NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:20 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YAN UWA MUSULMAI DA FATAN MUN TASHI LAFIYA UBANGIJI YA BAMU WUNI MAI ALBARKA DA DARE MAFI DARAJA A RAYUWAN MU AMIN, , , , ,

Mafiyawan muna cikin jirgin a nan zamu sauka ashe gurin ya cika makil da motoci da mutane nau,i daban daban sun fito sayayya don bukin kirisimeti.
Sai dana karewa wurin kallo kafin in bi ayarin masu tafiya da kafa muka shiga cikin plazan .
Sai ka turmusa wani kati da muka saya kafin kofa ya bude ka shiga ka hau na,ura mai tafiya da kanshi zuwa sama ko kasan ginan wurin.
Muna sauka muka shiga cikin plaza din komai nasu a tsare yake gurin wanan ne farkon zuwana gurin don haka na zama ba kauya a gurin.
Gurin kayan gwagwani na fara zuwa ina duba na halal kifi da naman gwagwani na kara siyowa sai pad da nafi bukata fiye da komai a lokacin.
Na juya wirin saida turare da kayan kwaliya na zabi wanda nake so mai isata kafin in juya gurin kayan sitiru na fara duba masu mutunci na zaba.
Ba wasu kaya bane irin namu sai gown da wanduna da su t,shirt haka na garo zuwa wurin biya kudi masu yawa aka chajeni na basu katina suka cire abinsu aka saka min cikin manyan kwalaye mai dauke da tambarin shagon nasu na fito.
Wanan karon taxis na nema don komawa gida saboda nauyin kayan dana lodo lokacin har bakin get din gidan mai motar ya tsayar da motar shi.
Da taimakon shi ya kaimin kayan har kofan shiga gidan gaba daya na biyashi kudin shi ya tafi sai lokacin na sauke ajiyan zuciya ganin naje lafiya na dawo lafiya ba abinda ya samay ko kadan wurin zuwa da dawowa.
Ina tura kofan gabana ne ya fadi jin kofan a bude lokacin hakana na daure ina shiga da kayan da kyat ta ciki.
A razane na juyo ina kallon shi jin muryan shi a daidai lokacin da ban zata ba daga saman benen yana fadin daga ina kike haka yanzu da wanan kayan ?
Tsare shi nayi da ido kafin in ce na fita sayayyan abinda nake bukatane .
Ya sake jefo min tambaya da izinin wa kuma dake da wa kuka fita zuwa sayayyan ?
Nace bada izinin kowa ba ni kadai na tafi naga idan sun fara bukin kirisimati komai wuya yake a kasan .
Kai tsaye nake magana na batare da jin komai a raina ba gamay dashi sabanin da can da nake magana dashi ina jin shakkun shi.
Tsaye yayi sororo yana kallon yadda nake magana ina aikin shigo da kayana zuwa ciki daga kofan gidan.
Tsaye yayi sororo tare da kare min kallo cikin yanayin mamaki karara a fuskan shi.
Sai da na gama jido komai zuwa ciki na dawo na samu ya shiga dakin sa ya rufe hakan ya ban daman shiga nawa dakin nabar kayan a nan falo daga sunan zuwa fitsari sai na tsaya na dauro alwala nayi sallah ban fito ba saida na sauya kayan jikina na sauko kasa.
Kitchen na fada dafuwa mai sauki nayi muna wanda ganye yafi yawa a cikin sa sai dan sauran abubuwa na jera muna a falo.
Wanka nayi na daura wani alwalan magariba na fito sallah na gabatar kafin in gyara jikina kwalliyan wando da yar t,shirt nayi a jikina na sauko don cin abinci.
Ban san da fitowan shi falon ba yana zaune yayi dadaya da kayan dana sayo na barsu a gurin yana kallo sai gani na fito daga daki.
Ja nayi na tsaya ina kallon shi da mamaki sai lokacin na iya tuna daga tafiya ya fito ban samu gaida shi ba na dan raba gefen kujera ina gaidashi tare da mashi yaya kawu da jiki da mutanen gida duk lokaci daya nayi mai tambaya a jere.
Dago kai yayi kamar da mamaki yana amsawa a takaice tare da fadin kayan abincin ki sun karene da kika sayo wanan ?
Basu kare ba ina dai ra,ayin canzawane kawai yasa na sayo su don kawar da zancen nace dashi ga abinci a dining yaya.
