NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Zama nayi yau na dauki kwalliya mai daukan hankali don yau ina son kaiwa yan uwan mamu ziyara tunda na haihu ban fita daga gidan ba sai yau duk dako yaya bai hanani fita inda nakeson zuwa.
Nafisa na zaune muka fito falon tun ina saman steps take bina da wani irin kallo har na sauko kasan inda suke zaune.
Da sauri fauziya dake fitowa daga dakin su ta zo ta karbe Abbati a hannuna tana fadin wai anty yaron nan fa girma yake karawa a kullun.
Tana zama a gefena da yaron a hannun ta take fadin hakan lokacin duban yaron Nafisa tayi take fadin na rasa wa yaran nan ke kwasowa da kyau haka kamar diyan larabawa dasu.
Kallonta nayi ina fadin Nafisa ke nan gashi kin fada dole suyi kama da su tunda suna da jinin su a gauraye dasu.
A daidai lokacin ne maria ta fito da sauran a cikin shirin su tsab suma ta bisu da kallo tana fadin wallahi dole yaya yaji dake har ransa ko don wa yan nan yaran Fatima.
Yara haka sai daukan ido a duk inda suke shiyasa nake fadawa shiyasa nake fadawa hjy ta bar yaya da iyalin su a kullun ko wani ahali ba a son rasu sukan rabu ba indan kaddara ta gitta masu.
Yanzu gashi ke baku rabu da yaya a yadda take so ba yanzu gashi batayi nasaran rabaku din ba ita da shekarun ta daddy ya hasale mata auren shi a kanta.
Na dago kai ina fadin Nafisa kin san abinda kike fadi kuwa yaushe wanan magansn ya faru kike furta hakan yanzu.
Wallahi Fatima anty salma ta dade tana min nasiha kan mu bar biyewa halin mama don shi kanshi yayan mu ba zaiji dadin halin da mama take sa muna nuna maku ba tare da laifin komai a garemu ba.
Ita dai anty salma ai ta huta da bata tsaya bin halin mama yanzu kinko ga ta zauna a dakinta lafiya ba wani tsangwama a yanzu.
Ga yaya ya ttaimakawa rayuwanta yanzu idan nayi magana ko ina son yayi min wani abin sai yace dani inyi aure kamar yadda yan uwana sukayi.
Fatima yanzu ta ina zan fara neman wani mijin Manir ne mun bata dashi kin sani tun kuna can ya dawo mu shirya mama tace bata yarda ba don ba zata bari taji kunyan mutane ba tunda har ya iya bata min suna a gaban kowa.
Amma har idan kina son shi har yanzu Nafisa mai zai hana ki fadawa yayan ki don nasan yaya zai fahince ki idan kin fahintar dashi gaskiyar maganan.
Shine kawai zai iya shawo kan wanan maganan har kowa ya yarda da shawaran shi in Allah ya yarda don yaso ace an hada auren ki dana Murja a lokaci guda.
Tun wanan dan hiran da mukayi da Nafisa dana lura abin duniyane ranan ya dameta tana neman abokin shawara har ta dan sake layin hjyn su garebi.
Munje gida anty don gaida ita tunda ta dawo daga kasan su bamu samu zuwa ba sai itace ma tazo inda nake dana haihu ta duba jikina.
Ina tambayanta yaushe su mamu zasu koma Nigeria ne take fadin suna son sai sunyi aikin hajjin banan nan a tare da ita zasu mayar da ita gida.
Nafisa kan sai mamakin irin arzikin su takeyi ga gidan babba ko ina yan aiki ne birjit a gidan kamar suna zaune a kasan su .
Ni kaina lokacin dana fara ganin su haka nayi mamakin abinda yasa har ta bude saloon ake mata aiki.
Take ce min ai ba a son mace ta zauna ba dan inda kudi yake shigo mata ko yayane ya kamata ace mutum yana da dan sana,an rufin asirin shi don ba komai ne zaka roki namiji ba ka samu kai tsaye.
