NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:11 – ????????????: .BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM, , ,

Akwana a tashi ba wuya a wurin Allah abubuwa sun faru da dama a cikin gidan kawuna wasu na jin dadi wasu ko na tashin hankalin zamantakewa rayuwan mutanen gidan.
Izuwa wasu watanin da suka shude har hjy ta gaji ta debe tsammani akan auren don irin shige da ficen da taitayi na ganin hakan bai faru tsakanina da danta ba.
Sai dai bata sani ba a maimakon abin yayi tasiri kamar yadda take son ayi sai Allah ya juye lamarin ya sako ma dan nata rashin son gida gaba daya.
Don kamar yadda take tunanen ba wanda yasan takon ta a gidan bata san a idon makwarwa take shuka ba.
Ba hjy maryam kadai ba har shi kanshi maigidan da baya barci yana raya daren shi a tsaye gurin mika kukan shi ga Allah yasan da abinda ta bizzine a gidan kan yayan ta.
Wanda a da can bai dauki abin komai ba yafi danganta lamarin da sherin mafalkine kawai ke rudin shi.
Sai daga baya ya farga da zaran ya gama nafilolinshi ne yana zikiri wanan abin kanzo mai a mafalki.
Inda yake yawan ganin hjy din tasa danta gudu kullun da bai san may yakewa gudun haka ba.
Har dai ya gaji inda yakai koken yawan mafalkin nasa akan danshi da take yawan yi idan barci ya fisgeshi.
Kwanaki malam ya bashi akan zai dawo yaji abayanin daga baya sukai sallama sai bayan sati biyu ne kamar yadda aka diban mai ya koma gidan malamin don son jin ba,asin maganan mafalkin.
Nan malam yayi mai bayani yadda zai iya fahintar shi kamar haka, da farko dai kana da yara maza da mata a gidan ka sai dai dukkan su suna da ma bambanta iyayye a gidan a yadda nake gani.
Sai dai wanan mai dan tsayin da kauri itace matsalan gidan ka don matsalan daga gurinta yake don tafi sauran hasala a cikin su.
Nan dai malam ya koro mai duk abinda ke nan har yadda hjy tayi aiki kan danta sai dai an samu akasin aikin don aikin ya juyene ranshi ya bar gida gaba daya yanzu.
Shiyasa kake ganin sa a halin gudu da kake ganin shi yanayi ba kakautawa a mafarkin ka .
Kafin malam ya gama bayani har Alh sani yayi zufa sosai a goshin shi lokaci daya sai maimaita innalillahi yake a ranshi hankalin shi tashe.
Bai bar gurin ba sai da malam ya bashi addu,oin da zai dingayi don samun masallaha a al,amarin.
Alhamdullahi shi ya rike kuma yana ganin hasken adduan a lokacin don bai cika sati daya ba sai ga kiran Umar ranan a wayan shi.
Mamakine ya cika kawu dayaga dan nasa na kiranshi a waya ya dauka da addua a bakin shi tare da sallama.
Jin kamar ba zai amsa ba sai can ya amsa yana fadin daddy i am very sorry na rashin kiranka tsawon lokaci.
A cikin hikima da nuna ba komai ya katseshi ta hanyar fadi umaru sanda mazan fama ga aiki ga ban tsoro.
Dan murmushi ya sauke tare da ajiyan zuciya ya kara fadin sorry daddy aiyukane sukai min yawa a nan .
Kawu yace umar na sani ai in kaji shiru lafiya ne yaya wurin ita matar taka da amarya na dan gajeren murmushi yayi yana fadin suna lafiya koda yake na kwana biyu ban tare dasu ina nan mun zo aiki a kasan italy.
Kawu yace haka na da kyau amma a kula da hakkin iyali a dinga sauke masu hakkin su kada a raja,a ga aiki kullun .
Nagode daddy yace tare da danyin shiru na wani lokaci Alh ya kawar da shirun ta hanyan fadin kun gaisa da mahaifyar taka ko ?
Yace daddy idan mun gama yanzu zan kirata itama sun dan dauki lokaci yana janshi da hira mai kama da nasiha, kamar babu abinda ke damun shi a rai.
Kafin suyi sallama umar din yana mamaki da babu abinda mahaifin nasa ya nuna mai na rashin zuwa gidan da baiyi kuma baya kiransu.
Don shi haka kawai yaji gaba daya kasan ya fice mai a rai ko aikin daya fara ya dakatar da yin sa gashi saura kiris ya rage komai ya kammala gare shi.
Yayi mamakin jin daddy baimai fada ba kamar yadda yayi tsamani sai gashi karshe sun kwashe da wasa da dariya da mahaifin nasa.
Yana mamakin hali irin na kawu da ko abu ya bata mai rai bai faye fitowa fili yai ma mutum magana a kansa ba sai in abin yakai intaha zakaji yai dan fada dasu.
