NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:29 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALHAMDU,LILLAHI RABIL ALAMIN, , , , , ,

LITAFIN KUDINE GA MAI BUKATA TA KIRA 08036959257 DON TURA KUDI TA BANK KUMA ZA,A IYA TURA DARI UKU KACAL TA WANAN ACC DIN KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KIBIYA KI KARANTA BA TARE DA DAUKAN NAUYI BA, , , , , ,

Na dade kwance a dakina ina tunanen hiran mu da anty Ramla da mukayi da safe.
A karshe dai na gano a kainane duk wani matsala yake tasowa a yanzu tsakanin yaya da matar shi.
Har yake kokarin sadaukar da kaddadarorin shi gareta don dai a zauna lafiya a tsakanin su.
To ni har wani mutunci ko halarci nayi mai da ya zabi hakan a kaina yanzu iya sani na ba wani so ko kauna irin na masoya a tsakanin mu.
Saidai yanzu abinda zance shine akwai shakuwa irin ta zama tare da mutuntawa irin na yan uwantaka da aurataya kawai a tsakanin mu.
Har dadin may yaji a gurina da zai sadaukar da komai a kaina har ina da wanan matsayin yanzu gare shi haka ban sani ba.
Idan hakane ya kamata in gyara halin zaman takewan dake tsakanina dashi a yanzu fiye da da can baya da nake daridari da zamana dashi.
Ta yaya zan gyara hakan kuma na tambayi kaina shawara da manya akace bai baci duk da nima macece yanzu saidai ilimina da wayo na ai baikai in gano hanyar mafita da kaina ba.
Mamu zan nema kowa da sauri nace no ba mamu ba sai wa na tambayi kaina a take amsa ya zo min anty farida ko anty Ramla.
To may zancewa anty Ramla din in naje gareta dan dama anty Farida akwai shakuwa sosai a tsakanin mu wanda har zan iya sakewa in nemo mafita a gurin ta.
Tunda dama har takan ban dan shawaran yadda zanyi in karkato kanshi zuwa gareni saida taga banda ra,ayin hakan ta daina bani shawara.
To amma ai da zan baro gida Amma tace min ni mace ce da kaina zan iya kama zuciyar mijina ba sai an koya min yadda zanyi hakan ba.
Sallaman da akayi daga kofan dakin ne ya katse min tunanena Anty Ramla ce dauke da dan madaidaicin ture a hannun ta ta shigo dakin .
Na amsa mata sallaman a hankali ina kokarin tashi zaune tare da kakaro murmushi a fuskana.
Tace ashe ba barci kikeyi ba, yau kinki fitowa waje ki dan sha iska yanzu maigidan ya dawo yake tambayan ki nace kina daki shine yace a dubaki ko lafiya kike.
Shine nace barin dan riko maki dan abinda mai ciki ke so ka zaki sha tana aje tire din a gefena take wanan magana.
Kawai dai anty na dan kwantane tace tana kaiwa zaune kodai maganan mu ta dazun ne ya daga maki hankali.
Dan dukar da kaina nayi kasa ina fadin bai daga min hankali ba anty sai dai maganan yasa na shiga wani halin tunane .
Da sauri tace tunanen may zahra ?
Sai danyi shiru sake tambaya tayi tana kallin fuskana tare da fadin wai kina mamakin abinda merry tayi ne ko may ?
Kin san ai ba tunane gare su ba dama kila da biyu ta aure shi ai da farko tana ganin zata iya juyashi zuwa akidar su.
Ko kuma wata kila don kwazon shi da himma data gani yasa ta leke may Allah kadai yasan niyar ta na auren shi tu farko.
Amma kowa yasan merry ai ba matar auren mijin ki ba abune dai kamar na rufa ido kin san halin maza abinda ka raina shi suke dauka da muhinmanci su a gare su.
Murmushi nayi tace mutum wanda keda mata haka kamarki danya shataf ga kyau ga kurciya in ba abin maza ba may zaiyi da wata merry arniya ma can.
Anty nace sai nayi shiru na kasa magana tace au kin dauka da wasa nake fadi nace ba hakabane anty sai na fara hawaye.
Subbahanallahi tace hankalin ta ya tashi a lokaci guda wanan maganan ai ban fadeshi don hankalin ki ya tashi ba zahra.