Yini mukayi sosai a gidan mun sake jiki don irin yadda matar gidan take jan mu a jiki gaba dayan mu har Nafisa.
Da yamma muka dawo gida bayan mun dan kebe da anty ta van sakon da dama nazo karba wanda kakata ta bayar a kawo min ta hannun su.
Baya nayi wanka na kwanta ne sai kuma tunane ya dameni don yau kusan kwana biyu ke nan banji kira daga yaya ba.
A take zuciya mai nashe nashe ta nasa min cewa ina zai kiramu yana can yana cin amarci da amaryan shi shike nan ya gama da mu nan ke nan .
Naji wani irin kishi ya rufe min zuciyana kamar yadda ko wace mace take jin wanan yayin da mijin ta yai aure.
Da kyat na samu na yaki zuciyana kan irin yadda nakeji din a raina na samu har barci ya dauke ni hakana.
Haka yasa washe gari na tashi da wani itin bakin rai a zuciyana kin ma fitowa nayi daga dakin ga baki daya ina kwance inata faman tunane a raina.
Ina kwance a hakana wayana ya dauki ringing ina kallo yai ringing har ka katse ban dauka kira kusan uku yai min naki daga wayana a lokacin.
Sai ga Nafisa na doka sallama a kofan dakin nawa wanda tun zuwan ta ban taba yarda ta shigo min dakin ba sai yau da dan uwanta yace a bani waya muyi magana dashi ta wayan ta tunda ya kira ban dauki wayan ba.
Bayan ta shigo da sallama na karba mata take fadin barci kikeyi ne dama nace ma yaya ina zaton hakan ai.
Tana magana take miko min waya idanuwan ta kuma yana yawo a kusurwan dakin da take bi da kallon mamaki sosai.
Dama tayi zaton hakan don ganin yadda aka tsara dakin yaran dana su maria tasan namu abin kallone shi.
Na duba wayan har lokacin yana kunne bai kashe ba nayi sallama a hankali ina sauraren shi.
Ina kike ne haka waya yana ta ringing baki daga ba nace ina daki kwance ya dan ja tsuki yana fadin wanan ai halin banzane ka bar waya anata kira baka daga ba.
Idan da dane cewa zanyi dashi yayi hakkuri sai dai yau baiji hakan ba don amsawan ma sanyaye nake amsa mashi magana.
Yace ya yaran da kowa da kowa a gidan nace lafiya a takaice yana jin hakan ya kashe wayan abin shi na mika ja tsuki don Nafisa tunda muka fara magana tabar dakin.
Runtse idanuwana nayi ina anyana yadda yake cikin annashuwa a can da amaryan shi muko muna nan.
Sai zuwa yamma na samu sa,ida a raina ina fadin wai me nakeyi haka zan bada kafan da Nafisa zata samu wani abin fadi a tare dani.
Mikewa nayi na shiga wanka na fito na shirya a daidai lokacin da yaran suka dawo gida suna zaune a falo suna cin abinci na fito.
Da murnan su suke gaidani ina masu sannu da dawowa na zauna a tare dasu muna hira sannu a hankali nake jin dan sauran abinda nake ji yana gushe min a raina har yakai na daina jin komai a yanzu.
Banda in ba yarana kullawan daya dace su samu tarbiya ingantattace a gurina na watsar da duk tunanen wata kishiya don tarbiyan yarana yanzu shine a gabana kawai na yanke shawara a raina.
Zaman mu da Nafisa a dan kwanakin ba laifi don mun gama fahintar halin ta muna binta dashi saidai ban yarda rainin wayau yana shiga tsakanin mu ba don kada taga kafan yi mu hakan.
Sam ban yarda wani rainin wayau yana shiga tsakanin mu ba don ba dogon irin wasan nan a tsakanin.
Ko zama wuri daya don bakuntar da tazoyi munane har muke dan dasawa saboda nasan bata da dadi salma ta fita dadin sha,ani.
Komai da aka ban ina amfani dashi kamar yadda sukace din nayi amfani dashi haka ya jawo min saukan wani ni,ima da kyau a jikina.
