NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ina kwance saman two seater na dunkule a wuri daya ga goran ruwan sanyi a gefena haka nake da zaran ansha ruwa banda katabus a jikina duk sai jikina ya mutu sai ruwa da zanta sha a cikina idan nayi azumi.

Mamu ta shigo tana fadin kin kuwa je kingaida mutanen gidan nan da shan ruwa sayadi ?
Na dago kaina da kyat ina fadin ban tafi mamu so nake in dan huta tace sayadi may yasa magana daya bai huda kunnen ki ne ke ?
May ye a cikin gaisauwa idan kin je ba sai ki dawo ki kwanta ba har na mike zaune ina bata fuska don ni banga wanda ke shigowa part din mu gaida ita ba yaro da manya na gidan.
Amma ni sai ta matsa min kan sai naje na gaida su wanda zuwan bai amfanani da komai sai bacin rai wata ma son karta karba haka zata kyale ni a tsaye kamar basu ganka ba.
Naji tana fadin watau ke ba ai maki magana kiji a gidan nan yanzu ashe fushi kike da gwagona don kawai.
Ita Amma ta faye surutu shi yasa na kama kaina da ita a gidan nan haka kawai zata sani gaida mutanen da basu ganin ki da daraja ko kadan kowa fa yasan zafin uwarsa mamu.
Hannu ta miko min da dakuwa tana fadin sannu mai uwa ai ban san kin san zafina ba don banga kina bin magana ta ba ke ma.
Na mike ina fadin ke mamu ai duk abinda mutum yayi kanki bakya gani ni dai gani zan je gaida su tace fauziya tabini ida banje gurin Amma ta fada mata idan mun dawo.
Da shiyan hjy maryam muka fara shida ke kusa damu inda na samay ta tana uwar daka sai yaranta neva falo ina shirin fita ta fito tana fadin A ruwa ce an shigo gaidamu ko anzo ganin abinda ke nan .
Nace abinda ke nan hjy ai akwaishi a gurin mu kila ma na aurin mu yafi na nan don yawan ku yafi namu a can.
Ina fadin haka na juya ina jin yar ta na fadin tau rasa kunya yau mommy mu zakiwa rashin kunyar naki ?
Uwar tace kyaleta tayi aiko ta dama akayi ta fada min magana tunda itace bata data ido ni dai na wuce ban kula ta ba.
Shiyan hjy jummai tun bamu shiga ba nake jiyo dararakun su da yaran ta haka yasa nasan suna cikin shiya na shigo da sallama ta ban san wa ya karba a cikin mazan ba.
Daga kofa na tsaya ina fadin hjy ina wuni banji ta amsa ba na sake fadin ina wunin ku ansha ruwa lafiya sun baje a kasa gaba dayan su suna buda baki ?
Lafiya aka sake amsa min daya daga cikin mazan da ba zan tantance muryan ko waye a lokacin ba cikin su na juya abina na fita.
Part din Ammace karshe da muka shiga da sallama muna shiga sai mama hadiye ke fadin kai yar nan kina gidan nan ban saki a ido ba kwana biyu ?
Kya ganta kwana biyu tana fushi dani tun ranan da saudaki ya sauka a garin nan a, a hajiya kems kya mata magana haka a cikin mutane bayan kin san yadda take mutanen nan ?
Yo ko basu so dai ina sai sun ganta a gidan nan kamar yadda dan kowa yake cikin gidan nan in banda lalacewan zamani A ruwa ne wai abin kishi gin yan gidan nan ?
Na kai zaune ina fadin mama ansha ruwa lafiya ya ibada ?
Tace ibada Alhamdullahi faima ki bar fushi da hajiya don kada ta shammace ki kinji.
Naji mama har karana takai gun mamu wai ina fushi da ita ban shigowa wurin ta don hadin fada kin san mamu da tsohuwar nan haka yanzu ta hauni da fada.
Salati Amma ta saka tare da fadin yanzu yar nan ashe sai da tayi maki fadan dana hana ta nace ai na kare da fadin ni dai bani fura insha in an jima.
Kinkoyi rashin sa, a don yanzu samari nan suka shaye furan sai dai idan wanda suka rage gashi ba yawa ki dauka.
Nace kai amma dai Amman nan ni zan sha ragowan wasu katai can da sauri ta tareni tana fadin yanzu ragowan yayyen naki ne ba zaki sha ba yar nan ?
Bafa zan sha ba amma nace ina mikewa ta kara fadin ga na jiya nan baiyi komai ba ni sai in sha wanan din.
