NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:37 – ????????????: YA ALLAH KA GAFARTA MUNA KURA KUREN MUN WANDA MUKA SANI DA WANDA BAMU SANI BA UBANGIJI KAJI KAN MU KA GAFARTA MU.
KASA MUNA YSORON KA DA IMANI A CIKIN ZUKATAN MU YA ALLAH KA BA MU IKON BAUTA MAKA BAUTA TSARKAKKE A SAURAN RAYUWAN MU AMEEN YA ALLAHU, , , , , , ,

Lokacin da nafito dan gidan baffan nawa bayan na gama jin umma saude tana kwala min kira wanda nasan kiran na dayan biyu ne ko aiki ko aike da bai kare min a gidan muddin ina cikin gidan sai idan Manjo ta hanani zuwa ko fita na ke samun sauki.
Shiyasa na kwammace zuwa gidan Atika ita kadaice kawata a garin tunda nazo tsiwa da fada bai bari muyi nisa da sauran kawayen da suke sona da kanwance a garin.
Amma ita Atika banda matsala da ita yanzun zamuyi fada mu koma mu shirya hakama mahaifiyar Atikan takan nuna min kulawan ta sosai kasancewa ta marainiya a gidan da ban samun kulawan da ya dace.
Da sallama na shiga gidan wanda doka ne hakan ko kana dan gida zaka shigo dole sai kayi sallama kafi shiga idan ba haka ba sai ka koma baya ka kara sallama zasu barka ka shiga.
Ba iri gida Baffa na ba da kirikiri kana sallama suna ji ka za, a kyale ka wasu ma suce ka damay su da sanaben yin sallama idan zaka shigo ka shigo kai tsaye.
Atika ce zaune tana tsifan kai a yar kujerar mata ina ganin hakan na bata rai don nasan za ai dayan biyu ko in taya ta ko mahaifiyar ta malle tace nima in sance nawa kan ai muna kitso a tare.
Wanda ban son hakan ko kadan naki jinin abinda zai taba min lafiyan kaina a rayuwana sai kitso yai min wata daya akai har tsagan kitso ya fara bacewa akaina ban sance shi sai wani yaji tausayina yasani sance kan dole zan kwance kan.
Atika tana ganina bayan karba min sallama da tayi tace yauwa kamar kin san yanzu malle ta gama maganan ki kizo mu kwamce kai mu tafi kitso yau.
Harara na watsa mata tare da fadin ki dai tafi kitso ni har yaushe kaina ya tsufa da zan sance kai tace lah yanzun wana kan da nayi kitso uku bayan wanan zaki fadi haka.
Fuska na bata ina zama tare da fadin kin san Allah Atika bana son abinda zai taba min lafiyan kan nan nawa ko kadan .
Tace rashin sabo da yi a koda yaushe ne yasa baki saba da taba kan ba har yanzu amma mutucin mace ai shine gyara kitso kuma na cikin gyaran mace don da zaran wani yaga kanki a haka sai yai maki kallon kazama.
Na harare ta tare da fadin kina nifin ke nan ni kazamace ko haka ma ranan ya sadi ya kirani da kazama wai na daga karyayi ball dani gurin da yake cin abinci.
Sai kuma naja tsuki tare da fadin koda yake wa yan nan ma ko may nayi haka zasu ce min don babu mai kaunar zamana a gidan don ciwon Malle kawai muke zaune a gidan nan.
Yanzun mu guduwa nayi ina jin umma saude na kwala min kira nasan wani aikin zata sani ga jaka sun samu a gidan ke nan ko ?
Atika tace ko basu son ki tunda Baffa shi yana son ki da Malle ai shike nan dama don Baffa di kuke zaune a gidan ai.
Nace matsalan ai shi Baffa baya zama agida kullun yana wurin tsaron shagon shi Malle kuma kinga ba maganan ta suke ji ba tunda sunga yanzun bata da kafa da zata mike ta daki mutum.
Mikewa nayi ina fadin kowa kibiyar in kama maki tace ke ba zaki kwance naki kan ke nan ba raina kara batawa ina fadin idan baki so na zauna.
Ta miko min kibiyan na shiga kwance mata kan muna hira wanda hiran duk zagin yan gidan mu nake muna fadin halin kowa a gidan.
Muryan Malle mukaji a kan mu tana fadin yau naga ikon Allah Fatima bana ce idan kin shigo ta fada maki ki sance wanan kan daya komar dake kamar mahaukaciya ba.
Ba dama in magana saboda nauyi da kunyan marar da nake ji a raina yasa na sakewa Atika kanta na samu guri na zauna.
Daki ta koma sai gata ta fito da wani kibiyan ta miko min nan na fara kwance kan nawa na dole ba don na so ba.
