NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Muna zaune dashi a falo wayan shi yai kara Aliyu ya ambata yana kallin lokacin agogon wayan nasa.
Sun gaisa sama sama Aliyu ya shiga jero mai matsalan da aka samu da hukuncin da kawu ya dauka kan maganan.
Yace please Aliyu don Allah kada ka kara kirana kan wanan maganan don ko me sukayi ai hjy ce tajawa kanta tunda kowa ya fada mata gaskiyan halin wa yan nan mutanen .
Ina zaune kamar ban sauraren abinda suke fadi a lokacin don na mayar da hankalina gun yarona ina wasa dashi.
Saidai hankalina yana ga abinda suke fadi a fakaice naji ya kashe wayan yana jan tsuki tare da fadin sun ma rainawa mutane wayau.
Na dago kamar ban fahince shi ba ina fadin su waye kuma dan kallona yayi kamar ba zaiyi magana ba can kuma sai yace wai wanan matar ce .
Uwar yarinyar nan Samira tazo gida da fada har abin ya kaisu ga bugaiya har suna kwance asibiti Nafisan da mama .
Ita mama ta tabu a bayan ta da hannu ta samu kariya itako Nafisan dai har yanzu bata farfado ba.
Innalillahi nace ya akayi hakan ya faru kuma yace maganan ne babu dadin ji ai yana mikewa.
Nace yanzu ya ake ciki don bai kamata a kyale wa yan nan mutanen ba gaskiya don rainin wayau nasu yayi yawa wallahi.
Kawun ki ai ya kashe magana don yace a sake su su koma gida a dan razane nace an sake su kuma may yasa kawu zaiyi haka kuma ?
Yace ko nine shi haka zanyi ai don shine daidai ko kin manta yadda mama ta rufe idon ta akan su taci wa kowa mutunci ido rufe.
Don suyi mata haka kema kin san daddy ba zai kyale su ba ai dole ya dauki fansa tunda ta nuna tana son su fiye da kowa.
Allah ya kyauta nace ya wuce ciki yana fadin Amin rai bace don nasan ba zai juri zaman da mukeyi ba a lokacin cikin yayan muna hira.

Washe garin wanan jidalin ne mamu ta iso gida ta samu wanan labarin mai tayar da hankali.
Ta samu kawu ya hana kowa ta bangaren shi zuwa asibitin ga hjy maryam da gulma ya addabeta tana son zuwa kada a bata labari da ba daidai ba.
Ga kuma gulman dawowan mamu da abin arziki da canzawan ta daya tayar mata da hankali sosai tana son samun abokin rage mata nauyi wanda zasuyi gulman hakan dashi.
Gaba daya mamu dan lokacin da tayi a can ya sauya mata dabi,un ta ta koma wata irin classic lady a idon kowa.
Yanayin ta gaba daya ya canza a lokaci guda sai tarin dukiya da aka hadota dashi ita da yara suka dawo Nigeria dashi.
Abin sai ya taru yaiwa hjy maryam yawa saidai da yake gulmane haka ta taushe zafin da takeji taje gun mamu tana tsugunta mata abinda ke faruwa bayan tafiyan ta.
Mamu dai kallon ta takeyi tana sauraren ta da mamaki a ranta tana fadin hali zanen dutse don har yanzu hjy maryam na nan da halin ta ashe.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:21 – ????????????: Tun shigan shi dakin nake zaune ina nazari a raina irin rikicin da aka kwasa har takai wanan abin ya faru a tsakanin su haka.
Na dade yaran suna wasa ina zaune sai jefi nake dan saka masu baki ga harkan su don Allah ya taimakeni.
Basu da yawan hayaniya da magana idan kaji kuka ko fitina sai idan sultana ce ta jasu fada kuma ita ke kuka a karshe.
Ban tashi ba sai da naga yaran duk suna jin barci a lokacin nasa maria ta kaisu daki don akwai school washe gari.
Na dan tsaya da maria dake aikin gyaran falon sai hadawa yaran abinda zasuci da safe don tafiya zuwa school.
Kafin in koma dakina inyi wanka lokacin fauziya da Abbati sun dade da yin barci ko haka na samu daman shirina tsab na bar dakin nawa zuwa dakin yaya wanda a zatona nake dauka yayi barci ko a lokacin.
Saidai ina tura kofan na samu ganin akasin hakan don yana zaune ya tasa computer a gaba yana aiyukan shi hankali kwance.
Sannu da aiki nayi mai tare da samun wuri na kai zaune a gefen shi naji lokacin da ya sauke ajiyan zuciya a fili ya dan dakatar da abinda yakeyi yana kallona.
