NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

A dakin da nake kwance kawu ya shigo  bayan sun fito sallah magariba ya samu su mamu a zaune inda suka idar da sallah yake fadin dare ya soma zaku fito ne mu koma gida.

Yaron fa a nan zamu barshi kodashi zamu koma gidan hjy ta tambaya tana kallon mamu don son jin amsan da zata bayar.
Kafin mamu tai magana kawu yace a barshi nan mana tunda an samu tana dan cikin hayacin ta yanzu.
Nima shina gani don ko munje dashi ba zai ci komai ba kamar yadda yayi dazun .
Kawu ya dan matso kusa dani yana fadin fatima mu zamu tafi yanzu dare yayi mun bar yara a gida .
Ina son ki kwantar da hankalin ki insha Allahu mijin ki zai samu lafiya da yardan Allah kuma yan sanda suna nan suna binciken wanda keda alhakin aikata haka .
Da kyat na bude baki ina fadin kawu don Allah kayi magana a cire min ruwan nan inje inga yaya umar din dakon da yake.
Zakije fatima kiyi hakkuri kema yanzu ba dadi kike ji ba har ruwan ya kare sai a rakaki ki ganshi ki mashi addua don yanzu adduan mu yake bukata fiye da komai.
Ina jin hakan na runtse idanuwana ina jin zuciyana kamar zai fashe a lokacin nasan yaya umar yana cikin wani yanayi mai muni ke nan a yadda kawu ke nufi.
Ban kara bude ido ba har barci ya daukeni a hakan yadda nake ina tunanen halin da mijina yake ciki.
Jin an dauki yaron dake manne a jikina yasa na falka firgigit ina bude idanu a tsorace sai nake ganin kamar mutanen ne suka kara dawo min a lokacin.
Ganin mama hadiye tsaye a kaina yasa na maida idanuwana rufe muryan yaya Ahmed naji yana fadin sannu fatima ya jikin naki.
Sake bude idanuwa nayi a hankali ina fadin da sauki salma ne ta matso bakin gadon tana fadin ya jikin fatima kai na gyada mata kawai ina datse bakina don yadda nake ji a lokacin .
Ina jin Ahmed na fadin har yanzu dai ba,a samu bayanin wa yanda sukai wanan abin ba ko ?
An sani ba kowa bane merry ce na bashi amsa don tun lokacin data zo garin nan zuciyana ya bani hakan kuma shi kanshi yaya na fada mai abinda nakeji game da ita akan yarana.
Kowa dake dakin ya dauki salati sai mama ke fadin ki bar fadin haka fatima tunda zato kikeyi don Allah .
Ba ita kadai yanzu ake zargi ba ai har hjy sabuwa da yarta suma ana zargin suna da hannu a cikin wanan abin ai.
Tunda ta fadi sai yaga abinda zatayi mai tunda yai masu haka a gaban kowa kinga ko dole a zarge ta itama.
Allah dai ya tona asirin duk wanda yai wanan abin Ahmed yace aka amsa da amin gaba daya.
Juyowa nayi a hankali na kalli salma ina fadin salma kinga yaya din wani hali yake ciki nace su bari in tafi in ganshi anki bari in tashi.
Fatima kiyi hakkuri kema kina cikin taki laluran ga ciki a jikin ki dake maki wasa sanadin wanan abin ga kuma halin da kike ciki.
Ba zaki fada min halin da yayan ki ke ciki ba kema salma ku fada min mana don Allah idan ya mutu ne in sani.
Wallahi bai mutu ba fatima yana dai cikin wani haline mara dadi don har yanzu baisan a inda yake ba.
Kuma likitoci basu bari a shiga inda yake sai yaya habbib da daddy da akace ya shiga dazun ya ganshi.
Zubur na mike zaune ina kokarun cire karin ruwan da ake min wanda yakici yaki cinyewa har yanzu don rage karfin ruwan da sukayi bai sauka sosai da sauri.
Sai subbahanallahi may kikeyi haka Fatima ina, zaki don Allah, don Allah ki natsu ke kanki baki da lafiya fa.
Shine abinda wa yanda ke cikin dakin suke fada min cikin tashin hankali suna kokarin kamani su kwantar dani.
Ku barni in inje in ganshi ko akwai abinda zan iya mashi a yanzu don Allah na fada ina karasawa da kuka .
Tausayi na basu naji mama na fadin ni banga dalilin da zaisa a hanata ganin shi ba dama don ganin shi shine kwanciyar hankalin ta a yanzu.
Jin abinda mama tace na juya gare ta ina fadin don Allah mama ku barni in ganshi don Allah saka hijab mu tafi inda yake saidai likitocin basa yarda kowa ya shiga dakin da yake ciki gaskiya.
Muma da muka tafi ta taga muka tsaya mukai mai adduan Allah ya bashi lafiya tana gaba ina binta a baya muka karasa har emergycy dakin babu kowa sai shi dake kwance ga na,ura saukan numfashi makale a hancin shi sai ruwa da ake kara mai.
Innalillahi na fara ambata sai dai duk da halin rudun da nake a ciki bai hana inyi nazarin yadda abin yake ba.
Juyawa nayi ina fadin mama ko zan iya ganin likitan dake kula dashi don Allah ?
Eh to habbib ne tare da wani likita abokin shi suke tsaye a kanshi dama ya Ahmed ya fada yana karasowa kusa.
Amma idan kina son ganin shi ai za a iya masu magana a yanzu sai a hadaki dasu ko , ?
Da sauri nace don Allah yaya idan ba damuwa zanso in gansu akwai maganar da nake son yi da likitan a yanzu.
Ya juya tare da fita wurin komawa nayi ina kara nazarin halin da yaya yake a ciki lokacin.
Saiga yaya ya dawo yana fadin likitan yace naje tare dashi da salma muka shiga office din nan ya nuna muna wurin zama yana fadin lafiya dai hjy kike son ganina hope ba wani matsala bane kuma yanzu.