Wanda ni kaina na hango hasken sirin abin a yana haskani yana kara min wani irin dau kaka ga duk wanda ya ganni a lokacin.
Don ko zama nayi na bar wuri zan barwa wanda zai zauna bayana kamshi da tunanen sirin kamshin.
Ga yarana yanzu sai wani irin kula na musanman da suke samu suma sai baiwan su sannu a hankali ya fara haskawa din.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:20 – ????????????: Suna zaune su uku a falon mahaifinsu sai mahaifin nasu dake dan kishingide yana sauraren bayanin kowanin su daya bayan daya tundaga kan Umar har habbib da Aliyu.
Baiyi magana ba har zuwa wani lokaci saida ya fahinci sun gama fadin abinda ke zuciyar su yana gyara zama yace.
Da fatan dai har zuciyan ku kusan banda laifi a cikin wanan magana don nine na aje jummai a gidan nan ba ita ta ajeni ba kamar yadda take tunane.
Na fahinci abinda kowanku yake ji a ransa game da wanan maganan sai dai kule tunanen haka don ita a bangaren ta hakan bawai ya dame ta bane.
Yau ankai har jimmai tana tunanen zatayi jayayya dani a gidan nan kan naba dan dana haifa umarni yabi take ganin ban mata daidai a rayuwan ta.
Sai yaushe zata gane niba makiyin ta bane wai idan bamu taru mun rufawa kanmu asiri ba a yanzu sai yaushe ake tunanen zamuyi hakan.
Sam a yanzu banga laifin jimmai ba don nine da sakacin dan na bata dama har ya wuce yadda ya dace ace an sakewa mace shine ya haifar da illa a tsakanin mu yanzu har jimmai take daukan kanta a matsayin miji nina koma mata.
Daddy hakkuri zakayi itama mams tasan bata kyauta ba abinda tayi a yanzu don duk wanda yasan gaskiya yasan babu gaskiya a cikin maganan nan.
Daga baya ke nan Aliyu don yanzu bukatan ta ya biya idon ta ya bude ko tunda tayi yadda take so ta nunawa duniya ban isa da danta ba.
Allah sarki daddy kada kayi tunanen hakan garemu don mu bamu da wanda ya fika a gare mu sai ita mama.
To aikai malam umar abinda take tunane ke nan take ganin ban isa ba gareku ta matan a karshen ikona take zaune.
Daddy a daiyi hakkuri a yafe wanan magana tunda har abin ya rigada ya faru sai a hakkura hakana a yafe.
Ai habbib idan kaga na janye sakin dake tsakanina da jummai a gidan nan to ta bi umarni ne shine za,a zauna lafiya dani don bata isa tace ni ban isaba ga idon duniya.
Shiru gaba dayan su sukayi falon don sun san idan yai irin maganan nan har cikin zuciyar shi yake nufin abinda ya furta.
Don kawu mutum ne da zaka dade kana mashi abu bai tanka mutum ba amma ranan daya tanka sai ran kowa ya baci a gidan.
Daddy a dai kara hakkuri don Allah wanan abin bamu jin dadin shi wallahi gashi yanzu muma muna da iyalan da zamu koyi da wasu halaiya naku a yanzu.
Tabbas hakane habbibu shiyasa ma nake son nuna aini ba lusarin namiji bane kamar yadda ta dauke ni .
Har zance ga abinda nake so ga dana yau jimmai ta fito a gaban jamma, a tace ban isa da abin nan ba ai kaga haka ba dadi ko.
Kowan su ya kasa magana sai can Umar yace daddy zamu tafi don wanan maganan yana son fin karfin mu ba zamu iya sasanta tsakanin ku ba.
Umar meye laifin ku a cikin maganan nan jimmai tasan da sharadi na ta zabi barin dakin ta don ta farauta ran yar uwarta na zumunci.
Zumuncin ma daga sama don ba zan matan da lokacin tafiya ku waje ba naje lagos kan mutumin nan ya taimaka min sabuwa da kanta ta hana shi ya taimaka sai barene can daban taba sani ba ya taimake mu.
