NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA

AYI HAKKURI DON ALLAH NA RASHIN JINA KWANA BIYU YAN UWA.
16/11/2021, 22:45 – ????????????: YA SUBBAHANALLAH, KARIMUN, RAHIMUN, YA HAIYYU YA KAIYUMUN, , , ,

A dakin Amma muke zaune dasu Aisha dan na fara dan sakewa dasu yanzu su kadai ne zan dan raba inji dan sanyi a gidan.
Kitso nazo suyi min sai dai har lokacin ban kwance kan ba su suka taimaka min na don haka nafi son zuwa wurin su duk sati suyi min kitson duk da mamu ta iya sosai.
An kusa gama kitson ne mama hadiye ta shigo falon tana fadin hajiya ashe mutumin ki zai zo kasan nan ne dashi da yan uwanshi.
Da mamaki Amma ke fadin wani mutumin nawa a ciki tace umar dai mana dan gaban goshin ki na gidan nan.
Da sauri Amma tace ina kika samo wanan labarin kuma yau ake wanan zancen daurin gindin uwarsu suka samu yo waya sani ko sin kai ga tara iyali ma a can tunda ba wanda yasan wainar da suke toyawa a can yanzu.
Haba hajiya da hankalin su zasu aikata hakan a kan su aiko wani da dangin shi yake kuri haka dai tasu rayuwa yake ba tunanen abinda kaje ya dawo gare su.
Amma ta tabe baki tana fadin idan ma zasu zo Allah dai ta kawo su lafiya idan muna da rayuwa ma gansu .
Lokacin azumi ya gabato saura yan kwanaki a tashi da azumi a fadin duniya don haka ake ta faman shirye shiryen taron watan mai alfarma a ko ina na fadin duniya.
Hiran su bai shafe mu ba har mama hadiya ta gama ta fita zuwa unguwa kasancewa ranan weekend ne bata fita gurin aiki ranan.
Sai da ta fita Aisha ke fadin wai Amma duk hjyan su salma ta haife su su ukun duka.
Amma tace wai kina nufin baku san yannen naku ba da kike tambaya koda yake ba yau yaran nan suka tafi ba har shi wanan da ya tafi daga baya din sai lokacin Aisha tace ya kamal ko shi wanan na sanshi mana yana zuwa gidan mu lokacin da muke gidan Abban mu.
Shi dai zaki iya shedawa su wa yan nan ai sin dade da barin kasan yanzu sun tasan ma shekara goma sha fa da tafi sai nayi karaf nace ashe tsufi ne ba yaraba.
Dariya sosai Amma tayi wa magana ta tace inda ba tsofi ko yar nan karatu suka tafi yi can waje shine shiru basu dawo ba kin san ita jummai tana da son komai nata ace ya fita daban dana mutane.
Yanzu gashi alama ya nuna yaran basu son kasan su ta haihuwa balle yan uwan su na jini kai Allah dai ya kyauta da hali irin na jummai wallahi.
Ban faye sa baki ba idan ina part din Amma ana hiran yan gidan kawu din don horona da hakan da mamu keyi ko yaushe sai wanan halin ya fara bi min jiki.
Koda naga sin buge da hiran sosai yasa na mike ina fadin barin leka mamu in taya ta aiki kafin yamma yayi sai Amma tace zaki gudu ke nan yarinya da radhin son shiga jamma,a haka.
Ina dariya na fita na barsu suna zancen su kodana shiga wurin mu na samu tana sallah bata fara aiki ba nima dakin mu na shiga nayi sallah kafin in fito in fara gyaran ko ina na part din namu don shi nakan fara yi idan zamu yi aiki ko ina gida.

ENGLAND, , , , , 

Suna zaune da merry a falo wayan shi yayi kara itace ta duba ta tabe baki tana fadin is from Nigeria da sauri ya karbi wayan a hannun ta yana duba mai kiran nasa .
Mama ya gani a rubuce saman screen din wayan sai daya dan daga daga yadda suke zaune da Merry din ya gyara muryan shi.
Ya dauki wayan da salma daidai lokacin yana kokarin gaida mahaifiyar tasu ta amsa mai a cikin jin dadi da annashuwa.
Bayan gama gaisuwan su take fadin ranan wanan mondya mai zuwa ne tafiyan ku ko a cikin mamaki yace mama zuwa ina.
Gaban hjy jummai ne ya fadi tace kamar ya zuwa ina kuma ina dan uwanka ya kirani yake sheda min zuwan ku ranan.
Cikin murya mai taushi yace hakane mama saida nada ni bane zuwa ranan sai nan gaba kuma idan Allah ya kaimu zan sa lokacin zuwa don akwai aikin a gabana da zai, , , , ,
Jinan babawo umurni ne ba tambaya ba duk abinda kakeyi kayi haraman zuwa gida a cikin satin nan mai zuwa don nagaji wallahi.
Na gaji da korafin mahaifin ku a kaina ko yaushe ya debo zugan shi a kan ku wurina yake sauke haushin shi.
May kake son ka zamane babawo kana ko da tausayin mu a zuciyar ka, baza kayi kokarin sauke hakkin mu dake wuyan ka ba sai bayan mun mutu ko may ?