Dago kai nayi ina fadin doctor idan babu damuwa zanso muyi magana insan abinda kukai ma mara lafiya amfani dashi da irin ci gaban da kuke ganin ana samu gareshi yanzu.
Wani kallo likitan yayi min yana kokarin cire glass din dake saye a idon shi.
Amma malama ke din wacece da zaki zo min da wanan maganan ya fada cikin daure fuskan shi aka kwankwasa kofa za a shigo office din.
Hakan ya hanani furta mai komai har wanda ya shigo din danaji yana mai sannu da zuwa amsawan maishi yasa na juyo daga inda nake zaune don ji muryan wanda na sani.
Shima anyi sa,a ya juyo yana kallon mu a cikin mamaki lokaci guda muke ambatan sunan juna.
The guy yace Fatima kece ko gizau idanuwa na ke min don na bincika an fada min kin koma second degree din ki a can London kuma.
Kai na gyada mai ina fadin hakane yanzu ma mun zo kasan nan don duba sarakuwata da bata da lafiya shine wani tsautsayi ya samemu a nan din.
Likitan ne ya karba da fadin kan isue din dana kiraka ke nan yanzu don abin ya shige min a duhu ni kaina.
Innalillahi ya furta tare da fadin how comes hakan ya faru is a long story sai dai da alama kasan ta a yadda naga kun nunawa juna.
Kallo na The guy yayi yana fadin wanan da kake gani aida nasan tana nan da ban baro Abuja nazo nan ba don duk abinda zan iya itama iam sure zata iya fiye dashi ma a yanzu.
Mu daina wanan magana muyi zancen mara lafiyan nan please don i am sure muna gab da rashi a yanzu saboda awowin daya dauka a hakan.
Nan na fara gin ma likitan tambayoyi yana min bayani sai na tuno da wani hikima da aka koya muna indan an harbi mutum.
Nan nayi masu bayani take likitan ya mike yana fadin shaf na manta da wanan idea din da kika kawo kiran doctor habbib yayi yana masa bayani sai yace gashi tafe.
A tare dani muka shiga da yaya dakin theater din aka yi mai duk wani abinda ya dace a lokacin kusan duk wani dan uwa na jiki yana tsaye a gurin an zubawa sarautan Allah ido kawai.
Ni kaina hankalina ba a kwance yake ba alwala nayi na tayar da sallah nakai kukana ga ubanginjin talikai mai jin roko da biyan bukatun bayin shi.
Ina sallamewa na zauna addua a gurin can kuma tunane ya dauke min hankali na yanzu idan yaya ya tafi ya barmu ni yaya rayuna dana yarana zasu kasance daga baya.
Ban kaiga karasa tunanen ba naji ana kiran sallah asuba don haka na mike don yin nafila.
Saida aka tada kabbara a masalacin dake cikin asibitin na mike don gabatar da sallah na idar kenan ina lazimi naga likitoci da sauri sun shiga dakin da yaya din yake kwance.
Da sauri na mike tsaye zuwa dakin saidai na samu sun rufe kofan hakan yasa na tsaya sanin shiga lokacin aikin su dokane.
Tunda ba aiki nake a gurin ba ina tsaye ina shawara naga wani nurse zai shiga dakin da sauri yana rike da kayan aiki a hannun shi.
Ban tsaya ba na jefa kaina a dakin nima a rikice suke su duka suna gani na dayan yace don me na shigo masu daki lokacin aikin su.
Ban damu da tambayan da yake min ba hankalina yana gun yaya da sauri na karasa ina fadin ya miko min spoon ko seazors kada yai mai alluran nan yanzu.
Nawan shi nagani wurin miko min abinda na bukata din da sauri na dauko na bude bakin yaya na saka mai tare da toshe hancin shi sai naji ya ja wani irin ajiyan zuciya lokaci guda a hankali numfashin shi ya fara dawowa .
Dakin yayi tsit kowa na kallin ikon Allah duk idanuwan likitocin yana kanshi har ni a lokacin sai na,uran da aka makala mai ke aiki cikin dakin nima duban na,uran nakeyi a hankali ya koma daidai na zare almakashin dake bakin shi.
Addua na fara jero mai na samun sauki a wurin Allah don yana cikin wani yanayi wanda ba,a son mutum ya kai a lokacin.
Juyawa nayi ina fadin ko za,a samo wani allura na fada don shine daidai aimai a lokacin ba wanda suke niyar mai ba a yadda yaken.
Alluran nan yana da wuyan samu gaskiya a yanzu wani ya fada min yake fadin basu faye sayoshi ba a kasan nan don ba kowane zai iya sayen shi ba.
Dayan likitan ne ke fadin yana ganin yana dashi a gurin shi daya sayo zaiwa wani mutum a lokacin kuma sai mutumin ya rasu.
Likitan mai duba yaya yace yayi sauri ya dauko muna nan ya juya ya fita dakin yayi tsit muna ksllin yadda numfashin shi ke tafiya a hankali har wanan likitan ya dawo da maganun a cikin wani kula don ba, a barin shi inda babu sanyi.
Karba doctor yayi suka fara shawaran mill nawa zasu mai ina jin hakan nace give him five is ok for him now.
Kallona sukayi dukkan su basuyi magana ba don the guy ya riga ya fada masu su yarda dani da duk shawaran da zan basu nasan aikina sosai.
Anyi alluran da kamar minti goma sha sai numshin ya koma normal sosai har zaka iya jin dan hantsari daga gare shi.
Sai lokacin na sauke a jiyan zuciya na juya ina fadin thanks tare da nufar hanyan fita daga dakin don kafafuwana ba zasu iya daukana ba a lokacin.
Na fito daga dakin idanuwan kowa a kaina don na samu har hjyn su tazo an kamota tana wurin da duk yan uwanta da na kawu sai wasu fuskoki da ban sani ba.
Rasa wanda zan amsawa tambayan da suke min nayi don kowa na son jin halin da yake ciki saboda hankalin su gaba daya ya tashi a lokacin.
Da sauki na fada na nufi empty kuran dana hango na zauna don ba zan iya tsayuwa ba a lokacin gashi nima ba lafiya ne a jikina ba.
