NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:04 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM WA, RAFANAHUM MAN KANA ALIYAN, , , , , ,

Koda Alhaji ya fito inda yake jin yayan bakin natsu ya tsawata tare da tambayan ba,asin maganan a daidai lokacin Amma da mama hadiye suma suka karaso gurin.
Kowa ya kasa magana suna tsaye cirko cirko kowa na hadiyan zuciya ya kara maimaita tambayan shi gare su a dan fusace yana kallon su.
Mamu tace akan dai maganan diyan ta ne da tayi min iyaka dasu yanzu ina zaune sai ga umar ya aiko yace matar tana son shan koko shine na dama na aika mai a gurin gwaggo.
Ina zaune sai gashi ya shigo yayi min godiya sai muryan su mukaji a kofa tana auna min zagi wai harda fadin ina son in cusa mai wanan yar sayadi ne zan kammale ta kan diya da asiri Alh may ya kawo fadin haka udan yaya ta san kanta.
Har take hada sayadi da umar wanda yake matsayin uba da wa a gareta.
Wanda za a iya zuwa gutin shi neman auren yarnan watarana amma saboda, , , ,
Muryan Alh ya katse ta da fadin idan ya aure ta laifi ne ko sharia bai yarda da hakan bane ke kika haife shi ke kadai da zaki hanashi hurda da mutane na.
Maimuna kanwatace kuma matana kinga yana da daman zuwa neman taimakon ta ta ko ina ke kuma da kike zancen Sayadi ya juya gurin mama har kina fadin wai kanwarsace ko yarshi addini ya hana ya aure ta a hakan ne ?
Ko addini ya yarda ni ba zan taba yarda da wanan bakin hadin ba muddin ina raye ai da gurin kwarai mutum kewa nasa fata ba jeka ka dawo ba.
Daga hjy har mijin basu taba tsamanin wanan kalamin daga bakin mamu ba uwa ke nan kowa yana son nasa zata iya taka kowa akan danta in dai uwace.
Amma tace ai bakin alkalami ya bushe don aure a tsakanin su ba fashi ko da bamu raye kuwa .
Wanan wani irin hauka kuke muna a gida na safe daban na rana daban haka da dare yanzu da kuke fadan nan ina shi wanda kuke fadan a kanshi yake.
Ke jummai har kullun wai baki hankaline da sanin ya kama may yasa idon ki yakan rufe akan diyan ki ne ?
Ina kara ne hakan da babu mai kulasu a gidan nan irin haka rayuwan ki zai maki dadi ne a mayar maki da diya bola dasu da babusu duk daya a gida.
Ai mai son ka tsakani da Allah a yara kake ganewa ni wanan jidalin naku ya isheni wallahi kawu yace hajiya ki barsu zanyi maganin su ga badaya tunda kowa ya koyi rashin hakkuri ga dan uwan shi.
Mama hadiye dake tsaye takaci ya hanata magana tace ina yanzu ya baro wurin kakanshi yace zai je ya gaida maman su yazo basu bude part ba shine yazo gutin hajiya su gaisa ya shiga gurin maimuna ne ashe ?
Nima ina kwace maryam ta samay ni da zancen yaya raina ba zai baci ba ace kana gida danka ya dinga nuna ma halin ko in kula sai kishiyar ka.
To kin gani wata kila ya kara samun wurin a rufe ne ya nufi gurin maimuna din maryam kin zama hadasana a gidan nan.
Kawu yace sunan take ne wallahi halin maryam.ya isheni hajiya mai ake da munafuki a wuri duk wani fitina da zakiji maryam ce ta hada shi a gidan nan.
Ke nan nice munafuka kake daukana hjy jummai tace kece kan don ke kika zo kika samay ni dazancen don ban san ya shigo ba.
Amma nima aikin samay da zancen may yasa nake basu fuska kada ta lalata min tarbiyan yara na nace maki idan mun ma Umar hakana bamu kyauta mashi ba bukatan taimakon mu yake so kan matar shi yanzu.
