NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:17 – ????????????: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI, , , , ,

Gida Nigeria kano ta dabo tunbin giwa gidan kawu sani yau tun da safe sun tashi da tashin hankali a gidan don ciwon kawu daya motsa mai tun yana dan yi a tsatsaye har ya kaishi kwance.
A cikin dare ranan dai basuyi barci ba don jikin kawu daya motsa mai da asuban fari mamu ta kira ya Ahmed a waya tana sheda mai halin da kawu yake ciki.
Yana idar da sallah a kofan gidan kawu gari ya dan haska mai don dan tazaran dake tsakanin gidan su dana kawu din.
Ya shigo kai tsaye gidan inda ya tun kari turakan kawu kai tsaye duk ahalin gidan har Amma suna cikin part din nashi lokacin.
Shigowan shi falon da sallama ya nufi inda Alh yake kwance matan shi dun kewaye shi gabaki daya da mahaufiyan har mama hadiye.
Ya dan dade tsaye yana kallon shikafin ya ciro wayan shi yana kiran layin Abubakar .
Ya amsa da gani kofan gidan na iso ba,a jima ba Sadiq din ya shigo falon shima ganin yanayin da surukin shi maigidan su yake ciki.
Ahmed bai tsaya jiran komai ba yace kamashi mukaishi mota ya fadawa sadiq kai tsaye yana kokarin dago Alh daga inda yake kwance.
Shima sadiq din yayi yun kurin dago dayan gefen da yake tsaye duk kawu bai san sunayi ba lokacin don jikin da yake ji din.
Mata da yara sai kuka sukeyi don halin da maigidan nasu ke ciki a lokacin hankali tashe da taimakon Allah suka samu suka saka tsohun a mota an rasa mai karfin halin shiga cikin su don a zaton su hjy ce ya dace ta shiga motan lokacin.
Saidai gane abinda suke nufi yasa mama hadiye fadawa motar a baya tare da Ahmed sadiq yaja motar tasu.
Asibiti suka nufa kai tsaye dashi cikin dan lokaci sun isa Ahmed ya fita ya kira akazo da gado daukan marasa lafiya aka dauki Alh .
Bayan wuce wansu ne Amma tace yau dai kun fara ganin manufar yaron nan da wanan hadin dayayi ga yaran nan .
Yau da yaran nan ba na jikin shi bane, ko suna rakan mu baza muyi bugun gaba dasu haka ba lokaci guda.
Kallon juna hjy da hjy maryam sukayi kafin su fara barin gutin daya bayan daya suna shiga daga ciki mamu tace gwaggo barin shiga in shirya in fito in bisu muga halin da suke ciki a can.
Ba abinda ya batawa hjy jummai rai kamar yadda Ahmed bai tsaya gaida su ba yana kokatin ceton ran surukin nasa a lokacin.
Wanda tun bayan badakalan da sukayi dashi lokacin buki bata kara ganin shi ba sai wanan ranan kuma.
Tana cika tana batsewa ga halin da take ciki na tashin hankali mijin su daya daga mata hankali kuma.
Kamar yadda ko wani gidan da ba hadin kai yake nan ma hakan ne ya faru don basu hada kafa wurin zuwa asibitin ba daya bayan daya suka isa gurin kusan lokaci guda.
Sun samu har an saka mai ruwa ana kara mashi har lokacin bai farfado daga yanayin da yake din ba har lokacin.
Suna zaune daga waje a cikin damuwa saidai babu mai ma dan uwan shi magana ko ta tsiya asalima ko gaisuwa hjy jummai ta yake duk wani alaka tsakanin ta da mamu a yanzu tun bayan faruwan auren yayan su.
Ahmed ne da sadiq suka nufo wurin dauke da lrdojin magani a hannun su wanda likita ya bukata su kawo.
Ganin su yasa sukaja suka tsaya sai lokacin suke gaida su ba tare da wani sakin fuska ba ko walwala a lokacin.
Suna gama gaidasu Ahmed yasa kai ya shige shima sadiq ya mara masa baya.