Abbana mama hadiye ta kawo min don in bashi nono karban yaron nayi duk ya langabe nasan yayi kukane har ya gaji don bai sansu ba.
Habbib suka shigo tare da Aliyu don tunda sukai sallah suka tafi gida daga can sai gashi an kirasu kan anga likitoci na shiga dakin da sauri har nima ina cikin dakin ba wanda ya san meke faruwu a ciki.
Bayan sun gaisa da mutane suke tambayan halin da dan uwan nasu ke ciki ake fada masu nice dai na shiga don su suna waje tsaye lokacin da abin ya faru.
Yaya habbinb ya tako zuwa inda nake zaune mun gaisa yayi min yaya jikin na amsa mai da sauki ya gyara tsayuwa tare da tambayan hakin da ake ciki ina mai bayani.
A lokacin sauran yan uwa suka matso don jin halin da ake ciki na fara mai bayani sai ga likitan dake dubashi ya fito daga dakin nan kuma suka koma gareshi akai mai caaaa da tambaya.
Wanan ba wani abin mamaki bane a kasan mu yadda masu jinya kan tasa likita gaba da tambayan halin da mara lafiyansu ke ciki.
Nunani yayi yana fadin yanzu itace likitan nasa ai don ta karantu a wanan fannin sosai fiye da tsamanin ku.
Zuwan ta nan ya tai maka muna sosai don a halin yanzu numfashi ya koma daidai yadda muke so.
Nan dai likitan ya kara kwantar masu da hankali sosai sai a lokacin hankalin kowa ya kwanta don ana ganin sauki a gareshi.
17/11/2021, 07:26 – ????????????: Ganin sauki sosai ga yaya hankalina ya dan fara kwantawa sai dai a kasan zuciyana tunanen wanda yai mashi wanan aika aika yake min yawo a rai.
Don zuciyana ta kasa tsayawa wuri daya a tsakanin abu uku da nake zargi nafarko dai itace merry da nake zargin tazo daukan fansan yarta a kanshi .
Sai na biyu itace samira da mahaifiyar ta da ake zargi suna iya aikata hakan don abinda ya faru a tsakanin su yan kwanakin da suka shude.
Wanda yan uwa da abokan arziki sunfi zargin hakan garesu don tun da yaya habib yaji abindana fada bai yarda ba shi sai cewa da yayi merry tsorone da fargaba kila yasata ta bar kasan a gigice.
Shi yanzu bukatan shi shine asan inda merry da ake nema ta shiga tun daren jiya din ba,a ganta ba kada dai kuma wani abu yazo ya faru da ita nan gaba a kuka dasu daga baya kan hakam.
Ni kawai jin su nakeyi don sanin wacece merry a yanzu da nayi don sanin halinta akan komai da yadda wayewan ta yakai a America din.
Dole na gyagije ga nawa ciwon muna fuskantan nasa don ni nawa tsorone da fargaba ya saukan min da ciwo na dan lokaci guda dama.
Saidai duk da na gyagijen bai hana kaga damuwa da tashin hankali a tare dani idan ka kalleni sau daya saina baka tausayi a yadda na koma.
Hjyn su yaya ita kanta ta fita daga hayacin ta sosai don nan gurin shi itama ta wuni a ranan duk da ga yan uwanta sun mata kara don sun cika asibitin sosai.
Amma hakan bai hana hjyn zama asibitin ba itama da ka ganta bata cikin hayacin ta ko kadan a lokacin kowa hankalin shi yana a tashi da faruwan al,amarin.
Yan sanda sai aikin su na bincike kan case din sukeyi basu gane komai ba sai washe garine da dayan mai aikin wanda bai mutu ba ya farfado suka samu dan haske gareshi kan al,amarin.
Don yan sanda najin ya farfado suka garzayo dakin da yake suna mashi tambayoyi yadda abin ya faru a gidan.
Yake fada masu da misalin karfe biyun da wani abu na dare suna kwance sukaji harbi bindiga.
A inda ya gane ba hausawa bane don turancin yaji suna yi akan harbin da daya su yayi ogan su na mashi fada kan hakan yana fadin madam tace damu bata son a harbi kowa a gidan nan kai gashi yanzu ka harbi maigadi kilama ya mutu.
Yaran kawai tace mu kwashe koda ba duka bane ko daya muka samu mu dauko mata kazo zaka batawa mutane shirin su kuma.
Yace oga yana da bindiga fa a hannun shi shi yasa na harbe shi kada ya harbe mu mutumin yace ina jin haka sai na shiga cikin tarkacen dake dakin na kara lafewa sosai.
Sun kai su nawa a naka ganin da suka shigo gidan dansanda ya tambaye shi .
Yace zasu kai su takwas ko fiya da hakan do su kasu kashi kashi a gidan don har wajen gida wasu sun tsaya daga cikin su.
Nima dai rabon wahala yasa na fito wajen da niyar in gudu a lokacin danaga hankalinsu ya dauke a cikin gidan injin karan harbe harbe na fito da niyar gudu.
Sai dai ban san akwai biyu ko uku a waje ba lokacin ne suka harbeni sai dansanda ya dakatar dashi da fadin.
Kafin ka suma bakaji wani karin kalamin da zamu rike a matsayin huja ba a bakin su sai mutumin ya girgiza kai alaman baiji komai ba.
Dansanda yayi mai godiya bayan yan rubuce rubucen da yayi a takarda a lokacin ne saurayin ke fadin yallabai na tuna da wani kalma danaji sun fada kwarai a lokacin.
Da suke fadin we should rush mu bar garin nan yau komai dare kada a kama mu sai dayan yake fadin Samuel fa da aka harba yace dashi zamu tafi.
Don barshin a nan risk ne gare mu don za,a iya gane hakan ta hanyar shi don haka zamu tafi dashi ke nan.
Dan nazari dansanda ya tsaya yayi kafin ya mike yanawa saurayin godiya tare da fatan samun sauki ya fito ya leka a dakin da yaya yake kwance.