Amma in dai shima ragowar su ne ba zan sha ba gaskiya tace wai da gaske kike baki shan bakunan su sai ta kyalkyale da dariya da ban san ma,anan shi nidai na shiga kitchen wurin fridge na dauki furan a cikin gora nayi masu sai da safe na fito.
Mun samu mamu tana cin anbinci take fafin fauziya ta shiga ko tace eh mamu sai na daga mata goran furan dana karbo a wurin ta.
Nan dai ta kara yi min nasiha akan hakkuri tana cin abinci muna dan hira sai fauziya tace mamu ki bar tura anty gaida hjyn su anty ikilima tana zagin antu idan munje .
Ita kuma hjyn su anty Nafisa sai ta kama hararan mu bata karba muna gaisuwan mu kullun.
Kallon inda muke tayi tare da fadin wai abinda take fadi gaskiyane sayafi nace gashi ko fauziya ta fada kullun haka muke dasu wai leken asirin abinda sukaci kike turani yi.
Kai ta gyada tana fadin karki damu da wanan mu dai muyi kokarin sauke hakkin mu na zama a tare dasu da Allah ya shari,an tawa musulmi nace insha Allahu mamu.
Don ban son zancen yayi gaba nace mamu kunyi waya da Addah na yaya manjo take ciki ina son jin muryan ta.
Ta dan tabe baki tace wallahi kwana biyu ban samun wayan ta ko da nackirata lambar baya shiga.
Mikewa nayi tsab ba tare da magana ba na shiga daki wurin tsofin litatafaina na nuna na kama bincika sai ga abinda nake nema na gani can kasan kayana.
Da sauri na fito zuwa falo inda nabar mamu a zaune ina zuwa na dauki wayanta na shiga loda nomban mahaifiyar Atika a ciki ya fara ringing can aka dauka.
Da sallama nima na amsa masu mamu ido kawai ta tsura min lokacin bayan mun gama gaisawa ne nace Umma Fatima ce.
Wata fatima sai na rasa abinda zance mata don kunya tunda nazo ban taba kiran su sai yau din dana kira layin don ina bukatan jin muryan kakata.
Wace fatima nace da sauri nace ta kano yar wurin manjo makwaciyar ku da sauri tace fatima kai amma yar nan yar kin tabbata yar halasa da yamman nan mukai maganin ki fa.
Fatima shiru haka tun tafiyan ki ba kira ni ina dauka baki da layin mu ne yasa baki kiramu ba gashi kuma ranan nayi rashin azanci in karbi layin mahaifiyar ki.
Umma kuyi hakkuri ba waya a gurina ne yanzu ma ina tone tone naga lambanki da na taba rubutawa ranan shine na kira ko zai shiga.
Aiko muna lafiya sai naji kunyar tambayanta wurin manjo sai ita din tace min kakarki ko ba lafiya sosai don har Addah ki ta shigo dubata.
Da karfi nace umma manjo ba lafiya may ya samay ta tace daga kafan nan nata daine sai ga abin kuma yana ci gaba .
Ban iya sauraren abinda take fadi ba na fara hawaye sai naji mamu ta karbe wayan a hannuna tana fadin hajiya ashe yar nan nada layin ku ?
Nan suka shiga gaisawa a tsakanin su inda mamu ke fadin ashe jikin babba kuma ya motsa banjin abinda take fadi a lokacin sai mannewan da nayi a jikin mamu don inji may suke fadi a lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:50 – ????????????: :BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHHIM AU,ZU BIKKALAMAT, TAMMA,AT MIN SHHARIN MA, HALAQ, , , , , ,

Tun wanan maganan hankalina ya tashi sosai da jin zancen da nayi na ciwon kakata manjo ranan ko abinci ban iya ci ba dan dama ruwan da nake sha.
Da asuba ban fito yin sahur ba kuma ba barci nakeyi ba raina ke min sake sake a kan ciwon manjo ganin ban fito ba yasa mamu shigowa dakin.
A kwance ta samay ni na lafe sai dai tasan ba barci nakeyi ba lokacin mamu tace haba sayadi sai kace ba musulma ba in banda abinki ai ciwo ba mutuwa bane.
Kuma kowa dole ya tausayawa hin da babba take ciki a garin nan ida ma mutuwa tayi wani ba zai iya tarewa wani mutuwa ba ai.
Don Allah ki tashi kina tayar min da hankali nima da wanan halin da kikeyi kukan ki kara sakani cikin wani hali yake banda natsuwa da zan nemawa babba mafita.
