NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ya fito zai shiga mota ke nan wayan shi yai kara ya dauko daga aljihun shi yana duba merry ce lokacin.
Yana dauka tace dashi Omar what are doying in that country of to know ko ka manta da kabar mutane a nan ne ?
Tambayan ta bashi mamaki matuka don haka shima ya mayar mata da mai zafi lokacin tare da fadin kada ki manta mahaifina ne baida lafiya .
Bayan haka ko kin manta Nigeria kasatace ta haihuwa da zan iya zama so raina.
Wanan katon sai ta kwantar da murya tana fadin naga kasan Christmas ya kusa zuwa dear amma baka dawo ba har yanzu almost to one month kake nema a can fa yanzu ?
Yace shima cikin kwantar da murya kamar yadda tayi din i will come back very soon insha Allah .
Ba tare da tambayan jikin mahaifin nasa ba ko wani na gidan nasu tace love you kawai ta kashe wayan ta.
Kallo wayan nasa yayi cikin takaici zuciyan shi cike da mamakin halayan merry din da mugun halin nan nata .
Ya fara zargin ta a ranshi daman boye mashi halinta na gaskiya tayi don ya sota don haka kawai idan ba halinta bane hakan ba zata iya hakan ba kai tsaye.
Don yanzu kanta da yarta kawai ta sani bata damu dashi ba balle wani nasa ta nuna mai kauna ko kulawa.
Ko wanan yarinyar daya kai da sunan kanwar shi da cewani bata tambayan shi komai a gamay dani din.
Har yakai inda zai tafi ya dauki nasir abokin shi bai kaiga samun mafita ba akan merry din .
Horn yayi Nasir din ya fito ya dauke shi suka tafi har lokacin bai sake ba sai Nasir keta zuba a motan shi kadai.
Can dai ya juyo yana fadin yaya dai mutumina naga kamar ranka a bace yake kuma yanzu bayan munyi waya dazun dakai lafiya.
Dan shafan fuskan shi yayi da hannun shi daya yana fasin kaidai bari mutumina har kan merry ne ke bani mamaki wani lokaci.
Kamar ya Nasiri yace dashi sai yace bari kawai mutumina wai ace matar nan fa tun zuwana duba daddy bata taba tambayana ya jiki daddy na yake ba ?
Dan murmushi Nasir yayi yana kallon shi kafin yace hausawa sunce kowa yasai lariya yasan zarayi yoyo ai ?
Ba mamaki su a wurin su hakan ai ba komai bane so kaga sai kayi hakkuri kawai da halinta tunda kana son matar ka.
Kasa ba nasir din amsa yayi do yasan magana yai masa a fakaice muryan Nasir din ne ke fadin ita wanan yar uwan taka fa kuna waya da ita kuwa don ita kan nasan tarbiyan muce ta musulman hausawa gare ta..
Yayi kamar baiji mai Nasir din ya fadi ba lokacin ya share shi ga zancen kawai yana tuki abinsa.
Nasir din ya sake fadi wallahi mutumina kaji tsoron Allah ka dauki yarinya karama kaje da ita inda bata san kowa ba kana gana mata boni can.
Ya juyo a harzuke yana fadin ubanwa ya fada ma hakan duk kokarin da nake kenan banyi ba ko.
Kai Nasir nifa har yanzu kallon kanwata ko yata nakewa wanan yarinyar har yanzu.
Amma ko bakai ma kanka adalci ba abokina kana ganin yanzu ita wanan matar taka zatai maka halarci nan gaba.
Ya juyo da kyau yana fuskantar shi yace ya kamata umar ka natsu ka fahinci mai mahaifanka ke nufi da hafin auren nan gareka.
Umar baka sanin kayi sakaci da daman ka sai nan gaba kadan idan girma ya fara zo maka.
Ko kana neman wani mukami a kasan nan a lokacin zakayi dana sanin watsi da wanan daman da mahaifinka ya doraka akai.
Ya juyo shima yana fuskantar abokin nasa cikin fadin ban gane mai kake nufi ba Nasir ?