Wiki wiki maryam tayi da ido tana fadin kai maimuna ashe ke munafukace haka ke rufamin baki munafukar banza da wofi kin hada wanan kinji dadi ki kara gaba ki gani idan zan kyale ki kawu yace.
Sai dai koda suka bar wurin sai maganan da akaiwa mamu ta baibai ya tsaya mata a rai duk aunin tana faman tunane nikan ina ta sharan barci na don ba inda zan tafi ranan.
Sai biyu idan nayi sallah nake son zuwa kitso don hakane ban tashi da wuri ba a can dan gaba damu akwai mai mun kitso idan kuma ina jin kiuya in tsaya Aisha ta jagwalgwala min kaina hakana duk da mamu ta iya bata tsayawa yi min kitso sai naci sa,a take kwashe min kan wai na faye tsawon gashi ga yawa ita bata da lokaci takan ce min.
Har lokacin dana yi sallah nashirya don zuwa aurin kitson na fito na samay ta zaune a falo tana dunkulawa Fauziya kai nace mamu nima inzauna ki min tace banjin dadin jikina Sayadi kije wurin kitso zaifi maki.
Na dan turo baki gaba alaman fushi ina dan kunkuni na nufi hanyar fita waje a cikin tsawa tace min kyauta zasuyi maki kitson a can.
Na juyo ina fadin gun Aisha zanje tayi min tace a tsawace zaki zo ki karbi kudi kije inda za a kwashe maki dakyau ko sai na bata maki rai yanzu da wanan dunkulan da Aisha kan maki a kai ba kyau gani.
Ina Aisha zata iya kama maki wanan kan naki haka da kyau tana magana tana watsa min harara nace mamu a can sai nabi layi dole fa.
Ta kara daka min tsawa daya razanani na makale gefen labule ina kallon ta a raina ina fadin lalai yau mamu ba lafiya kan.
Bada ke nake ba ko taurin kai kika koya ban sani ba nace da sauri a, a mamu naga rana yayi ne dama ba zan , , , , .
Ke karbi nan ban nemi jin komai ba ki wuce kije shagon linda tayi maki kitso yanzu na iso da sauri na karbi kudin ina fadin na gode na fice da sauri ina mamamin maike faru da mamu haka take a hasale ?
Haka na fito kamar ina tsoron takawa da karfi ina tunanen halin da naga mahaifiyata a ciki na bacin rai kodai dazu da barci ya fara daukana haniyar da naji sun fara ne ?
Part din Amma na nufa a lokacin ko Aisha zata tafi mu tafi tare a zaune na samay su suna cin abincin rana nace Aisha zakije shagon linda wurin kitso ?
Tace yau kuma kin tuna da linda ne zaki wurun ta ?
Nace ban san may ya samu mamun mu ba yau na tashi na ganta a cikin bacin rai da nace tayi min koke ki min sai ta hauni da fada wai inje can ta kwashe min kai.
Amma dake zaune tana jin mu ta tabe baki tace mai ko ya samay ta banda halin nasu sukayi yau muna nan naji fada ya kaure a gidan.
Ashe munafukan nan ce maryam ta samu jummai da tsegumin taga sadauki zai shiga gurin maimuna.
Ita ko da bata da tunane sai ta taso da fada tunda bata girma hankali bai zo mata na tunanen may ya kaishi can ba.
Aisha tace kai maman su ikilima ita ko kunyan munafunci batayi may ye a cikin wanan halin don Allah ?
Nace ita mamu bata rabuwa mata da diya a zauna lafiya tunda tana da yaranta itama Ammace ta katse ni da fadin.
Don may zata rabu da dan dan uwanta akan wani dalili mara tushe can idan ta rabasu yanzu zata rabasu nan gaba ne da yake shirin zama surikin ta ?
Aisha tace suriki kuma Amma tace wayan gobe banda Allah abu suke basu tunanen gaba dan tsaban kishin tsiya.