Abinda zuwa islamiya naki ya koya maki ke nan idan bawa ya shiga wani hali maimakon addu,a aita mashi kuka.
Ki tashi kije ga abinci can a falo kici kada lokaci ya kure ki fara wanke bakin ki kafin ki fito kai kawai na iya gyada mata na tashi jiki ba kwari zuwa bayi don ita har ta fita dakin ko ta koma falo.
Dana fito kasa cin abincin nayi na tasa shi a gaba ina kallo sai daga can mamu ta farga da bancin abincin tace bazaki ci abinci ba sai lokaci ya shige ko.
Cikin muryan kuka nace mamu Allah ban iya cin komai a yanzu na koshi wani irin kallo ta watso min wanda nasan kallon warning ne gareni .
Da sauri na mika hannu na dauki spoon din na fara dan cakulan abincin a hankali cibi daya da kyat na kaisa a bakina ina ji kamar guba ta bani don halin da nake ciki a lokacin.
Dubana mamu tayi tace ashe ba zaki wa kakarki addua ba idan da mutuwa tayi ko kin rasa wani daga cikin mu sai kuka.
Da kyat na iya bude baki da muryan kuka don a lokacin ji nake dai Manjo ta mutu ko don yadda naji maman Atika nawa mamu dogon bayanin da banji ba.
Mamu ban iya ci na koshi sai ta miko min kofin tea mai zafi danaga ta hads tun zamana ta aje gefen ta na karba babu mussu na kafa kai na zuka kadan na aje kofin.
Don banga amfanin cin wani abuba a lokacin masoyiya ta tana can cikin wani halin ciwo da ban san iyakar shi ba.
Maimakon inyi magana sai na fada jikin mamu ina kuka gwaunin ban tausayi ina fadin mamu banda kowa daga Allah sai ku bayan ke da manjo na .
Kai ki daina fadar haka sayadi ina kika baro Alh da Amma da suke nuna maki kauna na sahihi in Allah ya yarda ba abinda zai samu babba ina jiran gari ya waye ne in samu su gwago da maganan inji yadda za a yi.
Wanan kuka haka kina sare min gwiwa da shine sanan Alh ba zaiji dadin wanan kalamin naki ba bayan kokarin shi da yakeyi a kanki yana gwadawa duniya ke yarshi ce ta cikin shi.
Nayi alkwari muddin ina raye sayi ba zan taba barin kiyi maraicin mahaifi ba zan baki duk wani kulawan daya dace duk wata uwa ta gari ta baiwa yarta.
Ina rokan Allah ya haskaki a idon zurin an ku baki daya amma fa sak idan kin taimaka min haka zai samu gareki.
Duk da nasan kina da tarbiya sai dai ki kara kula yanzu da da ba daya bane a gare ki saboda haka ki kawar da idon ki aurin kula samari don nasan ko baki kulasu ba su zasu kula ki
Ki fita batun duk wani da namiji ki mayar da hankalin ki wurin karatun ki sosai don da kin gama ki samu gurbin shiga jami, a.
Don Allah ki kiyaye ki kare mutuncin ki ga kowa da idon shi ke a kan mu aga yadda zamu kwashe nan gaba da rayuwan mu a gaban ki yaya take fadin haukanta a kan yaran ta .
Ta manta Allah ke yi ba mutum mu tasan abinda gobe zai haifa ga namu yayan ba don haka fatima kiwa Allah ki natsu akan tarbiyan dana doraku akai.
Dagowa nayi da sauri na kalleta da mamaki don jin kiran sunana da tayi a karo na farko ke nan da naji ta ambaci sunana na yanka a bakinta .
Insha Allahu wataran sai labari da yardan Allah sai kin zama abin kwatance a idon jamma,a koda kuwa bana raye .
Allah yai maku albarka ya kare min ku daga duk wani abin ki, ya azurta min ku da ilimi mai amfani ya baku mazajen aure masu albarka da sanin ya kamata.
Da kyat ta kai maganan don muryan ta da ya juye zuwa na kuka Allah kadai yasan abinda mamu ke ji a zuciyar ta akan mu.
Gashi ba wasu dangin mahaifiya ke gare ta ba tun da mahaifiyar ta suka rabo da mahaifinta ta koma kasan su basu kara jin labarin ta ba har yau.
Nasiha mai ratsa jiki mamu tayi min wanda ya kara min karfin gwiwa da sanin matsayina yanzu a duniya wanda ya zama dole inyi taushi ko don kwanciyar hankalin mahaifiyata mai son ganin farin cikina itama a duniya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button