NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

NIGERIA LAGOS, , ,

Karfe bakwai na safe muka sauka Nigeria ta birnin ikko jirgin mu ya sauka nayi mamakin ganin wai yaya yana da gida a garin.
Maria ta biyo don dama kudi taje nema a can kuma ta samu yaya na bata hakkin ta yadda ya kamata.
Wanan yasa tace ba zamu barta ba a can dama tana son zuwa taga gida daga nan hakan yasa mukazo tare da ita kan sai munje kano tare taga wuri zata dawo ta tafi gida.
Ina jin dadin zama da maria sosai don bata da matsalan komai ta ko ina don hakane zaman namu ya dore sosai da ita.
Kwanan mu biyu a lagos wai sai yara sun huta yace kuma yana da abinyi duk da banga yana wani fita ba yana gidan ko wani lokaci makale da yaran shi a jiki.
Al,amarin yaya yana ban mamaki wani lokaci duk da na saba yanzu da irin halaiyan shi don dole na koyi wasu daga cikin halaiyan nasa.
Bai fadawa kowa zancen zuwan mu gida ba haka kuma ga maganan shi na gane nima baison in fadawa kowa zamu zo din.
Jirgin rana mukabi zuwa kano don haka hudu da wani abu muna cikin gidan shi na Kano inda gaba daya fasalin ginan gidan ya canza min ba tsarin farko akayi ba yanzu.
Anyi gyare gyare da dama a gidan an canza fasalin gidan da girman gida ya kara fadi da tsawo sosai ya koma wani aljannan duniya.
Mun samu ma,aikata maza uku da mata biyu dattijuwa da yar karamar matashiyar yarinya duk daga wurin Nasir abokin shi suka fito.
Abinci lafiyaye muka samu sun hada muna a falo muka yadda zango muka dan huta suna gaisawa da Nasir da Aliyu daya dauko mu daga airport wanda mamaki ya cika shi na ganin mu haka tafe babu sani ga iyali mun tara.
Yara kyawawa kamar mutun ya sace su don kyawo daga ba sai an fadama ba tashin turai su AC ta ko ina yana tashi a gidan.
A karshe na mike na shiga daga ciki don gabatar da sallah dake kan mu maria kuma ta kwashi yara zuwa dakin da Aliyu ya nuna muna nasu.
Sai Sultana ce ta makale min don ganin bakon yanayi taki yarda tabi maria tunda ya fita da sunan Sallah basu shigo sai dare dashi da Aliyu suka zauna sukaci abinci naji sun dauko maganan siri na basu wuri.
Da safe suke jin yazo a bakin Aliyu saidai daga haka bai kara masu ba sun dai san dan uwan yazo don yace ya aikeshi Yola zai tafi ya dawo a ranan kuma yake son ya dawo kano.
Uwar tace au yaushe ya sauka garin yace cikin dare suka zo jiya daga haka ya fita baiko tsaya ba da suka gaisa da mahaifin su kuma gaisa yake fada mai zai tafi yola yayan ya aikeshi.
Yana kwance bai fito ba nice dana tashi na fito wurin maria da yaran na duba su daga nan na zauna muka basu abinci.
Abdulsalam ne ya damu da tambayan daddy daddy na kaishi dakin da yake shigan yaron wurin shi yasa ya taso suka fito tare ya zauna dasu nan suna masa shirmay har lokacin a kage nake inji yaimin maganan zuwa gida.
Sai bayan ya karya ya sullace jiki daga yaran ya tafi yai wanka ya fito zuwa lokacin nima na shiga dakina nayi wanka na fito a cikin wata doguwar riga din kin yan chaina.
Rigan har kasa sai gurin hannaye aka budashi hannunwan suka dan sauka shara shara sai gyalen su da nayi rolin din kaina dasu kayan sun kara haskani sosai sun fitar min da shape dina waje.
Ina kara gyara fuskana ya shigo yana fadin kin shirya mu shiga gida mu gaida mutanen gida nace a shirye nake zamu iya zuwa yanzu ai .
Yaran fa nace nasan maria ta shiryasu tun dazun amma yanzu zan fito in duba su ya fita yana waya daga dakin.
Kara duba kaina nayi sosai banda makusa ta ko ina na dauko jakkana na fito tare da jawo kofan dakin na murza key don ban san irin mutanen da zamu zauna dasu ba a lokacin.
Da ganin shiga kasan akwai sirki a cikin lamarina yanzu don ba shigan mu na matan hausawa da muka saba nayi ba saboda sabo tun a can.
Wurin maria da yaran na leka nake fada mata zamu shiga cikin gidan mu ta kula da gida kafin mu dawo ta amsa da yes ma.
Kafin ma in fito na samu har ya fita da yaran suna mota zaune suna jiran fitowa na lokacin tun fitowana ya kura min ido wanda ban san dalilin yin hakan ba nazo na bude motar dake sheki da walkiya baka wuluk na shiga na zauna ya tayar da motar muka dauki hanyar gida sai bin ko ina da kallo nake ina tuna abubuwa da dama duk wuraren da muke bi zuwa islamiya wasu ancanza masu falin gina anyi shaguna wasu kuma an rushe ga baki daya ancaza ginan nasu kano ke nan ta dabo tunbin giwa koda may kazo anfika sukace.
Idona na lumshe a hankali cikin yanayintunanen irin karban da fassaran da hjyn su yaya zatai mun idan mun shiga gidan.
Da farkon shigan mu babu kowa a haraban gidan namu shine tsakiya Abdulsalam da Abdulrahaman suna daga ko wani gefen shi ya safa Sultana a kafadan shi.
