NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:22 – ????????????: Suna shiga dakin bayan sun karewa merry da yarta dake zaune falo tana ta waya kallon kwam suka shiga dakin da mamaki da gulman dake cin su a rai.
Don basu samu damar kebewa ba saboda ba lokaci a gurin da zasu samu magana kafin shigan su dakin da hjy take jinya a ciki.
Itama hjy zaune take da imanin ganin merry a hakan daya cika mata zuciyar ta da mamaki da tsana har lokacin da suka shigo dakin.
Amsa masu sallaman su tayi har lokacin tana zaune saman keken da aka tanadar mata don zama da laluran kewayawa a dakin.
Gaisawa sukayi ko karasawa basuyi ba hjy sabuwa ke fadin hjy jummai wanan ta zaune a falon ku da yarta wacece ita.
Naga wata katuwar arniya tayi kane kane zaune a falo tana busan iska a gidan nan kamar wata yar gida har yaya akayi wanan kafirar ta shigo gidan nan haka ?
Dan runtse ido hjy tayi daga zaune tana mai jin dacin kalamin hjy sabuwa a ranta ga nauyi da kunyar fada masu itacr matar dan nata ai da takeji tun shigowan su da hjy sabuwa ta fara magana.
Idon ta bude a hankali tana bude baki da kyar ta iya furta matar gidan ke nan ai hjy .
Itace kafiran da yake aure a can kafin Alh ya aura mashi wanan yar ta wurin maimuna daga baya.
Wanan din itace matar Umar din dama abu haka kamar ginan dare ba wani kyau ba fasali a tare da ita ko kadan.
Gane min hanya dai ta fada tana sauke wani nauyayyen ajiyan zuciya a tare da ita.
Sai lokacin samira da tun shigowan su tsana da kishin merry ya baibaye zuciyan ta a lokaci daya don yadda suka sameta a falon da ita ake mata rowan shigowan shi tana matar gidan saiga kafira ta gani a zaune tayi kane kane a cikin sa.
Jin an anbaci itace matar umar din ta kara jin wani kin merry din da yarta har cikin kokon ranta lokaci guda.
Yanzu wanan abar itace dear yake aure har yake iya fifitata dani dama wanan mai zubin samudawan farko ga kira da kama kamar suffan namiji.
Aike dai batu ne bai faduwa hjy sabuwa tace tana kaiwa zaune ga gulma nacin ta tace.
Me tazoyi a nan kuma yanzu tana fada tare da kallon fuskan hjy jummai tana son jin abinda ya kawo merry din kasan.
Yadda kuka ganta haka na ganta da safen nan nima rabonta da kasan nan tun tana dauke da cikin yar nan nata da zo muna a bazata tun wansn lokacin bata dawo ba sai yanzu.
Ikon Allah hjy sabuwa ta fada tana gyara zaman ta don taji labarin da dadi a kunnuwan ta sai kallon hjy jummai takeyi don jin tayi shiru ga labarin data dauko basu din na merry da yarta.
Jin shirun yai yawa tace dole ne Alh sani yai ma dansa haka jummai wanan irin abu hakan babu fasali ai kazantane ga kowa.
Uhumm kawai hjy jummai ta iya fada a lokacin don yanzu ta fara fahintar hjy sabuwa ta fara gane zama da su da takeyi ya hana ta sake wani zance mai zurfi kan iyalin nata.
Magana sosai suke sakewa kan merry da umar din tana jin su kala bata furta masu ba har suka gama don kansu tana fadin zata koma dama kwana biyu bata zo dibata ba yasa ta shigo yanzu.
Koda suka fito merry bata falo tana ciki da yarta sun kwanta sun so su kara mata kallon kurulla sosai saida bata wajen a lokacin.
Part din samira suka koma nan suka yada zango hjy dake fadin tana sauri sai gata har azahar a gidan suna kule kule da yarta a gidan.
Ya Umar bai dawo gida ba sai bayan la,asar don sun tafi wani gona nasa dake wudil duba shanayen da ake masa kiwo a ciki.
Dawowan nasa yayi daidai da tashin merry da yarta da suke barcin gajiya tun safe da suka shige daki.
Suna zaune suna cin abincin da aka hada masune ya shigo gidan a gajiye don ranan da ya kwaso a can wurin zagayen da yaje din.
