula da maraye .
Don Allah umar ga amana nan na baka nauyin komai nata yanzu ya rataya a kan ka kazama mata kaine uwarta kaine ubanta data rasa a kusa dakai.
Kan ahi na kasa idanuwan shi sun kade sunyi mai ja da wanan kalaman daurewan da mahaifin shi kemai a lokacin.
Daidai lokacin da kawu yake fadin fatima tana son karatun likita a ratuwan ta saidai ban san naka ra,ayin ba a yanzu ko zaka bari tayi wanan fannin ko kuma kana da naka ra,ayin ne na daban ban sani ba ?
Lokacin ya dago kai ya bude baki da kyat yace daddy karatu sai idan ita da bakinta tace ta gaji dhi insha Allahu.
Kawu yace nagode nagode ubangiji Allah yai maka albarka ya haskaka maka samun ka duniya da lahira nagode kwarai umar da wanan halarcin da kukai min kun nuna min ku diyane nagari a duniya ina alfahari da samun ku a duniyan nan.
Sai kuma ya fashe da kuka saida yayi mai isanshi shima umar din kukan yakeyi kawu ya tsagaita yace mahaifiyan ku takasa fahintana umaru.
Maina rage jummai dashi a duniyan nan duk abinda jummai keso shi takeyi amma kan wanan burin nawa nason raya zumuncin ku da yan uwana ko bayan bana raye ta kasa cika min shi.
Daddy kayi hakkuri don Allah zata gane abinda kake nufi da hakan daga baya ayi hakkuri don Allah mama ta dawo dakin ta.
Ko yanzu ka nuna mata kai namiji ne sama da ita ayi hakkuri don Allah bamujin daddin haka na faruwa a tsakanin ku.
Ai zanyi amma ina son jummai ta gane kuskuren ta ne na yin hakan agare ni ko don watan watarana.
Mama hadiye ne ta shigo falon tana fadin kai tsufin nan da rikici suke ganin umar falon zaune a yanayin da suke da mahaifin nasa yasa tayin turus tace ashe kana nan ma ?
Ai gara dana samay ka wanan tsohuwar ne kakan Fatima take kuka wai a barta taje tayi sallama da jikanta don Allah.
Kawu yace ku barta tatafi mana ku kaisu can don Allah ai zasu iya kwana a wurin ta don yau kawai ku kaita don Allah dai.
Gashi ina gidan zaka yanzu sai ku tafi ka saukesu dayani yace ba matsala daddy idan sun shirya sai su fito.

Gidan salma ta fara zuwa sun samu an fara watsewa a gidan sai gasu mamakin ganinta mutane keyi a gidan.
Ana taron su da zuwa ba wanda ya amsa daga cikin su sai kokarin shiga tana tambaya ina dakin da salma take ?
Aka nuna mata ta nufi kofan gadan gadan Nafisa ne ta fara lekowa don jin muryan su da tayi tace salma ga mama nan.
Wani irin zabura salma tayi tace da gaske wallahi ko nafisa ta fadi da sauri suka nufi ban daki suka rufo dukka su biyu sai kawayen su suka bari zaune a dakin suna mamakin su.
Suna shiga tun falon takebin wurin da kallon mamaki tace ma kawaye ina salma take da yake suna da wayo sun dan san halin da ake ciki sukace ta fita an kirata.
Bata fita ba tana dakin nan hjy rabi tace tana kallon kofan bandakin da idanunta.
Tana cikin bandaki ta rufe ko tace a hasale nan suka hau aika mata da zagi sai ta fito su wuce yau bata kwana wanan matsiyacin gidan wallahi.
Hayaniyan da matan sukaji yasa su shigowa dakin nan suka shiga bata hakkuri tace su suka haifa mata yar da zasu bata hakkuri ?
Ganin haka yasa wasu kiran Ahmed hankali tashe suna fada mashi ranshi ya baci ya kira kawu yana sheda mai.
Umar na shirin barin wuri mahaifin shi kiran ya shigo mai yake fada masu abinda ke faruwa a gidan nasu.
Jummai ko nada hankali kawu ya ambata hankali tashe haka yasa umar dake sa takalman shi tsaya daga kofan falon ya dawo ciki yana fadin daddy wani abin tayi ne kuma cikin sanyin murya yake magana ?
Wai gidan salma suke yanzu ala dole sai sun fito da salma gidan ta jimmai ko nada hankali ?
Barinje gidan daddy a kwatanta mun gida yace a, a kada kaje ai kaima tana tafe gidan ka kaje ka kwashi matan ku tafi ku barni da ita.
Badon yaso ba haka ya bar gidan ranshi a bace sun hadu dasu mama hadiye da saurin su zasu shiga wurin kawu din.
Yasan shine ya kirasu a kan maganan hakana dai ya wuce ya dan jira su manjo suka zo tunda suka shiga motan suke kwarara mai addu,a har yakai gidan baiyi magana ba.
Suna sauka yaja motan ya fita wuri ya samu ya faka ya kira layin habbib yana fada mai halin da ake ciki dashi da Aliyu.
Wai may yasa mama take biyewa su mama rabi ne tana bar muna abin kunya nafara gajiya da halin nan na mama habbib yace.
Yanzu ba wanan ba yaya za ayi shine na kiraku muji Aliyu yace ba daddy yace a barta dashi ba mu bari muji matakin da yake son dauka Aliyu yace.
Ina tsoron kada daddy yai fushi ya hadata da hukuma umar ya fada rai bace yace ba zai kaita ga hukuma ba nasani inji habbib.
Can kuma su mama hadiye na shiga suka samu suna cacan baki da Ahmed yana fadin kema kin san ba don ki na yarda da wanan hadin ba .
Kamar yadda kike kyamana numa haka nake kyaman halayan ki a rayuwana ban taba ganin uwarda bata san ciwon kanta irin ki ba hjy.
Amma jummai kinji kunya idan kin santa ai gasjkiya surikin ki ya fada yau yay da kawo yarinya ki gidan mijin ta kizo masu da tashin hankali haka ?
Sarka mai rikicin gangan yau kan sarka ta rikice a gidan Alh sani har bata iya haduwa don rikicewa.
Sun gwada mata suma yan zamani ne sosai don sun barda abin fadi kafin su bar gidan zuwan kawu mustapha gidan ya tsayar dasu.
Don dole badon taso ta bar gidan don taga abinda batayi tsamani ba gare su dan hakkin daka raina sukai mata.
Tana sababi a cikin motan tace dauki hanyan gidan babawo inje in fitar da yar iskan nan itama kafin in je gidan sauran yau yadda suka hana zuciyana sanyi suma nasu ba zai taba sanyi ba garin nan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button