Kai na girgiza mata ta dafani tace ki bar kuka kin san kina cikin wani hali da ba,an son tashin hankali a gare ki yanzu.
Anty ba haka bane kawai dai ina kukane don zamana da yaya ban taba kyautata mashi ba a rayuwana a matsayina na matar shi kamar yadda shi yake kokarin kyautatawa rayuwana a kullun.
Kada kice hakan don shima maganan shi ke nan a kullun kan bai kyauta maki ba ya cuta maki a zaman ku ya ha,inci iyayyen kuna gida da suka bashi amanan ki ya daukoki daga gida ya kawo ki nan yana cuta maki.
Kaina girgiza tare da fadin ko daya anty yaya ya inganta min rayuwata wanda har abada zan amfana dashi koda bamu tare dashi.
Anty damuwana daya yanzu shine hanyar da zanbi in gyarawa yaya abubuwan da nayi masa wanda ni kaina nasan ban kyauta ba.
Dafa hannuna tayi tana murmushi kafin tace kai zahra akwai da wani magana tsakanin mijin da mata babu wanan abinda kike tunane yanzu.
Keda kanki a cikin hikima da basira irin namu na mata zaki gyara kurakuran ki na baya gare shi.
Ba sai kin furta mai kalman nadama da kike zaton shi zaki amfani dashi ba gareshi a, a zaki gyara mu,amulan ku ne fiye da da can farko ta hanyan yawan kulawa dashi.
Damuwan shi ya zama naki harma ki fishi kulawa ki tsaya iya inda ya tsayar dake gyara tsabatan gida da jiki har na yara ya kasance ba sai ya fada maki kiyi ba.
Kizama tankar mage gutin mijin ki kina dai ganin yadda muke a gida nan nida mijina da yaran mu.
Kifishi son yan uwan shi na jini koda ya nuna baison abinda suka zo mai da bukata a wurin shi ke ki nuna mai idan bai basu ba wazai ba.
Lokacin cin abinci tankar yadda kika san zaki ciyar da yaro na goye abinci haka ya kamata ki ciyar da mijin ki kina kula kina tarairayan abin ki.
Idan yai tafiya ko ya fita office kira na zuwa yana dawowa kina masa barka da aiki ko barka da hanya.
Ke idan kin rike wanan kawai ina mai maki rantsuwa ga Allah babu wata mace da zata zo ta fiki gareshi koda kuwa tazo da nata sallon nakin nan dai daya saba dashi har lokacin yana da tasiri a zuciyar shi.
Ina fada maki ba merry ba koda Allah yasa zai auro maki ba hausa nan gaba yar uwarki ba zata fiki komai ba gareshi.
Ajiyan zuciya na sauke ta mike tana fadin bari in barki haka nasan yanzu daddy Amar ya fito daga wanka zanje in dubashi.
Ta fice ta barni da tunane ashe abinda mamu keyi kenan wanda su hjy basu gane ba suke ganin ta sace zuciyar mijin su ga baki daya.
Don mamu idan tana da girki ba mu gane komai a gidan nan ranan bata da lokacin kowa haka bamu gane kanta sai lokacin da ta fita girki.
Tsoho ma ya ji dadin kulawa irin haka may zai hana yaro matashi dan shekara talatin da wani abu son haka kamar yaya ?
Ke nan ni nayi sakaci don rashin mai gyara min ko lurar dani hakan shine daidai gaskiya da anty Farida tace min in zama karuwan gida naji haushin ta a lokacin.
Akan may zatace in koma karuwa do kawai mijina ya soni kada ya soni in sai nayi kwarkwasa da hilla zai soni.
Ashe gaskiya tayi fushi dani wurin ganin wautana kan abinda take lurar dani din ban dauka ba Anty farida tana daga cikin masu kaunana na gaskiya ke nan.
Haka na kwana cikin tunane da damuwa washegari anty Ramla ta same ni a daki kwance tace yau dai zamu gyaran kai da jiki dake don yau sati biyu da tafiyan mijin ki nasan yanzu bai nisa da dawowa kasan nan.
Murmushi nayi kawai don jin abinda ta fada din don haka kamar yadda tace nima din ina so dama ko banza ban gane ma jikin nawa ba lokacin don ga nauyin ciki ga shi na koma gajal dani.