Bayan tafiyan dansandane kowa ke fadin albarkacin bakin shi kan abinda saurayin dake muna wanki ya fada wanda daga kauye ya shigo gari neman kudi dama nasir ya dauke shi aiki a gidan.
Ban furta komai ba don magana yana dan fara dauko kamahin gaskiya sai nake jin ko a can gidan mu da yaran suke zaune kamar basu tsira ba a hannun makiyan.
Don zasu iya cin masu can su dauke su tunda sunyi niyar yin hakan a kan yaran nawa haka ya jawo hankalina kasuwa gida biyu a gurin tunane yanzu.
Zuwan mamu da kawu ne ya dan kwantar min da hankalun don sun samu labarin abinda mai wankin mu ya fada tun suna gida.
Kawu ne yakw fadin in kwantar da hankalina tunda har Allah yasa mi sanin gane wani abu mara kyau yana shirin faruwa da yaran naji a jikina kuma har hakan ya faru .
Sai in godewa Allah in dage dayin addua don addua itace takobin mumuni Allah ya kara tsarewa insha Allahu Allah zaibawa yaya lafiya ya tashi da yardan ubanginji.
Wanan kamar kina nunawa ubangiji rashin godiyane yau da ace wanan abin ya zama sanadin rasa umar fa ?
Ashe ba zaki zamo mai tawakkali ga jarabawan ubangijin ki ba fatima ?
Jin kalamin kawu yasa na dago kai ina kallin shi tare da kokarin share hawayen dake zubo min a lokacin.
Bayan kawu ya mike don shiga yaga dan nasa ya rage wurin dani da mamu sai Amma dake lazumi tana sauraren mu .
A hankali nace mamu yaran basu damun ki ko a can don nasan su da fitina idan basu ganin dayan mu tare dasu.
Saida mamu ta sauke ajiyan zuciya take fadin basu fitinan komai tunda ga sadiya nan da maria suna gani yau daine ita yar fitinan ta matsa da kiran mummy mummy ina jin maria tana lalashin ta itama kanta maria ai abin ya bugeta sosai don bata a cikin dadin rai duk yinin yau din.
Sai lokacin Amma data shafa addua take fadin yo ina zataji dadi wanda kake tare dashi yana a cikin wani hali haka mara kyau.
Mamu n fada maku ni zuciyana tafi karkata gun merry din nan don yarta da yaya ya karbe a hannun ta yanzu.
Kada kice haka sayadi don zato zunubine koda ya zama gaskiya don haka ki daina wanan zargin.
Sai ya kasance ita bata ma san da wanan zancen ba sai wani ya taka sawunta yai wanan aikin .
Abin ne da kama ai dole yar nan tayi zargin hakan don biri yai kama da mutum gashi an nemeta an rasa a garin nan tun jiya.
Wata kila tsoron taji kamar yadda habbib ya fada ai ana kan bincike dai insha Allahu gaskiya zata baiyana komai daren dadewa.
Fatan mu dai Allah ya tayar da kafadan shi ya bashi lafiya yasa hakan ya zamo mashi kaffara a yanzu.
To Amin Amma ta fada tana kawar da kai tare da fadin ni dama auren sadauki da kafiran nan bai taba kwanta min a rai ba sai ace ranon yar nan daine kawai ya kaishi ga auren ta .
Amma wanan ai ba macen nunawa tsara bane a fage don banga wani abinda yaja shi gareta ba.
Aurene gwaggo Allah ya kaddaro akwai aure a tsakanin su da rabon yar nan da kika fada yanzu.
Idan ba wani abuba ai sai ya bata yar ta karata can da ita ta bar dan nan ya zauna lafiya Ammake fadan hakan.
Amma wai kin san sai da wanan matar ta saka aka kwace wa yaya komai a can da farko kamar zasu rabo dashi sai gasu kuma sun kara dinkewa daga bayan nan.
Ke yar nan ki bar wanan zancen aka kwace mashi dukiya kuma yake zaune tare da ita ?
Kwarai Amma don kawai kara aurena da yayi daga bayan nan taimakon yaya guda shine tun farko sunyi alkawari a rubuce cewa ga addinin shi ya yarde mashi ya kara aure .
Kuma ta amince da hakan saidai lokacin da tasan da zancen aurena dashi ta kaishi kara kotu dole kotu ga al,adansu nacan ta raba dukiyan sa biyu ta bata rabi.
Bata san da yana dabaran turo arzikin shi gida ba daga bayan nan kuma da ta sani ta biyo shi har kasan nan da jidali wai a cewan ta tare da ita suka samu arziki don me zai munafunce ta yayi hakan ba tare da sanin ta ba.
Rikincin gangan ke nan wanan ta zama Sarka mai rikucin gangan arziki nasa sun hada karfi ne tare da ita ?
Gwaggo kin san su ga al,adan su ai haka abin yake na miji baida halin yin wani abin ba tare da sanin matar shi ba irin namu na nan.
Yau ina mahaukaciyar uwar shi tazo taji wace tafita famkama da abin danta ita da da anyi zance zatace ni uwar maza ne masu arziki kuma ?
Yoni wanan jahilci ko hauka za a kirawa jimmai yau dai idan umar ya fadi ya mutu ke A ruwa kin fita kaso a cikin abinda ya bari shine kawai bakin ciki da hassadan jummai dama dake.
Amma ni ban taba tunanen irin wanan ba a rayuwana idan za a barmin shi yafi a bar min tarin arzikin da hjy ke hange.
Affa ke kika san wanan Aruwa rikicin jummai ai ba sai da dalili ba abin ya zake mata a jiki don ita bata bar kowa ba.
Duk da wanan abinda ya sameta baisa jummai yin nadama ba don dazun nan kuna ciki wurin yaron nan take fadin wai dama ana son ya tafi a mamaye abinda ya tara.
Har abin yaso zama masu fada da hadiye shine dalilin dana tura hadiye gida dazun .
Don ba zamu taru anan ana sayar da hali ba mutane suna tafiya damu a baki.