Queen ne ta taso a guje zuwa taron daddy nata tana fadin tayi missing din shi tun safe daya fita.
Rugumar yarinyar yayi tare da dagata sama yadda ya saba mata idan tayi mai hakan yana shafanta yace miss you too dear tare da mayar da hankalin shi ga merry dake zaune a gurin dining.
Saida ya iso wurin ya sauke yarinyar ta hanyar zaunar da ita saman kujera ya dan kaiwa merry din kiss kafin ya zauna tare da tambayan ta yaya suke ?
Dan bata rai tayi kafin tace dashi not bad saidai kewan Us da sukeyi kawai don yanayin nan akwai zafi da yawa sosai.
Daga kai yayi ya kalli AC dake aiki a falo har biyu yana fadin kada ki manta da kema nan kasan kine ai ya bata amsa yana zama saman daya daga cikin kujerun wajen.
Kasanane saidai ba zama dole in fadi hakan ba yanzu tunda ina da shedan zama yar kasan America yanzu don acan aka haifeni.
Kaga na samu riban kasa biyu ke nan a rayuwana hira sukaci gaba dayi a wurin suna cin abinci gwanin bannsha,awa .
Yana kkatin nuna masu kulawan shi a kansu don bakuntar da suka kawo mai har kasan shi duk da yasan zuwan nata ba a banza tayo shi ba haka.
Saidai ya saka mata idone yaga iya gudun ta da abindaya kawo ta din don yasan zata fada da bakin ta saboda sanin halin ta dayayi.
Can sun kusa gamawa takira sunan shi ya dago yana kallon ta take fadin ya bata mamaki daya iya boye mata abinsa a yanzu.
Aje spoon din dake hannun shi yayi yana kallin ta a cikin mamaki tare da fadin me yayi mata har ya bata mamaki din shi a zaton shi wani abune can merry din taji game dashi kuma .
Omar can you imagin idan nice har na iya yima hakan na boyema wanan sirin nawa kana da kudin da zaka zo nan kasan kayi wani abu dashi ka kasa fada min in baka shawara akai wai sai kazo kasan nan da barayi da mayaudara sukai yawa ka gina company ba tare da sani ba Omar ?
Ajiyan zuciya ya sauke don jin abinda ta fada mai ya dan murmusa tare mayar da kanshi saman makirin kujeran da yake zaune akai kafin yace.
Merry nayi mamakin da har kikai saurin matawa hakan ko kin manta tsakani na dake kotu ta raba muna komai da muka samu a tare.
Baka manta da zancen ba ke nan ta fada tana kallon shi ya bude baki zai bata amsa takon tafiya ya tsayar dashi ga abinda yai niyar fada a lokacin.
Sin mayar da hankalin su ga kofan falon samira ce ta shigo taci kwaliyan dogon rigar shadda a jikin ta mai aikin stones har kasa sai sheki takeyi.
Hakan yana daga cikin abinda suka kitsa da uwarta kafin ta tafi dazun don hakane ta fara aiwatar da shirin ta a yanzu.
Tana zuwa direct wurun shi ta nufa duk da zuciyar ta na mata dardar karya tsuka ta a gaban merry din da yarta data same su a zaune.
Ga wani irin uban kishin merry din data gamsu a tare yanzu yana cin zuciyar ta tun kallin farko datayi masu dosowan ta wurin.
Dan dafashi tayi cikin karfin hali da daurewa cikin kissan mata tana kai goshinta a daidai saitin fuskan shi tana fadin ka dawo ashe duk da bata san fitan shi gidan ba a ranan.
Na dawo ya bata amsa cikin karfin hali yana dagowa daga yadda yake zaune yai balance saman kujeran a lokacin da suke magana da merry kan abinda ya kawo ta kasan.
Merry dake zaune imani da mamaki ya kasheta a lokaci guda sai kallon mamaki takewa Samira din tare da tambayan kanta ita wanan wacece gare shi kuma haka.
A yadda tasan mijin nata da kamun kai da rikon addinin shi baya wanan akidar da wata mace idan ba ahalin shi ba.
Umar daya dago daga zaunen yana gyara zaman shi yace ga matana merry da yarta Queen sun zo yau daga America.
