NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ban kwanta ba sai da nayi sallah na samu batci mai nauyi ya dauke ni can cikin barci na nake jin muryan kawo na mijin mamu yana fadin ina ita sayadi din.

Tana ciki tana barci nasan sai yanzu ta samu barci a yadda ta kwanta a jiya yace tayar min da ita .
Itama matar da ta fadi wanan bata kyauta ba bata ganin fatima yarinya ce kamar da zata sanar mata da wanan magana sanin yadda suka shaku da kakan nata.
Barcin data samu ne yanzu don nasan ta kwana tana kuka jiya yace kin gani ba wanan ai ba sakon yaro bane wasu haka suke basu da tunane.
Mamu ta shigo ta tayar dani na samay shi tsaye a falo yana jiran fitowa na daga daki na fito na dan rusuna ina fadin kawu ina kwana ?
Ya amsa min fuskanshi ba yabo ba fallasa yace har yanzu kukan kike yi fatima ?
Haba fatima ai ciwo ba mutuwa bane daina damuwa insha Allahu zata samu lafiya abubuwa ne sukai min yawa yasa na shagala da zancen kakanki a raina.
Murya Amma ne ke shigowa part din mu wanda zance duk zuwa na gidan baifi sau biyu ba data shigo part din sai kuma wanan karon.
Tana shigowa tace ashe kana nan yanzu maimuna ke fada min yar nan she kakanata jikin ya motsa kuma a can.
Ta juya wurina tana fadin haba A ruwa kiyi hakkuri ki daina kuka ciwo bawai an rabo bane gaba daya daurowa yake idan Allah ya saka ma bawa lalura sai addua yanzu.
Hawaye masu zafi suka zubo min wanda ban iya bambance na maynene ba ko na ciwon manjo ko kuma na irin so da kaunan da ake nuna min a gidan kawuna tsakan shi da mamu da Amma.
Wanda ada ba debe tsamanin samun irin wanan kulan na mahaifa a gareni sai wurin mahaifiyar uba da take kulani ita kadai wanda kesa nake ganin banda kowa a duniya sai ita.
Tashi ki shiga ki kwanta abinki tunda akwai barci a idon ki kawu ke fadi na mike tsam na nufi dakin kwanan namu.
Barin wurin keda wuya baji mamu na magana kasa kasa sun dan dade a wurin suna tataunawa wanda ban sa may suke magana a kai ba lokacin can dai har na daina jin su ko don barcin daya dauke nine lokacin.

Amma da ta fito daga part din mu tana komawa ta samu Aliyu da umar a falon ta sun shigo gaida ita basu samay ta ba.