Bayan shigan sune hjy jummai dake ta hare hare taja wani dogon tsuki tana kau da kanta gare su.
Tare da dan maganganu ciki ciki wanda ita kadai tasan abinda take fadi a lokacin don ba wanda ke jin ta.
Daga nan kowa dai ta juya ba maiwa wani magana har lokacin kowa da abinda ke ranshi a lokacin.
Can hjy jummai ta mike ta nufi kofan dakin ta shiga sai lokacin hjy maryam ta iya kallon mamu da zuman munafunci sai mamu ta kauda kai gare ta don mamu ta gane nufin ta.
Ahmed ne ya leko yana fadin hjy ku shigo daga ciki ku ga halin da yake ciki numfashin yanzu ya sauko daidai.
A lokaci daya suka mike don shiga dakin inda suka samu hjy jummai tsaye a kanshi tana kallon yanayin da yake ciki din.
Tsayawa sukayi sun kura mai ido kafin mamu ta sauke ajiyan zuciya tace Allah ya sauwaka yasa ciwo kafarra ne.
Mazan da hjy maryam da mama hadiye suka amsa mata da Amin lokaci guda hjy dai tankar bata san dasu a dakin ba ta nuna.
London a nan hakurina kullun karuwa yake duk abinda yaya zai mun ina kokari shanyewa a raina ban fasa yi masa biyayyan da nake masa a kulun gashi yanzu duk kwana biyu yakan kasance a gidan tare dani duk da ba wani mu,amula a tsakanin mu hakan yasa na dan samu sakewa sosai yanzu.
Mun shiga weekend hakan yasa washe gari ban fita zuwa ko ina ba gyaran gida nayi kamar yadda na saba yi din idan weekend yazo.
Sam ban sa rai da zuwan shi gidaba a ranan don ban ma saka shi a ido ba tsawon kwanaki ke nan.
Kwatsam ya fado min gidan kallon yanayin shi kawai da nayi nasan baya cikin hayacin shi a lokacin saidai halin sa sai ka fahunce shi zaka gane hakan.
Ina mai sannu da zuwa ya amsa da yawa yana zama saman kujera dan nisa dani kadan ya samu yakai zaune.
Kamar yadda anty ta fada min idan ya share ni in kula shi tunda halin sa ne kusan hakan.
Mikewa nayi na dauko mai abin sha na kawo mai gaban shi na aje na koma inda na tashi ina dan satan kallon shi.
Kallon inda yake zaune nayi na dan kura mai idanu cikin daurewa karo na farko zan gwada shawaran anty farida a fili nace.
Yaya me yake faruwa da kaine ne na ganka a cikin wani yanayi na damuwa yau din ?
Yayi firgigit ya dawo cikin yanayin shi tare da dago kai ya dan kalleni kafin ya dauki lemon da na aje mai yana tsiyayawa kadan.
Haka ina kallon shi ya dan kurba kadan jiki babu kwari ya aje cup din saman table ya maida kanshi saman kujera tare da lumshe idanuwan shi gami da dafe goshin.
Na mike kamar yadda tace in daina jin tsoron shi in dinga fuskantar shi kai tsaye kada in nuna darin shi ko tsoro idan zanyi magana dashi nace.
Yaya ka fada min may ya samay ka ko da wani taimakon da zan iyayi sai inyi maka don Allah yaya kada kace zaka boye min damuwan ka ni kamar yar kace ko kanwaka ta jini a nan.
Hannun shi daya dafe goshin shi ya cire daga jikin shi yana kallona sai kawai naga ya dan zamo yana dan kallona a cikin mamakin kalamina.
Sai da ya kaea dubana da kyau sai ya tsunci kanshi da bani amsa kai tsaye a lokacin don ba wanda zai amayarwa zuciyan shi yadda yake ji din.
Fatima ina cikin tashin hankali sosai tun jiya da aka bugo min waya daddy baida lafiya kwana uku ke nan bai farfado ba.
