NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Yana aiki a shago kira ya shigo mai bai dakatar da abinda yakeyi ba don kada lissafin ya kubce mashi sai da wayan ya tsinke inda ba lokaci wani sabon kira ya kara shigowa again.

Don haka ne ya dakatar da aikin ya rarumi wayan nasa a ciki fushi sai dai ganin wanda ke kiran shi ne yasa ya katse fushin yana mata sallama.
Tare da fadin Allah ya barmin min antyna ta kaina ya gida ya waje su inna kuma ?
Tace Amadu lafiya ba lau ba da sauri ya tare ta yana fadin anty may ke faruwa a gidan ?
Tace wallahi jikin baba ne yaki dadi yau kwana uku ke nan yau ma dai jikin nasa yafi tsanani gaskiya.
Cikin kidima ya furta subbahanallahi anty shine ba wanda ya kirani ya fada mi ko jiya fa munyi waya da Abu bai fada min komai ba.
Tace baban ke fadin kada a fada ma a tayar ma da hankalinka zai samu lafiya da ikon Allah sai dai kuma har yanzun jikin ba dama gaskiya.
Yace yanzun dare yayi anty amma gobe da yardan Allah da safe zan shigo garin sai a zauna da shiri idan nazo zamu wuto asibiti dashine don wanan karon ba zan yarda da zancen a barshi a gida ba.
Asibiti zamu zo dashi gobe a duba shi tace Allah ya kaimu Amado gaskiya yanzun kan dare yayi sosai sukai sallama ya kashe wayan lissafin da bai tsaya ya karasa ba ke nan ya nufi gidan uban gidan shi wanda yanzu ya zamay mai kamar mahaifi a gare shi.
Bai samu kowa a farfajiyan gidan ba don haka ya nufi hanyar shiga gidan kai tsaye Ahmed da yanzu ya goge ya zama dan birni sosai ga ilimin bokon daya samu har master sai da yayi ga na arabiya.
Don hakane yake aiki da ilimin shi duka biyu wurin gogayya da al,amuramshi na kasuwanci har kasan waje yake fita ya odo masu kaya irin wanda suke bukata a kasuwancin su.
Daga kofa ya tsaya yana kwala sallama bai yarda ya shiga ba kai tsaye duk da yasan baida shamaki yanzun a gidan.
Sallama biyu gana uku yaji zazzakan muryan salma na amsa mashi sallaman nasa ko ita yayi dace ne ta fito sashen Amma a lokacin wanda ba kasafai take zuwa ba sai idan taga dama takan dan je suyu barkwanci da tsohuwar.
Salma na farin cikin da zuwan Ahmed gidan su kodai da take kokarin boye hakan a zuciyar ta bata son wani ya fahinci hakan musaman ma hajiyar su data dauki karan tsana ta sakawa yaron.
Ahmed yayi aure farko a nan kano inda ya hadu da wata yarinya Alh sani ya tsaya mai har akai auren shida su Amma, gurin haihuwar farko matar tasa Allah yai mata rasuwa ta bar yaron da ta haifa har wanan lokacin bai kara wani aure ba.
Ita salma da farko bata dauka son Ahmed takeyi ba sai daga baya ta fahinci ta fada son Almajirin gidan nasu kamar yadda hjyn su take kiran shi idan ya bata mata rai.
Ya fahince ta sarai sai dai bai yarda ya bata fuska ba ko kadan sanin halin mahaifiyar ta da yayi ba mutunci ne da ita ba ko kadan .
Don hakane yake kara kaucewa duk wani abinda zai hada shi a gida Alh sani da ita balle kuma salma ba irin choce din shi bace don yana son mace mai addini da tarbiya ba wace zata iya yiwa babba rashin mutumci ba kamar uwar ta.
A cikin dakewa yace ke Alh yana kusa ba tare da ya bari magana komai ya shiga tsakani su a gurin tace yana falon shi a sanyaye.
Ya wuce baiko kara waigo ta ba yabarta a tsaye tana kare mai kallo murya mahaifiyar tane take fadi salma yaya haka kuma ?
Salma tayi saurin fadin ni da dan rainin wayau nan ne daga zuwa yana tambaya wai Alh na ciki ne kamar ya aje ni a nan.
Wanan yaron ai gani yake wuyan shi yayi kauri yanzun shiyasa yake ganin kamar daidai yake da kowa a gidan nan.
Salman tayi kwafa ta wuce ba tare da ta tsaya jin sauran maganan uwar nata ba don zata iya jin abin haushi a wurin wanda zuciyar ta ba zai so ba.
Ahmed ya tsaya daga falo yana ma Alh salma sai yaron wurin hjy maryam ya leko don ganin maima Abban su salma a lokacin.
Yana ganin Ahmed yaron ya washe baki yana fadin kazo min da keke na Ahmed yace bako gaisuwa boy don haka suke kiran yaron dashi.
Yaron yace ina wuni yana dariya sai daga ciki Alh yai magana yana fadin ba zaka bashi wuri ya shigo ba ka tsare shi da magana.
Yaron yana kokarin juyawa Ahmed din ya kama mai hannu suka shiga falon tare inda baya salman da ya kara yi ne ya shigo falon.
Gaida dattijon yayi da wuni wanda ke mashi kallon mamaki don ganin shi gidan a wanan lokacin do basu dade da rabuwa ba.
Wuri ya samu a kasan kafet din ya zauna kamar yadda ya saba yi idan ya shigo falo ya fara gaida Alh dake mai kallo mamaki har wana lokacin a fuska shi
Baya gama gaisuwan su ne Alh ke tambayan shi ko lafiya yace Alh da sauki yana gyara zaman shi a daidai lokacin da Alh ke tambayan shi may ke faruwa hjy jummai ta shigo falon tana cika tana batsewa.
Ahmed yace yanzu nayi waya gida suke fada min mahaifina baida lafiya sosai shine nake son gobe idan Allah ya kaimu in yi asubancin zuwa gidan in dubushi.
Sai Alh sani yace ka duba shi kodai azo asibiti dashi ai asibiti yakamata kaje ka dauko shi kuzo zai fi.
Yace haka nake so idan Allah ya kai mu din idan naje yace subbanallahi ubangiji ya bashi lafiya Allah yasa kafarane hakan Ahmed yace amin.
Hajiya jummai dake zaune kanzil bata ce dasu har addu,an da Alh sani yayi bata karba ba sai wani kada kafa da takeyi a saman kujera inda take zaune.
Alh sani ya juya wurin ta yana fadin Ahmed ne yazo yanzu ashe mahaifi shi ba lafiya kuma yanzu fa muka rabu ance baya baida kadan?
Tace Umm,wummm Allah ya sauwaka taci gaba da kada kafan ta da takeyi su kuma suka fita batun ta suna magana akan ciwon tsoho.