Saboda wanan kitson da muka tsayayi yasa na kai dare ban dawo gida ba abinda ya kara tunzura ran yan gidan mu ke nan fiye da yadda nayi tsamanin zasuyi min dama idan na koma gidan.
Ga laifin da nayiwa umma saude ga kuma wani na kara a samsn shi nasan kuma Manjo na can cikin damuwan rashin dawowana gida da wuri don duk dadewa na a gidan su Atika ban kai magariba ban shigo gida ba.
Ban yarda na shiga gidan ba kai tsaye sai da na dan leka ko babu kowa a waje ganin basu kusa yasa nayi wuf zan shige dan dakin mu wurin Manjo.
Naji an kai min duka a kai kumb tare da fadin shegiyar yarinya dazun da ake maki magana kika gudu gidan uba kika je har wanan lokacin ?
Yakara kai min wani duka ban san lokacin dana sake wani ihu mai kara ba da ya karkato da hankalin kowa gare mu.
Yar iska ba kina ganin Manjo na kama maki ba agidan nan yasa kike abinda kikaga dama yanzun.
Cikin kuka da jin zafin rikon da yai min nace may nayi ma da zaka mare ni don anga banda uwa a gidan nan kowa ke dukana haka ?
Shegiya an duke ki din kira uwar ki ta rama maki ihun dana sake yasa kowa na gidan fitowa a lokacin dama dukkan su hake suke dani.
Karawa yar iska marajin magana yarinyar nan yanzu ta fitsare a gidan nan da kike fadan haka wani ya kori uwar taki a gidan nan halan ?
Ummatu ne ke wanan maganan uwar gidan Baffa wani ihun na sake sakewa mai karfi don Manjo taji tazo ta cece ni don naga su ba hakkuri zasu bada ba sai ma zugashi yai min tsinanen duk yadda yake murdai murdai din nan.
Aikuwa manjo najin kuka na tun ihuna na farko ashe tana can tana kokarin tasowa daga daki ne sai muryan ta mukaji tana salati a bayan mu.
Tana fadin yau naga abinda yafi karfin ganina a gidan nan yanzu sadi kashe yar marainiyar Allahn nan kake son yi ko may ?
Wanan irin duka da kake mata har a dakina ina jin kara tana karasowa gurin take magana tana zuwa ta sa hannu zata kwace ni daga hannun shi ya kare rike gam don kada ta kwace yana min ketan daya saba.
Tana jan hannu na tana fadin shikata dan banza mara hankali da tunane yar nan kwara daya ta tsone maku ido a gidan nan .
Ina ga kannen ka nan baka tsawata masu su daina yawon banza ba sai wanan da aka san inda take ina nan gidan makwabta take shiga duk iya yawon nata.
Da taga yaki saki hannu nawa takai mai duka a baya tim yace wai wai wai manjo akan wanan yar kika dukeni haka yau ko sai na balla ta a gidan nan inga iya fitinan ki.
Baka isa ba dan banza uban ka ma yayi kadan ya balla ta balle kai yaron kawai sauran mutanen gidan sai abin ya koma basu dariya.
Don shi a zolaya yake mata magana inda manjo iya bakin gaskiyar ta take fada dashi zata kara kaimai duka ya sake ni da karfi na fada jikin ta da kadan mun fadi kasa Allah ya kare bamu kai kasan ba.
Tace dan kawai na gane so kake ka karasani bawai a yar abin naka ya tsaya ba yace in karasa ki in gane may manjo ki dai ji da kafan nan naki tukun.
Na dai gane zaman mu a nan ne baku so zan koma azare inda na fito da yardan Allah goben nan zamu bar maku gidan tunda na gane nufin ku.
Haba yar nan ita kadai ce a gidan nan kowa ya tashi dai A ruwa dau a ruwa yace ai da na kamata yau yadda nake so data zama a wuta.
Tace kai tafi can dan kawai kai kan bakayi hali mahaifan ka ba sam wallahi daka biyo su daka dace.
Yace halin ki na kwaso ai bakiga muna kama dake ba ta kara sukewa da yaron tana fadin ke kuma shige mu tafi kar ya karasa min ke don ba mutunci ne da su ba.
Har mun dan gwauta muryan ummatu mukaji tana fadin gaskiya babba ki dinga barin suna hukunta wanan yar.
Yanzu gashi akanta kike zagin wanan yaron haka kina wufinta shi akan yar da kika fi so a gidan koma dai yayane su duk ai jikokin ki ne kaf a gidan nan.
Saude zaki fita idona ko sai na bata maki don banyi tsufan da har sarakuwa zata wufintar dani a gidan nan daga can gefe nace Manjo kyalesu mu tafi ina jan hannun ta.