Subbahanallahi mama may yai zafi haka harda wanan maganan in sha Allahu cikin wanan shekaran zan zo gida da yardan Allah kamar yadda na fada maki da farko.
Ka dai ji abindana fada ma kuma gaskiyar magana ta kenan na fada ma yaya kake son inyi da surutun mutane a kanku ne ?
Ko jiya jiyan nan sai da muka kwasa da Alh kan zancen ku har yake fadin don kana takaman kana turo muna da abin duniya kake ganin ka fita hakkin mu ko may ?
Har yake fadin da goyon bayana kake komai don nice na daure ma gindi kake haka may ye a cikin zuwa gida ka gane mu idan kai baka son ganin mu.
Mu iyayyen kane muna son ganin ka a rayuwan mu tunda muna raye bamu mutuba idan kuma dayan mu ya mutu sai kazo gausuwa idan ka samu lokacin hakan .
Jikin shi yayi sanyi yake fadin Allah ya huci zuciyar ki mama insha Allahu zanzo kamar yadda na fada a dai dan kara hakkuri don Allah sai yaji kit ta kashe wayan.
Hakan ya tabbatar mai da ta katse layin ke nan kuma tana cikin fushi dashi abinda bata faye yi dasu ba ke nan indai ta fara yai mata alkawarin makudan kudi yanzu zata aje zancen da take fitina akai.
Sai dai yau an samu akasin hakan don ya lura mahaifiyar tasu ta hau sosai dashi duk maganan da yake merry ta tsura mai ido daga inda take zaune.
Don fahintar da tayi yana cikin wani yanayi kan maganan da yake a wayan saboda yanayinsa daya canza a lokaci daya.
Idan akwai abinda taki ninin ji shine taji ya ambaci zuwa gida yanzu hankalinta zai tashi su dinga rikici har sai taga ya janye tafiyan da yayi niyar yi din.
Duk da itama kasanta ne na haihuwa amma bata son abinda ta danganta ta da Nigetia a yanzu saboda son mijin ta da takeyi .
Don tasan ba abu kadan zai iya faruwa a tsakanin su ba idan har ya taka mahaifan shi yaje kano tasan sai yadda Allah yayi da al,amarin su ita kam.
Don kafinta samu kanshi ta aure ba karamin yaki tasha kan haka ya faruba sai data hada da gargajiyan su nan ta samu ta ciwo kanshi ya yarda ya aure ta.
Wanda tasan ba wani ahalin shi da yasan da zaman shi da ita don aure da sukayi snyi shine a can daga su sai abokan arzikin su.
Ba damuwanta bane sai wani nasa yasan da ita ita dai burin ta ta samu kan mijin ta akoda yaushe ta kuma samu yadda take so din.
Ko ita ta shiga tashin hankali lokacin da iyayyen ta suka samu labarin auren ta da dan kabilan hausawa kuma musulmi wanda abin gori ne da kyama a gurin su balle shi da tasan addinin su bai yarde masu da hakan ba kasafai.
Wanan dalili ne yasa bata kaunan abinda zai sa yace zai je gida don tana ganin zuwan shi wurin iyayyen shi komai zai iya faruwa da auren su din.
Kasancewan ta itama yar kasan Nigeria kuma daga yakin jos mahaifinta ya fito mahaifiyar ta ce yar kudu ko zo in kashe ka bata ji da hausa haka ma ita merry bata jin hausa sai dan gaisuwa da sauran kalama mai saukin haddacewa.
Dan dama mahaifinta yana danji koshi ba sosai ba yafi bada amanna ga yaren da yafito daga ciki bai yi rayuwan shi a gida nigeria ba.
Duk rayuwan su a kasan turai sukayi shi acan ya hadu da mahaifiyar merry din sukai aure wanda wanan dalilin yasa da merry ta hadu da Umar tana jin daga Nigeria ya fito suka kulla abotan daya zama aure a gare su.
Yanzun haka da ake maganan nan tana dauke da cikin umar din wanda suke expecting din haihuwan ta ban da wata shidda masu zuwa.
Kallon shi da yaga tananyi ne yace da ita is my mum tana magana akan rashin zuwana gida da banyi duk dadewan nan.
And kin san gaskiya ke ma don kin kusa zama uwa very soon kin san irin feeling din dake tsakanin da da uwarshi a yanzu.
Tunda ya fara magana ta kura mai ido babu ko kiftawa har ya gama sai lokacin tace may kake nufi da maganan ka Omar ?
Yace kin sani zan tafi inga mahaifa very soon don nima rashin zuwana gare su yana damuna sometimes ina jin kewan su ina son ganin su.
Ina son inga Family dina da, , , hannu ta daga mai tana fadin is eenough Omar ma,ana dai kana nufin gida zaka ka barni nan ke nan ?
Yace yes haka nake nufi zanje gida in duba su in kwana biyu a tare dasu su gane ni nima in gansu in yaso daga baya munyi settle da mahaifina zan dawo gare ki da baby mu.
