NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Yadda Ahmed yaje gida ya samu mahaufin shi hankalin shi ya tashi sosai inda ba bata lokaci ya dauko shi zuwa kano ko ina bai tsaya dasu ba sai asibiti
Hjy maimuna bata sanda zancen ciwon mahaifin Ahmed ba sai washe gari takd ji a gurin gwagon ta da maigidan su ne ya fada ma mahaifiyar shi zancen.
Batai kasa a gwiwa ba wurin kiran Ahmed din tana tambayan shi jikin mahaifin nasa lokacin suna hanyar kano daga katsina.
Ya dauki wayan bayan sun gaisa take fadin Ahmed ashe abinda ke faruwa ke na yanzun nake jin wanan maganan a gurin gwago.
Yace hakanane hjy yanzun haka muna nan hanyar kano zan shigo dashi asibiti tace subbahanallahi ashe jikin sosai ne Allah yabashi lafiya ya kawo ku lafiya ta kashe wayan.
Ajiyan zuciya ya sauke yana mai jin dadin kiran da taimai din don ta kula da abinda ya shafe shi sabanin hjy Jummai da agabanta ya fada ma maigidan nasa amma ba wani damuwa data nuna akai.
Sai dai shi Alh sanin yana ta kiran su koda yakai can ma sai da sukai waya da majincin kan shine yace azo dashi asibiti a duba shi.
San nan tsohon ya yarda zaizo don yana ganin zai dorawa mutane lalura ne kaishi can din da Ahmed yace zaiyi.
Shine Ahmed din ya kira Alh sani don yaiwa tsohon magana ko zai yarda su zo dashi asibitin.
Suna zuwa ba,a tsaya wani abuba gado aka basu inda aka daura mai drip aka fara gwaje gwaje akanshi.
Ana haka hankalin Ahmed a tashe saiga hjy maimuna sunzo ita da hadiye da Amma niki niki da kayan abinci da sauran abubuwan bukata har Alh sani kanshi yana asibitin akan tsohon don kafin su kawo kano ya gala baita sosai.
Sai zuwan su ne ma ya tuna da abinci da bai sawowa sauran mutanen da suke tare ba a lokacin yaji dsdin hakan inda ya kara ganin mutunci da kimar hajiya maimuna di sosai a idon shi.
Haka sukai ta zirga zirga akan tsohon kafin agane abinda ke damun tsohon wanda sai an mashi aiki dole akace .
Hjy maimuna bata gaji ba wurin hada masu abinci kullun sau uku a rana Ahmed din ke zuwa ya dauko ko ita da hadiye su kai masu asibitin.
Inda take shan zagi sosai a wurin kishoyin nata sai dai hjy maryam takan dan leka asibitin wani lokaci ta gaida su sai dai su basu sani ba.
Hakan ba karamin Alheri ya jawowa hjy maimuna a wurin maigidan nasu don bayan kimar da tayi har da alheri take samu wurin yin hakan ga maigidan nasu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:38 – ????????????: YA ALLAH KA SAKAWA IYAYYEN MU DA GIDAN ALJANNA, KASA MUTUWA TA ZAMO HUTU A GARE SU ALLAH KA RAYAWA KO WATA UWA DAN TA TAFARKIN ADDIN MUSULUCI KAYIWA ZURI,A ALBAKA ALBARKAN ANNABIN RAHAMA AMIN INA TAYA KOWACE UWA FATAN ALHERI GA ZURI,ANTA HAPPY CHILDREN DAY,, , , , , , , , , ,

Ina kwance dakin mu barci ya soma daukata hayaniyar dake tashi daga tsakar gidan mu ne ya falkar dani dagaz barcin dana soma din a lokacin.
Dagani har Manjo saurara abinda ke faruwa daga wajen gidan mukayi wanda hayaniyar ba iya cikin gidan mu kawai ya tsaya ba har wajen gidan muke jin hayaniyar yana tashi.
Hankali tashe muka fito daga dan dakin mu don ganin abinda ke faruwa a wajen kada a rutsa damu a ciki.
Mun isa wurin daidai lokacin da wani mutum ke fadin ku dai bakuyi halin mahaifin ku ba mutumin kirki duk unguwar nan kowa yasan mutumin arziki ne.
Don ba abinda ya taba hadashi da wani a cikin unguwar nan na assha amma ku, kun addabe mu kun hana mu zaman lafiya.
Kuna nema ku gurbata muna tarbiyan yaran mu a cikin unguwa yanzu may ye amfanin irin wanan ki dinga jawo muna mazan banza a unguwa suna zuwa suna tayar muna da hankali a cikin unguwa.
Yanzu may ye amfani irin wanan abinda ya faru daidai lokaci muna guri yake ta rabtako bayanin shi a hasale.
Manjo ke tambayan na kusa da ita abinda ke faruwa duk da matar bata sheda manjo sai fadi take .
Wallahi fa wanan fitsarar yarinyan gidan nan ne saliha tana tare da wani a mota suna iskanci ashe kuma ta gyayaci wani shi fada ya kaure a tsakanin su har da fashe fashen kai .
Salati Manjo da muke rike da hannu juna sarke da juna ta saka tare da fadin kai wanan yarinyar batai gadon arziki ba nasan fitsaran yaran nan zai kaisu ga hakan.
Da sauri ta tasa keya na muka koma daga ciki don kada mu karasa jin abin takaici yau ace jininta ne akewa wanan shedar haka ba dadi ji a bainar jamma,a.