Kai halin hjy sai ita duk da bawan Allah nan yana cikin wanan halin bautan ubagiji zukatan mutane baya a kwance take wanan furcin.
Mamu ne ke fadin wanan magana tana kada kai taci gaba da fadin wa take zargin ya aikata hakan yanzu gareshi ?
Na nisa tare da fadin ni zancen hjy bai taba damuna a yanzu matar da taje neman wace zata kifar da mutuncina a gidan yaya don kawai kiyayya irin nata.
Mai kuma zatayi ko ta fada a kaina yanzu inji zafin shi a kwance take amma zuciyar ta na cike da sheri.
Kawai lamarin hjy sai addua a gareta idan tana da rabon shiryuwa Allah ya gyara halin ta.
Na dauka wanan abin da ta sameta a yanzu zai sa ta yin nadama sai gashi har yanzu zuciyar hjy bai saduda ba ga yawan aikata sheri gana tare da ita .
Kafin wanan abin ya faru na fito da safe na samu mama asabe waje tana kuka nake tambayan ta.
Da farko bata so fada min ba saidana matsa da nuna mata damuwa na take fada min ita ta gaji da halin hjy.
Don duk dawainiyar da take da ita bata ganin haka wai jiya don tace a kiran in duba ta take fadin ta fahinci akwai makircin da muke kokarin kulla mata nida ita.
Don taga yadda take shige mun idan na shigo tana wani yabona to ta sani duk kilibibin da nake kallona kawai take don ta gane nufinmu a kanta.
So nake kawai na karasa nakasata sai nace mata haba hjy wanan wani irin magana ne yarinyar nan fa itace fa silar samuwan saukin ki a yanzu.
Sai cewa tayi dani koda banzo ba idan Allah ya nufa zata warke ne ta tsani ki ta tsani duk wani ahalin ki jin hakan da nayi nace .
Wa,iyazu billahi hjy mai yai zafi hakan uwar jikokin kine fa kike aibantawa hakan.
Nice shedaniya kike nufi da kike kore min shedan komai to bari kiji indai a kan wanan yarinyar da tayi sanadiyar barina dakin aurena kike kokarin karata a gaba ki sani bani bake asabe.
Dama nasan ba don Allah kike min abinda kike min ba don wani manufa takine kawai don da ba zaki goyi bayan yarinyar nan ba haka alhalin kin san irin kuntata min da sukeyi da ita da uwarta.
Mama asabe ta kare da fadin yanzu FFatima ya dace duk irin kokarin da nake da hjy tace min wai ba don Allah nake kulata ba .
Don haka ni na gaji wallahi tafiyata zanyi ba zan iya wanan abin ba gaskiya jiya sai abinda hjy ta manta bata fada min ba.
Nace mama don Allah kiyi hakkuri kada kice zaki tafi don yaranta yadda suka daukeki bazasu ji dadin hakan ba idan kin tafi.
Hjy halinta sai ita wallahi ya kamata ace iyanzu kin saba da wanan halin nata ita da kanta zata dawo ta nemeki ai .
Tunda ba zata iya yiwa kanta wani laluran ba dole sai an taimaka mata bamu rufe baki ba mukaji muryan ta tana kiran mama asaben.
Amma tace ke ki duba min wanan abin mamakin don Allah wai mutum na kokari da kai kake masa wanan bala,in haka don wani dalilin naka can.
Ganin su kawu sun mike daga inda muke iya hangen su a zaune suna magana sunyi cikin dakin da yaya yake kwance da sauri.
Saurin mikewa mukayi lokaci guda don bamu san abunda yake faruwa ba a dakin suka mike zuwa dakin nasa.
Kusan nice a gaba wurin shiga dakin a tsartsaye na samu su kawu suna gaida yaya din da yake kwance yana bin kowa da idanuwan shi.
Sai dai duk gaisuwan da suke mashi bai amsa ba sai binsu yake da idanuwan shi kamar wanda bai karkare farfadowa ba a lokacin.
Zuwan mu kusa dashi yayi daidai da karasowan su hjy gurin hjy tana ririke a hannun yan uwanta.
Ganin su yasa muka dan tsaya a bayansu kada sai gaidashi da jiki sukeyi mai ina gefe tare da mamu da Amma sai hamdala nake ga ubangijin talikai daya rufa muna asiri yaya ya samu lafiya.
Ganin ba za,a sarara ba a lokacin yasa na karasa bakin gadon na fara fadin yaya sannu ya jikin ?
Sai lokacin ya dan juya kanshi yana kura min ido kafin yayi kokarin budan bakin shi yana son yin magana.
Sai dai ya kasa sai kuma ya lumshe idanuwan shi a hankali ganin hakan da yayi ne wani kuka ya kubce min lokaci guda.
Bani kadai ba kusan matan dake dakin hawaye suke a lokacin Amma na fadin saudaki sannu ya jikin kuma tana share hawaye .
Jin muryan Amma din yasa ya kara bude idanun shi a hankali yana kallon mu ya kara dago ido ya kalleni a karo na biyu.
Kuka nake yayin da iyayyen mu maza ke fada dani akan in daina kukan sai ya dan saki dan murmushi kadan ya lumshe idanuwan shi.
Muryan likitan shine ya shigo yana fadin haba a rage yawa a dakin don ba,a son a dameshi da yawa hakan zai iya kara jefa shi cikin wani damuwa.
Jin yadda nake kuka yasa likitan dago kai yana fadin why doctor fatima kin san aikin ki kece kiba da muhinmiyar rawa wurin taimaka muna kan maigidan naki har muka kai ga nasara.
Dakin yayi tsit yayin da wasu matan suke ragewa kamar yadda likitan da kawu balarabe suka umurta.
17/11/2021, 07:26 – ????????????: Dan juyo kanshi yayi kadan tare da kokarin mika hannayen shi gare ni lokaci guda sai kuma ya kasa yin hakan don jikin shi da yayi mai tsami a lokacin.
Ganin hakan kawu sani ya fara fadin Alhamdullahi da alama aiki yayi kyau ke nan tunda har ya iya sheda matar shi a yanzu.