Wai yau wa yan nan mutanen Jimmai ta jawo min cikin a hali har ta zabi farin cikin su da nats nan gaba me kake tunanen za,a yi a gidan nan idan ina lamuntan haka na faruwa tun yanzu.
Gaskiyane daddy na fahinci abinda kake ji kuma kake nufi a kan wanan magana zamu zauna da mama mu fahinci juna yana fadin haka ya mike sauran ma mikewa sukayi suna mara mai baya bayan sunyi sallama da mahaifin nasu.
Tuki yakeyi hankali a tashe gabaki dayan su cikin motan babu wanda ke iyayiwa wani magana sai faman sake sake suke a ransu.
Nauyayyan ajiyan zuciya Habbib ya sauke lokaci guda yana fadin yau danine a matsayin ka bros yarinyar nan ba zata kara kwana min a gida ba.
Don ba zan yarda kan auren wata mace na uwana ya mutu ba ga banza ni bansan abinda mama take nema a gurin wa yan nan mutanen marasa mutunci .
Don naji ana fadin ko wurin bukin wullakanci suka so yi mata a lokacin salma ne tare da wasu suka taka masu birki.
Duk maganan da yan uwan keyi a motar Umar baiyi magana ba har lokacin gaba dayan su sun fahinci baya cikin dadin rai a lokaci.
Gidan shi ya nufa inda suka samu mahaifiyar su saidai sunyi rashin sa,a tana da baki yan uwanta sun ziyarce ta a lokacin.
Suna jin muryan su da kalaman su har inda suka tsayar da motar su part din mu suka shiga kai tsaye har lokacin ba wanda yake iya yiwa wani magana.
Mama Asma,u dake ta wajen kofa tana wayane taga shigowan su gidan har shigan su part din akan idon ta haka ya bata daman sace jiki zuwa wurin su ba tare da yan uwan nata sun sanda haka ba.
Ta shiga wurin su suka gaisa ta danyiwa umar din murnan aure da yayi sai kuma ta kare da fadin saidai kuma wanan abin bai kawo kallo ba.
Ace sanadin wanan auren yaya tabar nata dakin da tai shekara da shekaru a cikin sa haka bai taba faruwa a tsakanin su da Alh ba sai akan wanan bakin auren haka.
Don mu auren baki yake a gurin mu don shine sanadin wanan abinda ya faru saidai yannen nawa basa son gaskiya don basu lurar da ita gaskiya sai kara dulmiyar da ita sukeyi.
Mama mun sani shine abinda ke kara daure muna kai ace da girman su mama wanan abin yake faru haka ko yaushe a tsakanin su.
Yanzu sun tsameni cikin al,amarin su zasuyi abu ban sani ba don fadin gaskiyana danake masu yasa ake abubuwa bada sanin nawa ba.
Ko wanan auren naka ban san dsshi ba sai ji nayi daga sama don ban dauka abune da zai yuyu ba a tsakan zurian mu dasu.
Sai gashi ashe har hurdi Alh yayi mata amma yaya ta rufe ido har ta yarda wanan abin ya faru tsakanin su haka.
Yau ma din ninaje gidan mahaifin naku dan in mata ban gajiyan buki sai hjy maryam ke dan tsegunta min abinda ke faruwa wanda banji dadin hakan ba.
Naso ganin Alh aka ce min bai tashi ba yana kwance har lokacin haka yasa na shiga neman inda yaya din take nazo.
Saidai banji dadin zaman ta a inda na sameta ba don tun yanzu an fara samun matsala don yarinyar bata son zaman yaya a nan din.
Gidan ubanta ne nan din da bata son hakan habbib ya fada rai bace cool down mana habbib, umar ya fada yana kada kafan shi cikin takaici.
Don shi kadai yasan yadda yakeji a lokacin wayan shi daya dauki kara ne ya tsaya dubawa cikin mamaki yayi received din wayan yana mamaki a ranshi na kiran danayi mai na bazata.
