NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:04 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMAN RAHIM HASBUNALHI WANI,IMAL WAKIL SUBAHUL HAIRI YA JAMA,ATUL MUSULMIN, , , , , , ,

Ba Amma kadai tayi mamakin mamu kowa da akai case din a gaban shi ya kwana da mamakin mamu a ranshi ranan.
Mu saman hjy jummai data dauko ta shirya wullakanta mamu sai gashi taga mamu ta gasa mata magana a bainan jamma,a kan itama batai na,am da wanan hafin da nata zuri,an ba .
Wanan abin ba karamin kona ra hjy jummai yayi ba sosai har mamu da take ganin fakiriyace bata da komai zata bude baki cikin jamma,a tace bata kaunan hada jini da ita may wanan yarinyar take takama dashi ne a gidan ?
Shi kanshi kawu ya kwana da wanan rufa idon da maimuna tayi a bainan kowa ta nuna bai isa ba da yarta sai dai ya danganta abin da zafin kishi irin nasu na mata.
Don yasa gatan da zaiwa marai niyar yarta ke nan ya gama da ita sai kash maimunan bata gano manufar shi ba kan hakan da yayi.
Dayake shi namiji ne sai ya shaye maganan a ranshi ta yadda babu mai iya fahintar shi ko kadan.
Bangaren yaran hjy sun hade a gidan dan uwan su suna kallon irin aikin da yayi a asirce ba tare da sanin kowan su ba har iyayyen su.
Aliyu ne yace wace mai sa,an mace ce aka shiryawa wanan gidan haka bros ya dan kai ma Aliyun duka yana fadin ina ka kai merry da ranta ita ke da wanan gidan.
Habbib yace merry kam bata zama a garin nan kuma kun sani sai dai wanan yar kwalar da daddy ke shirin lakaka mai har uwarta na jan aji.
Kai haba nasan fa halin bros kwanton yayiwa su daddy tunda kaga yayi shiru bai tankawa kowa ba kan wanan zancen rana daya zasu memashi su rasa ya ware abinsa.
Umar dake dan taba wani guri da yake ganin kamar aikin gurin baiyi ba ya juyo yana fadin habbib kaga laifin maimuna ko.
Aliyu yai saurin fadin ni dai ban gani ba don babu uwar da zata so hada sarakuta da mama a yanzu don maganan maimuna ne yar zata zo zaman bauta ne da masifa.
Kai komai zaka iya fada yanzu akan mama tunda kun bata da ita amma aikoma may nene bai kamata ta fadi wanan maganan a gaban mu ba.
Kamar wata ya can wace takai mace ko wani aji take dashi da har take iya budan baki a gaban kowa ta nuna bata son hadin daddy.
Habbib ya fada ba tare daya kalle shi ba yace zaka so ka aurar da yar ka inda bata da daraja ka kwantata a kanka halin da maimuna ke ciki a gidan mu ka gani.
Matar nan ko a munafuce take muna abinda take taci a dan yabe ta sai dai kuma babu wanan gun mama mutumin daya tarbi naka yasa a jiki har kuma shine zai zama makiyin ka a yau.
A da nadawo da niyar ciwa duk wani wanda ke taka mama a kasan mutunci sai kuma nazo na samu abin ashe ba haka yake ba.
Idan baku sani ba ku sani yau mama da bakinta take kiran matana da arniya wanda ya dace idan wani ya fadi haka ran mama ya baci.
Amma sai ya kasance a gabana mama ke furta hakan kaya wanan da merry ke son irin namu na hausa sai da mama ta karbi kudi shi a hannu na kuma har yau ba a dinka kayan ba.
Wanan maimuna din danabata kudi ayi cewa tayi nabar shi kawai ayi yakai maimuna ita ta shigar da merry da karfi da yaji a gidan nan wurin kowa.
So yau don maimuna ta fadi haka ni sam baga laifin ta ada ina zargin da hadin bakinta kamar yadda mama tace aikai komai sai yanzu na gane bata ma san da wanan zancen ba ashe.