Jin hakan hjy ta fara kiran sunan shi da babawo ya jikin naka ya kake ji yanzu ?
Kawu yana ganin hakan ya gane mai hjy take nufi yasa ya bar dakin ta hanyar yiwa matan shi dake wurin nuni da kofa ba bata lokaci suka bi bayan shi suna Allah ya sauwaka tare da adduan kara samun lafiya gareshi.
Dakin ya saura daga ni sai hjy da yan uwanta a tsaye mun zuba mai ido duk da ba magana yake iya yiba a lokacin sai numfashin da yake mayarwa a hankali.
Ganin yadda suke basu ko nuna alaman cewa sun san dani a wurin ba yasa na yanke shawaran fita daga dakin lokaci guda duk da ina son kara duba yadda jikin nasa yake a lokacin.
Wurin Amma na koma na zauna basu fito ba saida nurse tazo tayi masu magana suka bar dakin duk muna zaune a inda muke tare da Amma sai kara kwantar min hankali da takeyi.
Shigan likitan ne ya sa a kirani nazo da sauri yake fadin mara lafiya ne yace a kira mashini ina shiga hjy da suke daga gefen mu suka taso sai dai likitan ya rufe kofan babu halin shiga gare su.
Banji dadin yadda na samu yaya ba a wanan shigar don numfashin shi ba kamar dazun ba da muka barshi.
Isa nayi bakin gadon da yake kwance hankalina a tashe na kai hannuna saman goshin shi lokacin ne ya bude idanuwan shi a hankali yana kallona.
Ido ya dan kura min kamar bai ganeni ba sai kuma naga ya sakar min murmushi a cikkn karfin hali da daurewa na kara matsawa kusa dashi.
Hannuna dake saman goshin shi yake kokarin lalaba a hankali gane hakan da nayi yasa na kai hannuna da sauri na kama nasa.
Ji nayi ya rike hannun nawa sosai ya furta zahra na amsa da hawayen dake zuba a fuskana.
Stop crying yace min a daidai lokacin da likitan ya budewa yaya habbib da Aliyu kofan suka shigo.
Zahra zan tafi in barki da dawainiyar yaran mu ke kadai kiyi hakkuri da hakan zahra haka Allah ya nufa da ra, , , sai ya dan fara shakuwa.
Gaba daya rudewa sukayi Aliyu kan kasa zama a dakin yayi ya fito yana kuka wanda hakan ne ya jawo hankalin sauran mutanen dake waje.
Saida shakuwan ya lafa mai yake fadin habbib ko kasan merry ce ta saka ai min hakan dan yarta .
Wani kuka ne na sake sakewa mai sauti ga hannayen shi rike cikin nawa ya rikesu gam habbib yake fadin mun san da hakan bros don Zahra ta fara fadi.
Habbib i can’t survive don haka komai ritsi kada ku bata queen ka hada ta da yan uwanta ku rike min su amana bazan rayuwaba habbib.
Bros ka daina fadan insha Allahu zaka warke habbib ke fadi innallilahi nake iya fada a lokacin sai kalman shahada da nakeyi a fili a cikin gigita.
Dago idanu yayi ya kalleni idon shi gaba daya sun canza kala irun yanan da ake jefawa bawa yayin barin shi duniya sun sauka a idanun shi a lokacin .
Hakan dana ganine ya kara rikitani sosai yaya habbib yake fadin in fita dakin kada in kara daga masu hankali.
Kaina girgiza naki fita dakin don koma nace zan fita din hannayen mu yana sarke da juna yana murmushi jin fadan da yaya ke min a fuskan shi na kara kai dubana gareshi a lokacin idanuwan shi sun kara canzawa ga baki daya.
Allah ya ban hikimar kara furta mai kalman shahada sai naji ya karba min daga haka naji hannayen shi sun sake lokaci guda a take na kira sunan shi da karfi.
Saidai ina Allah ya riga da yayi ikon shi ya karbi abinsa lokaci ya cika babu sauran magani ni din dai da hjy ta tarewa ganin shi take hana in shiga dakin.
Allah ya nufa yaya zai cika a hannuna ta faru ta kare sai mu yanzu tamu ta rage shikan ya tafi abinsa ubangiji ya bamu cikawa da kyau da imani idan tamu tazo.
Likitan ne yayi dan aune aune yaja zanin ya rufe yaya umar a gaban idon mu muna ganin abin kamar a mafalki mai rabawa ya raba tsakanin mu da yaya umar din.
Ban samu kukan ba lokaci daya idanuwana suka kankance ina gani dishi dishi likitan yace yaya habbib ya kamani.
Fitowan mu yasa kowa ya gane abindake faruwa gurin Amma yaya habbib ya kaini itama Amman kuka take sosai hhaka yasa yaya habbib kiran su kawu yana sheda masu abindake faruwa.
Kafin wani lokaci labarin ya zagaye yan uwa da abokan arziki yaya Ahmed ne ya kaimu gida shida salma da Amma gaba dayan mu kuka muke sosai a lokacin.
Dare yayi don haka aka bari sai safe a kawar da yaya zuwa makwancin sa gaba daya lokacin ban san a inda nake ba don rudewa.
Hankalin kowa yana a tashe da wanan mutuwan mai girgiza zukata dayazo muna lokaci guda ga zancen merry dake ta yawo har an fara neman ta a ko ina a cikin fadin kasan nan.
Ba karamin jama, a yaya umar ya samu ba da sukai masa sallah da rakiya zuwa gidan gaskiya ga sheda na alheri da sai a yanzu muke jin irin alheri da taimakon al,umma da makwabta da yaya yakeyi idan yazo Nigeria ashe.
Dama ba a fadin halin ka sai bayan ranka kowa ke fadin albarkacin bakin shi a kanka Allah ya bamu ikon cikawa da imani Amin.
Karfe goman safiyan jumma,a aka kawar da yaya zuwa makwancin sa nayi kuka kamar raina zai fita banci bansha sai idan an tsareni don dole zan dan kurba ruwan kunu a cikina.