Tana shiga ta gansu a zaune kowa hankalin shi yana ga wayan shi ba maima wani magana a cikin su.
Da sallama a bakinta ta shigo part din kamar yadda tsofi keyi a duk inda zasu shiga wuri koba kowa sai sunyi sallama a guri.
Dago kai sukayi suna amsa mata sallaman ga baki dayan su Aliyu yace ji wanan tsohuwar ke da baki da kafa ina kika je da safen nan haka ?
Tace bari kaidai yar nan A ruwa ce aka bugo wanan wayan wai kakarta mahaifiyar ubanta bata da lafiya.
Waye kuma keda wanan sunan banzan wai a ruwa ke yanzu har kina da kafan shiga makwabta a hakan.
Kaji ja,iri sai ana maganan kwarai ya jefo shirmay yar nan mana yar gurin maimuna na dake gidan nan.
Ba wanda ya amsa masu daga ciki ita kan taci gaba da fadin wallahi abin akwai tausayi yar kaka wace take gani taji sanyi yanzu kuma ance kafa ba lafiya gara ni ai tashine aiki a wurina yanzu.
Haba Amma ko gausawa bamuyi ba kin damay mu da zance wata wace bamu da hadi da ita a wurin mu.
Dan nan kana da imani a ranka kuwa Amma ta tambaya cikin mamaki da bata fuskanta.
Yanzun kai ko tausaya mata bakayi a matsayinta na tsohuwa balle ace yarta jinku ce ita aiko don yar uwanku ka tausaya mata da addinin ka.
Ke kowa fa ba irin ki bane sarkin tausayi haka kawai kina kokarin lika muna yarinya a jiki don kawai wani alaka can.
Haba please kasan may kake fadi aiko don zamanta a gidan nan ko yar aiki ce zamu tausaya mata balle yar maimuna ce fa yarinyar.
Ku daina irin wanan maganan please ya karasa yana maida fuskan shi a wayan shi sai Amma tace.
Fada mashi dai dan albarka shiya nake kara son ka saudaki don ka biyo ni sak wurin fadin gaskiya da tausayin mai bukatan a tausaya mai.
Ni da banda tausayi sai kisa a rufeni ki daina ganina a duniyar nan ga baki daya .
Wai ba abinda habbib ya karato ke nan ba Amma matar tana ina ne sai ya duba ta ido Aliyu ya zaro waje da sauri yana fadin wani habbib din zaije aikin kalar dangi.
Dakuwa ta nuna mashi da hannu tana fadin kaci gidan ku yaro ana baka kana roko idan baiyi ba abu na kudi sai wasu suyi.
Ke ma dai kinsan habbib bai wanan aikin don bai fara duba kowa ba a kasan nan balle ya fara da tarkacen ki.
Wai wanan dan may ka dauki duniya ne kadai bi duniya a sannu don Allah bani fatan haka a cikin zurian dana haifa.
Rashin imani da tausayin mabukaci ba wanda yana cikin abinda ke kai mutum Aljanna idan an dace anyj wurin daya dace din.
Amma don Allah dai ki barshi zanyi magana da habib din ansan abin daya dace a kai tace sannu dan albarka yadda kake da zuciyar nan ubangiji ya tausaya maka ya jibanci al,amuran daka sa a gaba duniya da lahira yasa maka albarka ga zurian ka ya baka mata tagari mai irin zuciyar ka.
Yace Amin amma na gode Aliyu zaiyi magana ya daga mai hannu yana fadin please please ka barta hakana kana sa kaina yana ciwo wallahi .
Yana fadin haka ya gyara ishishirewa saman kujera yana dafe kanshi da hannun shi daya mikewa Aliyu yayi yana fadin ke dama ba a zuwa maki abin arziki ni kinga tafiyana .
Lokacin ya cire hannu a goshin shi yana fadin jinan kada ka fara ka tari habib da wanan magana yace naji bros ya fice.
Ban san yaya akayi ba sai kawai naji ranan mamu na magana wai za a dauko manjo a dubata a nan kano ranan murna a wurina ba,a magana ina Allah Allah gari ya waye in bude ido inga manjo don ance Addah ce zata zo da ita.
Washe gari basu iso ba sai bayan la,asar Ahmed aka tura ya dauko su tasha daga shagon su ko gida baizo da ita ba don yanayin daya ganta ya wuce asibitin da akai bucking da ita daga can .
Sai zuwa yayi yake fadin abinda ya faru a can mamu ta samay su bata fada min halin da ake ciki ba don kar hankalina ya tashi.
Azumi yana damuna gashi na gama girkina mamu ta fita ban san inda taje ba sai shirun yayi min yawa na yanke shawaran muje part din Amma kafin lokacin shan ruwa yayi.
Muna shiga ban kula da mutum a falon ba na nufi inda Amma take ina zhwa na kwanta saman jikin ta ina fadin Amma zumi ga mamu ta fita tundzun bata dawo ba.
Idan ta dawo wani abin zatai maki na gyara kwanciya saman jikinta nace wallahi Amma yau akwai azumi sosai.
Ta dan turani tana fadin ke dallah ja can raguwar banza da kike hawan jikina an fada maki ni ban azumin ne halan ?
Muryan namiji naji a hankali kamar yana rada nayi saurin juyawa wurin yana zaune yana waya jikin shi saye da yadin shadda mai laushi da maiko brown color saj walkiya takeyi.
Tun ganin da nake mai da yazo wanan karon na ganshi a cikin kayan mu na gargajiya sai na rasa da kayan mu dana turawan da yake sakawa wani yafi mashi kyau a lokacin.
A hankali na mayar da kaina baya ban kara kallln shi ba abinda naji yana fadi da harshen turancine ya dan girgizani.
Mace mai suna merry yake waya da ita sai dai wayan nasa kalaman rarashine ne yake mata inda yake fadin tayi hakkuri ya karasa abinda yazo yi.
Sai kuma ya tsaya dan saurarenta can naji ya fadi a dan tsawace kada ta soma ta biyo shi nan ko ranta ya baci saurin juyowa nayi na dan kalle shi yadda yake magana a hasale kamar mai fada da dan shi.
Nace a raina shegu sun gama watsewan su a turai sai da suka gaji suka dawo gida kilama abokiyar shashancin shi ce ta matsu ta kirashi yanzu.
Bankai karashen tunane ba naji muryan shi yana fadin Amma zan je masallaci lokacin sallah ya kusa tace a dawo lafiya dan albarka.
Yana fita naja tsuki ina fadin kamar na Allah da sauri amma ta juyo tana fadin wa nace wanan jikan naki mana Amma.
Yanzu fa ya gama waya da mace a gaban ki kuma baki masa fadan haka ba tace lah ha,ila ha, illah yanzu yar nan ki rasa wanda zakiwa sheri sai dan nan ?
Sherin may kuma amma inji abu da kunne na kice min sheri da wata merry arniya fa yake waya a gaban ki dan gwara takai min a kai tana fadin lalai yar nan kin iya sheri.
Na mike ina fadin don na fada maki gaskiya shine zaki dangware ni bari ki gani idan na sake zuwa wurin ki duk abinda kikaga dama ki mun.
Na mike tana kirana naki koda juyowa yan kanne dake a takure rashin sanin inda mahaifiyad mu ta tafi suka biyo ni a baya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button