Gyara akai min sosai don shagon kitso da kumshi irin namu na Africa ta kaimu ance wanda ya fika dadewa yafika sanin kan gari.
Don ban taba tunanen akwai irin wanan wurin a kasan nan ba sai gashi kamar yadda miji da matan dana taba haduwa dasu ranan suka kaini wurin cin abinci ranan haka naga wurin.
Saidai abinda ya ban mamaki bai wuce irin kallon mamakin da mai shagon take bina dashi ba don tazo zata shige office din ta ana gaida ita tana wani shan kamshi .
Harta dan shige sai kuma ta juyo don hangoni a jikin mirrow din dake wurin datayi ta dawo baya.
Yaren su na yan libiya ta fara min ban san dani take yare ba sai da wace ke min gyara tace dake ake magana cikin harshen turanci na dago kai ina kallon ta.
Ta kara min yaren taji ban amsa mata ba sai ta juya da harshen turanci tana tambayana bana jin yaren su na arab ne ?
Na girgiza mata kai kawai ta dan tsaya jim tana kallona na dan lokaci kafin tayi yare da mai min kitson ta shige office din ta.
Ban kulata ba ban kuma tambayi mai kitson abinda tace ba sai da aka gama min aka fara wanke kafa da akaifa a hankali.
Saida aka gama komai naga matar ta shiga office dinta sai gasu sun fito tare da mai shagon wanan karon tana fara,a a fuskanta.
Take fadin tana son yin photo dani don ina kama da wata yar uwanta sosai muyi photo kala kala da ita a gurin kafin mu tafi.
Bata barmu mun tafi ba saida ta karbi layin wayana ni dai ina mamakin ta a raina bamu kara bi ta kanta ba muka koma gida bayan mun biya munyi dan sayayya abin bukatan mu.
A gajiye na dawo nikan wanka nayi naci abinci na samu wuri na kwanta don in huta gaba daya kamanin na sun sauya don gyaran dana samu a ranan.
Kwana biyu muna zaune sai kawai ganin yaya mukayi sun shigo gidan shi da oga Yusuf abin ya bamu mamaki don bai sanar damu dawowan shi ranan ba.
Baiji kunyan kasancewan Yusuf da matar shi wurin ba ya rugume ni yana wani sauke numfashi kamar wanda ya dade bai ganni ba.
Anty Ramla ce tace da fatan dai na iya kiwo ko ince mun iya ajiya nida mijina sai lokacin ya sakeni yana murmushi ya daga mata hannu alaman ta iya gaskiya.
A hankali na rada mai yaya Oga Yusuf na wurin fa yace zai hanani in duba ajiyata ne ya fada yana kallon Yusuf din.
Yusuf din yace ko daya duba abinka da kyau hakan yana da kyau ai suka kwashe da dariya .
Wurin kujera ya jani ya zaunar dani yana tambayana yaya kuke zarah kin canza min ga baki daya may Ramla take baki ne haka ?
Da alama taji dadin yaba mata da yadda ya ganni a har lokacin yana rike dani cikin rashin damuwa da wai suna gurin tsaye.
Yasa nayi kokatin mikewa in bar falon don kunya dariya suka kwashe dashi kafin Yusuf yace zaka koyawa yar mutane rashin kunya.
Dakina koma na zauna bakin gado nayi tagumi ina tunanen irin yadda zan tarbe shi idan ya shigo.
Sai gashi ya shigo yana fadin tunanen may kike hakane kuma dan firgita nayi ina fadin ba ba komai zuwan bazata da kayi muna ne kawai yake ban mamaki naga ko dazun munyi waya dakai da safe baka fada min zaka dawo ba.
Banson ki shiga damuwa saboda ina hanya ya hana in sanar dake dawowana yanzu ba gani na dawo ba .
Da sauri na dago kaina kalleshi a daidai lokacin da yake zama a gefena na kai kaina saman kafadan shi ina sauke numfashi a hankali.
Yusuf ya fada min sun kaiki asibiti last week may sukace mamaki da kukaje ya tambayeni yana kokarin kallon fuskana.
Nace sun dai min bayani ne kawai kan haihuwa zuwa yaushe sukace zaki haihu nace ba zakai wanka yanzu bane ka kwaso gajiya ?
Ya dan yi murmushi tare da fadin baki son zancen ke nan to mu barshi zan tambayi Yusuf yai min bayani ai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button