NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:52 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALLAHUMA INNI AS, ALUKAL HUDA WAL TUKA WAL FAFA WAL LUDAIINA, , , , , ,

Gaba dayan su ba mai iya furta komai sai innalillahi wa inna alahim raji, un bamunan su ke iya ambatawa.
Da kyat hjy jummai ta iya furta hajiya wanan maganan ina ya fito haka wani sabon sherin kuma ake son kulla wa diya don kawai anga sun dawo kasan nan lafiya cikin wadata.
Ke dakata don Allah a nan wa kike fanin zai kullah wa umar sheri a cikin mu ko hajiyar ce zata kulla mai wanan sai Amma tayi murmushi tace in banda abin jummai sunan kin haifi yaron nan saudaki ne kawai amma baki fini son shi da shakuwa da shi ba.
Ina nan zaune yaron nan ya samay ni fuskan shi da yanayin sa a cikin damuwa kwana biyu na shiga damuwa sosai sai daga baya yake labarta min damuwan shj dana damay shi da tambaya.
Farkon wljin wanan maganan vun yar kakabun nan na fara ji A ruwa take min wanka da jurwaye da zancen.
Da sauri mamu tace Sayadi kuma gwago ina ta jiyo wanan maganan itako babban magana irin haka ?
Allah masani ke dai yar nan anan ta samay ni cikin damuwan rashin walwalan shi kwana biyu kin san itace abokiyar firan nawa wani lokaci ina magana shine take fadin wai kai sai kuma ta kasa fadin abinda na fada mata ranan don ganin idanun da sukai mata yawa lokacin.
Ehh lalai wanan yarinyar takai shu,uma har sherin yakai gun yarana haka a hasale kawu bala yace ke jummai ki bari mu fuskanci matsalan da ya kunnu muna kai ki daina muna wanan shirmay.
Ko ta fada yanzu ai ba abin mamaki bane don kila a wani wurin ta samu labarin don yanzu maganan duniya ba boye yake ba mama Altine yayan mama hadiye ke fadin haka.
Yanzu naji inda wanan sherin ya tafito a gidan nan dama ko ba,a fada ba kowa yasan a rina har bakin cikin yakai haka ban sani ba.
Ke jummai na fada maki ki daina muna wanan shiman may ye na bakin ciki da diyan ki ina abinda yai yaran ki shiyayi yar nan da kike son zargawa magana.
May ye abin zargi a cikin maganan nan Bala sadauki da kansa yazo ya samay ni da zancen yana son in roka mashi gafaran ku.
Tun fara maganan Alh sani bai iya furta komai ba sai zufa yake yayin da kanshi yake duke zuviyar shi tana batun bugawa a lokacin.
Sai mama hadiye ta katse mai tunane da fadin yanzu may ake ciki da wanan zancen mai daure kai yaya.
Sai lokacin Alh sani ya dago kai yana fadin may ko ake ciki hadiye illar yaje ya nemi wasu iyayyen tunda ya nuna yana dasu cikin duniya .
Ni dai na zamay hannu ga duk wani alamari Faruq a gidan nan yaje ya nemi iyayyen shi can duniya ce fadi gare ta ke kuma jummai kin kai ga yadda kike so Allah ya isar min a gare ki yana fadin haka ya mike yana sharan hawayen dake barazanan zubo mashi a idanuwan shi.
Ba hajiya jummai duk wani wanda ke falon a lokacin ya tausayawa Alh sani da kuma firgita da kalamin Alh sani daya furtawa hjy jummai.
A hankali hawayen bakin ciki ya fara zo mata na nadama tana fadi a cikin kuka yanzu may ye nawa a cikin wanan zancen don Allah.
Yaron yanzu ne ka haife shi baka haifi halin shi baka shedan dan yau har kina kokarin dora laifi kan yar mutane sai Amma tace .
Balle zancen yar nan dutse ne don zaman su da arna take magana na kwabe ta ashe bamu tsira da zancen ba.
Yaya yanzu mainene abin yi don Alh ya tashi a cikin fushi bai tsaya an samo ma maganan mafita ba.
Tunda ya riga ya aikata har an kai ga rabo ai sai a san yadda za a gyaro maganan yanzu kuma mama Altine ke magana don su din yayyun mahaifiyatace yasa nake kiran su da mama sabanin yaran gidan da suke kiran su da gwago.
Ni banga wani abin bata lokaci ba ai gaskiyan Yaya din daya ce duniya da fadi yaje tunda dangin matar shi sun fi mai da zaiyi abu gaba gadi babu sanarwa.
Amma ta dan girgiza kai tace zanso muji ta bakin umar din don ya fada muna dalilin shi na yin haka ba tare da sanin mu ba saboda kada mu yanke mai hukunci a cikin duhu .
Yanzu sai mu bari har wani lokaci idan mun kara tataunawa akan zance sai mu sake zama sai maganar gaskiya wanan yaton bai kyauta muna ba wallahi.
Hjy Jummai kamar ruwa ya cita a gurin don zaune take tun bayan da zance ya tabbata gaskiya shi yazo da wanan maganan mai kama da tatsuniya a wurin su.
Da dadaya suke ficewa a falon kowa ranshi a bace da wanan zancen da yazo masu na bacin rai inda hjy jummai ta bi bayan su kawu Bala ta fice a cikin wani yanayi.
Duk ido matan dake falon suka bita dashi lokaci daya kowa yasan irin halin tashin hankalin da take ciki a lokacin don duk wata uwan da tasan zafin dan ta bata kaunan wanan abu ya faru dashi.
Bayan kamar yan dakiko mama Altine ta fara magana tana fadin irin abinda akewa gudu ke nan wallahi.
An sosa wa hjy maryam rai don zuciyar ta fari yake kal kan wanan zancen don tasan komai na iya faruwa tsakanin hjy jummai da maigidan su a yanzu.
Tace dama idan kace baka son ran yaro ya baci kai naka sai yafi dubu bace don yaya bata son afadi laifin yayan ta ko kadan.
Don haka ne ko kaga yaro yana abu a gidan nan kaidai iyakan ka ido yau ina alfaharin da ake muna yaranta sune gida su suka iya, , , ,
Haba anty maryam wanan magana bai dace ba don wanan abu ya shafi kowan mu a nan sannan duk mu nan iyayye ne idan daji bai gama cin wuta ba ba aiwa kukuture barka don babu bare a nan yanzu cikin mu.
Mama hadiye ta amsa da wanan haka yake gaskiya indai baka tausaya ba bakace kuma gwai ba ai ba.
Tace ba haka nake nufi ba kowa a nan yasan halin yaya akan rashin son a fadi gaskiya akan diyan ta shine nufi na.
Sun dauki lokaci ana magana a wurin kafin su watse kusan lokaci daya mamu da hjy maryam suka fito daga part din.
Hjy maryam bata daddara ba tace maimuna baki gane nufi na ba zakice baki jin zafin yawan gorin da alfaharin da ake muna gidan nan ne.
Don kawai mu an maishe banza a gidan nan damu da yaran mu ana daukan mu damu da babu duk daya ne a gidan nan.
Kai duniya amma wanan maganan naki baiyi ba wallahi Allah ya kyauta tana fadin haka ta shige ta barta tana hadiyan kili bibin dake cin ta lokacin don ita kan a wurin ta hakan yai mata dadi taga kurin zuwa turan yaran da ake mata ga tsaraba turai ta samu dan ta ya jajibo mata arniya a matsayin sarakuwa a gida da gari duka.