Yana nunawa samira din su merry da hannun shi cikin dakewa tace au wanan ce kafiran da ake fadi kana aure ashe, tana maganan tana kallon merry din da yarta.
Who is dis woman merry ta tambaye shi tana kallon shi don san jin ko ita waye a gare shi kafin ya fada samira tace his third wife.
Da sauri merry tayi wani zabuwa a inda take zaune sai kuma ta koma ta zaune tana sauke numfashi ba merry kadai ba har Queen da take yarinya a cikin su kallo tabi samira dashi lokacin.
No no no you can’t be my father wife he’s only marry my mum and twin’s mother right Dad tana kallon fuskan uban nata.
Dan murmushi yayi kafin yace right my Queen wanan tana fakewa a gidan nan ne da sunan uwata OK ?
Kai yarinyar ta gyeda mai alaman gamsuwa yayin da su duka suke kallo umar din da yai wanan maganan with one mind a fuskan shi.
How comes merry tace ya bata amsa da as you can see now yana kokari tashi daga wurin don duk a matse yake a lokacin dama merry din ta dakatar dashi wurin wanka yake son yi yaji sanyi a jikin shi.
Yasan baza a rasa wace zata biyo shi ba hakan yasa ya rufo kofan nasa yai masa key lokaci guda tare da sauke ajiyan zuciya.
Sai a lokacin muka fado mai a rai zama yayi bakin gadon yana kokarin balle aninan rigan shi yana kiran layin mu duk da yasan lokacin dare ne can sosai.
Kiran na batun katsewa na daga idona yana cike da barci a lokacin da sallama a bakina ya amsa min.
Kun kwantane ya tambayeni nace eh yau banjin dadin jikina nida Abdulsalam may ke damun ku ya tambaya da sauri .
Na bashi amsa da sanyi ne yai yawa ya saukar muna da zazzabi sai ciwon kai da mura da kowa ke fama dashi.
Kun tafi asibiti ya tambaya nace nakai yaran dai don har babana kwana biyun nan duk baijin dadi shima.
Shine baki fada min ba da mukai waya jiya dake nace naga ba wani sosai bane ai a jiyan yasa ban fada ba.
Idan jikin ba sake ku ba ku koma asibitin a gobe idan Allah ya kaimu muji mai zasu ce har sanyin ya sauka hakane daya fara ba mutane wahala.
Sanyi ake sosai a nan yaya bama fita ko ina duk kwanakin nan muna gida rufe sai yau da muka fita zuwa asibiti din.
Idan har sanyin zai maku illa haka gara ku dawo nan ku karasa hutun ku don tsaron lafiyan ku ya fada.
Ya jikin hjy na tambaye shi cikin kulawa yace da sauki tana gida an sallamota tun jiya fadin hakan da yayi ya gagauta mikewa tsaye yana fadin zan kira da safe inji jikin naku.
Daga haka ya kashe wayan nasa wanka ya shiga a gurguje don yana son leka hjyn su a lokacin tunda ya dawo bai lekata ba ya samu merry falo ta tsare shi da magana.
Barin falon shi aka tsaya kallon kallo tsakanin merry da Samira kowa nawa dan uwa kallon tsana.
Banza kawai samira tace tana jan tsuki tare da juyawa zata bar wurin taji merry tace mata mara fuck you bich .
Hakan yasa ta juyo da karfi itama tana fadin fuck you too yar iskan banza kawai kafira mai fitsari tsaye nan zagi ya kaure a tsakanin su kowa na aikawa dan uwa zagin daya zo mai a baki lokacin sunawa juna kallon tsana.
Hjy dake daki tun tana dan jin yaniya kadan kadan ta fara jin sauti na tashi ga muryan samira daya karade gidan .
Haka yasa tayi kokarin hawa keken ta da dabara sai ta fado kasa daidai zata hau din wani kara ta sake mai karfi saida fitsari ya zubo mata duk ta bata jikin ta dashi don zafin da taji.
Gashi ta kasa dagawa daga inda take duk kokarinta na son ta dago da kanta da takeyi din ta kasa hakan.
Gasu kuma muryan su da duk ya karade gidan do hayaniya sule sosai a falon har wanda ke wajen haraban gidan zai iya jinsu a lokacin.