Ko case din merry yasan ya batawa daddy rai ne sosai yasa yai mashi hakan sai lokacin ya tuno da alkawarin auren dake kanshi wanda ya manta da zancen sam a cikin ranshi.
Gaban shi ne ya fadi har ya furta oh shit to amma kuma yaya akayi yanzu daddy bai jefo min zancen nan ba a hiran mu.
Wayan maman shi ya kira kamar zai tsuke ba,a dauka ba sai kuma can aka dauka tana fadin hello a kausashe.
Yayi sallama tare da fadin hjy mama an wuni lafiya tace yau kaga dama ka tuna damu ?
Ya danyi murmushi yana fadin mama tuba nake don Allah wallahi aiyukane sukai min yawa nan.
Rufa min baki aiyuka ko matarka ta dauke maka hankali gare mu har ka fara mantawa damu.
Babawo ka lissafa yau wata nawa rabonka daka kirani mu gaisa koda a waya ne ?
Yace mama ayi hakkuri abubuwa ne sukai min ya, , , ,
Kada ka mayar dani mutumiyar banza babawo ka tuna ban daga cikin irin uwayen da yaro zai min son ranshi ba zan gama wahala daku ba yanzu hutu yazo kace zaka manta damu don ka samu wata mace.
Shiru yayi yana sauraren yadda mahaifiyar nasa ke kwasan fada dashi tace watau abinda nake guje maka ga auren yar wurin maimuna shine kuma zaka gwada min ga wanan mai guntun bujen naka ?
To idan ma dan abinda kake turo muna ne ta hana ka sani yanzu ba kai kadai bane mai bani don bakai daya na haifa ba.
Wani irin yaji a ranshi ba dadi hakan yasa ya shiga bata hakkuri yana kokarin kare merry akan ba laifinta bane sai dai uwar bata bashi daman korafi ba.
Suna gama waya ya cika mata account dinta da kudi masu yawa haka yasa ta daina jin zafin shi da take ji da farko.
Ranan ma ya kira Amma sun dan taba hira take tambayan shi ko lafiya taji shi shiru haka kwana biyu ya dinga tuna gida da iyayyen shi shiru haka sai hankalin mutane ya tashi ai.
Yace Amma za a gyara da yardan Allah komai zaizo da sauki insha Allahu sukai sallama.
Daga wanan karon kuma saida ya dauki lokaci bai kira wani ba duk dai kawu yana kan addua ga yayan nasa har lokacin.

Mun samu mun kammala karatun mu lafiya yanzu gidan wa yanda suka rage sai kanana mai dan girman cikin su itace yar gurin hjy maryam kanwar ilkilima a cikin masu zuwa school.
Har lokacin ba wani jittuwa a tsakanin mu sai dai ba yawa fada tunda bamu shan innuwa daya dasu balle mu hade ayi fada ko islamiyan da muke zuwa kowa tasa yake zuwa.
Mun gama da kamar wata daya ranan kawu ya shigo wurin Amma ina falon ya kalle ni yace Fatima tunda an kare karatu yanzu sai ki shirya muje bauchi ko ki gaida su.
Wani dadi naji a raina har bansan lokacin dana saki ihun murna ba suka kwashe da da dariya shida Amma.
Nan na bar kawu wurin Amma na nufi part din mu ina murna na samu mamu ina fada mata kawu yace in shirya zai kaini bauchi wurin su manjo in dubasu.
Tace yanzu yake fada min saidai yace ai ba zaki dade can ba na bata rai tare da fadin ni dai a barni can inyi koda wata uku ne mamu wallahi ina kewan su sosai.
Tace da wuya saidai ai tsakanin ki da kawun ki ne kila idan kin lalasheshi zai yarda.
Don zumudi tun ranan na fars shiri ina daukan kayan da zanyi tafiya dasu ina jefawa a yar jekkana da wanda zanyi kyauta dashi idan naje can.
Har kwana biyu banji kawu yace min komai ba nikuma ban fasa shirina ba har lokacin ba karamin kaya na kwasa ba , wai duk kyauta zanyi dasu a can idan naje.
Da dare ranan bayan kamar kwana uku da maganan ran daren jumma,a sai ga kawu ya shigo yana fadin mu shirya da safe zamu wuce.
Haba murna wurina ba a magana na matsu gari ya waye Ingani a garin misau gaban manjo da Atika inga yaya Atika ta koma itama.
Da safe muka fito a cikkn shirin mu wanan karon duk yaran zamuyi tafiyan dasu wanda hakan yai min dadi sosai a raina.
Mun sallami kowa a gidan don sai da mamu ta turani nayi sallama dasu ba don naso ba ssi da muka fito shiga motane naga ashe ba mu kadai zamuyi tafiyan ba har da wasu abokan kawu sai dai mu tamu motar dabance.