Bayan mun shiga dakine ta juya gare ni tare da fadin ke ma kingane ki bakya jin magana .
Kinfi son ko da yaushe su dinga dukan ki kamar sun samu jaka ko ?
Haka kike yi da muna gida ina kike fita yanzun kinzo nan kin koyi halin yaran banzan nan da uwayen su basa son ai masu magana.
Yanzun akan na hana yaron nan sadi dukan ki yasa saude ke son fada min maganan banza goben nan idan Allah ya tashe mu lafiya zan bar masu gidan nan indai akan nasa ido haka suna ci muna fuska ne.
Na bata rai tare da fadin nifa manjo ba da gangan naki dawowa gida da wuri ba kin ga kaina dole malle ta kwance min kai aikai min kitso an gama kuma tace sai nayi wanka naci abinci zan dawo gida saboda tasan halin gidan nan.
Tunda na dade haka ba lalai bane su bani abinci don ba bakin, ta suke ba gun sanin halin su malle tace to kin gani har makwabta sun san da bakin halin su.
Ki kama kan ki cikin yan uwan nan naki na kula ba son ki suke a cikin su ba don hakane nima bana raga masu ko kadan.
Wallahi Manjo dukan da yai min ai banso ki masa kadan ba tace rufe min baki iya karafina ke nan da dukan bai maki ba ai sai ki ramawa kan ki.
Ni dai abinda nake so dake ki koyi natsuwa ki kama mutuncin kan ki kodan mahaifin ki dake kasa kwance.
Ina jin haka bace manjo yanzun banda natsuwa ne ko may ina fadin haka na koma daga karshen dakin na zauna na bata baya alaman nayi fushi ke nan.
Kyale ni tayi na dan lokaci nasan ba zata juri ganin fushina ba da ita sai naji can tana fadin ga abincin naki dauka ki kara don nasan ma basu saka maki ba kada ma ki tambaye su don ba baki zasu yi ba.
Kyaleta nayi kamar banji ta ba sai can tace ke dadina dake baki da fahinta da wayau ni ina nufin ba baki da natsuwa bane ina nufin ki kara kama mutuncin ki da kowa mutuncin mace kimar ta.
Nagane may take nufi wanan maganan dashi na bude kunnuwa na a gurin ta kullun nasihan manjo ke nan a gare ni tun ban fahinci mai take nufi da hakan ba har na gane .
Mikewa nayi ba tare da nai magana ba na dauki kofi nayi hanyar waje tace ina kuma zaki bazaki zauna kici abincin ba nace ruwa zan debo a famfo.
Da na debo ruwan na dawo na dire a gabanta tare da dauko mata abincin data ce inci don nasan tun dan abincin rana data dan taba bata ci komai har wanan lokacin da take kokarin sadaukar da yuwanta ta bani rabon ta inci.
Dago kai tayi ta kalle ni tare da fadin yaya kuma kika aje a gabana nace Manjo kici ni a koshe nake wallahi na fada maki naci biski a gidan malle sai dana koshi .
Kai ta gyada tare da saka min albarka kamar nice na girka abincin ko na sayo aka girka nace baffa ya kamata ki sakawa albarka shida ya kawo aka dafa.
Bude abincin tayi ta ja tsuki don can yake manne a kwano har yayi sanyi kalau sosai tana shirin magana mukaji sallaman Atika a kofa.
Tana tafe da kullan abinci ta shigo ta dire a gaban manjo tare da gaishe ta tace manjo biski ne malle tace a kawo maki tasan kya so.
Manjo na washe baki tace usse, usse, malle ko ta kyauta min yau tayi min abinda naji dadi sosai ga abinci ga yar nan ta koma goshi na mata kyalli saboda gyara.
Atika tace Manjo don ma Fatima bata so gyara aida tasha gyara gun malle to ita fatiman ne idan an mata gyara sai an dauki lokaci bata kara ba.
Malama ban fa son kushe kin fini gyara ne ko may na fadi ina hararan Atikan sama da kasa da sauri tace , a,a ni na kai can.
Dallah rufe mana baki ke badon Allah yayi ki fara ba ai da bamu san iyaka ba kin gode kin kwaso iyayyen ki duka a gurin fari har makin so ki fisu da kina gyaran jikin ki aida kyaun ki badai nan ba.
Bude kulan da Atika ta shigo dashi nayi sai kamshi ya tashi a daki yana daukan ido nace kinga Atika manjo fa bataci komai ba tun kan na fita gidan nan dazun har yanzu don Allah bari ta danci wani abu kada ta fadi muna.
Nan na tursasa manjo taci abincin taci abinci ni kuma na hau ba Atika labarin yadda muka kwashe da yaya sadi lokacin dana dawo gidan ina sanda.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button