NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Azumi saura kwana daya a cikin dare na tashi da ma tsakaicin ciwon mara mai zafi da zogi a hankali na fara nishi ina dan bugun gado a hankali don kada in tayar dashi daga barcin don bai gama susucewa ba a kaina barci ya dan dauke shi lokacin.

A firgice ya tashi yana fadin subbahanallahi zahrah lafiya meya samay ki kuma ?
Da kyat na buda baki ina fadin wayyo yaya marata kamar zai fashe min yaya nake ji gaba daya ya rude yana min sannu.
Ya sauka daga saman gadon da sauri yana fadin barin kira Yusuf muje asibiti ga gajiyan da ya kwaso don tun daya dawo garin bai zama a gida sai dare yake dawowa tun safe idan ya fita.
Hakan ya fita da waya a hannun shi zuwa waje sai ga Anty Ramla hankali tashe tana fadin subbahanallahi zarah ko haihuwan ne yazo ?
Banda bakin bata amsa a lokacin don yadda nakeji tunda nake duniya ban taba jin wanan yanayin ba a rayuwana.
Da taimakon ta na samu na shirya muka tafi asibiti inda ba bata lokaci suka karbe ni zuwa matenity din su aka fara dubani.
Sunyi zaton zan iya haihuwa da kaina don haka suka taimaka min da dan abinda zai rage min pain kawai a lokacin .
Saidai kamar basu min komai ba a yadda nakeji lokacin wuya matuka na shashi tun ukun dare har zuwa safiya abu bai lafa mun ba.
Yaya da kanshi yaga likitan yace su cire min baby din kawai zaifi don wahalan yayi min yawa.
Basuki ta nasa ba don suma suna gab da bashi wanan shawaran don a wurin su suna ganin nayi kankanta da haihuwa shiyasa nake wanan wahalan haka.
Lokacin da za a shiga dakin tiyatan hankalin shi idan yai dubu ya tashi yayi tunane kala kala a lokacin gashi bai fadawa kowa zancen cikin jikina ba balle yanzu ya kirasu yace ga halin da nake ciki .
Hakana ya fawwala ma Allah yabar komai daga shi sai Yusuf da Anty Ramla ke zirga zurga a wurin babu kowa nawa da zai tsaya mai.
Karfe hudu daidai na yamma sukai nasaran fitar da abin cikin nawa wanda hikiman su ya bace basiran su ya shige basu gane diya biyune a cikin nawa ba don tun farko yaya yaki yarda da binciken da suke yi na sanin abindake cikin mace lokacin.
Diya biyu ne maza suka fitar daga jikina sai mamaki da farin ciki suke a fili kamar sune akaiwa haihuwan .
Mamaki ko fari cikine ya hana yaya ya aiwatar da komai lokacin da nurse din suka fito da murna suna sheda masu .
Saida komai ya kammala aka kirasu suga yaran suna da kama sosai da junan su kamar har ya fi na yan biyun mamu.
Ban san komai ba don wuyan dana sha sai dana farfado yaya da Ramla suka shigo min da yaran a hannun su.
Zahrah ya kira sunana na bude ido da sukai min nauyi da kyat na dan kallesu anty Ramla tace ki bude ido zarah kiga kyautar da Allah yai maku keda mijin ki.
Dan murmushi kadan na sake a fuskana a galabaice nace nagode na kara rufe idanuwan nawa har lokacin ban cikin hayacina sosai.
Har lokacin hankalin yaya bai kwanta ba yana ganin kamar wani abu zai samu rayuwanane shiyasa ya kasa gane farin ciki yake na samun karuwan ko tashin hankalin rashin lafiyana.
A daidai wanan lokacin da suka fito daga dakin da nake kwance ne sun mayar da yaran a dakin da suke wayan shi yai kara ya dauko daga cikin aljihun shi yana dubawa.
Mama ya furta a fili yasan bata kiran shi sai idan ya kirata koshi sai idan taga dama take dauka ba wani magana mai dadi kuma zasuyi har su gama wayan.
Saidai duk karshen wata wanan ka,idane zai tura mata dari biyun nan bayan haka tana iya mai korafi kafin karshen wata zata iya mai text tana bukatan fiye da hakan ya tura mata.
Mama kece a wanan lokacin yace lokacin daya daga wayan .
Nice ko na yanke ma jin dadin kane na takurama da kira a wanan lokacin yace haba dai mama jin dadi yafi naji muryan ki a kowani lokaci.
Kawai dai gani nayi yanzu ma a wurin ku darene sosai yasa na fadi haka mama da fatan dai kuna lafiya.
Ni zaka mayar yarinya babawo ka daukarwa kanka fitinan da kake son yafi karfin mu nan gaba na fada ma ga yadda zakayi kaki kayi .