Kana tunanen zan shiga siyasa ko wani abu a kasan nan ne nan gaba ko kana tunanen zan daukowa kaina maganan da zai ja min tozarci.
Kai Nasir ya girgiza yana fadin baka dai fahinceni ba abokina mu bar zancen nan bawai ina kalubulantar matar ka bace ko daya wallahi gaba nake hango maka kawai yasa na fadi hakan.
Huci yayi gami da furzo da iska daga bakin shi yana sauke ajiyan zuciya tare da dan buga sitiyarin motar a hankali alaman jin haushi a ranshi.
Baisan lokacin dayace mata mata ba babba ba yaro a cikin su halinsu daya ne abokina in fada ma yanzu haka a cikin takuran hjy mu nake tun zuwana kasan nan .
Don har yanzu hjy bata janye maganan ta ba Nasir kan yarinyar nan taya kake ganin zan yaudari daddy in affaka wa yar karamar yarinya saboda in bata mata rayuwan ta a banza Nasir.
Duk abinda mutum zaiyi yayi zurfin tunane a cikin sa bazan taba son aiwa yata ta cikina ko kanwata yadda mama tace tana so in mayar da yarinyar nan karamar bazawara.
May karamar bazawara ke nufi Nasir in lalata rayuwan yar mutane in sako masu ita a wullakance Nasir ba zan taba yin haka ba a rayuwata yar maimuna kamar jinanane Nasir.
Ido Nasir ya zuba mai a cikin mamaki yake kallin abokin nasa can yace idan har hjy ta furta hakan batayi maku adalici ba dakai da mahaifinka abokina.
Shawaran da zan baka a nan shine kada ka yarda ka saki yarinyar nan koda daddy baya raye a duniyan nan don wanan yarinyar kamar makamine a rayuwan ka nan gaba.
Shiru sukayi gaba dayan su bayan fadin haka da Nasir yayi kowa da irin abinda yake tunane a ransa gama shi umar dake tuna zancen kanin sa Aliyu a ranshi.

Ina zaune akan kujeran dining dake falon ina karatu don test din da muke dashi satin nan kafin aje hutun chrismas da duk kasan sai faman shiri sukeyi ko ina kafi shirye shiryen zuwan lokacin sukeyi a kasan.
Wayata ta dauki ruri lokaci daya hakan yasa na duba da sauri na furta mamu again ?
Da sauri na dana dauka tare da sallama ina gaida ita ta karba min tare da fadin ga su fauziya ku gaisa kamar yadda nayi maki alkawari dazun.
Mun gaisa da kanne na dukkan mu muji dadin hakan karshe sai mamu ta karbi wayan a hannun yaran tace sayadi na amsa da naam.
Tace dazun nice na kashe wayan don jin abinda kike shirin yi a gaban kawun ki.
May nayi mamu na tambaya a maraice tace kina zaton idan kin fadi magana kadan akan zaman ki da mijin ki hakan zai iya kara jefa kawun ki cikin rikicewa.
Jin muryan ki dayayi yau bakiga yadda yake faman saka maku albarka ba duk wanda ya shigo bayan kunyi waya yasan Alh yana cikin farin ciki yau.
Jikina yayi sanyi sosai lokaci daya na kasa furta komai mamu tace sayadi ina karatun ki da abindana koyar dake idan kana cikin damuwa kayi ?
Shin kin mata da irin rayuwan gidan nan da kika barni cikin sa irin makamin da nake fani dashi gare su baki daya shine addu,a.
Sayadi kiyu ta addu,a a rayuwan ki komai yayi tsanani maganin sa Allah ni kaina na sha ji a jikina irin zaman da umar keyi dake a can.
Saidai kona fada ba yarda za,ayi dani ba don hakan magana baida amfani gare mu maganan ma tonawa kanmu asirine kawai zamuyi.
Kiyi hakkuru a tafi a hakan kodon makiya kada su gane halin da ake ciki duk nan an baza kunne da idone aga yadda zaman naku zai kaya.