Sai na dauka kila dama wani abu kawu zaije yi can bauchi din yaga ta dace ya kaini gida.
Su Aisha har wurin motan mu suke sun min rakiya sai da muka tashi suka bar gurin sai kuma naji ba dadi a raina.
Sako mai yawa Amma ta bayar akaiwa manjo ina ta godiya kamar nice manjo din da akaba sakon.
Mun isa musalin daya da wani abu na raba wai dukda mun daka sakko da safe muka taso amma sai kusan azahar muka isa garin.
Gida yana nan kamar yadda na barshi saima kara lalacewan da yayi lokacin a idona ko don na saba da gidan kawune yanzu nake ganin hakan.
Wani dadi naji a raina na kalli gidan su Atika shima yana nan kamar yadda na barshi bayan motar ta tsaya ne na fito da zumudi mamu ta kalleni tace ki natsu mana kin san yanzu kowa idon shi zai koma kanki ne.
Hakan yasani na gyara da kyau duk da hakan banyi yunkurin yin wani sallo ba can sai dai ban san komai nawa ya canza ba a yanzu don su ganin gaba daya na sake masu ne don gani ga yayan Atika mai koramu karatu bai gane ni ba nima ban masa magana ba.
Na hango wasu gungun maza matasa zaune a darbejiyan dake duban tsohon shagon isah mai shegwo har yanzu shagon na gurin sai dai ba kamar da can baya ba da yake cike har baki muna zuwa sayen abu a gurin shi kusan duk unguwan anan ake sayen abu.
Yanzu ko shagon ya watse ba wanan kayan irin na dacan baya a shagon don har cikin shagon zaka iya hangowa daga inda muke .
Mazan ne naga sun zubo muna ido suna magana ban tsaya bin ta nasu ba na nufi hanyar shiga gidan.
Da sallama na shiga gidan mama saude ne zaune tsakar gida da daura gaba tana tsifan kai.
Jin sallaman mu ne yasa ta dago kai tana kallin mu gurun ta na nufa ina rike da yan kanne su biyu fauziya tana rike da mamu suna bin gidan da kallon mamaki.
Nace mama ina wuni tace wa nake gani nan kamar fatu nace nice mama ina murmushi a fuskana.
Tace ku fito yau ga fatu a gidan nan tana fadi da yar fara,anta sai gasu sunyo waje ruuuu daga cikin tsohon falo namu.
Fati ce nan fatin manjo fa sai ga umma ta leko itama da daura gaba a jikin ta tana fadin fatin manjo ina kuma ta fito nan ko tayi halin natane can suma sun koro, , , ,
Ganin yanayi ga kuma mamu a bayana yasa ta katse maganan datayi niyar fada gare ni ta washe baki tana fadin ashe tare kuke tafe da maimu.
Itama na gaida ita kamar yadda na gaida mama saude din da farko sai fadi mama saude take ina zasu shiga ne yaya ?
Mun barsu a waje tsaye mama tace a, a dakin tsohuwa zasu kin sani nan na juya na nufi dakin kwanon manjo da nai rayuwa a ciki a baya ya kara lalacewa har an tare shi da su leda da ragga dai sauran tarkace nasan don ruwan sama ne.
Manjo na zaune a sama tsumakara wai katifa sai ganina tayi kamar a mafalki ina fadin manjona na fada saman jikin ta.
Salati ta fara sai kuma ta fashe da kuka tace wallahi tunanen ki nake a raina yar nan nace manjo ai gani nazo tunane ya kare.
Sallaman mamu kofan dakin ya katse muna tace ashe tare kuke da uwar taki sannun ku da zuwa tana kokarin tashi na hanata don rabin jikina a jikinta yake.
Tace daga jn tashi in gyarawa uwarki wurin zama mana nace ki zauna manjo in gyara mata tace tsintsiya yana daga waje ki dauko.
Dakin ne ba mai gyaraw sai ni idan na dan ji daman jikin nakan dan kora in samu wurin sallah.
Na fito daukan tsintsiya naji yaya hamshin ya shigo yana fadin wai wa nake gani kamar fatin manjo gidan nan ya nade kafan wandon shi daya da ganin shigar shi kasan har yanzu sai a hankali.
Nayi murmushi ina fadin sannu da zuwa yaya hashimu sake baki yayi yana kallon ikon Allah kafin yace wai da gaske kece fati kika koma haka ?
Nayi far da udanuwana nace nice yaya mun samay ku lafiya ?
Sai mamakin canzawa yake ya kasa amsa min niko banga abinda sukewa mamaki a jikjna ba yace fati kin koma kamar wata baturiya haka dake ?.
Dan dariya nayi ina fadin kai yaya hashim kuma har da zolaya yace ba zolaya ko daya kin canza fati kin koma yar birni dake kamar bake bace fatin manjon dana sani.