Shiru yayi min ba tare da ya amsa ba na dauka ba zaici ba don bai kula da maganata ba sai kanshi daya dafe ya mayar da bayan shi saman kujeran.
Tambayan dana jefo mai yasa ya dago kai ina fadin yaya yaya su Amma da mamu suna lafiya ?
Su kika sani ke nan ya fada yana mikewa daga inda yake ya nufi gurin abincin ciki ciki nace don nasan su zasu ce a gaidani mana.
Ya juyo yace OK to su din ma basu ce ba don ban fadawa kowa zuwana nan ba.
Mikewa nayi zuwa bakin dining din na bude abincin da sai tururin zafi ke tashi cikin cooler na fara zuba mai ba tare dana kalle shi ba.
Nima na zuba nawa naja kujera na zaune daga gefe na fara ci ba wanda ke magana a cikin mu sai abinci muke ci da sake saken zuciya.
Bell yayi kara da alaman akwai wani a waje yana son shigowa gidan da dan mamaki ya kalloni nima kallon shi nayi kafin in mike zuwa kofan cikin raina ina mamaki.
Na bude kofan a hankali ina kokarin duba kowaye a kofan wata farar fatace tsaye a kofan dauke da kwalin cake tana murmushi tace min happy chirismas tana miko min kwalin dake hannun ta.
Murmushi nima nayi don na sheda ta makwaciya ta ce matar duk da babu ruwana dasu sai wani lokaci mukan dan gaisa sama sama, da safe da ita.
Hannu na mika na karbi kwalin da take miko min nace same to you thank you wishi you many many years retune.
Matar taji dadin addu,a danayi mata tace saboda ni makwabciyar tace duk da taga ban kula kowa a layin yau dai ta daure ta kawo min kirismas gift har gida.
Nace na gode hannun daya mika zai dauki ruwan dana aje mai gefen shi yasa ta farga dashi ta dan juya tana gaidashi ya amsa mata ciki ciki.
Tambayana tayi wanan yaya kuke dashi na bata amsa da brother dinane shi tace kuna da kyau family din ku sosai wani ya taba fada min hakan kuwa ?
Nace mutane da yawa suna fada min hakan ba ita bace ta farkon fadin hakan ta juya tana fadin zata tafi ta gode da karramawan da nayi mata a gidana.
Tana fita na rufe kofan na juyo na samu ya kakafeni da idanu yana min wani irin kallo mai tatare da ma,ana.
Ban koma wurin abincin ba sai na nufi wurin kayan da nasayo ya watsar min dasu a falon na tsuguna rai bace na fara tattara kayan a hankali.
Muryan shi naji yana fadin har makwatabta kika fara janyo min a gida ashe ke wata irin yarinyace da bata jin magana haka ?
Ban iya bashi amsa ba illa shirun da nai masa naci gaba da dauke kayana a kasa ba tare da na juya ba a yadda nake.
Wayan shi da aka kira ya rabamu ranan don tunda na shige da kayana ban sake fitowa ba sai washe gari.
Ban tabbatar da yana gidan ko bayanan ba nidai na hada breakfast dashi ranan na koma daki nayi wanka na shirya cikin daya daga cikin dogayen rigunan dana sayo jiya rigan jace andan bude gefen shi don hakane ni nasaka dogon wando daga ciki don kada sharabana ya fito fili.
Ina matukar son abu kalan ja ko baki da yellow da sky clour saukowa nayi na nufi kitchen fridge na bude na dauko lemo kwalba na fito.
Yau haka kawai naji zaman ciki ya isheni don haka ina son shakan fresh air a waje.
Dan barandan gidan da mutum zai iya tsayawa yasha iska na bude na fito akwai kujeru biyu wurin da aka tanada don wanda ya tsaya wurin.
Saidai ban zauna bani staye nayi ina karwa gidajen makwabta kallon yadda suka kawata gidajen nasu da shaguna don kawai zagayowan wanan bukin nasu da muke hutu a kansa.
A yadda nake tsaye gurin daga gani babu tambaya na samu nishadi sosai a lokacin .
Saboda yadda nake tsaye ga airpiece makale a kunnena ina shan wankan larabawa mai take Allah Allahu ya baba asalamulaikum ya, , , ,
Shi nake saure a lokacin ya shagaltar dani saboda dadin wankan da nake ji ina dan kurban lemon dana tsiyayo a cup a hankali idan na kurba in mayar da hankalina ga titi .