Don a gaban ku ta nuna reaction din ta kan zancen yaya mama take son mu zauna da mutane yau tace tayi muna iyaka da wanan gobe tace wanan kawai ta yarda muyi hurda dashi shin har yanzu mu yarane ?
Kiri kiri tun muna yara mama ta hana zaman lafiya a tsakanin mu da yan uwan mahaifin tun bamu so har yakai wanan halin yanzu yabi jikin mu.
Tun shigowan mu gatin nan akwai wanda ya leka wurin dan uwan daddy ba tare da wani dalili ba ?
Sai nake ganin daddy yana kula da hakan shiyasa yai amfani da nashi karfin ikon akan mu duka ya nuna ma mama iyakarta na mace a gare shi kuma ya kawo hujja mai tsauri ya kidanya a kan maganan.
Kaga daga mama har mu ya daure kowan mu da jijiyoyin shi ke nan kin wanan maganan ta daddy a wurin mu yana nufin baraza ga auren mahaifiyar mu.
Sai dai kash ita mama a yanzu bata gane illar abin saboda idon ta dake rufe kan kishin su na mata dawani dalilai nata.
Idan muyi mata biyayya mun ba mahaifin mu baya akan maganan shi hukuncin saki zai hau mama wanda sai daga baya gaba dayan mu zamuzo muyi damun sani akan hakan.
A karshe duniya ba zata zagi mama sai mu za,a dauka marasa tarbiya da rashin biyayyan mahaifa sai laifin ya dawo gare mu.
Gaba datan su ido suka tsurawa dan uwan nasu jikin kowanin su yayi sanyi lokaci guda suna sauraren shi.
Ya dafa habbib yana fadin yin biyayya ga mahaifin mu yana nufin ceto rayuwan auren su da mama ne da mukazo duniya muka samay su a tare.
Wanda kuma yin hakan gun daddy rata zumuncin sane da yake ganin a bayan sa zai watse kun san daddy yana sane da rashin kaiwa yan uwansa ziyaran da ba wanda yayi a ckin mu.
Fuska habbib ya bata yace yes munyi maganan dashi a ranan da nake fada mai zancen wanan gidan nawa sai naga baiyi murna ba kamar yadda na alkawarata mashi zamu ziyarci yan uwan shi da yardan Allah.
Abinda nake son ku gane akwai aiki a gare mu babba daga ko wani bangare namu ga mama da shi kanshi daddy din don cikan farin cikin su dukan su.
A yanzu mama zata ga cewa mun goyi bayan daddy ne ga nashi kudirin amma a gaba zata gane yin hakan shine farin cikin ta da namu baki daya.
Don haka ni a shirye nake badon naso ba in karbi kaddaran auren yarinyar nan da hannu biyu kamar yadda daddy ya umurce ni dayi.
Duk da nasan abinda zan fuskanta a gaba yafi wanan matsala a gare ni yanzu don haka kowan ki yaje yayi shawara ya zabawa kanshi farin ciki.
Shiru sukayi gaba dayan su kowa yana nazarin maganan nasa Aliyu ne ya nisa tare da fadin bros ai shawaran ka shine final decition kowan mu ya hakkura da kaddara ya fada a cikin rashin damuwa.
Habbib daya gama cika a lokacin yace kai ina yaya za ayi in auri yarinyar da ban sani ba ban san kalar ta ba hakama ba zai yuyu bane.
I will live dis country by all means ba sai sun ganni zasu daura min ita ba kawai mutum na early age din shi za a dauko wani wahalan aure a lakaka mai a kai .
Duk mama ce ta jawo muna wanan fushin a wurin daddy data tsaya sun fahinci juna ga yadda yake so da abin bakai haka ba.
Dan murmushi umar ya sauke a fuskan shi kada kaga laifin mama duk nine na jawo maku wanan matsalan da ace banbi son zuciya na yarda na auri merry da yanzu abin abin ahankali don ran daddy ba zai baci haka ba.