Koda umar ya fito bai tsaya ba a gurguje ya saka kaya duk da doguwan rigan jallabiya ya sakawa jikn shi yana sauri ya leka mahaifiyar shi a lokacin da tun shigowan shi bai samu lekata ba.
A lokacin ne kuma yake jiyo hayaniyar matan nasa a falon da sauri ya karasa fita falon nan ya same su suna abinda sukeyi kamar zasu buga a tsakanin su.
Wani irin tsawa ya buga masu tare da nunawa samira kofan fita daga falin bata fita hakana ba sai da tace dashi .
A kan wanan kafiran matan naka mai fitsari a tsaye kada ka daka min tsawa don Allah dama wata mace ce ba wanan abin banza da kake takama wai mata ba gareka.
Duk da merry batajin me take fada tasan bakar magana take fadi game da ita shiya bata kyale ba tana jefa mata irin zagin su na yan America mai zafi.
Juyowa yayi wurinta yana fadin zatayi shiru ko sai ranta ya baci itama yana fadan haka ya wuce zuwa dakin da hjyn ke ciki.
Tun a kofa yake jiyo nishinta ya shiga da sauri yana fadin mama lafiya yadda ya same ta kwance a kasa ba saman gado ba ba saman kujeran ta ba.
Yasa shi fadin mama lafiya ya hakan ya faru dake cikin kidima yake magana hankali tashe.
Hjy babu bakin magana har lokacin sai wani irin kugin wahala da take fitar wa kawai takeyi a dakin kokarin daga ta yayi sai lokacin yaga abinda tayi wanda yasa dakin yake bashi a lokacin.
Hakana cikin dauriya ya daga ta yana kalon irin yanayun da take ciki rausayin mahaifiyar nasu ne ya kara tsarguwa a ransu lokaci guda daukan ta yayi zuwa bayi ya hada ruwa tare da duk yadda zaiyi ba tare daya wani wuri na jikin ta ba ya gyara ta ya fito bayan ya barta ta takara inda babu halin tabawa a gareshi ya fara gyaran dakin da kasan zuciyar shi cike da tausayin mahaifiyar tasu don yasan wanan na daga cikin jerabawan ta da Allah ya aiko mata.
Bayan ya gyara dakin ya fesa kamshi sosai ya koma ya samu ta gama haka ya daukota zuwa dakin ya azata saman gado sai faman sannu yake mata a lokacin.
Fita yayi da sauri zuwa falo ya hadu mata abinci da kanshi duk da yasan an bata abinci a lokacin sai yanzu yake tunanen ina mai aikin da aka dauka don kula da hjyn kawai a gidan ta tafi ?
Koda ya dawo dakin bai samu tambayan ta daga ta yayi ya bata abincin taci sosai kafin ya kawo magani ya bata tasha.
Sai barci mai nauyi ya dauke ta duk da magariba ya gabato a lokacin ya dan dade dakin zaune yana tunane a ranshi ranan ba kalan tunanen da baiyi ba a zuciyar shi.
Kafin ya fito zuwa haraman yin sallah babu kowa a falo daya fito son haka kai tsaye dakin shi ya nufa ya dauro alwala ya fito zuwa sallah.
Bai fito massalacin ba sai baya isha,i takwas da wani abu dakin mahaifiyar shi ya leka ya samu har lokacin tana kwance tana barci saboda maganin da tasha.
Ya dan dade tsaye wurin kafin yaji motsi daga kofan alaman mutum a wurin ya leka dakin wanan matar ne ke dan rabe rabe mai kula da hjyn a cikin dan daure fuska yake fadin ina kika je kika barmin mahaifiyata ciwon ta ya tashi.
Mun daukoki ne dan laluranta sai ki tafi ki barta a cikin matsala badon Allah ya kawo ni ba yau ban san abinda zai kasace da ita ba.
Jin yayi shiru tace Alh ba laifina bane hakan nima sai da nai gudun hakan amma hjy tace in tafi wurin aiken da taimun a gafarceni Alh hakan ba zai kara faruwa ba insha Allahu.
Kala baice mata ya fita daga dakin yabar matan tana sauke ajiyan zuciya a dakin ita kadai sai hjy dake kwace sharkaf da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button