Zaka dauko min fitina ka jefa min cikin zuri,ata daga baya tazo ta buwayemu gidan ga baki daya.
Barci nake yanzu nai mafalki da wanan yar banzan yarinyar ta wurinka a yanayin da naganeta tana kokarin ta bunkasa tafi kowa a gidan nan ga baki daya.
Cikin natsuwa ya tambayeta tafi kowa kamar yaya mama tace kwarai kuwa don ba zan taba yarda yarinyar ta zo ta zarta yaran mu ba.
Yayi maza yace mama wanan kuma ai abune na Allah idan haka Allah ya nufa babu mai hana hakan ya faru ga bawa.
Rufa min baki mara hankali wanan shedaniyar yarinyar inayi kamar bana yi sai kudi nake narkawa a kanta amma abu yaki jada baya kasan irin kuskuren da kake shirin muna kuwa.
Idan har yarinyar ta gama karatunta ta dawo muna kasan nan kasan yadda diyan mu zasu koma a bayanta nan gaba.
Mama ki daina fadin hakan da ita dasu dukka Allah ne yayi su shi kuma yasan rayuwan da ya zanawa kowa a cikin su.
Kai wanan kafiran matar taka tafi mun wanan yarinyar a gurina kasani ban kaunar wanan yarinyar da kai har abada inma shirin mayar da ita mata kakeyi kamar yadda ubannin ka suka bukata.
Ta kashe wayan ta barshi da mamaki a zuciyar shi yana bin wayan dake hannun shi da kallo.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:29 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR,RAHAMANIN RAHIM, , , , ,

Mama mama da kin san halinda nake ciki a yanzu da baki fadi haka kan yar mutane ba da kinsan Zahra ta haifa maki jikoki har guda biyu a yau godiya ya kamata ki mata.
Wanan wace irin rayuwace da da kiyayya haka mama da har zaki zabi merry fiye da zahra a rayuwan ki.
Wani hali mama kike son jefani ciki a yau din nan yarinya tana kwance bata san inda take ba kike furta wanan kalamin haka gare ta.
Shi a ganin shi ai kamata yayi duk wani abu da mama keji game da zahra yanzu ace ta aje wanan abin wanan masifa da may yai kama hakane ?
Yana zaune ya hade hannayen da gwiwan hannun shi yayi tagumi da hannayen shi biyu a ciki damuwa daidai lokacin Oga Yusuf da Ramla suka karaso inda yake zaune.
Man lafiya na ganka a haka ko wani abin ya samu zahra ko yaran ne kuma da sauri Ramla tace ba abinda ya samesu don bamu dade da fitowa gurin su ba.
Mai yuyuwa wayan da aka bugo maine daga gida dazun ya sakashi tunane dai.
Da kyat ya dago kai ya kalli Yusuf din da idanuwan shi da suka kade sukai mashi ja yadan yi murmushin takaici ya furzo iska.
Dan wayancewa yayi ya basar da abinda suke fadi yace ina tausayawa yarinyar nan ne ga halin da take ciki a yanzu.
Ya dace ace akwai wani na gida a tare da ita a daidai wanan lokacin da zata gani taji sanyi a rayuwan ta sai dai ban shirya hakan ba tun farko don wasu dalilai na na daban.
Ka kwantar da hankalin ka mana muna tare da ku ai ko abinda muke maku bai gamsheka banr kake wanan magana.
Dan kallon shi yayi yayi murmushin dole a fuskanshi Ramla ta tare da fadin na fahinci abinda yake tunane haihuwa yafi danan baban Amar.
Ko wace mace take cikin wanan halin zata so ace wani nata yana tare da ita a wanan lokacin yarinyar tasha wahala sosai gaskiya idan kunyi duba ga shekarunta a yanzu.
Wanan ba komai bane nake gani fatan mu a yanzu Allah ya bata lafiya shine abin roko a wurin Allah ka kwantar da hankalin ka ko wace mace da irin yadda take haihuwan ta.
Ya dafa kafadan umar din yana fadin be a man with a strong hart haka maza suke daurewa hakan da kakeyi sai ka sare mata gwiwa kuma.
Kallon Yusuf yayi yana girgiza kai a ranshi yana fadin da kasan halin da nake ciki yusuf da baka fadi haka ba a yanzu.

Mamu ta tashi hankali a tashe don yawan mafalkin da takeyi dani kwanakin tayi neman layin wayana tun safe layin baya shiga.
Tana jin nauyi da kunyan kiran ya Umar ta tambayeshi ni don tana ganin idan tayi haka kamar bata gode mashi bane.
Abin yaki fita mata a rai duk yinin ranan tana cikin damuwa saukin ta ba itace da girki ba a ranan don hakane ta bayan yara sun tafi islamiya ta koma wurin Amma.