Addah ta koma ta barmu da kewan ta bayan tayi muna sati biyu tana duban mahaifiyar ta kamar yadda take muna tun lokacin da mukazo misau din.

Tun tafiyan ta sai gidan ya koma muna babu dadi zaman dai ga munan ne a cikin sa haka yasa na dan fara shiga gidan su Atika don in debe damuwa a raina na rashin Addah.
Tun ina kunyan su na kaurace masun da nayi na kwana biyu don zuwan Adda din har yakai na sake jikina mun koma kamar yadda muke a baya don banga wani alaman sauyin fuska ba a gare su kaf gidan.
Sai dai yanzu ina zuwa makarata ban yarda in daga kafa da zuwa school din tunda Addah tayi min nasiha akan hakan.
Irin nasihohin da taimin ne ya ratsa min jikina na daina fashin zuwa karatu har da islamiyan da Atika ke zuwa yanzu a tare muke zuwa kullun.
Haka yasa wani irin natsuwa ya fara shigana a hankali wanda ban san inayi ba sai dai nakanji mutane na fadin zuwan Addah ya canza ni kwanan nan.
Nidai sai murmushi nake masu a dole ina son fita daban da yaran gidan baffa da Addah tace tana son inyi ga kuma manjo kamar zuwan Adda tazo mata da maganine don ta samu lafiya yanzu sosai ba kaman can baya da take a rabke ba.
Don Addah taja min kunne sosai kan in kula da Manjo don kada in rasata don in manjo ta halaka ni zanfi kowa shiga damuwa.
Banso abinda zai taba manjo har yakai ga halakata don haka na daure ko bayan wucewan Addah ina kula da kakata yadda ya kamata kamar yadda na Adda tana mafa data zo.
Sai ga tsohuwa tana samun sauki sosai ashe dama damuwa da kuma yunwa ne yake batun halaka yar tsohuwar a gidan.
Ko baffa Adda bata kyaleshi ba akan kula da mahaifiyar tasu haka yasa yanzu duk dare sai ya dan sawo mata dan abin kwadai ya miko muna da yake dakin mu ba a cikin part din matan shi yake ba mu muna daga waje farkon shigowa gidan.
Wani lokaci dan kunshin nama ko burodi da kayan shayi ba tare da iyalin shi sun san yana hakan ba don idan sun sani ba zasu bari ba.
Ranan da baida zarahi kuma yakanzo yai tabata hakkuri kamar wanda zaiyi kuka a ranan hakan ba karamin fahintar dani darajan iyayye a guri da yayi ba.
Kamar yadda na canza hakane yake sa ko na dan shifa gidan su Atika ban dadewa koda yaushe kazo gida zaka samay ni a dakin mu ko ina wani aiki wa kakata.
Sai dai haka bai hanani aikin wahala ba a gidan Baffa din inda hakan ke bata ran manjo tayi fadan haka din har ta gaji basu daina ba.
Don haka na taso aikin wahala baya damuna ko kadan sai dai abinda ban sani ba a gamay dani ashe kafin tafiyan Addah sun zauna sunyi magana a kaina.
Inda Adda ta zaunar da manjo cikin hikima da dabara ta fahintar da ita illan barina in tashi a gidan baffa da suka hango min itada mahaifiya ta.
Wanda hakan yasa jikin manjo yayi sanyi don jin ance zan iya lalacewa ko samarin gidan Baffa su lalatani yasa tsohuwan saurin yarda da shawaran su din wanda bata fatan haka a gare ni .
Ni da take gani yanzu farin cikin rayuwanta kamar don ni ni kadai Allah ya bar muna ita tace ba wani gardama duk sanda mahaifiyata ta shirya tazo ta dauke ni.
Ta Amincr da zamana a gurin ta muddin rayuwana zai inganta a can kano din da wanan maganan suka tsaya har ta tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button