NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:50 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, LA, ILLAHA ILLA, ANTA SUBBAHANAK INNI KUNTUM MINAL ZALUMIN, , , , , , , , , ,

Mamu bata shigo ba sai bayan shan ruwa koda ta shigo bata wani tsaya ba sallah tayi tare da umurtana in biyo ta kitchen.
Sai nake mamakin mai kuma zamu hadda da daren nan bayan mun kammala abincin ranan da zamuci har asuba.
Kuloli ta jawa ta miko min in wanke bayan na wanke ne naga tana ta faman zuba abinci a cikin kulan tare da fadin in zuba ruwan zafi a flask.
Muna gama hadawa Ahmed ya sallama mata tare da shigowa falon namu ina zaune takure saman one seater na dunkule kafafuna a saman kujeran na takure a wuri daya kaman mai jin sanyi.
Shigowan shi bai sa na canza zaman da nayi ba kamar wace ke a cikin damuwa ina ganin shi daga inda nake zaune na gaida shi.
Naji mamu na fadin ka iso ashe yace banje nisa nan muka sha ruwa da Alh a falon shi don kada mu makara.
Bata wani tsaya ba ta kallo inda nake zaune tana fadin ku tufe part din nan idan nafita in na dawo zan buga maku.
Na amsa da to kawai suka fita ya karbi kayan abincin ina mamaki a raina ko may suka samu kuma ?
Ni dai ko da ta dawo na dubi lokaci naga sha daya da rabi na dare na shige na barta a falo zaune.
Washe gari ne tunda safe zanfita na fito tunkan in karasa naji mutum yana waya daga kofan shigowa gidan haka yasa ban bude get din gidan ba na dan saurara inji ko waye.
Daidai lokacin kunne na jiyo yana fadin merry giwa kika sha da cikina a jikin ki kina haukane ko may ban fada maki shan giyan nan zai rabamu.
Gabana ya fadi ina sauri inga ko waye a cikin su yake wanan maganan bansan lokacin dana taba kofan ya bada kara kiiiiiii,
Ya juyo yana duban kofan yaga mai fitowa wanan lokacin da sasafe haka ina kuma mai shi zai tafi ?
Karaf muka hada ido dashi daga cikin nikaf din da fuskana ke rufe ido ya dan dauke gareni tare da ci gaba da wayan shi Umar faruq ne dai wanda yammacin jiya naji yana wayan shedanci da mace.
Yau kuma da safiya na kara jiyo kalamin da ya girgiza min zuciyana daga bakin shi wai cikin shi a wata mace bayan Amma tana fadin baiyi auren fari ba to a ina ya samo mace mai ciki kuma.
Na sakar mai harara bayan na kware dan nikaf din fuskana don ma ya shedani da kyau kuma na jishi.
Da ace a cikin su zanji wani yayi irin wanan magana a kanshi zan iya karyata mai shi a lokacin don shine yafi kowa shiru shiru da dan kirki zaka gaishe shi ya amsa kuma gashi ibada bai wuce shi.
Ke da wata murya a kausashe ya kirani kamar kada in tsaya sai kuma na juya ina dan magana da baiji nace ba sunana ke ba malam.
Ashe yaji abinda na fada yace idan ba sunan ki ke ba waye sunan ki ko da yake sunan ki da sanin shi da rashin sanin shi a gare ni duk daya ne.
Ina zaki fita da wanan safen haka kin wani bat da kama kamar wata ninja dake dan baki na murguda nace ba dai yawan banza zan tafi ba kaga abinda ke hannuna ai .
Juyawa yayi ba tare da yayi magana ba bayan ya sauke idon shi akan litattafan dana rika a lokacin.
Na dauke kai nima na fara tafiya yace kin iya labe kina sauraren mutun ko kamar kada in jiyo sai kuma na tsinci kaina da juyowa ina fadin.
Laben mai zanyi ko inji may inji aikin da kake aikatawa kana fuska biyu a gidan ku ?
Kallon mamaki yake min karamar yarinya da irin wanan maganan a gare shi har yaushe raini ya shiga a tsakanin mu haka ?
Fuska biyu har na wuce yana maimaita magana ta a ran shi koda ya dago kai nayi nisa da tafiya ko haka yasa ya kyaleni bai sake magana ba.
Nikan har nakai makaranta ban daina zagin shi a raina ba ina tsine masu gashi Ahmed ya hana ni fita yau ma ganin ya dade baizo ba yasa na fito sai naga na iso school din a cikin lokaci.,
Muna tashi na dawo gida da sauri don zuwa tafsiri da mukeyi da mamu har lokacin ina mamakin rashin zuwan Ahmed ranan.
Sai dai koda na shigo ban samu mamu ba ta fita na tsaya ina mamakin mai mamu ta samu ne ina take zuwa haka don ban santa da yawo ba yawan zuwa unguwa don ba wasu kawayene gare ta ba sosai.