Ni dai ban damu da zancen Amma ba don raina a bace yake ga halin da na ji ya batawa mamu rai har take son sauke haushi a kaina ga banza.

Hjy jummai ne a falonta tana zuwa tana dawowa ranta a bace kallo daya zakai mata ka fahinci halinda take ciki na bacin ran.
Su Aliyu dake zaune suna karyawa a lokacin don da dare sosao suka iso kano daga Abuja sunje can cika wasu takardu nasu ya dan kalli uwar yana fadin mama yau ko lafiya ?
     Ta juyo gare shi fuska daure tace kira min yayan ku.

Yace to ya dauko wayan shi dake gefe ya shiga neman layin yayan nasu kira biyu ya dauka yana fadin Aliya ya akayi ne ?
Bros mamace ke son magana da kai yace lafiya wani abu ya farune kuma ?
Ta karbe wayan a hannin Aliyu a lokacin tace sai wani abu ya faru ke nan zan kiraka ko ?
Kiyi hakkuri mama ba haka nake nufi ba .
Ta dan gyara tsuke fuska tace duk inda kake kazo gida yanzu ko a ina kake ina son ganin ka yanzun nan.
Mama gashi yanzu ina, , , , ,
Ban tambayeka inda kake ba umurtan ka nayi da kazo yanzun nan ina jiran ka tana fadin haka ta katse layin tare da mikawa Aliyu wayan shi.
Aliyu daya gama karanta bacin rai a fuskan uwar tasu yace mama kila yana wani gunne kin san yanzu aiki yayiwa bros yawa.
Ta katse shi cikin daga mai hannu tana fadin Aliyu ka fita idona tun kan na saba maka rai a wurin nan.
Habbib dai yana zaune sai cin abincin shi yakeyi bai tsinka mata ba kamar bai gurin a lokacin.
Haka suka zauna zurun zurun zaman jiran zuwan dan uwan nasu don suji abinda ke damun mahaifiyar tasu haka tayi mashi kiran gagawa hakan.
Da sallama a bakin shi fuskan nan a daure da baka ganin fara,an shi ya shigo part din yana bin su da kallo a yadda ya samay su zaune din tare da fadin lafiya dai ko ?
Sai Aliyu ne ya nuna mashi mahaifiyar tasu da hannu yana fadin muma dai haka mukaji kiran bamu san dalili ba bros.
Hjy ta dago rai bace da idanun ta da sukayi ja jajir tayi mai kallon ni ka raina tace babawo ashe ban isa da kai ba a gidan nan ?
Ni zaka mayar mutumiyar banza a idon mutanen gidan nan kana kokarin ka nuna masu ni ba kowa bace a gare ka yanzu.
Haba mama mai yayi zafi haka har kike wanan irin magana yanzu tace daga yau nayi maka iyaka da duk wata mace a gidan nan.
Ba maimuna ba kawai kowa nake nufi da hakan idan kuma kace bazaka ji magana ta ba you will see my worse a kan ka mara tunane kawai.
Akan wata yarniyar matarka can kake son take magana ta don kawai ka dadada mata rai niko nawa ya baci suna shigewa suna maka kulle kullen sheri kai baka sani ba wake yarda da mace idan ba kuba sakarkaru.
Ka shiga hankalin ka dani a kan maimuna da wani tarkace nata if i see you near her again i will show you my true clour.
Haba mama bros namiji ne fa ba mace ba Aliyu ya ce wani wawan mari ta yarfa mai da bai zata ba a lokacin sai da kowa na falon ya dago yana kallon ta.
Aliyu ya dafe gun don marin ya shige shi sosai har cikin ranshi ya jishi idanun shi suka juye a lokaci daya sukai kwamcin jini ya mike tsaye tare da mata kallon ni kika mara ?
Daga haka ya fice a falon rai bace dakin su ya nufa ya fara harhada kayan shi a ckin fushi.
Yana fita ta juya gurin Umar dake kiran Aliyu din tace kai kuma ka kiyayyeni don ina kyale ku kuna abinda kuka ga dama kada ku dauka tsoron ku nake ji hakan.