Mikewa tayi tana fadin wanan ba zai taba yuyuwa ba Omar banki ba in kace mu tafi tare wanan zan dan yarda dashi.
Da kuma sharadin idan munje zamu sauka a gurin iyayyena ba a garin ku ba har sai idan iyayyen ka sunyi acepting dina a matsayin daughter inlaw din su.
Wani kallo ya watsa mata kafin shima ya fara magana a hasale yana fadin kada ki manta da alkawrin mu kafin muyi aure na fada maki koni waye kika yarda.
Don haka idan kina son muci gaba da zama a cikin salama dake ki bari in fuskanci iyayyena ta ruwan sanyi bada garaje ba kamar yadda kike nufi din yanzu a kaina.
Ganin da gaske yake idan akwai abinda ta ki a wayi gari su rabu da umar din ta don haka dole ta kyale shi a lokacin don tasan muhinmancin alkawari sosai.
Ya juya ya barta wurin sha waran da kawai ya yanke shine zai tafi Nigeria cikin hakan kuma zai sanar dasu zancen auren nasa inyaso ayi wace za, ayi tsakanin shi da mahaifan nasa.
Da wanan tunane ya kwana a ransa na yadda zai kalli ifon mahaifin shi da wanan laifin dayayi masu yasan cewa mahaifin shi mutum ne mai ra,ayi akan addinin sa sosai.
Uwa uba irin tarbiyan daya basu tunda farko bai sako yaro wani kasa sai ja haddace alkurni da dan taba wasu litttafan addini.
Shikan shi yakanyi mamakin yadda ta samu kansa dumu dumu da auren Merry koda kuwa ace itama din yar addinin shi ce ya kamata ace iyayyen shi sun san da auren su tun farko.
Sai dai kaddara ta riga fata don Merry ta zama wani bangare na rayuwan shi yanzu zama suke a tsakanin su na so da kaunan junan su sosai.
Yasan merry ba yarinya bace ko zai girmay mata da kadan ne a wurin shekaru sai dai hakan ba illa bane idan akwai so da kaunan juna.
Auren shi da merry yanzu shekara hudu ke nan sai bana tayi ra,ayin haihuwa don a ganin ta ya kamata su zama iyayye a lokacin.
A karshe dai daya gaji da tunanen sa sai yaga bai kyautawa merry sa ba a yadda suke akwai fahinta mai karfi a tsakanin su sai dai bai san dalilin ta na rashin son zuwa gidan shi ba.
Gashi ita tana zuwa wurin nata iyayyen sun shirya da sukaga bata sake akidar taba na christanci dama su shine damuwan su.
Haka dai yai ta sake sake a zuciyar shi har barci barawo ya sace shi ranan washe gari bayan ya gama abinda yake yaga har lokacin baiga merry ba yasan fushi take akan maganan su ke nan.
Ya shiga daya dakin da take a ciki don idan tayi fushi haka sukeyi ko shi idan yayi fushi da ita.
Tana kwance fuskan ta yana kallon daken din dakin ya shigo har inda take a kwace din yana fadin kin dai san condition din da kike a ciki da kikai wanan kwanciyan yanzu.
Ta dago ido tana kallon shi yana tsaye ya harde hannayen shi a saman kirjin shi yace ko ba zaki gyara bane in gyara maki.
Sai lokacin ta gyara tana fuskantar shi ya samu wuri ya zauna a gefeb gadon yana fadin ban san may yasa kike son yanke alakata da iyayyena da yan uwana ba.
Ke baki tunanen lokaci yayi da zan fuskace su akan matsalan auren mu da basu san nayi ba don unborn baby din mu dake zuwa ?
Ko kina son baby mu yazo ya samay mu a wanan halin na rashin wani nasa daga bangaren mahaifan shi ne ?
Kai ta girgiza don jin abinda ya fada wanda tasan gaskiya ya fada ta bude baki da kyar tace a a ba haka nake nufi ba dear.
Ina dai tunanen kamar in ka tafi ba zaka dawo gare mu bane kuma idan suka san da zaman mu a wani matsayi zasu karbe mu can.
Yayi murmushi yace ina son ki gane idan naje gida nasan zamu sasanta da iyayyena akan abinda muka dade muna boyewa gare su nasan surely zasu fahince ni.
Don aure nayi ba zaman banza nake dake ba and nasan halin iyayyena duk abinda nake so suma zasu so abin nan.
So zama haka a cikin duhu ba zai yuyu akan mu ba, idan naje nasan babu wani dogon matsalan da zamu samu a gare su matukar na zauna nayi masu magana ta fahinta akanki.
Sai lokacin mery ta danji sanyi a ranta taga zuwan nashi yana da amfani gare su matuka ta tace yanzu na gane na fahince ka amma kabi sannu kada kazo kaje a samu wani matsala kuma ya biyo baya.
Yace kada ki damu da wanan ni nasan yadda zan fito masu da zancen ba tare da an samu matsalan komai ba.
Da haka dai ya ciwo kan merry din har take ta faman taya shi shirin tafiya gida da zaiyi ba tare da an samu matsalan komai ba a tsakanin su don kawai unborn baby din su ya samu saki a wirin dangin mahaifan shi shima.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button