Duk da naso in tsaya inji kan maganan don ban fahinci komai da matar nan ta fada muna ba sai dai ba yarda zanyi dole in bi manjo mu koma ciki tunda haka take bukata din.
Shigar mu gidan ba daki muka shiga ba daga waje tsakar gidan muka tsayawa tayi waje anan tsakar gidan tana surfa masifa tare da nuna yaran halin iyayyen su mata suka biyu ba jinin ta ba.
Har tayi ta gama basu kulata ba da kyat na jata zuwa dakin mu ranan dai ina ganin batayi barcin kirki ba saboda bacin ran abin kunyar da jikanta ta jawo mata a gari.
Washe gari da safe kamar yadda baffa ya saba zuwa ya gaida manjo kafin ya fita yauma haka ya shigo daga kofan dakin mu inda muna ciki kwance don sanyin da akeyi.
Mukaji muryan shi a sanyaye ba kamar kullun ba shima dai ko ba a fada ba nasan da bakin cikin abinda saliha tayi jiya ya kwana dashi.
Ciki ciki manjo ta amsa mashi jin hakan ya bani haushe don lokacin wayau na bai kai ba don haka banga laifin baffana a cikin maganan ba sai laifin iyayyen su mata da basu son aiwa diyan su fada naji.
Don haka na amsa mai da karfi yadda zai fahinci ba barci mukeyi ba a dakin hakan yasa ya cire takalman shi ya shigo dakin da ganin yanayin sa yana a cikin damuwa sosai.
Ya samu wuri ya fara gaida mahaifiyar tashi ya samu ta karba mai da kyat tana cika tana basarwa sai dan shiru ya biyo a dakin ganin haka yasa na fara gaida shi da kwana.
Sai lokacin ya dan sake fuska yana fadin fatima kun tashi lafiya yaya daren kuma na amsa da Alhamdullahi ina kokarin tashi don in fice a dakin don ba zan so manjo tai mashi magana ba a gabana.
Ya dan dade a dakin kafin ya fito ranshi bace ya fice daga gidan duk da iyalin nasa duk suna waje bai samu wanda yai mashi a dawo lafiya ba daga cikin su.
Sai ni dake tattara kwanukan da akai amfani dasu a daren jiya don in wanke nake fadin Baffa a dawo lafiya yace dabi tare juyowa Amin yar albarka.
Wanan kalman yana mun dadi idan yana fada min hakan bayan fitan shi baiko gama ficewa ba naji muryan mama saude na fadin wa yanda ba,a sawa albarkan ba ace su mutu.
Ina jin ta ban dago ba sai danaji muryan yaya hashimu yana fadin ai wanan shegiyar yatinyar iyayi ne da ita da sanabe ya fita baicewa kowa komai ba sai itane mai mashi a dawo lafiya.
Haushin maganan shi naji nace babu ruwan kowa dai dani tunda ba mutum nacewa hakan ba dama yafi kowa zama dan iska a gidan.
Don sai yayi kwanaki bai leko gida ba yana can gurin shaye shayen shi ko dabanci da yakeyi aiko ban san ya taso ba yana bayana sai jin gau gau ya sharara min mari har biyu a kumatu na.
Wani irin kara na sake daya ruda gidan wanda yasa manjo yin tsale daya sai gata waje daga dakin mu tana fadin kai kai may ye hakan may taima ka doke ta ?
Yace ko zaki rama mata ne kin wani fitowa kina tambaya a tsawace tace nace may taimaka ka doke ta da safen nan haka ?
Bai ankara ba yaji duka a jikin shi dim dim sake baki yayi yana mata kallon mamaki ta juya tare da ja min hannu tana fadin bar dan banza wanke wanke ma ba zakiyi ba su da suka bata su wanke abinsu ba baiwa na kawo maku ba ai a gida.
Muna shiga dakin daki tace garin nan zaki bari maganar Addan ku ya soma zama gaskiya zaman ki a gidan nan ba zai yuyu ba don yaran nan suna iya illanta ki wata rana.
Cikj turo baki nace ba nace maki mu koma misau ba kin ki tace bana ki bane A ruwa lafiyata nake nema a nan idan bashi ba may zai kaini zama wannan gidan ina ganin bakin ciki tunda baffan naki bai iya tsayawa ga iyalin shi.
Nace manjo may ye laifin baffana a nan dole fa ya fita ya samo abinda za a ci tace nasan da hakan.
Matan kirki ne dai bai aurowa diyan shi ba tun farko ai wanan halin daga gun uwayen su suka kwaso shi nidai yanzu so nake yar nan tazo ta tafi dake kano wurin ta hankalina zaifi kwanci gaskiya idan kin daga daga gidan nan.
Da sauri na dago kai tare da fadin kano kuma manjo ni dai gaskiya ban zuwa kano ki mayar dani misau mukoma can ko gurin Addah.
Kano gidan da basu son bako gidan da ba,a fita kullun ana daki gidan da suke fada kullun ni gaskiya ban son kano din nan manjo ko kadan.
Bata tankani ba sai dai shirun da tayi tana tunanen tunda nace ban zuwa kano sai dai ta hakkura ta koma misau inda muka fito duk da gidan namu yanzu duk ya lalace yana son gyara yana daya daga cikin abinda ke kara maga gwiwa da komawa misau fin don gidan ya tsufa sosai.
Da taji na matsa da mita akan kanon sai tace to ai shike nan tunda bakya son can din sai muyi hakkuri mu zauna a nan din kafin Allah yayi muna mafita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button