Da akai kwana uku yaya habbib yazo akan in koma gidan mu in zauna kada a bar gidan babu kowa don masu zuwa gaisuwa haka yasa muka kwasa muka koma can dani da manjo da Amma da suke tare dani a kowani lokaci.
Iyakata da mutane shine idanu idan kaji maganata sai yara suna kusa dani tunane babu wanda banyi a lokacin ji nake dama mu duka aka harbe da zaifi da barin na da yaya yayi a duniya ni kadai.
Sannu a hankali har na dan fara sabawa da rashin yaya a tare damu inda abin yazo min da sauki har yaran da yake shi yaya mai yawan tafiyane a lokacin da yake a raye haka yasa ko yanzu sai nake ganin kamar tafiya yayi zai dawo.
Hakama yaran kan dameni da tambaya yaushe ne daddy su zai dawo kamar yadda suka saba tambayana idan yayi tafiya.
A wansn zaman makokin da akayine aka samu aka shawo kan kawu ya mayar da hjy dakinta tunda Allah ya raba akan wanda suke fitina a kanshi.
Da farko kawu ya kafe akan har abada bazata dawo gidan shi ba tunda har yanzu bata saduda ba ko bayan mutuwan yaya saida ta tafka wani tsiyan ma.
Don kawai na aiki driver da motar yaya din ba kuma aiken shi nayi haka kawai ba shine yazo min da maganan akwai wasu takardun yaya da zai tafi ya karbo nace ya dauki motar ya fita da ita don sheda.
Shine aka fada mata tunda safe tayi min tas a gidan tana fadin sai a bari a raba gadon yaya da muke kwadayi nida uwata da yan uwana.
Wanan maganan ne yakai kunnen kawu yazo gidan yaiwa hjy tas akan ta fita harkata ta barni inji da abinda ya dakeni na rashin mijina.
Wanan abinda tayine yasa kawu cewa ba zai mayar da ita gidan shi ba saida aka taru dattijan unguwa suka bashi hakkuri da kyar ya yarda da sharadin ba zata kawo mai wani tashin hankali ba a yanzu kuma.
Gidan ya rage dagani sai yarana sai yan aikin dake gidan yaya habbib da yaya umar dama Nasir babban abokin yaya suna tsaye a kan mu bamu nemi komai mun rasa ba a rayuwan mu tankar yaya yana raye.
Mun cika kwana arba,in cif da yake inada karamin ciki wanda hjy sai daga baya ne take jin zancen cikin jikina din tayi fadan hakan kamar tsiya .
Inda take fadin wai da gaiya nake zuba haihuwa haka a gidan yaya dan kawai gadon mijina ga gadin nan dukiyar ai anbar muna muci.
Ni dai tashin hankalin yai min yawa na hjy don kulun safiya da irin fitinan da zata fito dashi duk kashedin da kawu yai mata kafin ta koma bai hana hjy tsula halin ta ba garemu.
Kamar ba dan cikin ta ta rasaba a lokacin gaba daya abinda ya bari a duniya ya rufe mata idon ta sai tsakure tsakuren maganan da takeyi.
Nazo ma kawu da zancen komawa na school tunda yaya dai ya tafi ke nan ba zai taba dasowa gare mu ba kuma gara in nemi na kaina don in kula da yarana da suke kanana tun yanzu .
Don gaba daya ban gane mai ake ciki da dukiyan shi ba kodan ban sawa kaina damuwa da hakan bane a lokacin oho ?
Saida kawu ya tambaya aka fada mai mudfin zan kula da kaina in tsare mutuncina zan iya komawa can in kammala har zuwa lokacin da zan haihu don dama idda ya saura min kuma ga ciki a jikina.
Aiko hjy najin zan koma London da yara ta samu kawu da zancen bata san wanan maganan ba har idan zan koma ne ma sai dai idan za a hadani da wani muje tare don ita sam bata yarda in koma ni kadai ba saboda ba,a san abinda ya bari acan ba.
Kawu yace a kausashe jummai kina da hankali kuwa kin ko san abinda kike fada kuwa da alama dai kamar kin dan motsu.
Tace da hankalina sarai Alh yardane kawai banyi da ba da ko wace mace ba matarshi bace tayi sanafin barin shi duniyan nan don me yanzu zan yarda da wata kuma.
Kiran habbib yayi bayan ta fita don kawu bai kara kulata ba yace suzo yana neman su bayan sunzo ne yake fada masu bukatana.
Sai habbib din yace nima nayi tunanen hakan gareta tun farko sai dai ban sani ba ko tana da daman yin hakan ga addini tunda tayi nisa ga karatun nata.
Kawu yace to ba wanan ba dazun muka gama magana da mahaifiyar ku ta nuna bata yarda Fatima ta tafi ita kadai ba don ba,a san abinda ya tara a can ba kada ta tafi tayi rub da ciki dasu ita kadai.
Innalillahi suke maimaitawa tare da fadin kai haba mama koma mai yaya ya bari a can ai ko fatima taci abinsu ita da diyanta taci bana wani ba.
Ku kuka san da hakan kawu ya fadi lamarim mahaifiyar ku a yanzu sai addua don abin nata kara yawa yakeyi ko yaushe.
Kafin su fita suka aje magana kan za,a bincikeni yaushe ne zan koma don su sani a shiryawa tafiyan mu don sun amince na koma harda yaran gaba daya can har zuwa lokacin da zan kara sakewa .
Naji dadin wanan halarcin da sukai min din don dama yadda za a rabani da yarana nake ji dashi nake kwana nake tashi a raina.
Sai gashi abin yazo min da sauki sosai ba bata lokaci na shirya na koma London nida yarana inda za a dinga kulawa damu a karkshin oga mansur mijin Ramla.
Mun tafi mun bar hjy da tarin dukiyan da take fada a kanashi inda bata san can ma dan nata ya bar arzikin da bata taba tsamanin irin sa ba gareshi.
Don aikin yaya ba karamin samu sukeyi ba wanda yake harkan international samu yake kamar ba gobe a kullun.