Gaba daya na mayar da kallona gare shi cikin damuwa da tashin hankalin abindaya furta a lokacin.
Nace ya umar wai kawuna kake nufin baida lafiya har hakan yace tun jiya Aliyu ya bugo min waya yana sheda min nayi kokarin yau din nan in wuce zuwa Nigeria sai dai hakan bai samu ba gareni.
Bai farga da halin da nake ciki ba a lokacin sai daga baya ya kula da yanayin dana shiga a rude ya tashi zuwa kujeran danake zaune ya fara jijigani a hankali.
A rude yake kiran sunana yana son tabani yana jin shakku yi hakan gareni.
Ba yadda ya iya ya dagoni dole badon yaso ba ya fara jijigani a hankali kafin ya juya inda ruwa dana aje mai ya dan debo yana yayafa min.
A jiya zuciya na sauke a hankali tare da kokarin bude idanuwana a hankali na sauke a gare shi.
Yace ke fatima da dan karfi nace yaya idan kawu ya mutu na shiga uku a duniyan nan kawu da mamu sai Ammane kadai masu sosai a kano sai ko kakata data haifi mahaifina manjo da take misau zaune a yanzu cikin halin rashin lafiya ko yaushe.
Ido ya zuba min yadda nake magana kamar wata wacce bata cikin hankalin ta zama yayi gefen kujeran da nake zaune a kai yakai hannun shi a hankali ya rike hannayena yana fadin.
Waya fada maki kawun ki zai mutu a yanzu attack kawai ya samu karancin kayan aiki na kasan mu shine dalilin da yasa nake son zuwa a san yadda za ayi muzo dashi nan a dubashi.
Din haka ki kwantar da hankalin ki kefa kika ce in fada maki zaki iya taimaka min baki taimaka mi din ba kuma kina kokarin ki kara sakani cikin wani tashin hankali yanzu bayan wanda ke gaba a yanzu ?
Yaya kayi hakkuri na daina daga ma hankali don Allah ka samowa kawuna lafiya ban son wani abu ya samu kawu a duniyan nan na fada gwanin ban tausayi.
Kafadana ya dafa a hankali yana mikewa tare da fadun insha Allahu kawun ki zai samu lafiya very soon ya fada ya fara tafiya a kasalance.
Yaya yaushe zakaje can din nima in shirya mu tafi na fada kamar wata yar karamar yarinyar da bata da wayau.
Dan juyowa yayi ya kalleni da mamaki kamar na isheshi a lokacin da surutu yace karatun naki yaya zakiyi dashi .
Bayan hakan ai nan zamu dawo tare dashi a duba lafiyan jikin shi idan mun tafi dake wa zai tare mu a nan ya fada yana tsureni da ido.
Sai kuma ya juya ya fara tafiya bayan yaga na dukar da kaina a kasa kamar ina tunane lokacin.
Har ya shiga dakin shi yana tunanen wani itin so da shakuwane haka tsakanin mu da daddy su don yanzu ya fahinci yadda shima daddy yake ji da al,amarin nawa a ranshi duk da yana boyewa don sauran iyalin shi.
Shiga yayi ya zauna a bakin gadon shi tare da hade hannayen shi guri daya ya sauke kanshi kasa yana tunane.
A gaskiya yayi kuskuren rike wanan yarinyar da kowa ke nanata mai ya rike amana marainiyar Allah a kasan mutane.
Yasan dole yayi hakan don kare mutuncin shi da lafiyan shi saidai kuma yasan rabuwa da fatima kamar yadda ya shirya zaiyi .
Hakan zaiyi matukar yin nadaman hakan mara adadi a rayuwan shi dolene yayi hakkuri da zabin mahaifin shi a gareshi.
Don a yadda ya fahinci yarinyar tana da saukin kai gara yabita a sannu yana kwantar mata da hankali tunda tana mashi biyayya yadda yake so.
Amma sai ya biyewa zugan shedan wanda haksn ke nufin bijerawa mahaifin shi a rayuwa yayi ke nan.