Tsaye yake yana karewa yanayi da nake cikina nishadi kallo banda damuwa a tare dani yanzu ko kadan.
Yana mamakin sauyawana da sakewa a dan lokaci kankani duk yaga komai ya sauya daga bangare na.
Wani irin tausayina yaji ya rufe shi lokaci guda yasan yana danne min hakkina da komai amma daidai da rana daya ban taba nuna mashi hakan yana damuna ba ko a fuska.
Na dago ido na dan juya don jin kamar mutum a tsaye bayana sai nayi arba dashi tsaye ya saka suith a jikin shi ash clour yana tsaye ya saka hannayen shi a aljihun wandon shi ya zubo min idanuwan shi.
Dama naji hakan a jikina ana kallona da sauri nakai kasa ina fadin yaya ina kwana.
Mai hali baya barin halinsa kamar bashi bane ya gama tausaya min yanzu dan harara ya galla min tare da fadin .
May kike a nan kuma mutane suna kare maki kallo a haka da kika fito ?
Yana fadin haka yaja guntu tsuki tare da juyawa yabar gurin ya koma ciki cike da takaicin da bai san dalilin yinsa ba.
Bayan shi na galawa harara ina mai takaicin yadda ya tsaya na kare min kallo a fakaice gani kaina babu ko dan kwali lokacin.
Ban bar wurin ba saida na kare shan lemona da kallon wasu yara masu tseren keke a gaban gidan mu.
Na shiga falon bai ciki gurin labulen gaban gidan naje na daga na hango shi yana kokarin shiga motar shi .
Ya hanani tsayawa idanake ganin mutane shi kuma ya fita ya barni kamar manya a gidan ni kadai na fadi a fili.
Ni kadai a cikin gida sai faman mita nake kai kace da wani nake zance a cikin gidan wurin tv dake falon na nufa na kunna.
Ko wani tasha nasu nakai babu abinda sukeyi sai hasko bukin wasan kirisimeti da sukeyi .
Haushi naji ina fadawa saman kujera na kai kwance tare da lumshe idanuwana take zuciyana ta anyana mun shiya dawo da yaya umar kasan nan.
Zubur na mike nakai zaune tare da fadi a fili tabbas abinda ya dawo yi ke nan don matar shi waya sani ma ko shima chocin yake zuwa.
Kai amma ko idan hakane anyu hasarare a gurin nan ya zama dole inbi kwakwafin takon shi in gane ko yana cika sallah shi.
Taya zan gane hakan na tambayi kaina mutumin da kullun yake faman daure min fuska kamar baisan inda na fito ba.
Ta yaya kawu zai dauka harni zan iya gyara mai akidun shi bayan baya son kowama ya rabe shi sai wanan kafirar matar tasa.
Nasan akwai abinda mijin anty farida ke son fada ranan gamay dashi sai kuma yayi shiru bai fada ba koma may ye shiya sani nidai in samu in karasa karatuna in koma gida kawai don ba zan yarda in zauna kasan da bansan kowa ba inta rayuwan kadaici saboda shi.
A ranan nasha mamakin makwabtana don kusan mutum uku suna kwakwasa kofa suna kawo min charismas gift har gida ina godiya ba wani abu bane sai cake da sukayi da sauran irin su sweet da biscuit.
Mamakin hakan nayi sosai a raina don tunda nake dasu ni wani gaisuwan kirki bai taba shiga tsakanina dasu ba ma sai gashi duna buga min gida suna kawo min kyauta har gida don kulawa.
Shiko yaya tun fitan shi ban kara ganin shi ba yau kwana biyu ke nan sai dai dama na kudurta a raina wanan karon idan yace zan tafi can dayan gidan nasa wurin su merry zaisha mamakina don ba zan tafi ba yin bukin shedanci.
Da zaman ya isheni ni kadai a gida na ina jin kamar zan kamu da ciwo don haka na shirya tafiya gidan anty farida in kai masu yawo.
Saidai nayi rashin sa,a sunyi tafiya wata makwabciyarsu yar kasar lebonon ke fada min sai lokacin na tuna amfanin waya ashe dama kiranta nayi inji ko tana gida kafin inzo.