Bros ni bani ganin laifin ka dama abin haka yake muna rubuce a littafin so kaga mutum bai wuce kaddaransa ke nan.

Mamu ce bayan fitan mu zuwa makaranta ta shirya tafiya zuwa wurin mahaifin ta don ta sanar dashi halin da take ciki.

Ta samay a farfajiyan gidan shi yana shan iska tare da sauraren redio a gefen shi ya dan jingina jikin shi da filo.
Sun gaisa yake tambayan ta yara tace suna makaranta baba sai uku suke dawowa daga nan nake son in biya idan na fita na kwaso su.
Baba magana mazo wurin ka dashi yace to maimuna injin dai lafiya ta sada kai kasa tana fadin lafiya baba sai dai wani abu ne ya tasa a gidan akaina da kuma yarinyar nan.
Yace subbahanallahi Allah yasa abinda zan iya maganin sa ne baifi karfina ba tace in sha Allahu baba zaka iya.
Ya nisa tare da fadin kada inyi rashin hankali ina ita gwaggon naki da baki fada mata matsalan ki har kika zo nan wuri na anya yin hakan ba zataga mun juya mata baya.
Baba itama gwaggon nawa mun zauna da ita a kan matsalan tasan da zancen yace to shike nan don kada muyi abu a cikin rashin sani yace ina sauraren ki.
Ta fara rabbatabo mai duk yadda sukayi da mijin ta da kuma gwaggon nasa bata boye mashi komai ba.
Bata kai karshe ba yacewa ayyah maimunatu kina cikin hankalin ki kuwa ?
Yau sani ne kike son ki watsawa kasa a ido haka yayi bugun gaba da yar ki don baki da kunya har zaki wanko kafa kizo wurina kina fada min maganan banza ga tsohon banza kin samu ko ?
Idan ke mai hankalice maimunatu ai godiya ya kamata ki masa don ba karamin gata yai maku daga ke har yar taki da kike fada a kanta yanzu.
Yanzu kin kwaso kafa kinzo gurinane in bude baki ince ni musa ban yarda Sani ya aurawa dan shi jikata ba komai ?
Yanzu yace zai bada yarki ga dan sa kince bai isa ba yanzu wa kike ganin ya isa ga yar taki tunda kin iya rufe ido kinwa sani haka.
Maimunatu samun wurin naki har yakai ki fara yiwa dan uwan ki wullakacin kin manta da gatan da yai maki ya rike maki yar tankar shi ya haifi abinsa.
Shin samun mutum mai hakkuri irin Sani ya jawo har kin fara mai iya shege to ki sani ba sani kika watsawa kasa a ido ba gwaggon ki Ammatan kika watsawa kasa a ido don ita kika wullakanta yau ace kina fada akan jikanta jinin ta don baki da kunya daga ke har kubura ku iya duban idon ta kije mata da wanan zancen.
Dama jiran ku nake dayan ku ya tunkare ni da wanan zancen don tuni yaya ta kirani tana fada min iya shegen da kikayi masu.
Kin nuna masu cewa basu suka haifar maki yar ba banta sanin ke sakariya bane shasha in banda sakarci yauko dan baro sani yace zai aurawa diyar ki ke har kinada bakin musa mashi.
To ko ni nan yaya tana da iko dani a yanzun haka don tana gaba dani kuma ita kadai ta rage min a duniya.
Shi al,amarin aure in yazo ai sai addu,a ga yaro don ya wuce duk yadda ake tunane abinda yakama ace kinyi baki tsaya kinyiwa yarki ba.
Mamu ta buda baki tace a cikin kukan da yaci karfinta baba ni ba maganan yaya na raina ba cewa nayi ya bata kowaye amma dai dan jummai ba.
Wani kallo mahaifin yai mata kafin yace Jimmai din ita keda dan ko sani zai fita yai tunkaho da jummai ne a waje ?
Nan taci kukanta saida ta gaji ta tashi tayi mai sallama bai ko amsa mata ba ta fita da kunan rai a tare da ita.