Yaran sunyi barci ke nan ya tambayeni nace tun dazun suka kwanta ai mun tsaya da maria ne a falo.
Ba tare da ya dago kan shi ba yake fadin yanzun na kare waya da Ahmed da sauri na dago kai ina fadin mijin salma ya gyada min kai kawai batare da yin magana ba.
Ya fara aiki da kune na tambaya ina kallon fuskan shi sun fara ya ban amsa a takaice ba tare da dago kai ba har lokacin hankalin shi yana ga computer shi.
Mansur na bashi shawara ya dawo kano da zama don jigila zai mai yawa tsakanin bauchi da kano din sai abin hawa da zasu samu don rage dawainiya gare su.
Kallon mamaki nayi mai don ban taba tsamanin Mansur mijin Atika ya samu aiki ba shima a gurin su kamar yadda na roka a sama mashi din.
Hamdala nayi ina fadin kai ban ma san irin godiyan da zanma ba yaya wallahi naji dadin wanan maganan sosai yaya .
Din Atika ta taimaki rayuwana a lokacin daya dace a taimakeni nima yanzu kuma ka wanke min zuciyana da irin sakaiyan da zan mata a kullun shi nake tunane.
Ni nasan ai irin godiyan da zaki mun idan baki sani ba ke ki bari ki gama sai in nuna maki kalan shi.
Dan mutmushi nayi ina girgiza kai kamar yadda in yai min irin wasan nan nasan me yake nufi da hakan.
Nace basai ka nuna min ba yaya ni da kaina nake son in godema ai amma ka dan ban lokaci nan gaba in gama tunane.
Na baki yace yana rufe laptop din tare da juyowa gareni yana fadin idan ban rufe wanan abin ba zaki saka in tura sakon da bai dace ba .
Ganin ya rufe laptop din yana fuskantana nace mai barin koma dakina in barka kayi aikin ka hankali kwance.
Wanan kuma shine baki isa ba dakin ki dauko me Fauziya tana tare da baba don haka baki da matsala da komawa daki yanzu.
Har kwana biyu ban sake jin halin dasu hjy shi ke ciki ba ga gulma kuma ya cika min ciki gashi ya dace ace na kirata in mata ya jikin.
Saidai ina gudun jawa kaina wata fitina don nasan halin hjy sarai zata iya yaba min bakar magana mai zafi idan na kirata.
Don ba abinda zata so inji bane tunda tsakanun su dasu hjy sabuwane abin ya faru hakan akwai kunya da nauyi gareta.
Hankalina kwance nake karatuna dagani har yarana yayin da yaya shi kuma yake faman kujiba kujiban neman haliyan shi ko yaushe.
Mutuwan mahaifin merry da wata daya yake fada min zancen bukin rufeshi ya taso don haka zai tafi a cikin sati mai zuwa.
Kallin shi nayi nace ai muna zamu tafi don mu nuna mata kulawa tunda abin ya shafe ka ai amma idan hakan ba zai zama matsala ba.
Babu wani matsala don kun tafi kawai dai bana son ina danganta lamarin sune daku ya bani amsa.
Wanan ai mutuwa ne don haka ya kamata muje a jajanta mata don in ba a yanzu zamu tafi babu lokacin da zamu hadu da ita kuma.
A kwai lokaci don ina ganin kina gama karatun nan gaba daya zamu tattara mu koma gidane don na gaji da zaman kasan nan zan koma gida inyiwa kasata aiki haka.
Dadin hakan naji har kasan raina a lokacin nace Allah yasa hakan shine alheri a garemu ya amsa da Amin.
Washe gari da ya fitane sai gashi yazo muna da kayayyaki da nawa dana yaran dukka bakake wulluk sai dai mu mata namu jallabiyane dogaye yan kasan Jordan.
Sai mazan yara dashi daya saya masu suit bakake daidai su masu kyau sosai.
Ni dai banyi magana ba duk da naji zafin hakan kenan dole idan munje muyi akidar su ke nan a gurin yake nufi.
Ni na dauko zancen tafiyan don haka dole na shanye komai a raina na nuna ba komai a hakan.
Shirin shiga US mukeyi wanan satin ga tafiyan yai muna daidai don andan samu break a lokacin daga ni har yaran namu haka yasa zamuyi tafiyan babu takura.
Saidai a raina ina tunanen irin taron da zamu samu a wurin merry din idan mun tafi koma dai menene ai kulawa zai kaimu.