Hajiya Jummai a har gitse ta shiga shiyan ta dama kiris take jira ta fashe da kuka don ba karamin daurewa tayi ba na controling din hawayen kada su zubo a gaban makiyan ta.

Jin sheshekan kukanta yasa su salma saurin fito da sauri a rude suke suna tambayan abinda ke faruwa sai dai ba baki kuka kawai take rusawa zaune.
Wanan ya tayar da hankalin salma ta daga waya tana kiran yayyun ta tana fadi suzo gida babu lafiya hjy ce daga an kirata part din Amma ta dawo masu tana kuka cikin tashin hankali take maganan.
Umar din data kirashi tana fada mai yace shi yana lagos tun da safe baya gari a cikin zuciyar shi cewa yake am fasa kwan ke nan shike nan Amma ta fasa kwai a gidan.
A rude su Aliyu suka shigo gidan kowa ya gansu yasan hankalin su a tashe yake dan sun dauka wani rikici ne ya faru a gidan sun shiya cin mutunci yau ga ko waye don basu iya jure ganin mahaifiyar su a kullun cikin bacin rai hakana.
Mama may ke faruwa ne haka may ya faru dake kuma mama ta kasa basu amsa daidai lokacin sisters din ta suka iso suma.
Tambaya daya suke mata suma ta kasa basu amsa saida suka matsa mata da kyar ta iya bude baki tace yau ni Alh ke jawa Allah ya isa akan babawo.
Salati suka saka lokaci daya suna fadin may yai zafi haka kuma har yakai ga furta hakan gareki kuma ?
Wai ashe babawo yayi auren arniya a can ban sani har tana dauke da cikin shi yanzu haka yaron nan bai fada min ba asan mafita sai a bakin kakarshi nake ji.
Salati suka saka tare da fadin aure arniya kafira mara sallah kuma a can ko a nan ne ai ya jawo muna abin kunya gare mu.
Yanzu ina babawon yake ne dayan yar uwar nata ta tambaya Salma tace bros yana lagos tunda safe.
Ta juya tana fadin kinji ba nasan duk wanan abin ba a banza bane mahasda sunyi muna yawa a tattare damu.
Haba mama may ya kawo zancen hassada ga wanan zancen da ya shafi bros a can kawai yayi aure sai kuyi mai fatan alheri ciki ai yanzu bros shiba yaro bane zai iya yin abinda yake so.
Habbib ne da ya fara gajiya da irin halin mahaifiyar su yake fadin haka yace ni banga abinda zai sa ki wani tayar da hankalin ki haka ba sai dai in akan kalamin daddy ne ?
Shi daddy may zaisa ya furta hakan don kawai ke kika haifi bros ko may yana da incin da zai auri wace yake so yanzu ai.
Balle auren yau fa kusan shekara hudu kenan da yayi shi komai kuma bai faru ba gare shi so ni banga wani abin tayar da hankali ba a nan ?
Kallon shi sukayi suna fadin kun san da wanan zancen baku fadawa mahaifiyar ku ba amma ko kunyi kuskuren boye mata dai .
Mama may ye a ciki don yayi auren shi a can ba a can yake zaune bane zai zo nan yayi aure ne kuma idan matan nan basuyi mashi ba fa.
Sai lokacin tace ni ba abin bakin ciki gare ni duk da naji haushi wanan zancen amma wai yadda aka tara kowa ake fadin wanan maganan kamar kaina aka fara hakan gaban maryam da maimuna fa Alh ya kirani suke fada min.
Amma ai mashi auren gata a cikin dangi kamar kowa a mutunce ai zaifi yaya arniya kafira zata shigo cikin mu da sunan sarakuta ?.
16/11/2021, 22:55 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANI RAHIM YA HAIYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTA GIS, , , , ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button