Tun shiganta falon yanayin ta ya nuna tana cikin damuwa don hiran da mama ke masu mamu bata kada bakin ta ba a cikin zancen su.
Lafiya kike yau yar gwaggo mama hadiye take tambayan mamu cikin yanayin mayar da kallon ta gareta .
Nisawa mamu tayi kafin tace yau dai gani nan dai tun dare nai mafalki da wanan yarinyar hankalina yake tashe.
Na kira layin ta yafi a kirga baya shiga haryanzu da sauri Amma tace cikin sauri kinyi sadaka akan mafalkin ?.
Yanzu da yara zasu islamiya na basu abin sadaka a rabawa yara idan sunje.
Ubangiji Allah ya karba tace suka amsa da Amin mama tace in kaji shuru lafiya ke nan ai da mijin yakira idan da matsala.
Shiru mamu tayi batai magana ba har lokacin hankalin ta yana a tashe din tana ganin wani abu yana faruwa dani a yanayin data ganni cikin mafalki.
Tashi mama tayi don girki takeyi a lokacin Amma ta kalli mamu tace kwanakin baya nayi irin wanan mumunan mafalkin da su ban fada ba kada hankali ya tashi.
Nayi ta yawaita sadaka a garesu har abin yazo ya fita mun a raina na kama harkokina don haka ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu komai sai alheri.
Sun dan dade da gwaggon nata suna hira kafin ta koma part din ta yayi daidai da yara sun dawo daga islamiya hakan yasa hankalin ta ya dan dauke garesu.
Goma na dare har ta rufe part din ta tana shirin kwaciya wayanta yai kara ta dauka da sauri ganin bakon layi na kasan waje yasa jikkin ta na rawa tai received din called din.
Sallamu alaikum ya fada a lokacin ta sheda muryan mai kiran nata da sauri ta karba mai suka fara gaisuwa tare da tambayan shi muna lafiya.
Yace to Alhamdullahi saidai da sauki idan babu damu naso muyi maganan siri dake don ina cikin damuwa a nan.
Da sauri mamu tace subbahanallahi may ke faruwa dakune yace da fatan ke kadaice a wurin a wanan lokacin tace ni dayace umar ina dakina har mun rufe.
Sai yayi ajiyan zuciya sai kuma yai dan shiru kafin yace watau dama naso in sheda maki cewa da farko dai ki gafarce ni na rashin fada maku da banyi ba da wuri.
Wani abu ya faru da matar takace ta fada a razane yace eh saidai ba wani abin tashin hankali bane sosai .
Ina son ki fahince ni nasan zaki gane may nake nufi ga bayanina watau zarah ta sauka a yammacin jiya din nan.
Ciki ke gareta dama bamu sani ba yace eh ban fada bane na kuma hana ta fadawa kowa a gida don tsoron lafiyan ta da kwanciyar hankalin mu ga baki damu daku.
Kin dai san komai gamay da maganan auren nan namu wanda tun farko har wanan lokacin ina cikin barazanan kan wanan maganan.
Na sani Faruq kamar yadda take kiran shi tun farko Allah yasa hajiya ta gane gaskiya yace Amin.
Saidai haihuwan yazo mata da matsala don sai da akai mata CS don tasha wuya sosai kafin ta haihu yara suna nan maza biyu Allah ya bamu.
Masha Allahu ubangiji ya raya muna su akan sunna yasa masu albarka yaji dadin wanan addu,an har yana rayawa a ranshi dama ace tashi mahaifiyar ce ke mashi wanan adduan ga zurian shi haka.
Yace yanzu ina gida tana asibiti da da zan bata waya ku gaisa sai dai nayi iya tunane nan akan wace zaki samo muna ta zauna da ita a cikin karshin kasa ba tare da kowa ya san da hakan ba ta wurin Nasir abokina zai gudanar da komai gamay da wace za a turo muna din.
Zan bincika in gani wace ya dace in turo maku raino sai idan an hada da wace tasan kai Allah ya bata lafiya ya raya muna su.
Ya sake fadin amin tare da fadin zai kira yaji shawaran data yanke sai dai yana rokon ta da ta bar zancen kamar yadda ya barshi a rufe har zuwa lokacin da kowa zai sani.
Sukai sallama tana mashi godiya yace ba komai ta dai tayamu da addua ya kashe wayan.
Iska ya furzar daga bakin shi yana sauke ajiyan zuciya yayin da mamu ta bangaren ta ranan ta kasa barci ta kwana nafila da safe ta aika da sadaka makaratuni da duk inda ya kamata akai sadaka.
Duk da Amma tana cikin kwantar wa mamu da hankali saidai bata yarda ta fadawa kowa zancen ba kamar yadda ya roketa kada ta fadi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button