Bai fada mata komai ba game da zuwan mu sai ganin mu kawai merry tayi a kasan sai dai ba,a gidan muka sauka ba kamar yadda ya tsara.
Mun saukane a wani katafaren hotel mai kyau da tsaruwa nayi mamaki a raina ganin a hotel zamu sauka ba a gidan merry din ba.
Saida yaga komai yayi yadda yake so damu kafin yai muna sallama zuwa gidan merry din.
Rayuwana yaso ya baci da hakan da yai muna sai da wata zuciya ta gargadeni kan hakan don zan bata rawana da tsale idan na nuna hakan.
Asalima ai wanke kaina da gyaran kaina a idon mijina nake hakan tunda ban ko san yaya merry din zata karbe mu ba ma.
Ban yarda mun fita ko ina ba muna dakin daya kama muna din munci mun sha daga nau,in cimar da suke dashi a cikin hotel din tare da dan taba hira da maria.
Na irin yanayin kasa da namu kasashen irin bambamcin kasashen da rayuwan mu a Africa don ko wani lokaci su basu taba rabuwa da ni,ima a turai.
Banyi barci da wuri ba na dade ina zaune ina adduoin neman kariya a wanan tafiyan namu daga ni har yarana na gama na shafa tare da nade abin sallah na koma saman kujera na kwanta don in barsu su sake a saman gadon .
Can barci ya dan fara dauka na bayan na gama dan tunane tunanen yadda haduwan namu zai kasance a gobe da merry din.
Mafalki nayi wai merry tana ganin mu ta haukace a wurin tayo kaina ni da yaran tana fada tana fisge fisge ana riketa sai kawai ta nufo gadam gadam zata caka min yuka.
Da sauri na zabura daga barcin ina fadin innallilahi sai zufa nakeyi lokaci guda duk da sanyin dake dakin na AC dana yanayin garin.
Kasa komawa barci nayi ina bin dakin daya dan gauraye da duhu da dan haske da muka bari don haska dakin.
Wani irin tsorone ya rufeni a lokaci daya sai adduan da duk yazo min a rai nake karatowa don neman kariya ga abinda na gani a cikin mafalkin nawa.
Tsoro iya tsoro na jishi a wurin wasa wasa ga barci ya gagareni mikewa nayi zuwa ban dakin na kara dauro alwala na fito nayi sallah neman kariya ga duk wani abin kin da zai tunkaremu a wanan tafiyan.
Daidai lokacin da yaya yake can suna kwasan rikici da merry din a gidan ta kan rashin zuwan shi da wuri da baiyi ba duk da kuwa tasan a satin ya dawo yai tafiya zuwa kasan chaina wani aiki a can.
Yaya baidai fada mata tare damu yazo ba sai sauraren ta yake har tana fadin gabadaya ya sauya mata daga umar din data sani zuwa wani umar din.
Zagi da cin mutunci dagani har shi babu wanda batai muna ba tana fadin dama itace ba a so dashi yasa aka aura mashi yar uwan sa gashi kuwa yana nuna mata hakan a fili.
Yana kwance yana jin ta uffan baice da ita ba lokacin don ranshi babu dadi don bayan kudin daya bata don tai hidimar saida bai fito fili yace da ita don bukin ya bata kudin ba.
A gaskiya irin kudin da merry take wawura gurin shi ko kwatankwacin rabin shi bamu samu nida yarana .
Nasan da hakan amma ban taba nuna bacin raina ba a kan hakan tunda bani na nema masa ba.
Sai washegarine ya shiya da safe don duk hankalin shi yana gurin mu a lokacin saboda banda layin kasan a wayana.
Dakin ta shigo tana kallon shi cikin mamakin ganin ya shirya a cikin bakaken kaya kamar shigan su don bata tsamaci hakan ba sam a gareshi.
Mamakin ganin hakan yaki boyowa a fuskanta daga inda take tsayen tana mai kallin mamakin sai ta fashe da kuka mai kama da kukan murna lokaci guda.
Tana karasowa inda yake ta fada jikin shi tana ci gaba da kukan nata a hankali bayan ya rugume tane ya fara dan bubuga mata baya a hankali.
Sun dan dade da hakan kafinta zare jikinta daga nasa tana mai dago kanta tare da mashi godiyan yin hakan da zaiyi mata don bata taba zaton zai tafi wurin birne mahaifin nata ba .
Don tun bayan rikicin su a kan queen data nuna mai bata yarda da yarinyar ta koyi addinin shi ba wanda hakan ya kawo rashin jittuwa har wanan lokacin a tsakanin su suna sama sama da junan su ne kawai.