Sosai na mayar da hankalina ga karatuna inda nake tare da maria sai manjo da na wuto da ita don kara debe min kewa.
Hakan baiwa hjy dadi a ranta ba sai jefa magana takeyi tana fadin wai rashin tsoron Allah yasa aka turani in koma don ansan abinda aka kitsa na koma na wawashe abinda aka bari a can tunda nan babu halin ci a gareni.
Itace tace nayi ta haihuwa kamar bera dama mun san abinda muka shirya a kanshi merry sawun barawo kawai ta taka.
Duk da ina samun kulawa a bagare daban daban daga yan uwa da abokan arziki na yaya umar hakan bai hanani kewan mijina ba muna tsaka ga exam din shiga matakin karshe na haifo dana mai kama da ubanshi sak wanan ba inda ya ragewa yaya umar shi wurin kama.
Tun fitowan shi na fara kiran shi da habibi da kuma wanan sunan oga mansur yayi mai huduba watau umar faruq.
Gida basu samu labarin haihuwana da wuri ba don nina hana a fada ba saboda komai ba sai don in dan samu natsuwa don hjy na iya tayar da fitinan in dawo tunda na haihu ayi suna a nan gida.
Ban damu da fadan kowa ba a yanzu idan ma har koyone na koyi halin boye sirina a wurin uban diyana.
Tunda labarin haihuwana yazo kunnen hjjy ta dan bada lokaci sai kuma ta matsa sai in dawo gida a raba gado tun tana boye hakan da farko tana fadin in kawo yaron dana haifa su gani har dai ta gaji ta fara fadin in zo asan inda kowa yake zaifi.
Kin dawowa nayi nace duk abinda sukayi daidai ne a gareni ba don komai naki dawowa ba sai don yarana da nake jin kishin kishin din za, a rabani dasu wai idan muka dawo gida haka yasa na share kowa nayi zama tare da yarana a can .
A haka na samu labarin wai hjy dai zaman yaki ta tare yanzu a gidan mu kuma tana amfani da babbar motar da yaya yake amfani dashi.
Duk wanan bai dameni in dai ina tare da yarana hankalina yana kwamce gasu da jikjn girma sunyi wani girma hausa ma ya fita bakin su.
Kodana kara karatuna na samu aiki a can ta hanyar oga mansur mutumin kirki da bai gazawa damu ga business da mukeyi nida mamu ina shiga kashe ina saro kaya in turo nan kano yaya Ahmed yana kula min da sana,a ta.
Bani nazo gida ba saida na share shekara biyar da watani a can koshi don ciwon Amma da aka buga min bata da lafiya na shigo.
Lokacin na kara bunkasa na zama wata wayyaya dani ko dole yanzu yaji shakkan takani kamar yadda ake min a baya.
Don a karskashin WHO nake aikina idona ya bude sosai bani daukan raini a gurin kowa a yanzu.
A bangaren merry kuwa tunda ta samu ta bar Nigeria a furgice bayan barin ta gidan lokacin da abin ya faru ta koma America a firgice tana nadaman abinda ta aikata din har labarin rasuwan yaya yazo mata gashi bata san inda yakai mata yarta ba ya rasu kuma.
Gashi taji labarin ana neman ta a Nigeria ido rufe kan zargin kisan mijin ta da tasa yan bundiga suka zo har gida sukai mai.
Wanan dalilin yasa ra boye kanta ga kowa bata yarda ta kara waiwayan yar nata ba ga rashin ya ga rashin mijin da tayi don bata san abin zai kai ga kisan shi ba.
Hakan ya jawo mata gaba da yan uwan mahaifiyar ta da suka bata shawaran ayi kidnaping din yaran sai ya fito mata da yarta a bashi yaran shi sai gashi plan din ya basheta.
Mun iso Nigeria mun samu Amma abin ba dadi don jikin ya matsa mata sosai tun rasuwan yaya data saka damuwa a ranta.
Muna da sati biyu da zuwa Allah ya karbi rayuwanta mukayi wani babban rashi tsohuwar arziki a cikin mu.
Duk da Amma tsohuwace saida wanan mutuwan nata ya taba kowa na halin don anji mutuwanta sosai a gidan.
Saida komai ya lafane sai ga yaya habbib ya tsiro da wani zance wai yana son a daura muna aure dashi ya maye min gurbin dan uwan shi.
Wani sabon tashin hankali kuma ke nan don hjy naji ta hau bakin ta da bala,i ga kuma matar kawu balarabe da ta fito da nata bala,in ina muka fito nida mamu.
SARKA MAI RIKICIN GANGAN ina wuta su sakani na dawo bauchi wurin gaisuwan umma da ta rasu na samu wanan fitinan kuma duk ina jin su ban samu ba kowa amsa ba.
Sai ji sukayi kawai na koma na bar kasan koshi da kyat kawu ya yarda na koma don shi ya amince da zancen yaya habbib din.
Har London yaya habbib ya biyoni da zancen na nuna mashi hakan ba zai yuyu ba saboda me ya tambaya nace ko ya manta da wace yake aure yar uwata ce ita.
Ko bayan hakana yasan zancen da ba zai taba yuyuwa garenu bane don hjyn shi bazan sake zama a karkashin ta ba har abada.
Wanan amsan dana bashi yasa shi har zuka wai idan hakane sai dai in bashi yaran su dama suna daga min kafane don haka tunda ban yarda ba zasu dauki yaran su yanzu .
Nan kuma na nuna mai bai isa ba muka rabu baram baram dashi babu dadi haka yasa na samu sa,ida ga lamarin su.
Iyakata nazo mu kwana biyu da yara mu koma ina kula da abina tunda Allah ya hore min abinyi yanzu ban damu da dukiyan yaran ba don da aka raba cewa hjy tayi saidai su su rike na yaran a wurun su har yara su girma.
Wanan shine labarina mai cike da rikici har mai rabawa yazo ya rabamu da yaya hjy bata barni na huta ba saida taga na fita zancen komai da yaya ya bari a duniya kafin ta dan sarara min.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button