NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:42 – ????????????: HASBUNALLAHU WANI,IMAL WAKEEL, , , , , , ,

Ke mai kikai mata salma ta tambaya cikin wani murya ba tare da na juyo daga inda nake zaune ba nace ai gata nan ki tambaye ta .
Cikin kuka take magana tana fadin wallahi dukana tayi fa anty sallama tace what ke kika duke ta fa ??
Ashe akwai tsiya yau a cikin motar nan nace ayi tsiyan mana wake jin tsoron ku wallahi kaf din ku ina iyawa daku na fada ina zare idanuwana gare su.
Ganin hakan yasa Aisha ta dan duka tana mata magana a kunne ashe fadi take kinga yarinyar nan salma akwai abinda ta taka tunda kikaji tana fadin hakan.
A cikin daga murya tace may ko ta taka a rayuwan ta Aisha yau sai na koyawa yarinyar nan hankali gobe ba zaki kara rashin kunya ba haka.
Driver daga inda yake yana tsawata muna amma baisa mun bari ba idan sun fada mi in fada masu mai zafin da yafi nawa daci.
Har motar ya tsaya muka fito tana kaimin dangwara a kaina a zikin zafi na rike hannun na murde ta ba tashin mu daya ba dasu suda sukai tashin gata daga falo sai mota ba wani abincin kwarai ake ci ba kuma.
Sai gata tana batun faduwa nan sauran yan uwan sukayo kaina da duka nima na haukace masu ina kai masu duka iya karfina sai duk suka dare.
Wani malami da abin ya faru a gaban shi ne ya kiramu mun fara mai bayani sai ya gane rikicin gidane muka kawo har school don haka ya kwashe mu sai wurin pc.
Sai da ya gama sauraren bayanin kowa yace mahaifin ku zan kira don wanan abin ba za a kawo muna shi nan ba ku lalata muna sauran dalibai da rigima.
Nan wurin ya daga waya bayan ya nemi layin Alh a addimition book ya kirashi sun gaisa ya fara mai bayanin komai yace ya bari gasu nan zuwa.
Ba,afi awa daya ba muna rusunne a cikin rana duka yan gidan sai ga Alh tare da Ahmed sun iso hankali tashe yake kallon mu.
Nan pc yayi mai bayanin komai ranshi ya bace ya juya wurin salma yace salma yaya akayi haka ya faru da girman ki bayan kece babba a cikin ku.
Salma a ina kika koyi wanan halin banzan na rashin tausayi da zage zage a bakin da har kike iya budan baki ki zaki uwar mutum a gaban shi.
Yana fadin a cikin yanayin bacin rai a fuskan shi karara kukan da salma keyi ne ya taba min zuciya naji ba dadi a raina nace don Alh a yafe muna mun yi kuskure Salma kiyi hakkuri.
Jin hakan yasa kowa na office din kallo na da mamaki har abokan fadan nawa saida na basu mamaki.
Nan dai akai muna fada sosai kada mu kara irin hakan nace a fada masu su bar zagan min uwa a gabana don ko gobe aka zagi uwata ba zan kyale ba Abba.
Yace ba ma za a sake ba sayadi insha Allahu na amsa da to Abba nan dai muka shige zuwa azuzuwan mu har munyi nisa na cin ma salma da sauri nace kiyi hakkuri sherin shedan ne .
Batayi magana ba sai kallona da tayi kasa da sama ta wuce abinta sai dai kafin mu bar school din har labari fadan ya karade school din ko.
Inda yan ajin su salma da yake siniors ne su suna gaba damu da shekara biyu don tana matakin karshe ne ita inda su Aisha su uku muke classmate class din mu daya da Aisha.
Haka seniors sukai ta shigowa suna ba punishement iri iri ranan sai dai duk ban dauke shi wahala ba a gurina nida na saba da wahalan samarin gidan baffa na .
Don duka da zagi ba wanda basu koya min wahalan shi wasu senior har zagina suke wai don ina da kyau nake son daukan kai wa mutane.
Nan dai yan matan ss suka kewayeni kowa na fadin albarkancin bakin shi a kaina wai ni da nazo gidan su salma cin arziki nake son in kawo masu rainin wayau wai sai inba salma hakkuri a gabanta in durkusa in taba takalman ta.
Muna cikin haka sai can naji wani na fadin kai ga dan rainin wayau nan ya tunkaro ajin nan kila wani dan gulma ya kai mai tsegumin muna nan.