Bata kaiga karshen mamakin ta ba sai lokacin daya kwaso mu zuwa inda suke bidi,an nasu muka tun karo wurin a cikin shiga daya burge kowa don jallabiyan jikin mu dake daukan ido da nuna martaban mu a gurin.
Dan nisa kadan da inda suke muka tsaya muna nuna namu jimamen kan mutuwan mahaifin nata daya mutu ya karawa kasa nauyi.
Juyowan da merry zatayine tana magana da wata ta kusa da ita ta hango mu a inda muke tsaye din tare da iyalina .
A bazata ta ganmu saida ta kare bude idanuwan ta don ta tabbatar da abinda ta hango din a lokacin.
Sai bayan su a halinsa sun dibi kasa sun fara zubawa a ramin sauran jama, a suka dinga diba daya bayan daya suna zubawa sai masu kada flawer a ramin da sauran tarkace.
A wurin daida muke nan muke ban yarda mun gusa ba har lokacin da suka kare akidan su aka fara watsewa bayan addu,oi.
Yana rike da merry dake ta faman share hawaye a fuskanta sai queen da itama tasha adon bakaken kaya da suka matse jikin ta sun fitar mata da suran ta sosai.
Mutane merry suna zuwa daya bayan daya suna dan rungumar ta alaman yi masu sallama da jajanta masu mutuwan .
Alama nayiwa maria mu tafi inda motar da mukazo da ita take tun kan a farga damu a wurin.
Duk da hakan saida wasu suka dinga kallon mu sun dai san mu musulmai ne tun daga yanayin shigar mu har zuwa tsarin rayuwan mu a gurin.
Merry ce suka iso inda muke tsaye a gutin motan muryan ta naji tana fadin Fatema you are welcome for dis funeral.
Sai kuma ta fara hawaye don maganan da take son fada ya makale a bakin ta saboda kukan daya zo mata a lokaci guda.
Tausayi sosai ta bani a gurin nima hawayen ne yazo min na fara dan sharewa da gefen gyalena dake rufe a kaina nayi rolling.
A cikin shakaken muryan tana kuka take fadin a tafi damu gidan su inda za,a hadu ayi last respect ga mamacin a can.
Sai da ya dan yi magana da ita kafin yazo ya shiga mota muka dauku hanya zuwa gidan mahaifin merry din .
Gidan yana makil da ire iren su saidai akwai musulmai dake da dan alaka dasu a gutin saidai bamufi yan tsiraru ba a gurin.
Merry ta bamu lokacin ta sosai a wurin koda tana data ciki dai ta boye muna hakan don duk abinda na zata zatai muna batayi shi ba a gurin.
Sai na dangata al,amarin da karfin addua ya kai ga hakan don a yadda merry take jin zafina a ranta.
Tana ganin nice na shigo rayuwan su na raba farin cikin dake yabe a tsakanin su ina kokarin raba jin dadin su koma na raba din .
Merry sam bata yarda da sharing din miji a tsakanin mataye ba don hakan ne koda ya tafi wurin su suke kwasa rikici kafin su dan daidai ta.
Wani zubin haka zaije ya koma ba tare da komai ya wakana a tsakanin su ba wanda hakan har ya fara bin jikin shi ya fara rashin jin dadin mu,amula da merry din ta ko ina a yanzu.
Bamu jima ba do mutanen da suka fara fahintar mu su waye ga merry din dan gulma yana tashi ana kus kus tare da zubo muna ido.
Wanda mahaifiyar merry din ne tabar bakin cikin dake damun su na rashin mijinta ta dauko kishi ta saka a ranta tana ji kamar tayi poisining din mu dani da yarana a gurin.
Ganin yadda uwar ke son muna rashin mutunci ne yasa merry kiranta daki tana ja mata kunne a kanmu kan kada ta yarda ta nuna muna wani halin da bai dace ba.
Koma meye a yanzu na gama mata komai tunda har na iya zuwa tayata bakin cikin bizzine mahaifin ta wanda suke daukan hakan da sai masoyin kane zai ma hakan.
Ko ruwan su bamu yarda mun sha a gurin ba komai aka bamuba wanda muka kalla a gurin.
Indana kara godewa Allah shine yarana basu da daukan ido irin na wasu yara komai bai faye shiga ransu ba a lokaci guda na basu tarbiyan kada su karbi abu a hannun kowa koda ka basu sai su girgiza ma kai alaman basa so.
Da haka mukai sallama muka bar gidan zuwa masaukin mu don a ranan zamu koma London zamu bar yaya a nan don mun gama abinda ya kawo mu kasan US.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button