Dama da kafa nake don in motsa jikina haka na tako da kafa na kamo hanya ba gida na nufa ba dayan hanyan nabi da kafa ina kallon gari.
Naji dadin wanan fitan don naga mutane gungu gungu suna wasan ni a layin da kama layin na talakawan garine ko dai wani wurin nishadi.
Haka nayi tabin layin ba tare da nasan takamaimai inda zani ba can naci karo da miji da mata suna tafiya a hanya kamar a mafalki naji suna yaren hausa a tsakanin su.
Sam basuyi zaton zanjisu ba matar tace iko Allah su kuma a haka wai bukin murnan sallah sukeyi haka wai ?
Mijin yace kin san abinda ka yard dashi ko aka haifeka a cikin sa ban san lokacin danace sannun ku da hutawa ba .
Gaba daya lokaci guda suka juyo suna kallona dan dattijon yana kare min kallon mamaki saidai yanayin shigata nasan bana banza bane nayi lokacin.
Na sake fadin ina wuni ku har lokacin da mamakina karara a fuskan su suka amsa min kusan lokaci guda.
Da barka dai yan mata kema kin fito bude ido ke nan ko matar ta tambayeni ?
Eh hjy zaman kadaici ya damay ni na fito kawai inga yanayin bukin su na bata amsa tace ayyah akwai kadaici tundai a irin wanan lokacin da suke zaman gida suna shagulgulan su ta wanan shirmay nasu wai bauta.
Mijin yace kada ki zake da yawa don ita din baki san ko wacece ba Ramla ya fada yana tsareta da ido.
Nace a a ha baba ni din ma musulmace yar uwar ku sunana fatima daga Nigeria nake nazo karatu ne nan kasar tare da yayana gidana yana bayan layin nan kadan.
Kai amma ko nayi murna da haduwa dake yan mata zaman kadaici ba dadi ke gareshi ba tundai a irin wanan kasashen na turawa.
Nayi murmushi saboda jin kalaman matar ganin kamar mijin bai yarda dani ba yasa nace nagode da dan lokacin da kuka bani zan tafi sai watarana idan Allah ya sake hadamu kuma.
Da sauri matar tace haba haba yar uwa tun yanzu aini ina ganin ki kamar naga wata ta gidane wallahi.
Muma daga Kasan ghana muke sai dai shi maigidana dan Nigeria ne don yafi zama a can kowa nasa yana Nigeria sai mahaifiyar shi ce yar kasar ghana.
Ba zaki tafi ba tunda kina ke daya a gidan ki kizo mu zagaya a tare muyi kallo ikon Allah wai kin san al,adun su na gargajiya abin mamakine sosai.
A yadda na fahinta matar tana da son hira sosai da kuma son mutane sai nake tunane duk wanda ke wani kasa haka yake idan yaga dan kasan su wani gari.
Ranan naji dadin wanan fitan don na sake jikina sosai mijin matar ya kaimu wurin cin abincin mai kama data kasan mu kowa yaci abinda ranshi ke so.
Har gida suka dawo dani sai da sukaga shigata gida suka ja motar su suka tafi sai lokacin naji wani irin ba dadi don kamar kada su tafi su barni naji lokacin.
Ina kokarin juyawa mukai ido biyu da yaya umar dake tsaye cikin damuwa a kofan gidan hannayen shi duka biyu suna saye cikin aljihwayan shi na wandon jikin shi.
Dan raza nayi kai kace wani abin tsorone a gabana lokacin yana huci yana cika yana batsewa sai lokacin na saita kaina nace sannu da zuwa yaya kamar kullun .
Ke dakata daga ina kike wa yan nan mutanen kuma su waye su da suka sauke ki ya tambaya cikin daga muryan shi.
Mun fita cikin gari ne na bashi amsa sunan ta anty Ramla mun hadu dasu ne a garin nan.
May kike son zamane Zarah kina son ki zama watsartsane a garin nan komai ?
Naji zafin kalaman watsartsar daya kiramin don haka bansan lokacin da zafin rai yasa nima na daka mai tsawa ba kamar yadda yai min.
Nace kai yaya ya isheka haka nayi maka kama da mara tarbiyane a shiga ko kaga wani abin Allah waddarai a tare dani.