Da sauri suka juya don ganin wa take fadi ganin mai zuwa tare da tawagan shi ajin sai naga sun fara natsuwa ni na dauka wani malami zangani sai naga ashe dan makaranta ne shima wanda ke sasu natsuwan.
Yana gaba makaraban shi suna biye a bayan shi su biyar har yan class din naga sun shiga natsuwa a lokacin.
Tsayawa yayi daga kofa yana kare masu kallo a raina nace shi kuma waye wanan din daya shigo suka wani kamay lokaci daya.
Idon shi ya sauke a kaina lokaci daya tare dan tsura min ido sai kuma ya juya gare su yana fadin may tayi maku haka ?
Da sauri wata ta juya tana fadin zagin Salma sani tayi don tana ta, , , , ke tashi don Allah yace dani sai dana tsaya kamar ba zan tashi ba ya sake fadin baki ji bane ya sauke min kallon shi dake girgiza yanmata a kaina.
A hankali na mike ina karkarde buje daya dan kwashi kuran wurin a hankali daga haka ya juya mutanen shi suka mara mai baya da sauri naga yan matan suna ficewa class din.
Suna fita yan aji sukayo kaina suna fadin ke kan kina da sa,a don yau sai sun dandana kudan su suma a wurin shi.
Ko a mota da zamu dawo gida inajin suna magana ta kasa kasa banda salma da har lokacin tana a cikin fushi sosai da kowa.
A ka,ida idan mun dawo da mun gaida mamu sai in kwabewa kanne na kayan school muje bayi in masu wanka daga nan sai in wanke uniform din mu.
A daidai lokacin ne Nafisa take fadawa hjy jummai abinda ya faru ai yarinyar bata karasa ba uwar ta mike tsaye zubur tace wace Fatima kuke magana dai ?
Wanan dai yar ta mamu data zo zataci gaba da bata labarin yadda abin ya faru uwar ta daka mata tsawa da fadin dallah rufa min baki .
Ta juya ta fita sai part din mamu ta shigo babu ko sallama mamu na zaune tana sakawa yara tufafi a jikin su sai ganin ta tayi ta shigo tana huci.
Da sauri take fadin hjy lafiya nagan ki a hakan shiya kawo hakan don yar agolan ki ta dakar min yarinya don tsaban rainin wayau.
Ashe dama da biyu da uku kika dauko ta gidan nan don tazo ta tayaki kishi akan yayan mu .
Hjy wanan wani irin magana zaki shigo min dashi haka ban san hawa ba ban san sauka ba asali ma wanan yarinyar tunda ta shigo bata fada min wani abu ya faru a tsakanin su ba yau.
A daidai lokacin na fito zanje inshanya kayan dana wake a kofan baya wanda ake bi ta kitchen din su a fita a lokacin na tsinkayi abinda hjy jummai ke fadi.
Tana gani na tace ehhe gata ma ke may ya hada ki da yaran gidan nan har kika iya daga hannun ki kika mari Nafisa.
Mari hjy har abin yayi muni haka dama bashi kika sata tayi ba zaki wani nuna baki san komai ba yanzu akai.
Ta sake juyowa inda nake tsaye tace tambayan ki nake samun aurin yar angola har yakai ta daki yaran gida kina tunanen ki zauna lafiya.
Nace cikin dan tsiwa uwa ta take zagi niko nasan zafin uwata shine na kwabe ta na bata amsa da hakan.
Eyye ke gaki mai uwa ko to an zagi uwartaki ko ita tai abin zagi ai zaginta za a yi balle ke agolan gida.
Hjy wanan maganan bai kamata yana fitowa a bakin ki haka ba naga dai yar nan kema dai yar ki ce idan ga kara ko.
Kin bari an kara maki ne da kika shigo da fankama da isa a cikin mu suna cikin hakane sai ga hjy maryam dan gara ita ta shigo da sallama falon saida ta bimu da kallo tace.
Yanzu ran nan ke fada min abinda ya faru dazu da safe ai naje can ban samay ki ba sukace min kina nan.
Ai dole inzo gutin wanan gitsaran yarinyar da aka jajibo muna a gida da sunan agola dama nasan shigowan yarinyar nan cikin zurian mu ba alheri bane gare mu gidan nan.
Hjy maryam tace nima abin ya bani mamaki wallahi wai ace kamar wanan yarinyar ta daga hannu ta mari nafisa habadai.