Sai ni dake gefen shi tafe da yar hand back dina da nake rataye dashi a kafadana cikin shigata ta alfarma da daukan ido.
Daga part din Amma murja ta fito da gani fita zatayi a lokacin ganin mu kawai tayi tafe da farko bata sheda mu ba sai daga baya ta fara gane yaya ta sake waro ido da kyau tace A ruwa ?
Sai kuma ta juya da gudu tana ihun kiran Amma da mama ga Aruwa ga Aruwa Amma.
Ihun ta ya kara jawo hankalin sauran mutanen gidan lokaci daya hjy maryam ta bude kofa da sauri ta fito kafin kowa ya fito.
A,a sai kuma taja tayi turus ta tsaya tana kallon mu da mamaki tace ikon Allah duk wanda ya fito abinda yake fadi ke nan sai a kallemu cikin mamaki.
Kowa ya kasa karasowa inda muke sai fitowan Amma data fito tana fadin a, a, a lale lale lale marhabin da mutanen turai.
Lokacin na wuce yaya da sarsarfa na isa wurin ta da gudu na rugume ta sai hawaye a lokaci daya suka zobo min.
Itama Amma kukan ta fara hjy maryam ta karsa inda yaja ya tsaya yaran suna make mashi a jiki cikin rashin yarda.
Ikon Allah tana mika hannu zata karbi Sultana ta kara make mahaifin ta sosai alaman bata zuwa ta mikawa su Abdul suma suka yi kamar yadda yarinyar tayi da farko.
Wanan abinda mamaki yake yara har sun kai haka bamu da labari a daidai lokacin da Nafisa ta bude kofan part din su ta fito tana ganin shi da yara taja ta tsaya da mamaki sai kuma ta juya da gudu ta koma ciki tana kiran sunan hjyn su.
Aruwa duk yaran kine wa yan nan diyan murja da farin ciki ya kasa boyuwa a fuskanta tana tambayana.
Na dago kai ina girgiza mata kai nace yaran ki ne ba nawa ba cikin zolaya tace A ruwa yaushe kika haifi yaran nan haka bamu sani ba ?
Amma ta sakeni tana mayar da hankalin ta inda yaya yaja ya tsaya da yaran yana kallon mu yana murmushi.
Na dago kai ina kallon part din mamu da har lokacin banga wanda ya fito ba daga part din a daidai lokacin Fauziya ta bude suka fito da gudun su a cikin murna.
Nima da sauri na karasa na rugumay su ina murnan ganin su mun dade rungumay da juna dasu.
Saudaki kakai miskili sai kuma ta fashe da kuka shidai murmushi yake a fuskan shi yana sauraren ta.
Kafin yace may kuma nayi Amma daga zuwana yanzu ban yarinyar in dauka ka make ya ka hana mutane iya shegen ka umar yayi yawa saidai addua kawai.
Kin zuwa sultana tayi wurin ta a nan ya fara tafiya da yaran yana fadin bari mu shiga wurin mama mu gaisa.
Yaja yaran shi suka nufi hanyar dakin mahaifiyar shi sun rigani shiga don haka ban nan suka fara kwasa dashi.
Yana shiga tana zaune a cikin mamaki takaicin labarin da Nafisa tazo mashi dashi yayi sallama ya shigo falon.
Yana aje yaran saman kujera tare da fadin mama mun samayku lafiya ?
Lafiya ta amsa mai a takaice tare da fadin wa yan nan yaran fa daga ina kazo dasu kuma yaran waye kuma ?
A daidai lokacin da ya kara rungume Sultana a jikin su su Abdul suna haye mai jiki cikin nuna shi din mahaifin su ne.
Saidai hakan bai hana hjy yi mashi wanan tambayan ba ya dago kai a hankali yana fadin jikokin ki ne mama yaranane.
Babawo yaran ka ko may kake fada min haihuwa kayi da wanan yarinyar ko may ?
A daidai lokacin muka shigo part din tare da murja da fauziya da sallaman mu don yana wucewa Amma tace jeki ki gaida sarakuwan ki.
Shine muka nufi part din ina rike da hannun fauziya a makale dani muka shiga part din.
Sallama mukayi yanayin da muka same su a ciki ya nuna muna wani magana sukeyi mai muhinmanci a lokacin.
Har kasa na kai irin gaisuwan al,adan malam bahaushe cikin ladabi nake gaishe ta da mama ina wuni mun samay ku lafiya ya gida ?
Sai daya dago kai ya kalleta tace lafiya tana basarwa mun anzo lafiya ta fada tana kawar da kai gefe.
Lafiya kalau na fada saina koma na zauna a kasa nayi shiru tare da dukar da kai ina wasa da hannun Fauziya.
Falon yayi shiru na dan lokaci sai shi ke dan hira da yaran shi yana tambayan su may suke so.
Hjy dake mai kallon kasa kasa imani da takaici ya kashe ta a lokaci daya don gaba daya ma bata a cikin hayacin ta a lokacin.
Can na dago ina fadin zan shiga in gaida mutanen gida bata tanka mun ba sai shine yace kada ki dade kin san yaran nan ba sake jiki zasuyi ba idan basu ganin ki a kusa.
Ka bata yaran ta ta tafi dasu wurin kakannin su mana bazasu tafi bane idan ban tashi ba yacewa uwar .
Tayi mai wani irin kallo na kaidin tare da kawar da kanta gefe daya kokatin amsan Sultana nayi daga hannun shi akai sa,a yarinyar bataki ba a lokacin ta biyoni muka fice tare muka barsu nan.
Zama yayi har ya gaji batace dashi kalaba karshe ma tayi wani nishi ta fice daga falin zuwa cikin dakin kwanan ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button