Ka sani koda bani gaban iyayyen mu nasan abinda nake don ba tarbiyan banza sukai min ba ban kuma taso naga ana abin asha ba a gidan mu balle inzo nan in koya a garin mutane.
Yaya kake son inyi da rayuwata yaya ka daukoni kazo dani kasan mutane ka watsar dani ba kulawa ba komai nima fa mutumce yaya da dole ina bukatan wani a tare dani.
Banki duk yadda kace min ba ina kokarin ganin na bi duk wani dokan ka na tsare shi yanzu kuma zakace kada in fita in ga mutanen arziki.
Na sani da sunan aure muka bar gida amma kaida bakinka yaya kace kada in sake in nunawa wani a kasan nan akwai aure tsakanina dakai.
Duk da nasan hakan ba gaskiya bane ina kokarin nunawa kowa kai yayanane najini karatu ka kawo ni yi kasan nan kamar yadda kake son in nuna din.
Ko zanyi iskancin da kake zato inayi din da mata da mijin ta zanyi yaya ?
Ido rufe nake magana duk cikin bacin rai yasa bansan ya karaso inda nake ba sai jin saukan mari biyu masu kyau naji a fuskana.
Dafe fuskan nayi yayin da nake duke na kasa dagowa sai can na iya dagowa na kalle shi yana tsaye yana huci akaina.
A hankali na ja kafana na tura kofan zuwa ciki ban tsaya a falo ba na hausama inda dakunan kwanan mu suke.
A hankali na tura kofan na shiga na mayar na kulle nasa sakata gadona fada na nemi farin ciki da nishadi dana dawo dashi na rasa a lokaci daya.
Rutse idona nayi a hankali na furta mamu wayyo Amma wayyo ni manjona da wani irin karfi.
A daidai lokacin da yake rufo gidan yaji wanan karan dana sake lokaci guda daga kai yayi ya kalli kofan zama yayi saman kujera tare da kokarin sasauta tie din wuyan shi.
Ya mayar da kanshi saman kujera tare da runtse idanuwan shi wayyo mamuna don Allah kizo ki kwace ni a hannun wanan azzalumin kafin ya kasheni.
Abinda ya shiga kunnen shi ke nan, kai ya girgiza ya ya kara runtse idanuwan shi zancen kanin shi Aliyu ya tuna yaya matse zai iya sa ta dauki matakin da bai dace dakuba.
Ba wai ina nufin tursasaka akan iyalin ka bane a a ya kamata ka rage wasu abubuwan da kake mata itama fa yace kamar kowa.
Why ba doki wanan yarinyar yaya akayi har nakai hannuna a jikin ta ya dade zaune yana tunane barkatai.
Kafin ya mike ya hausama tun a matakalan yake jin sautin kukana a kunnuwa shi wanda yake jin zuciyan shi na kara tabuwa da baci a lokaci daya.
Har ya tura kofan shi zai shiga yaji na kara fadin wayyo mamu na zai kasheni zai kasheni a garin mutane sai ya dauka waya nake a lokacin.
Fasa Shiga yayi dakin nasa ya nufo nawa dakin ya tura kofan ya jishi a rufe gam.
Ya tura ya tura yana rufe juyawa yayi ya koma inda ya fito har lokaci yana jin wani iri a ranshi ba dadi.
Da kyat na iya tashi nayi sallah isha,i ban tsaya cire kayan jikina ba ranan haka na fada kan gado tun ina tunane har barci ya dauke ni gurin ban sani ba.
Washe garima haka na falka da bakin rai yinin ranan ban fita daga daki ba ina daki ko falo banyi gigin lekawa ba.
Komai ban saka a bakina tun safe har ukuna rana ban fito ba bandamu da sanin ko yana gidan ko ya fita ba lokacin tunda zuwan shi ko zaman shi gidan sai yaga dama ko yazo yin wani abin da yake sirine gare shi zai shafe lokaci yana dakin yana aiki da laptop din shi.
Kadan kadan yake dago kai ya kalli hanyar benen kamar may kallon wani abu ba komai yake kallo ba sai fitowa a lokacin tun safe yake zaune a falon sallah ne kawai ya tayar dashi yana idarwa ya dawo ya sake zama gurin.
Jin shiru ban sauko ba har lokacin yasa shiikewa yahau benen kofa ta ya nufa ya tura har lokacin a rufe kofan yake.