Wanka nayi bayan na na fito na shirya na hada ma kanne na abinda zasu karya dashi sanan na kara kwanciya ina jiran dawowan mamu anan barci mai nauyi ya dauke ni na barsu suna kallon katun a falo.
Bani na falka ba sai daya na rana koshi fitsari ne ya damay ni a lokacin yasa na tashi bayan na fito daga falo ne na samu mamu ta dawo lokacin .
Tana zaune a falo da yara tana waya sai dai tana ganina tace bari ai zan dawo yanzu dama wanka nazo inyi a gida.
Ta dago bayan ta kashe wayan tana kallona nace mamu fita zaki kara yine kuma ?
Tace eh yanzu ma nake fadin in tayar dake ai don tun da na shigo kike barci a gidan nan kinga sai karfe hudu zaki dora girki idan ban dawo ba ta fada min abinda zanyi,
Bata dade ba ta fita na cewa yan uwana mu leka Amma mu gaishe ta muka dunguma zuwa sashen Amma din a zaune muka samay ta tana gyagyadi ita kadai.
Dan sanda nayi zuwa gaban ta nace agudu ta mike zubur tana waige waige tace ja,ira ubanki sani kika tsorota.
Na turo baki nace ke Amma daga dan magana sai ki kama zagin mutum dakuwa ta kara min tace gidan ku ki fita idona yar nan .
Ni zaki ba tsoro a dakina nace ke halin ki ke nan da anzo wurin ki sai kin batawa mutum rai tace yanzuma waya kiraki ko kinga sakona gare ki ?
Ina jiya nan kikai fushi dani aina dauka zuciyar naki zakiyi a yanzu ma nace da yake kin iya hadi ba inyi fushi ki hadani da mamu ko kiji dadi.
Baki da kirki wani lokaci A ruwa yanzu ki rasa wanda zakiwa sheri sai sadauki yaro natsatse mai hankali da sanin ya kamata .
A wurin ki ba nikan ai a tafin hannu na yake Amma don nasan abinda baki sani ba wanan mai fuska biyun zaki wani ce wai natsatse dashi.
Wani kallon haushi ta aika min nace ai in an kawo maki goyon dan shege kuma na kafira zaki bayani .
A take annurin fuskanta ya kara gushewa gaba daya tace a cikin wani murya da ban taba jinshi gare ta ba.
A ruwa sherin naki har yakai ki kalli tsaban idona ki fada mi wanan maganan lallai da akace da wasa da yaro gara kwana da yunwa na yarda yau.
Ganin ran tsohuwar ya baci sai jikina yayi sanyi nace Amma don Allah kiyi hakkuri naga tobashina ne ban zaci ranki zaikai ga baci haka ba.
Sai naji ta sauke ajiyan zuciya tana tana girgiza kai tace badon kece kikai min wanan wasan ba da yau anjimu a gidan nan.
Shiru nayi kafin in kara fadin yi hakkuri Amma don Allah tace ai ya wuce amma kayiwa dan uwanka fatan alheri shine kyau.
May ye laifin yaron nan da yai tsaye sai da yaga an dauko kakarki an kawo ta garin ya tsaya tsayin daka sai dan uwanshi ya dubata.
Da sauri na dago kai nace Amma ban fahince ki ba wai wa kike magana akai tace barshi kawai idan baki sani ba sai lokacin ta tuna da basu son in sani don kada in daga hankalina a yadda take.
Ganin tayi shiru yasa na kasa kwantar da hankalina kafin in magana sai tayi kokarin mikewa tana fadin lokacin sallah yayi kinzo kin tsatsare ni da wanan surutun banzan naki ni kinga tafiyata zuwa alwala.
Ta barni ina binta da kallon mamaki da sauri wani tunane yazo min nace a raina kodai shi yasa nake ganin mamu bata zama tana busy tun jiya.
Zubur na mike ina kokarin tattara yan kanne dake wasa a falon suka karbe key din suka sheka da gudu.
Ina tafe jiki ba karfi hankalina ya tafi ga tunane banyi aune ba mukai karo da mutum da sauri na dafe goshina da naji zafi ina dago kai don ganin waye.
Habbib ne sun fito zasu mosque da dan uwan shi yace a hasale ke wata irin balagazan yarinya ce mara tarbiya ke mahaukaciyar inace ?
Ka barta yace daga baya shin inji yayan nasu kila iskacin nata zai kawo gare mune da nine ball zanyi da yar iska a wurin nan.
Tsuki yaja yana fadin may yasa baku da tunane wanan yarinyar haka take da rawan kai ku kyale ta kada mu rasa sallah.
Daya bayan daya suka wuce ni suna magana akai a hankali nake bin su da kallo har suka fice gidan.
Naja kafana da kyar ban dade da shiga ba sai ga kiran sallah anayi haka yasa na shige bayi na dauro alwala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button