Haka yasa ya fara tunanen wata kila wani ba lafiya ko wani abin ya taso tasa nake neman shi a layin shi sai ya dauka yana fadin .
Zahra ya lafiya ko tambayan nasa ya bata min rai saidai na dake ina fadin lafiya kalau yaya mu kiraka ne kawai muji lafiyan ka gasu Abdul suna son jin muryan ka na fada a kunyace don Nafisa na gurin zaune tare damu ta kura min ido tana sauraren mu.
Ya dauki lokaci yana waya da yaran shi hankali kwance yayin da su mama Asmau suke dan tataunawa dasu Aliyu kan zancen da sukeyi da farko.
A karshe yace suba maman su waya duk a cikin harshen turanci yake magana dasu nice mai dan kokarin koyawa yaran harshen hausa don kada su taso basu iya ba.
Saiko zuwan fauziya yanzu ba karamin taimakona zuwan yarinyar yai min ba lokacin.
Na karbi wayan ina sauraren shi yace i miss you Zahra how far ya Abbati na amsa a sanyaye da muna lafiya ya Amaryan ka kuma ?
Dan murmushi yayi babu amsa yana tambayana baku dai da matsalan komai ko ko a turo maku kudi zaku sai wani abin ?
Babu abinda zamu saya yaya we are ok mun gode yace take care of your self and the children nace in sha Allahu yaya .
Kaima ka kula muna da kan ka yana fadan hakan mukai sallama na kashe wayana ina jin zuciyana ba dadi a lokacin.
Badon komai bane sai don tunanen shi can yana more rayuwan shi da wata mace can ta daban mu muna nan ya barmu a cikin maraicin shi.
Gashi ba lafiya nake dashi ba don ban gama helling a jikina da akai min aikin wurin cire baby har yanzu ban gama warwarewa ba sosai.
Da kyat suka samu zama da mahaifiyar su kan hujjan da mahaifin su ya kafa game da komawanta dakin ta.
A take hjy ta hau fada inda take shiga ba nan take fita ba karshe ma sai nuna masu tayi ai mamune ta jefo masu bakin asiri daga can har haka ya kasance a tsakanin su.
Kai amma dai mama idan wanan halin zaki ci gaba dayi gaskiya akwai matsala babba don kina daukanwa kanki nauyi ne.
Ina wanan maganan kin san shi tun kan ayi auren nan da kika matsa ayi din kin amince da hakan ke nan .
Yanzun kuma zaki dauko wani zancen daba shi ba mama ki dora kan matar da bata ma san anayin wanan abin ba a nan.
Wai kai habbib haihuwana kayine ko me da kake kokarin nuna min kuskurena a kowani lokaci na dauko zancena.
Mama kiyi hakkuri abinda kikeyi ne wani lokaci ke kanki kinsan ba daidai bane sai kuma ki yarda shedan ya rudeki a ciki.
Don Allah mama ki bar wanan yarinyar ta koma inda ta fito tunda dai itace duk ta jawo wanan matsalan a tsakanin ku da daddy .
Inyaso mu lalaba daddy ya hakkura ya mayar dake dakin ki don Allah wanan abin kunyan ya, , ,
Habbib kabar falon nan tun kan na sabawa rayuwan ka anya kuwa yaron nan baya shaye shaye zaman shi a turai tana magana idon ta yana kan babban nasu umar.
Dan murmushi yayi yana dagawa habbib hannu yace bai shan komai mama halin turai dai ya kwaso na fadan gaskiya ga ko waye idan bukatan hakan ya taso ayi.
Mama gaskiya yake fadi don a kan auren wata can ba zamu taba yarda ke naki auren ya samu tangarda ba muna kallo.
Nan ko ta hau fada tana fadin na gane yan uwanane baku kauna a tare dani don an riga da an zuga ku akansu.
Don haka ku barni da yan uwana komai zai faru ya faru ba matsalan ku bane.
Ta mike har takai kofa ta juyo tana fadin kai kuma babawo sai ka shirya shiga gurin amaryan ka don ban fahinci manufar ka ba na kin shiga gurin ta.