Don haka karnaji karna gani kowa ban yafe ki fadawa wanan zaman ba shima ya iya boyewa shida yake namiji sayadi sai ke mace ce ba zaki iya ba.
Yanzun haka ina jin wai wai a gidan nan tun zuwan shi kasan nan uwarshi ta hasa mai wuta kan lalai sai ya rabu dake .
A tonanen ta ya riga da ya bata maki rayuwan kurciyar ki don hakan idan ya sakoki bakin ciki da rakaici ne zai cimu har kawun naki.
Don haka nake son ki kara jajircewa sosai ki bishi yadda yake son zaman ku kada ki yarda ki nuna mai gazawa a bangaren ki kan hakan.
Kina jina ko sayadi ban son inji komai gamay da zaman ku sai dai idan kiyi hakkuri gaba zakiji dadin hakan sosai don hakkuri bai taba faduwa kasa banza .
Kina jina ko sayadi na amsa mata da eh mamu tace Allah yai ma rayuwan ki albarka yabaki zuria masu albarka a sanyaye na amsa da amin naji ta kashe wayan baya ki kula da kanki ki tsare mutuncin ki data fada min.
Na dade zaune ina kuka ina tunane na duba dare yayi sosai lokacin ga ruwan sama da ake ta tafkawa kamar da bakin kwarya.
Mikewa nayi zuwa daki bayan na kashe komai na falon da nake amfani dashi ina shiga dakin na aje waya da sauran abubuwan da na shigo dashi na nufi bandaki.
Alwala na dauro na fito na shimfida abin sallah a cikin natsuwa da kulawa na gabatar da sallah na har lokacin tuwa ake sosai a garin .
Na idar na dade a gurin zaune ina tunane ga dare yayi sosai barci ya kauracemin a idona sai faman sake sake zuciya da nakeyi.
Na fadi a fili a hankali ni yaya zanyi da rayuwata anty farida ta fada min nata shawaran yanzu kuma ga mamu da nata shawaran duk dai akan abu daya ake magana wanda ni hakan ma bai damay ni ba sam.
Gara maganan mahaifiyata duk a kan hakkuri ne gareni ba wani zancen bada kai ga miji illar in daure in samawa kaina madogara nan gaba.
Kaina na dafe daga yadda nake zaune nace Allah kaimun gata ka bani mafita kan wanan mutumin idonane ya fara zubar da zazzafan hawaye lokaci guda.
Bazan kara yarda da in takurawa rayuwata ba ko kadan zan watsar da komai in kama harkan gabata.
Kada watarana azo a samu na mutu ni kadai a gida ya zama dole in fara shiga mutane kamar kowa a gari .
Tun ranan naba kaina salama ga komai yadda yaya daukeni hakan zan dauke shi nima mu zuba mu gani dashi.
Ganin za,a shiga bukin addini a kasan na yanke shawara a raina in fita in sawo abinda raina ke so tunda akwai kudi a hannuna da ban san adadin su ba idan ya ban ajewa kawai nake ban komai dasu sai dan hawa taxi da sauran abubuwa.
Mun samu hutun makaranta muna gida don haka na shirya zuwa siyayya abinda raina yake so .
Nasan dan kwanaki ya rage manyan shaguna su zasu cika da jama,a don shagalin bukukuwan chrimas da zasuyi kwana biyu kuma su rufe.
Na shirya cikin riga da siket yan kanti har kasa sai dan hijjab dina dana saka a saman kaina takalma masu dan tsini ne a kafata jakkata na dauko na rataya na fito na rufe gidan.
Iskan garin na shaka mai sayin ke kadawa don ruwan da akayi aka dauke a lokacin takawa nayi zuwa inda zan samu taxi ya kaini gurin shiga jirgin kasa da yake tafiya a saman mono rail.
Shi wanan jirgin a sama yake tafiya anyi mai yar siririyar igiyar bi wanda ke cikin jirgin zai iya hango mutane da motoci a kasa .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button