Kai har ka isa ka turo dokan dana sa a kanka kake gani yanzu daga yau ina son ku sani ban magana yaro ya ketare min zance na a gidan nan.
Amma mama kan wanan maganan kika mari Aliyu haka a gaban kowa mu har da kannen sa ta daga hannu zata mare shi habbib yace kada ki soma mama is enough don Allah mama may ke damun ki yau marin bros wani fitina ne babba a gare mu.
Waye shi da ba za mare shi ba ko a gaban kowa da zaice zai fada min abinda ya dace dani mama wanan kuskure kike a rayuwan ki.
Kan maganan ku na kishi bai kamata ace kina sakamu a cikin shi ba ko salma da take mace ai bai dace su shiga zancen ku ba balle mu.
Irin haka ke sa muna nisa dake wallahi ni badon Aliyu daya matsa muna kan lalai sai mu dawo gida ba babu abinda zan dawo inyi a nan yanzu din nasan abinda zamu dawo mu tarar a gidan.
Haba mama yanzu ai mun wuce wanan hukuncin haka a gare ku idan kina muna haka ta yaya na bayan mu zasuga girman mu tunda a gaban su kike muna komai ni wanan zuwa gidan Allah ya gani banji dadin shi ba wallahi .
Dama nasan kai fitsarare ne sai ka zo ka rama mashi marin tunda kaji zafi abinda nai mai da bakazo ba kaga sakona ne.
Zai kara magana Umar dage gefe kanshi a sunkuye sai idanuwan shi da ke fitar da kwala ya daga mai hannu yace habbib mamace ka kyale ta tana da iko da daman yi muna duk hukuncin data ga ya dace damu idan mun kauce hanya.
Ya juya wurin ta yace Allah ya huci zuciyar ki mama shike nan ina iya tafiya ya fada murya a sanyaye.
Tace kadai ji abinda nace yace na gode ya juta ya marawa habbib baya daya riga da ya fita kafin shi yana kiran sunan habbib din.
Kafin ya kai Aliyu ne ke fitowa jaye da jakar kayan shi ranshi a bace ya nufi hanyar fita gidan da sauri suka nufi gurin shi .
Daidai da fitowan mu da Aisha zuwa gurin kitso ke nan muka tsaya muna kallon su don dagani ba lafiya ba dai kowa ranshi a bace.
Ban san lokacin da Aisha ta sulale ta kira Amma ba saboda kallon yadda suke faman rike dan uwan nasu da sukeyi yana fisgewa sai jin muryan Amma nayi tana salati tare da mama hadiye Amma na fadin yau may zan gani haka a gidan nan ?
Haka yasa na juya da sauri inda nake jin sautin muryan nata ina kallon ta tana sauri ta karasa gurin su.
Mama hadiye sai kokarin kiran kawu a waya takeyi a lokacin may haka kusan yaki may ya hada ka da yan uwanka da alama kokarin barin gidan kake gadanga kusan yaki.
Da kyat habbib ya buda baki yace bada mu yake fada ba tsohuwa da maman mu ne ya dau zafi.
May kuma ya hada shi da uwar taku tana kokatin kama hannun shi da umar ya rike suna kallon juna sai dai ya kasa magana a lokacin don zafin ran da yake ji.
Ina jummai din mai tayi mai haka naga kamar kwancin jini a idanuwan shi dukan ka tayi komay haka ?
Umar ne ya yi karfin halin bata amsa yace dan matsala aka samu amma shine ranshi ya baci yake shirin tafiya wai.
Ta kara rikeshi da kyau tana fadin ji nan gadanga ba, a fushi da iyayye fa daga yau ka daina hakan kayi fushi da uwar ka har kace zaka bar gida.
Ka nuna mata abinda tayi ma yai maka zafi ke nan ko may laifi ne idan iyayye suka tsawata wa diyan su baku gani ga mahaufin ku har gobe bai wuce fada a gurin mu ba ai.