Nan dai shima aka haushi da fada da tashin hankali da kyat ya samu fada mata mama zanyi yadda kikace insha Allahu .
Tana fita daga falon ta nufi hanyar shiga part din tun daga nesa ta hango part din a saye har takai ta tura kofan taji shi a rufe.
Da mamaki ta dan tsaya tana buga kofan shiga part din har ta gaji ba wanda ya bude kofan mamakine ya cika mata zuciyan ta lokaci guda.
Ta rasa yadda zata fassara wanan abin ko dai yarinyar ta fita unguwane bata sani ba.
To waima wani unguwa kuma yarinyar da bata wani kwanaki da shigowa gida ba har zata fara fita haka unguwa.
Tana tsaye tana wasi wasi a kofan daidai lokacin aka bude kofan dayan part din gaba dayan sune suka fito a part din kamar yadda ta barsu a ciki su uku.
Da mamaki suke kallon mahaifiyar nasu wace take tsaye a rakube kofan part din samira din a cikin damuwa.
Lafiya mama Aliyu yayi saurin tambaya yana isa gurin da sauri wallahi na fito kawai na samu kofan a rufe yanzu
Daga inda umar yake yace kamar ya kofa a rufe mama ya takowa zuwa wurin da take tsaye da mamaki fal a fuskan shi.
Yana zuwa ya fara dukan kofan a cikin wani irin hasala can yaji ana kokarin bude kofan habbib kan lokacin har ya kai wurin motar shi don shi haushin hakan bai bari ya tsaya jin meke faruwa ba a wurin.
Wata yar bakar yarinya ce ta bude kofan a hasale tana fadin wai waye ke damun mu da dukan kofa hakane don Allah anty tana kwance fa.
Tana karasa budewa sukai arba da umar dake tsaye a hasale cikin wani kakausar murya yace ke waya baki umurnin rufe kofa haka gidan nan ?
Ta fara dan inda inda tana fadin dama dama anty ce tace in rufe bata son damuwa zata kwanta.
Anty waye anty a gidan nan kuma ya tambaya da mamaki karara a fuskanshi da sauri hjy tace samira take kira da anty ai.
Yace a hasale common bude kofan nan kada kiyi gigin kara rufe kofa a gidan nan da rana yana fadin haka ya juya rai bace da sauri ya bar gurin.
Aliyu dake tsaye ya kalli mahaifiyar tasu yana fadin mama shiga a cikin wani irin sanyin murya yake magana rai bace shima.
Sun kama hanya gaba dayan su an rasa wanda zaiyi magana daga cikin su sai Aliyu ne ya iya fadin amma wanan yarinyar bata da kunya mamane ta rufewa kofa ko me ?
Ita ta rufewa mana baka san halin zurian hjy sabuwa ba ko wanan ma ai kadan mama ta fara gani wurin su.
Ka daina fadan hakan Habbib kamar baka damu da halin da mahaifiyar mu ke ciki ba don Allah.
Mama a yanzu idan ka kula dabara na kokarin kubce mata ne don in ka kula duk abinda takeyi ba a cikin hayacinta takeyin sa ba umar ce yana sauke numfashi.
Kaike daukan hakan yasa suke kokarin gara ka aiko shi daddy ya dawo daga rakiyan halin su ne yanzu duk wanan damuwa ne ke damun ta don bata taba zaton daddy zai iya mata haka ba gaskiya.
Ya juya wurin Umar da kyau yana fadin yanzu kaine zaka kawo karshen wanan matsalan gaba daya nake gani.
Hannun shi daya kare fuskan shi dashi ya sauke yana kallon dan uwan tare da fadin as how zan kawo karshen abin ?
Kwarai kuwa ya kara fada yana jijiga kai kafin ya fara fadawa dan uwan nasa maganan abinda yake gani shine mafita kan mahaifiyar tasu dasu nan gaba.
Gaba dayan su shiru sukayi kowa na nazarin zancen a ranshi can Aliyy yace kana ganin mama zata yarda da wanan hukuncin kada kuma wani abu ya biyo baya a karshe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button