Bata tafi dauko mu ba kamar yadda ta tsara don tabar gidan kafin lokacin tashin mu yayi don haka ta nufi gidan babba lami da rake dauka takar mahaifiyar ta.
Don matar aminiyar mahaifiyar tane a unguwar da suka taso har izuwa yanzu bata daina mata biyayya ba.
Saida babba lami ta gama sauraren ta tace assh maimuna baki kyauta ba yau ko baki gidan Alh ai shi mai bugun gaba da yarkice yaba duk wanda yake so.
Ai yanzu sai yaga kamar baki daukeshi uba ba gareta don bashi ya haifar maki itaba da tun farko kika zo nan da ban yarda kin aikata hakan ba.
Ai wanan abin bake aikawa ba ita akaiwa ita da ta nuna ko gidan bata kaunar ganin ki a cikin sa yanzu karewa yarki kuma zata auri danta.
Kinga ko anan kin nuna mata rinjaye don ba ita ke yiba Allah ke ikonsa a inda yaso tafadi ta mutu.
Yarki fa mace ce ke ke ganin ta yarinya yanzu babu yara babu manya a gidan aure sai kiga yarinya kankanuwa ta baki mamaki.
Don haka ko yanzu kin gara zuciyar ta ki barta da tabon bakin cikin da kika samata ya isheta kaya.
Ki san yadda zaki gyara da mijin ki kadana karajin kin daga wanan zancen kuma sai dai kada ki kuskura ki zake a fili har ta dauka kina dokin auren dan nata da yarki ne ta samu daman gasa maki magana nuna mata kema hakan baki so a tafi a hakana.
Tai mata godiya tare da jin dadin shawaran ta ko ba komai ta samu hanyar da zata cusawa hjy jummai bakin ciki ke nan itama taji idan da dadi.
Ta biya school din mu dauko mu ta samu mun biyo motar su salma duk da a lokacin ina ganin sun dan daure min wanda ni ban san dalili ba amma haka na daure muka biyosu muka dawo gida.
Motan ta ya tsaya a daidai lokacin data su umar da merry suka shigo gidan da ganin yanayin mamu basai an fada ba tana tare da damuwa a lokacin.
Yana tsaye bakin motar shi har mamu ta fito daga nata motar har ta karaso inda suke don dole sai tabi ta inda suke da ta canza hanya don nauyin shi daya kamata a lokacin ta tsunci kanta da dan jin nauyin shi yau.
Ta karaso a daidai inda suke ya dago yana fadin barka da iso ya hanya ashe bakya gidan ma ?
Na dan fitane ne ta basu amsa a cikin murmushi itama kamar yadda shima din bai wani daure mata ba can.
Tadan juya inda merry take tana fadin yau jikin ya sake kenan kin samu fitowa ?
Merry tace nayi missing din ku kwana biyu nasa yau ya shigo dani in ganku tace my dear help me to carry that load.
Ya juya ya bude mota ba kunya ko jin nauyi ya dauko manyan ledoji daga bayan motan tasu ba tare dajin komai ya dauko ledojin.
Ganin haka yasa mamu ta fara tafiya ta barsu a gurin har ta bude part din zata shiga ta yadda take iya jiyo hayaniyar mu a ciki yace am dama naso in ganki mu danyi magana akan abinda ya faru ranan.
Dou ban samu shigowa sai yau don Allah ki kara hakkuri wanan tashin hankalin kuna kara sa daddy a cikin wani matsala ne a gidan nan.
So ranan naga ranki ya baci sosai shine na baki time ki dan huce gashi kuma naga har yanzu kamar kina a cikin damu up to now.
Mamu tace ba komai wallahi komai ya wuce gare ni don ni bani rikon magana a raina abinne ya ishe ni wallahi shine ranan idona ya rufe har nakai ga bata amsa.
Yace ba komai ga wanan merry ta saya maku a hanya tace a nan zata kai dare yau.