Muryan manjo ne take fadin wai ina kike ne kin bar mutane a tsaye nace gani nan na barshi na wuce tsaye a gurin yana mamaki na.
Suma can dai ciki gulman sukeyi kan canzawan danayi cikin shekara biyu da rabin danayi rabona dasu.
Saida na share dakin na fito da shera nake fafin ai ina su anty kubura ne ban gansu iba tambayan mama saude tace sadiya tana ciki kubura ina jin ta fita.
Bayan an gama gaisawa Mamu tace ai mata magana da baffa don zasu komane su yau aka tura a kira baffa din yazo.
Bai dade da zuwa ba suka fice wajen harda mamu nan suka barni na fara gyaran abinda zan iya a dakin na kusa karasawa ne sai jin murya Atika nayi tana fafin ina Fatin take ne ?
Na yarda tsintsiyan hannu na na fito muka rungumay juna da ita a wurin mun dan jima muna hira ta tayani gyara dakin kafin su shigo sai fadi Atika keyi kin ganki kuwa fati kin canza fa ga baki daya wallahi ni dai murmushi kawai nake mata ina kallonta.
Da gani yanzu duniya ta dan basu baya ganin yanayinta kawai yasa na gane hakan koko din girshi ta fito ne ban sani ba.
An dauki lokaci a wajan don har na fara tsarguwa sai ga mamu ta shigo yara suna biye da kayana a bayan su tana fadin kije kuyi sallama da kawun ki kafin mu fito.
Atika ce ta rakani wurin shi na samu wuri na tsugun na yace Fatima kinga gida kin shige kin manta da mutane ko ?
Nayi murmushi ina fadin kawu mamu tace yanzu zaku tafi yace eh kinsan hanyan sai a hankali gara mu bishi da wuri ido na ganin ido zaifi tunda mun ga baban naki.
Nan dai yadan ja min kunne akan in natsu kwana biyar zanyi driver zaizo ya dauke ni mu koma nace kamar in kuka don ba haka naso ba ni tunda na gama karatu ai da a barni na kwana biyu nace a raina.
Hannu yasa a aljihun shi ya ciro kudi masu yawa ya bani yace ki rike wanan na karba ina godiya yacewa Atika itama ga nata ya sake kirgo wani yace i bawa mutanen gidan idan na shiga .
Muna wurin sai ga su mamu sun fito har da yan gida kawu din da sukai mata rakiya don ta jikasu da alheri dumus.
Nabar gurin kawu Atika tana biye dani na kwanta a kafadan mamu ina fadin mamu har nafara ji kewan ku fa.
Tace yau ga tsiya ni dagani mu wuce zaki ga sako acikkn hand bag dinki na saka maki kidai kula da kanki don Allah.
Uwa dadi kamar ince na fasa tsayin kuma nake ji yanzu a raina na nuna mata kudin da kawu ya bani tace kuma yabada wani fa da farko kuma a baki nace to ko in baki wanan ki tafi dasune mamu ?
Tace bar abiki yadda naga gidan nan sai a hankali ki tabbatar da kuna cin abinci mai kysu kada ku zauna da yunwa nace to mamu ina shafa kan samir daya makale mun nikuma ina jikin mamu kamar zan koma ciki.
Sai muka ba mutanen dake kallin sha,awa yadda muke abu kamar wasu ya da kanwacan haka sai ina kallo suka tafi ina daga masu hannu.
Nace mu shiga in gyara kayana kafin mu shiga wurin umma nasa ba zan fito maza ba idan naga umma yau.
Mun shiga na gyara wuri komai tsab na fito tare da Atika da kallona bai isheta ba har lokacin don har ga Allah ba Atika kawai ke mun kallon kurulla ba kowa na gidan ne.
Haka muka fito zuwa gida su Atika ban fita ba saboda sabawan da nayi yanzu sai danaje na fadawa su mama saude zan shiga gidan su Atika in gaida umma.
Bayan na wuce ne aka sa topic dina a gidan mama saude tace ai na fada maki ba dawo da ita sukayi ba baki ganin yadda iyayyen keyi da ita kamar zasu mai data ciki.
Koma dai maynene ai dai bata canza uba in kuma tasa tsiya in hana malam ya barta ta koma muga tsiya.
A gidan su Atika na shiga da murna ina kiran umma tace har nayi fushi tun dazun muna nan muna saka idon ganin ki sai ji mukayi shiru.
Na rungumay umma ina fadin umma na tsaya sallaman su mamu ne amma kina raina wallahi ranan dai mun sha hira kamar babu gobe sai dare na koma gida bayan yayan su Atika ya sawo wa mamu nama mai yawa da abin sha mai zafi nakai mata na samu ta idar da sallah har ta fara barcin wahala ba abinci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button