Nocking ya fara yi tun yana yi a hankali har ya fara duka da karfi yana kiran sunna na ina jin shi naki budewa.
Ko dagawa banyi a inda nake ba ya kara kiran sunana da karfi yana fadin ki bude kofan nan ko in karya in shigo dakin nan in saba maki nan ma ba amsa sai shiru.
Hankali shi ne ya tashi sosai yana ganin kamar wani abu ya samay nine don marin da yai min din.
Tun yana fadin zarah zarah har ya koma fadin Fatima nace ki bude kofan nan karna karya shi.
Jin shiru ba amsa zuciyar shi ta fara kaduwa da fargaba a lokaci daya.
Ya koma yin magana cikin marairaice murya yana fadin kiyi hakkuri zarah ki bude kofan ba dukan ki zanyi ba .
Ina jin shi na kasa tashi saboda yanayin da nake jin kaina na yunwa da kukan dana sha kaina da jikina gaba daya ina jin su kamar ba nawa ba.
Muryan shi na kara ji cikin wata marainiyar murya yana fadin zarah don Allah ki bude kofan nan ko hankalina zai kwanta kinsan amana kike a gareni kasan nan.
Nasan nayi maki ba daidai ba don Allah ki bude kofan nan hankalina a tashe yake da rashin fitowan ki daga dakin nan.
A hankali jiki ba karfi na dago daga kwance tare da sauko da kafafuwa daga saman gadon da nake kwance.
Jikina ba karfi don yunwan daya ci karfina a lokacin ga kaina kamar zai fashe don ciwon da yake min.
A hakali na bude kofan tare da murda marikan kofan jin ana kokarin bude kofan har ya juya yana shawara a ranshi yakira security din unguwar suzo su balle kofan sai gashi yaji ana bude kofan.
Ya juyo yana kallon kofan da na riga dana bude a lokacin ina kokarin komawa sama gado in kwanta.
Turo kofan yayi da karfi tare da fadowa cikin dakin daidai lokacin dana kai saman gadon ina kokarin zama a bakin gadon.
Wani irin kallo yakewa yanayin daya riskeni a ciki don na gala baita sosai bakina duk ya bushe tun rigan dake jikina lokacin da abin ya faru shine saye min har wanan lokacin.
Ga kaina babu dan kwali gashina dana tufke ya dan barbaje saman kaina har ya zubo saman goshina.
Take yaji wani tausayina ya kamashi ya iso inda nake da sauri yana fadin zarah kina son ki kashe kanki ne kija min magana a garin mutane ko may ?
Sai kuma ya juya zuwa waje da sauri ya dan dauki lokaci har na kai kwance sai gashi ya dawo dauke da kofi yana tururi da ruwan tea a ciki.
Zuwa yayi har kaina ya tsaya yana fadin ki tashi ki sha wanan tea din hanji ya warware.
Kamar badani yake magana na kyale shi ya ja tsuki yana fadin idan baki tashi ba zan dura maki shi ta karfin tsiya yanzun nan wallahi.
Jin hakan nayi kokarin tashi zaune saidai na kasa da taimakon shi na samu na dan zauna a hankali karban kofin nayi jannuna sai rawa yake na dan kai bakina.
Zafi da dacin shayin naji lokaci guda na sauke kofin ba shiri da sauri ki sha mana ya fada cikin tsatsareni da idanuwan shi.
Kisha nace ko in kira ai maki allura yanzun nan tunda haka kike so jin hakan yasa na kara daga kofin ina kokarin kaiwa a baki na.
Na kama kurbawa da dan sauri don ban son alluran danaji ya ambata min yasa na daure ina dan sha badan ina so ba.
Wayar shi ta dauki ruri ya ciro yana kallon wanda ke kiranshi hakan yasa ya dauke kai a gareni ya mayar da hankalin shi gun wayan .
Merry naji ya ambata daya daga waya yana fadin Ina nan mana ina zanje ban fada maki ba wani irin amai ne yazo min lokaci guda na sako shi har wandon jikin shi zuwa kafan shi sai daya taba.
Haka yasa ya fita zancen wayan yana fadin subbahanallahi kinga zaki halaka kanki ko a banza.
Wai wai nake fadi cikin jin ciwon da cikina keyi a bangaren merry tana sauraren abinda ke faruwa sai magana takeyi a wayan shiko hankalin shi yana gare ni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button