NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

A cikin amincin Allah yarana suke wani irin girma zakace kamar wani abin girma ake basu lokacin.
Kula sosai suke samu daga mahaifinsu da Addah da maria nawa dasu nono kawai idan na dawo in dan basu su sha sai kuma idan zasu kwanta in kara masu.
Bazakace wai nice ma na haifesu ba idan ba an fadama ba don uban ya fini kula da yaran don hakane ma sukafi shakuwa dashi fiye dani.
Don idan yana gida gaba daya shine mai masu komai ko Addah dake zaune damu lokacin tana hutawane saidai abinda ba,a rasa ba.
Na murje na zama kamar wata queen dani wayewa sosai ya zo min duk da haka ban yarda na bar al,aduna ba.
Ina bisa umurnin shi da dokan shi karatu yana tafiya a yadda yake so don akwaini da kokari sosai a fanin karatuna.
Yarana suna da shekara daya da wata bakwai na fahinci ina dauke da wani cikin duk da yaran suna saman kafarsu har an fara kaisu daycare suna dan daukan darasi.
Hankalina ya tashi sosai akan cikin dana gane ina dauke dashi lokacin yaya bai gari yayi tafiya sati uku.
Nasha wahalan cikin sosai wanan karon ba kamar cikin farko da aka ban sadakan shi ba wanan amai da kasala da yan ciwarwuka yake sakar min.
Har abin yaso ya shafi karatuna ga shi yanzu muna matakin karshe in zama likitan mata da matsalolin su don shi yaya ya zaba min.
Haka ya dawo ya sameni a cikin wani hali bai huta ba duk da naje asibitin bai yarda da zuwa naba ya daukeni muka garzaya asibitin.
Bayan yan gwaje gwaje aka tabbatar mai da ciki ke jikina na sati bakwai shi kanshi yayi mamakin hakan.
Ganin yadda na tayar da hankalina dole ya rufe nasa ya shiga aikin lalashina kan na kwatar da hankalina wanan ba komai bane ai, kuka kan nayishi sosai a lokacin.
Dole na hakkura na maida hankalina ga karatuna Addah kuma tana kara min karfin gwiwa da ban musalai iri iri wanda hakan ya kara kwantar min da hankalina.
Daga baya na fahinci kamar yaya ya shirya da matar shi don yawan zuwan zuwa America da yakeyi lokacin .
Ko kuma yana garin zaice min ba zai kwana a gidan mu ba zai tafi wancan gida nasa ya kwana.
Ban taba tambayan shi ko nuna mashi bacin raina ba kan hakan kuma ban taba mashi maganan ko sun shirya da matarshine.
Shima kuma tunda nasan ba mutum bane mai yawan magana ko fadar sirin shi da damuwan shi hakan yai masa dadi.
Muna waya sosai da mamu da kawu dasu Amma inda wani lokaci sukan tambayeni waiku har yanzu dai shiru saidai kawai in masu dariya in wayece zancen akan karatu nakeyi ai.
Amma kanyi fada sosai tace karatu zai hanaku aje iyali idan suna waya da Amma mutum yana kusa zaisha dariya sosai a lokacin.
Zuwana England zuwa yaya Nigeria uku bai taba zuwa dani nima ban saka raina ba tunda yace sai na kare karatuna zan tafi gida ban san dalilin shi na fadin hakan ba.
Haihuwana na biyu ma CS akai min aka cire yarinyar a cikina wanan karon kusan ince namafi wancan karon na haihuwan yan biyuna wahala.
Saukin abin Addah tana tare damu don taso komawa gida saboda kewan gida dakan addabi mutum a can.
Da kyat yaya ya lalasheta ta yarda don cikin dake jikina a lokacin da haka har Addah ta zauna damu na sheka biyu da wasu watani a kasan kafin ta dawo gida don hankalin ta ya koma gida ga baki daya lokacin.
Haka rayuwa yaita gudana al,umurah mai kyau da mara kyau suna faru suna wucewa kuma har dai lokacin abindana sani ba kauna tsakani da sarakuwana.
Don a gaba zasuyi waya zata tambayi merry da yar ta bata taba tambayana ba halin da nake ciki.
Shekaran dana kare karatuna a shekaran ne kamar yadda yai min alkawari wata rana kwatsam yaya ya dawo dags tafiya yazo min da maganan zuwa gida.
Ba karamin farin cikin jin hakan nayi ba ban kuma kawo fargaban yadda zamu kwashe idan muje ba a raina ko kadan.