A yanzu zai yaki zuciyar shi akan zama da wanan yarinyar ko a hakan da yake mata sai dai zai rage daure mata fuska da takuran da yakeyi din ya bata freedom din ta a matsayin tana yar adam dayasan yana tauye mata.
Sai dai merry ce matsalan shi yanzu don sanin dokar kasan nan daman shi ma da yake suna zaune a central London inda kowa ke iya yin al,adun shi a nan kai tsaye don da dama sosai sama da American.
Yasan zasu kwasa da merry duk ranan da ta fahinci fatima matar shi ce ta aure matar da iyayyen shi suka zaba mashi ya aura a rayuwan shi.
Kwance yakai yana sauke ajiyan zuciya a hankali yana ci gaba da tunane tare da shirya abubuwa da dama a ranshi.
Wayan shine yai kara ya dauka Steven ne abokin shi yake fada mai an gama komai na tafiyan shi a cikin daren nan zasu tashi.
Bayan gama wayan ne ya mike ya shiga bandaki ruwa ya watsa a jikin shi tare da dauro alwala ya fito ya tayar da sallah ya jima a gurin yanawa mahaifin shi addua kafin ya mike ya shirya duk abinda zaiyi tafiya dashi don merry bata kasan tana can American ya barta a can gurin aikin ta.
Sai yamma lis ya fito ya samu har na hada abinci nayi mamakin ganin shi yau yana magana dani tun kan ya sauko kasa yace yar gidan kawu har yanzu tunanen kawun kike ko ?
Ina zaune nayi tagumi da hannayena kafauwana suna saman kujeran na takure a wurin daya tare da zubawa kasan falon ido.
Yace shike nan yau dai nayi maki Aprilfull don na ga yadda kike son kawun ki da mamaki a fuskana na dago kai ina kallo shi yadda yake magana kamar bashi ba yau.
A dan maraice nace yaya dama wasa kake min don Allah kasani a wani hali da ban taba shiga ba a rayuwata ?
Yaya bana son in rasa kawu yanzu kamar yadda na rasa mahaifina a baya tun ina karama bai more min ba shine nake tunanen yanzu idan na rasa kawu fa ?
Ba zaki rasa kawun ki ba Fatima ya fada yana jawo kujera ya zauna naso ma in kira maki shi sai dai nasan zaki iya fada mai gwada kin da nayi yai min fadan hakan.
Ba zan fadawa kowa tsakanina da kaiba yaya ka yarda dani mamu ta haneni da yayin hakan tace in zama mai boye sirin tsakanin mu.
Kallin wata yar karamar baby yake min mara wayau ga yadda nake fadin magana abincin ya fara budewa yayin da nake sake ajiyan zuciya daga inda nake zaune din.
Bai kara magana ba ya gama ya fita ina zaune mamaki ya cika min ciki wai yau ni yaya kewa April full a gidan nan in dai hakane yako kamani da kyau sosai don na shiga wani hali a lokacin.
Ya dan jima bai shigo ba da zai dawo ne sai gashi da kayayakin abinci dans sha kala kala ana shigo min dasu gidan ina dakina lokacin don haka har yagama jida ya kai min store dina ban san hakan ba.
Bayan isha,i ya leko dakina yana fadin in rufe gida zai tafi can gidan ya kwana yana da aikin da zaiyi a can din sai da safe nayi mai ya tafi ya barni da mamakin sauyawan shi a raina.
Ashe Steven yazo ya dauke shi tafiyan ke nan Nageria yayi ban sani ba nikan yana fita na rufo gidan tare da kashe komai na kwanta sai safe.
Da safe koda na tashi ban tsaya komai ba shirin fita nayi do har lokacin ina ji zuciyata babu dadi daga wasan ciwo kawn da yayi min din .
Duk da ya kamata inji dadi hakan ganin sakin fuska harda wasa irin na al,adan nasara da yai min a karo na farko do har lokacin kaina bai kawo wuta ba in gane cewa watan April ya wuce ai tun lokacin bukin su merry .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button