A, a umar kakaita part din mahaifiyar ku kamar yadda ta bukaci ku dinga zuwa can wurin ta ai yanzu merry ta zama yar gida a gare mu kaga idan kaje sai ku bata wanan tsaraban zataji dadin hakan sosai a ranta.
Kallon mamu yayi yace ba ita muka rikowa ba don da sunan ku ta saya sanan kuma ina daddy ai ya kashe wanan maganan ko ?
Bin umurnin ta yana da kyau gare ka zanwa merry magana yadda zata fahinci ne dan bamu dama tana tafe yanzu.
Na gode yace ya fara tafiya suka danyi magana da merry ya nufi part din hjyr su sai dai yana tun kara yake jin muryan su kamar fada ita da hjy maryam.
Wani irin takaici yaji a ranshi da sauri ya taka ya karasa shiyan fada sosai sukeyi wanda bai tsaya sauraran abindaya hada fadan ba yace haba mama haba dai.
Rai bace yake maganan tare da ba hjy maryam hakkuri batare daya damu da abinda ya hada fadan ba.
Gumi ya dinga karyo mai na bacin rai kadan ya rage hawaye ya zubo mai a lokacin don takaici ganin hakan yasa jikin su yai sanyi suka bar tankiyar da sukeyi din.
Merry ce a tsaye kofan dakin tana kallon abinda bata saba ganin wanan halin na sarakuwar nata ba.
A ranta take fadin wai wanan matar itako ta haifi my dear ko dai mum din shi bata nan ne amma kuma yanzu step mum din shi taga fada min inzo dakin mahaifiyar shi mu gaisa ma.
Itace dai mahaifiyar nasa don suna kama da kanin sa habbib sosai dan juyowa hjy tayi taga merry tsaye daga kofa tana kallon su.
Dan wani malalacin kallo hju jummai tayiwa merry tana fadin au ashe tare kuke tafe kace ta shigo mana ta tsaya tana kallon mutane wani iri.
Da hannu ya kira merry ta karaso zuwa inda yake sai data zauna ta fara gaida su bayan sun amsa ne hjy maryam ta juya tana fadin yaya ni kingana tafi tunda kinyi baki.
Wani kallo tayiwa maryam din tare da fadin babawo din ne kuma baki ke fa sai ana zaune kalau kike takalan mutum.
Yaro ne dakan dazo ya zubar da sharan da ake tarawa a kowani part yayi sallama da ledoji a hannun shi yace gashi hjyan shiyan can tace in shigo dashi.
Merry tana ganin ledan ta dan dago tace no retuning to her is her own tana bata fuska hjy sukayi tsaye suna kallon ta kasa hakkuri tayi tace wanan kuma kayan waye.
Bai dago ba yace na maimuna ne tazo mata dashi ba wani abu bane a ciki sai tsaraban yarane da sauri hjy tace kai ilu kawo ladan ka wuce.
Cikin harshen turanci merry tace no ma is not you on is for other hjy tana fadi tana dan buga hannun ta guri daya cikin bata rai.
Hjy tace look merry exchange words with you ki bar wanan kayan a nan daga haka ta juya wurin umar tana fadin ka fara ganin abinda nake fada maka ko ?
Mama ki bar wana zancen hakan bai dace ba wallahi irin dawainiyar maimuna gareta yasa ta sayowa yaranta chuculet.
Nan babu yara na datun farko damu ra saba zata san wata maimuna ne can ?
Mikewa meery tayi duk suka kalleta lokaci guda yana tambayanta ina zuwa tace the other part daga haka ta fice daga part din.
Ehyeh wanan kafirar dani take wasa zan sasaba mata a gidan nan ita wacece da har zatai bugun gaban kanta ka fada mata ta dawo nan yanzu ko in saba mata tasan halina.
Yacw haba mama hakan bai dace ba gaskiya bakuwace fa kuma su ba al,adan su bane hakan suna zamane da wanda zuciyan su ya kwanta ne.
Babawo kana son mu gama dakai lafiya to ka kiyayyeni a gidan nan wallahi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button