Tun a ranan daya fada min zancen tafiyan tyn wanan ranan na soma shirin zuwa gida duk na fita naga wani abinda ya ban sha,awa zan sayowa kannena da mamu da sauran mutanen gida.
Duk wanan shirin bai san inayin shi ba a bangarena Allah Allah nakeyi watan dayace zamu tafi ya kama kawai in ga kaina a gida cikin yan uwana.
Wani tafiya daya dawo muna zaune naji yace zan baki kudi kuyi sayayan abinda kike bukata wanda zamu tafi dashi gida.
Na dago ina fadin sai dai idan kara masu zanyi don ni tsaraba ban san yadda ma zan dauke shi ba daga nan don tun ranan daka fada min na fara shirina.
Wanan kuma naki ne ki tafi ki sayo wanda nace da kudina azo a hada kayan wuri daya a tura ta ruwa su wuce dashi kafin mu tashi don akwai kayan da nake son za a wuce min dashi a cikin satin nan .
Ba halin inyi mussu dashi dole na karbi kudin daya bani na fita da zuman sayo wani abinda zan kara dashi.
A wanan fitan ne muka hade da wanan matar mai sallon don nayi zuwa barkatai bamu haduwa da ita wai ashe ta tafi libiya ne duk dadewan nan bata nan.
Itace ta shedani don ni ban ganeta ba tunda an dade wanan lokacin ta bukaci in bata address dina da layin wayana kan tana son magana dani wanda bai yuyuwa a nan.
Mukai musayan layi da ita mun rabo nayo sayayya sosai kudin daya bani kamar ban taba ba .
Kwana biyu da haduwan mu da ita sai gata a gidan mu taro sosai nayi mata na karramata.
Bayan mun dan taba hirane take tambayana ko ina da yan uwa dake zaune a libiya nace mata gaskiya ni ban san kowa ba a can.
Tace ban taba jin labarin ina da yan uwa a kasan ba na girgiza mata kai da a,a tayi shiru can ta zaro wayan ta daga cikin jakkan hannun ta ta dan taba sai ta miko min na karba.
Sak da wace ke cikin hoton kamar mu daya kusan kuma shekarun mu daya da mai shi saidai zata dan girmay mun.
Ajiyan zuciya na sauke nace lalai muna da kama sosai tace shiyasa ta matsa min da tambaya tace inje gaba in duba akwai wasu photuna na family din su.
Kallo nake cikin nazari sosai don kamannin yan cikin photon da nake gani da mu sosai.
Tace a Nigeria kowa naki yake nace eh kowa nawa yana nan kasan tayi shiru can nace saidai mamata nakan ji ana fadin babbarta ba yar Nigeria bace ita kuma tun da ta tafi ta barta a zanin goyo har yau basu kara ganin juna da ita ba.
Da sauri tace min ko zaki bani photon maman naki ingani don Allah ?
Na neme photo mamu na nuna mata a wayana wanda nayi zoming ta tsurawa photon ido sosai sai ga hawaye yana fita daga idon ta.
Kallon mamaki nake mata tace wanan yar yarmu ce data bari a Nigeria ko tantama ba zanyi ba yar uwar muce wanan.
Yar uwarku na tambaya ina mamaki tace kwarai wanan kamar haka ba zai tafi a banza ba saida dalilina jini mai karfi
Ko zaki iya kira min mahaifiyar taki a waya yanzu muyi magana nace zan gwada in gani ko layin ta zai shiga.
Sai akai rashin sa,a layin yaki shiga haka yasa na bata layin mamu akan zata kirata suji idan itace.
Ta tafi ta barni cikin halin damuwa da tunane tare da fargaba cike a zuciyata sai bayan tafiyan tane yaya ya dawo gidan nake labarta mai zuwan matar.
A ina kika hadu da ita ya tambaye yana kallona a cikin mamaki nace a shagon ta mukaje gyaran kai da anty Ramla ranan tun ina da cikin su Abdulrahaman na bashi amsa.
Duk wanan dadewan baku hadu ba sai yanzun kuma na bashi amsa da eh sai shekaran jiya muka hadu a shago wurin sayayyan danaje.
Shiru yayi na dan lokaci yana nazari yace gashi kuma jibine tafiyan mu banda lokaci da sai mu ziyarce ta in karajin wani bayani a gurin ta.
Yanzu sai idan Allah ya dawo damu lafiya zamu neme ta Allah ya kaimu kawai na iya furta mashi lokacin don yanayi sai ina jin shi wani iri.
Komai da zamu tafi dashi ya tura gida ta jirgin ruwa sai wanda mukafi bukata da zamu tafi dashi tare damu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button