Ina yake shirin zuwa muryan kawu ya na tambaya a hasale yana kallon Aliyu din a lokacin kam kowa na gidan yana waje har Ahmed da suka shigo da kawu din.
Kawu ya kalle shi yace maida kayan ka ciki kafin muyi magana ba musu ya juya da kayan zuwa part din su daga haka bai fito ba ya samu wuri ya zauna.
Kawu ya juya gurin umar yace umar faruq kaine babba kayi kokarin koyar da yan uwanka hakkuri .
Kana kallo yana irin wanan tabargazan haka a gaban kannen shi da kowa ba kunya wai gida zai bari.
Daddy kuyi hakkuri abinda muke lurar dashi ke nan kuka iso nan yanzu yayi kuskure ba zai sake ba insha Allahu.
Ku tafi bayan sallah magariba ina neman ku dukkan ku har iyayyen naku kawu yace yana wuce wa abin sa suka amsa da Allah ya kaimu daddy.
Daga hakan kowa ya watse cikin shi cike da gulma don ba wanda yasan mafarin maganan sai su yasu yasun su yan part din.
Umar kan fita yayi gidan yayin da habbib ya samu Aliyu a dakin shi yana kara bashi hakkuri kan kuskuren da yake son tafkawa.
Hjy jummai tana part din ta bata fito ba bakin ciki nadama damuwa da tashin hankali sun ishe ta a lokaci daya ta rasa inda zata dafa taji sanyi a ranta lokacin.
Don tana ganin yaran suna son sufi karfinta a lokacin don irin yadda take ganin take taken su a lokacin.
Amma kan dasu mamu da mamaki a ransu kowa ya shiga part din shi suna mamakin abinda yai zafi haka har ya jawo wanan matsalan.
Mun bar gidan tun kan su bar gurin muna hanya umar yazo ya wuce mu da motar shi lafiyayya mai daukan ido.
Aisha tace sukan masu kudi nan najin dadin su kiji wanan motar kamar a baka ka lashe don kyau na kalle ta nace ke motar yayan su salma ne fa baki ganta a kofan gidan mu ba aje da zamu fito.
Tace bata kula da motar ba ai yanzu shine a wanan hadadan motar nace sai dai babu matar sakawa a motar ba .
Kin kashe masa mata ne Aisha ta tambaye ni cikin kallona nace wanan arniyar zai nuna a matsayin matar shi idan ba don baida kunya ba.
Tace A ruwa kin san abinda ya daure min kai naso fa inji abinda ya hada yaya Aliyu da maman su har sukai fada haka wanan matar mai son diya kamar ta mutu balle tana ganin su sun zama taurari.
Nace wallahi niko haushin su Amma naji da suka hanashi wucewa don dai kawai ranta ya kara baci kamar yadda tasa Mamun mu bacin rai yau.
Ke muguwace Aruwa idan tsiyan ki ya tashi idan an barshi ya tafi wa yasan halin da zai shiga a can kilama ya wuce inda ya fito a daina jin labarin sa.
Nace to wa ya damu dasu dama mutanen da basu taimakawa iyayyen mu uwar su kawai suka sani ni kin san karin takaicina dasu tace a, a sai kin fada.
Nace yadda suke kiran mamu da sunan ta gatsau hakana kai tsaye ai ko banza taci hjy ko gwaggo a wurin su dai.
Tace ba mamaki fa hjy ce ta hana su kirata aiko su salma haka suke ce mata wani lokaci yanzu dai ne naji suna dan cewa maman fauziya din.
Wallahi duk ranan da suka kira sunan mamu a gabana sai naje gaban uwarsu ince ke jummai kaza sai ta kai min duka a kafada tace zaki iya shi shago ina son ki wurin jidali ai.
Haka mukai ta shakitanci a kansu har muka isa saloon din bamu dawo ba sai gab da magariba muka shigo gidan yana tsit kowa na dakin sa nasa ya damay shi a rai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button