Yo ba zata mare ta ba an sakata rashin mutunci don tana yar ido to bari kiji idan ma daurin gindi kika samu nayin hakan zamu zuba a gidan nan muda ke a gani.
Wanan marin sai ya zamo maki fitina da bala,i a cikin gidan nan don ba kyale ki zanyi ba ki daki banza .
Hjy wanan maganan ga yarinyar nan bai dace ba gare ki don fadan yara babba bai shigan sa don kunya zaiji daga baya don haka a tsawata mazu dukkan su kada su kara nan gaba.
Kyace haka mana tunda kin kawo muna jangwagwan a gida idan dai har sayadi jangwagwan ne a gidan nan ke nan sauran yaran suma sun zama jangwagwan a gare ku data mareta may yasa bata rama ba.
Kinga da abin wata kila baikai haka ba a ranki tunda kinji zafin marin da akai mata amma bakiji zafin zahin datayi ba.
Ranan dai sunyi nasifa sosai akan maganan inda da kyat mama hadiye da Amma suka shiga tsakanin su.
Kowa abu daya yake fada mata akan fadan yara bai kamata kuna shiga ba haka inji mama hadiye.
Kiran fatima da agola kuma fatima ta wuce a kirata da agola a cikkn gidan nan yanzu don itama gida tazo ba agolanci tazo yi ba a nan koda kuwa maimuna baga gidan nan fatima mai zuwa ne ta zauna daku.
Mama hadiye bata kai kafshen maganan ta ba tayo cikin ta tana fadin dama nasan ku da daurewa karya gindi sai dai dadin abin sunan ta dai agolan gidan nan .
Har mai gidan ya dawo gida daga kasuwa ya samu ana fitina a gidan tu a get maigadi ke fada mai yau gidan ba lafiya tunda rana ake abu daya a cikin gidan.
Wucewa yayi ba tare da yayi magana ba yana jin muryan matan ya shige part din shi don rage kayan jikin shi ranan su salma basu leka islamiya ba suna daki suna zuga uwar su wai mahaufin nasu ya goyi bayana a school daya je.
Sai bayan isha,i ya bukaci kowa ya hallara a part din shi ko wace ta shigo tana takama yana aiki shi bai kula da su ba sai bayan wani lokaci ya dago yana gyaran murya
Yace hjy mai ke faruwa a gidan nan har na dawo ina jin muryoyin ku abinda naki jini da gani a gidana abin bakin ciki ace gidana ake wanan abin.
Shiru falon yayi sai daya kara maimaita tambayan shi gare su ne hjy jummai tace Alh a gaskiya bakai muna adalci ba daga mu har yaranka yau.
Yace ni din nan danayi maku mai kuma Alh yanzu ace daidai ne ka goyi bayan yar nan yar gurin maimuna don kawai tazo agolanci sai ta taka muna yara kuma ka dauki laifi ka basu.
Jummai kin san abinda kike fadi kuwa ?
Tace ai dama yanzu kullun magana ta ba daidai bane gare ka a daki mutum kuma a hana shi kuka.
Yace su yaran suka fada maki hakan naje school din su kan fitinan da sukayi yau na basu laifi tace kwarai kuwa a to ka basu laifi mana tunda su kaiwa fada.
Mikewa yayi zuwa waje ko anan ma daya barsu sai da suka dan taba don wanan karon hjy maimuna bakin ta bai mutu ba gare su.
Karshe tace ko an sake ni na bar auren Alh dole dai ku gan mu cikin gidan nan don ba inda zamu tafi daga ni har su.
Hjy tacr ina ko zaku tafi tunda ba a iya komawa gidan tsohu aci tuwo da kuka yanzu.
Saukin abindai anan mata ta samay ni ba kuka kuma gidan kowa ana cin shi don ba abin raina wabane inji hjy maimuna din.
Kada ki sake kice zaki zagan min iyayyena ban iya wanan ba don nasan darajan mahaifana sai ga Alh ya shigo damu falon buuuu a bayan shi.
Wuri ya nuna muna mu zauna kowa ta nemi guri ta natsu ya fara tambayan karaman yar gurin hjy maryam ta koro magana tiryan tifyan ta fada mashi.
Kallon gurin da take yayj yana fafin ki fada min goyon bayan da nayi a nan don Allah ta wani tabd baki tana fadin koma maynene aikai kaja muna shidai a gidan nan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button